Free chapter 路 Read without an account
Chapter 25-26
by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...
馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮
Story & writing
By
Mrs Muttala (Amanar cool)
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Sadaukarwa ne ga Aysharcool
Free book鉁嶏笍
Page 25&26
__________Abba gudu yake sosai kamar zai tashi sama, ko gaban shi baya gani, cikin ikon Allah ya isa asibitin lafiya, ko da ya isa a lokacin Ammi ba ta ko iya 蓷aga hannunta, da sauri aka shiga ciki da ita domin bata taimakon gaggawa.
Mami ta na shiga 蓷akinta, ta saki dariyar mugunta, cikin murna da farin ciki ta fara taka rawa, sai da tayi mai isarta, sannan ta ce "Shegiya tsinanniyya, ki ka ce asiri baya kama ki, ni na san sai idan baki ha蓷u da shegun ba, sai na ga ta yanda za ki 蓷auki ciki a gidan nan, yanda ban haifa ba, haka kema baki isa ki haifa ba, da dai 茩addara ta sanya kin haifa tun kafin na zo gidan, to ba yanda zan yi, amma yanzu dai baki isa ba wallahi, ko da na haifa ni, ba zanta蓳a bari ke ki haifa ba".
Shiryawa tayi ta fito, a tare suka fita harabar gidan, Mudan ya bu蓷e mata mota ta shiga, sannan ya ja suka bar gidan.
Abba ya kasa zama, ya kasa tsayi, sai safa da marwa yake yi, addu'a yake Allah yasa cikin bai fita ba, ji yake kamar ya shiga 蓷akin ya ga halin da take ciki. A 蓷akin kuwa da 茩yar likitoci suka samu jinin ya tsaya, duk wani gwaji da yakamata su yi sun yi, sai dai ba suga abin da ya haifar da wannan matsalar ba. Sai dai cikin ikon Allah cikin bai fita duka ba, alluran bacci aka yi mata domin ta samu hutu, Abba na ganin fitowar 蓷aya daga cikin likitocin da sauri ya isa gurin shi, yana tambayar shi wane hali take ciki, umarni ya ba shi da ya biyo shi, officer. Bayan shi Abba ya bi.
Bayan sun zauna likitan ya dubi Abba ya ce "Alhaji duk wani gwaji da zamu yi mun yi, amma bamu ga abin da ya haifar da wannan matsalar ba, amma Alhamdulillah mun yi nasarar tsayar da jinin, kuma wani ikon Allah cikin bai fita duka ba. Zamu bata maganin da zata yi amfani da shi, in sha Allah cikin zai yi, sai dai zai rage yawan kwanakin sa".
Tun da Abba ya ji cewar cikin bai fita ba, yake godiya ga Allah, cikin farin ciki ya ce "Likita na yi matu茩ar farin ciki da jin cewar cikin bai fita ba, amma to wane hali take ciki?" "Ta na nan mun yi mata alluran bacci domin ta samu isashen bacci, saboda ta wahala sosai, yanzu bari na rubuta maka magungunan da za a siyo ta na tashi zata fara amfani da su". Kar蓳ar takardar ya yi, ya 茩ara yi wa likitan godiya ya fita. Yana fitowa ya ga su Mami sun shigo, da sauri ta 茩araso gurinsa ta na fa蓷in "Alhaji lafiya? meyafaru ne? Mudan ya ce mini ya ga ka fito da Zainab a hannu ka sakata a mota, kun bar gidan, da jin hanka na san ba lafiya ba, shine hankalina ya kasa kwanciya, na ce ya kawo ni asibiti na gani ko nan ku ka zo".
Abba ya ce "瞥ar uwarki ce ba lafiya, haka kawai ta fara bleeding".
"Subhanallah! Alhaji ina fatan dai cikin bai fita ba?". Kamar wanda a ka kullewa baki ya ce "Yanzu dai ba abin da take bu茩ata sai addu'a, da fatan Allah ya bata lafiya ". Cikin iya 茩warewa a munafunci Mami ta fara matsar 茩walla, ta na fa蓷in "Zainab Allah ya yaye miki wannan matsalar, a ce da mutum ya samu ciki sai ya zubi, kai Allah ya yi mana maganin wannan masifar".
Ha茩uri Abba ya bata, sannan ya mi茩awa Mudan takardar maganin ya ce ya je ya siyo magungunan, kar蓳a ya yi ya fita, wata likitace ta kuma fitowa daga 蓷akin da Ammi take. Tambayarta Abba ya yi ko za su iya shiga su ganta? ta ce "Za su iya ganinta, sai dai ta samu yin bacci, suyi a hankali kar ta farka, ana son ta samu isashen bacci".
Ko da suka shiga ta na kwance, fuskar nan tayi fayau, kallonta Mami tayi, tana addu'a kar Allah ya tashe ta, tana fatan daga nan sai kushewarta. Babu 蓳ata lokaci Mudan ya dawo da magungunan, kar蓳a Abba ya yi, tare da sa masa albarka. Sannu da jiki Mudan ya yi mata. Sun da蓷e zaune a 蓷akin, sannan Mami ta ce "Alhaji ya kamata ka je gida ka yi wanka, ka ci abinci, in ya so ni sai na zauna da ita kafin ka dawo, gudun kar ta farka ba kowa a kusa". "Saratu ba zan iya tafiya ko ina ba, sai na ga yanda yanayin jikinta ya yi, ki dai koma gidan ki ha蓷a mini abinci, ki ba wa Mudan ya kawo mini, ki ha蓷o masa da kayana ina so zan yi wankan a nan". Ba dan ranta ya so ba, haka ta ha茩ura, ta so ya je gida domin ta ida nufinta akan Ammi, amma sai ta ce "To Alhaji hakan ma ya yi, bari mu wuce, Allah ya bata lafiya". Da Amin ya amsa, sannan suka bar 蓷akin.
***********
Bayan an tashi su Maryam daga makaranta, bakin titi suka fito domin neman abin hawa, wata mota ce ta zo, har ta wuce sai kuma ta dawo baya, dai-dai gurin su ta tsaya, duban motar suke yi, suna tunanin me ya tsayar da ita gurin su, sauke gilas 蓷in motar aka yi, Sharifa ce, ta na murshishi ta ce "Sisters sannunku" Feena ta ce "Yawwa sannu" Maryam shiru tayi bata ce 茩ala ba, Sharifa ta kuma cewa "Ina fatan dai kun gane ni? sannan idan ba damuwa ku zo na rage muku hanya, na ga kamar abin hawar zai yi wuyar samu a nan 蓷in, ga rana ana yi sosai".
Caraf Maryam ta ce "Bama bu茩ata, ki yi tafiyar ki". Feena ta ce "Haba Maryam me ye haka? wallahi Allah idan muka tsaya a gurin nan wahala zamu sha". "Da蓷ina da ke Fenna gidadanci, shikenan bamu santa ba, bamu ta蓳a ganinta ba, bamu san daga inda ta fito ba, sai ta ce muzo ta rage mana hanya, muku ma gamu kwa蓷ayayyu sai muje".
"Wallahi Allah Maryam na san kin gane ta, ita ce fa budurwar da muka ta蓳a ha蓷uwa da ita a napep 蓷in nan" . "To dan mun ha蓷u da ita a napep kin san daga ina ta fito?" . Sharifa kallon ikon Allah take yi, duk da ta san Maryam 蓷in na da gaskiya, nan ta ji yarinyar ta 茩ara shiga ranta, "Haba 拼ar uwa ki na tunanin zan cutar daku ne? dube ni ki ga na yi kama da masu cutar da mutane?". "Shi mugu ya na da kama ne? ai ba a gane shi ta fuska, kin ga mun gode ki yi tafiyar ki kawai".
An kai ruwa rana kafin Maryam ta yarda, suka shiga motar, Sharifa da Feena ce a gaba, Maryam na baya, Feena aka fara saukewa, Maryam cewa tayi a sauke ta a nan, amma Sharifa ta 茩i sai da kaita har 茩ofar gida, fitowa Maryam tayi, ta ce "Muna godiya" ita ma Sharifa fitowa tayi, tana 茩o茩arin shigewa gidan ne, ta ji "Sharifa ta ce "茦awata tsaya mini na shiga mu gaisa da su Mama". Da har zata yi magana sai kuma tayi shiru.
Tare suka shiga gidan, ko da suka isa Mama na zaune, Afnan kuma na 蓷aki, har 茩asa Sharifa ta du茩a ta ce "Mama barka da rana ya gida?" "Lafiya 茩alau Alhamdulillah, Maryam wannan kuma wacece?" "Wata ce da muka ta蓳a ha蓷uwa da ita a napep, shine yanzu ta ganmu a bakin titi bamu samu abin hawa ba ta rage mana hanya" . "Ta ko kyauta, sannunki da 茩o茩ari, Allah ya yi albarka, tashi daga du茩en zo ki zauna ga shimfi蓷a, ke Maryam kawo mata ruwa tasha". Tashi tayi hau tabarma ta zauna.
Ruwan ta 蓷ebo mata, babu 茩yan茩yamin komai Sharifa ta kar蓳a tasha, sannan ta ce "To Mama zan wuce ina sauri ne, amma in sha Allah zan samu lokaci na kawo muku ziyara". "To shikenan, Allah ya kaimu muna godiya, Allah ya bar zumunci" tana 茩o茩arin mi茩ewa tsaye Afnan ta fito daga 蓷aki, da idanuwa Sharifa ke bin ta da kallo ko 茩iftawa ba ta yi. Afnan ta ce "Mama ba茩uwa muka yi ne?" "Eh tare da Maryam ta zo, ta rage musu hanya ne".
Sharifa ta ce wa Afnan "ina wuni"
"Lafiya 茩alau ya kike?"
"Alhamdulillah"
Daga haka ta yi wa Mama sallama, har zata fita sake juyowa ta kalli Maryam ta ce "茦awata ko rakiya ba zan samu ba?". Tayi maganar ta na murshishi. Mama ta ce "Aikuwa dai, wannan 茩awar taki sai a hankali, sai dai kuma har zaki tafi ban san sunan 拼ar tawa ba". murmushi tayi ta ce "Sunana Sharifa". "Ma sha Allah Sharifa Allah ya yi albarka, a gaida gida". 茦ara duban Afnan tayi sannan ta juya, Maryam ta mara mata baya, har wajan mota ta tarakata ta ce "Na gode sosai, ki yi ha茩uri da abin da ya faru 蓷azu, kin san wasu yaran masu ku蓷i akwai su da jiji da kai da raina mutane, ni kuma ba na son wula茩anci, shi ya sa ki ka ga na yi hakan".
"Babu komai Maryam ai ki na da gaskiya, ina fatan dai zamu 茩ulla 茩awance dake?" "In sha Allah, ai na ga kina da kirki". "To ya yi ina godiya da amsa tayi na da aka yi sai na sake dawowa, yawwa Maryam wannan da na gani Auntynki ce?" "Eh ita na ke bi" "Ayya Allah Sarki, da alama dai tana da kirki" dariya Maryam tayi ta ce "Ai na fita kirki". "Ba shakka ni shaida ce ai". Shiga motar tayi ta na 蓷agawa Maryam hannu, ta ja ta bar gurin, ita kuma ta koma ciki.
*******
Mudan ya kawo wa Abba abinci da wasu kayan sakawa, wanka ya yi, ya ci abinci, sannan ya je ya yi sallan azahar, Mami ba ta farka ba sai misalin 茩arfe hu蓷u da rabi, da 茩yar ta iya bu蓷e idanunta, Abba sai jera mata sannu yake, a hankali ta yun茩ara zata tashi Abba ya taimaka mata, ta tashi ya rakata 蓳an蓷aki ta gyara jikinta, ta fito abinci ya zuba mata ya na bata a baki, bayan ta gama ci ya bata magungunanta ta sha, likita ne ya yi shigo, ya ganta a zaune, ya ce "Ashe ta farka kenan". Abba ya ce "Eh ta gata nan har ta ci abinci ta sha maganinta". "To ma sha Allah, ya ki ke jin jikin na ki da sau茩i?".
"Da sau茩i"
"Alhamdulillah, ina ga Alhaji zamu sallame ku, sai ta kiyaye shan maganinta akan lokaci, sannan kuma ta kiyaye yin wani dogon motsi saboda yanayin da ta ke ciki, ba a bu茩atar tayi dogon motsi". Abba ya ce "In sha Allah za a kiyaye" . Sallama ya basu, tare da yi musu fatan Alkhairi, godiya sosai Abba ya yi masa sannan suka bar asibitin.
Mami na zaune ta na 茩arewa Huda kallo, gaba 蓷aya yanayinta ya sauya, sannan ga wannan sabon iskanci da ta tsiro da shi na rashin zama cikin mutane. Ta na 茩o茩arin yin magana ne ta ji alamun bu蓷in get, tashi tayi ta li茩a ta taga, tsaki tayi ganin su Abba ne, da har zata zauna sai kuma ta bu蓷e 茩ofa ta fita.
Amanar cool ce 鉁嶏笍
***