Free chapter · Read without an account
5
by Ramlat Abdulrahman Manga · Kishi..... A tsakanin zubda jini!
HAKKIN MALLAKATA
#tue-Aug-2021
KISHI..!!
~_A Tsakanin Zubda Jini🩸_~
Mai_Dambu
*Sadaukarwa ga Halimatu kangiwa (haliloss). Mrs J Moon. A'isha Fareedah Ya'u Nusaiba Sulaiman Ayuba jikalle na*
*5*
_Wannan Littafin mallakina ne!_
Free Page.
Daga
JARUMAR BOROROJI.
Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda.
Lokacin da ya farka ya kalli kafar shi a yanke, wani irin hakuri ne ya shiga ranshi, tare da share wasu tears din da suke zuba, uwar gidan shi mai suna Hajiya Tahirah share kwalla tayi cikin kuka tace mishi.
"Alhaji ka hakura da siyasar nan! Tun yanzun ka fara rasa wani muhimman sassan jikin ka, ina kuma alamarin ya ta'azzara, don Allah ka duba shekarun ka, ka bar siyasan nan haka."
Murmushi yayi sannan ya dauki madubin shi ya saka, kafin ya juya ya kalli babbar Yar shi yace mata.
"Kin tab'a ganin zaki ya gudu a dawa? Ko kin tab'a tsinkayo wanda ya gujewa mutuwar shi." Yaja wata irin iska, kafin ya fesar sannan ya kalle ta, yace mata.
"Yanzun aka fara, domin ban ci ta zama ba. Ina da goyan bayan al'umma kuma suna mara min baya taya zan yi gudun hijira? Idan mutuwa bibiyata take Tabbas ni ba zan guje mata ba, zan cigaba da bin sawunta dan haka kar na kuma jin maganar ki a cikin al'amarin siyasa ta."
Ganin yadda ya zafaffa al'amarin sai ta zuba mishi ido, domin bata son tashin hankali, kuma bata son abinda zai had'a su. Jama'a da suka fahimci ya farfaɗo suka shiga zuwa duba shi ana girmama al'amarin tare da kammaba. Musamman Yan bani na iya, suka shiga ririta Al'amarin da bai kai a ce an yi tashin hankali akan shi ba, suka fara magana kan cewa.
"Dole muyi bori k'in gwamnatin PLP domin ba zamu zuba ido ana cutar da masu tsaya kare mana hakkin mu ba."
Ai kuwa suka fusata tare da amincewa za a tashi hankalin mutane.
**
"Labaran Duniya, Ke sauraro dani Rahama Ayman, a yau muka samu labarin Mai girma Gwamna ya kafa kwamitin bincike akan harin da aka kaiwa Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda, wanda yayi sanadiyar rasa kafar shi daya. Har yanzun kwamitin bata bada wani gamshashen bayani akan yadda zasu tafiyar da binciken su ba.
Shugaba kasa Abba Mai nasara ya samu lambar yabo a majalisar dinkin duniya, akan shine shugaba mafi nagarta a yankin Arewacin Afirka. Yan tadda kayar baya, sun samu damar kafa gwamnatin a kasar Balbale, Shugaba Tiriko na kasar Yuno ya rigamu gidan gaskiya, har yanzun ana samun kananun tashin hankali a yankin nahiyar fure. Mu zauna lafiya, sai arziki mai yawa ya shigo jahar mu, wannan sakon daga ofishin sakataren Gwamnatin jaha ta dauka tare da hadin gwiwar matasa masu kishin jahar mu.
Ana samun bayanin akan cewa talakawa sun shirya zanga zanga akan rasa kafar da dr Abdul Hamid Jamil Bagauda yayi. Anan zauren Zuwa da kai yafi sako muna tare da Comrade Habibu Kani karkashin jagorancin hukumar kare hakkin Dan Adam na duniya, wato human right, sai gefe na akwai brrts Sabo Bako na had'akar kungiyar Bagauda Trust Grp. Assalamu alaikum, da fatan bakin namu sun iso lafiya."
"Waalaikumin Salam, Rahama Ayman, yau gamu a cikin shirin naku na zuwa da kai yafi sako."
"Masha Allah! Zamu fara yayye kallabin shirin da Comrade Habibu Kani, shin me kake gani dangane da wannan yunkuri na talakawa kan lallai sai anyi adalci akan abinda aka yiwa Dr Bagauda? Wani kallo kakewa Gwamnati a wannan lokacin?"
"Alhamdulillahi, kin tabo inda yake min kaikayi, amma kuma ba zai hana mu magana ba, Abinda talakawa suka fito yi lallai haka shine Alkhairi, domin suna da damar fita niman hakkin su. Idan akace yau wani ya tsaya miki idan kika yi kuka shi zai budewa duniya suji kukanki, ai sai san Barka, toh an wayi gari mai tsaya miki ya koma gefe a matsayin ki na kishi da kishin sa ai dole ki fusata akan gwamnatin nan, sannan a yadda abin ya faru, kowa yasan yaran nan yan Sara suka ne, kuma suka ce lallai idan nai fito ba zasu kona ofishin jami'ayyar, wanda yake dauke da mutane babu adadi ai tashin hankalin yayi yawa, dan haka Dattijon arziki, Mutumin kirki. Ya sadaukar da rayuwar shi domin al'umma dole ran talaka ya b'aci sannan.."
"Comrade Habibu Kani, ban katse maka hanzari ba, bari muji abinda Brrst zai ce akan dokar kasa, Barister ko akwai abinda dokar kasa tace akan kundin tsarin walwalar jama'a?"
Cikin gurbatacciyar Hausar shi da bata zauna akan harshen shi ba yace.
"Toh Rahmah Ayman,a dokar jahar nan dai an bawa kowa damar ya gudanar da abinda yake so! Sannan doka bata bawa kowa daman cin zarafin wani ba, sannan suma ta ɓangaren gwamnati ya kamata su kama yaran nan su hukunta shi, domin ko jiya naga duguja da Uban zuga, idan har irin su zasu kaiwa Babban mutum mai daraja haka farmaki meye mu kuma zamu ce?
Ana gani ana ji an sare Dr Bagauda har sai da aka cire mishi kafar shi me talakawa zasu iya, fatana guda daya ne! Talakawan da zasu fito zanga zanga don Allah kar gwamnatin jaha ta cutar dasu domin suna kaunar Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda"
"Comrade Habibu Kani,shin wani tsari hukumar kare hakkin dan Adam, na karkashin kungiyar ku ta ce akan haka wai nufin akwai wani abu da za a iya musu ne?" Inji Rahama Ayman,
"Toh alhakika mun samu damar tura sakon mu zuwa babban Ofishin mu ta kasa, ita kuma ta tura zuwa babban Ofishin mu ta duniya baki daya, sannan a taron da za ayi na Afrika Insha Allah muna saka ran za'a taso da maganar nan, idan baku manta ba Dr Bagauda ya rike member ba majalisar dinkin duniya, sannan yayi aikin diplomatic na tsawon shekaru goma, ya zauna a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sannan ya shiga hadakar kungiyar sa kai na kasashen Afrika zuwa nahiyar Turai. Dr Bagauda ya jagoranci wata tawagar zuwa kasar Hura, akan zaman lafiya.
Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda, ya jagoranci yankin kasashen Larabawa akan rigimar su da taki ci taki cinyewa, Dr Bagauda mutum ne masanin al'amuran siyasar duniya, kuma anan kasar mu ma, ya jagoranci yankunan karkara akan Cigaba da inganta musu rayuwa, ya taimakawa matasa dari biyar, suka dogara da kansu, Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda ya bawa ya'yan kaji hatsi sunci sun share bakin su, kai har yau salon siyasar shi ce ake gudanar."
"Toh gashi ka dibo bayani amma lokaci abokin tafiya sai hararanmu yake, Dani Rahama Ayman tare da Comrade Habibu Kani da Barister Sabo bako. Muke muku Barka da rana daga gidan Radio gama gari FM."
***
"Hmm" inji Nuhu, lokacin da ya jefa kosai da bread a bakin shi yana gyada kai, Raees da yake kallon shi.
"Adam baka ji abinda ake fada ba ne?" Inji Nuhu,
"Toh kai Nuhu ban da abinka me yasa ba zaka fadi abinda yake ranka ba?"
"Toh amma wallahi indai Mutum irin Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda zai ajiye hidimar shi ya fada siyasa wallahi babban cigaba ne, amma kaga yadda aka butulce mishi." Inji Nuhu,
Murmushi Adam yayi bayan ya tsiyayyi tea yana kallon Raees da idanun shi yake lumshe kamar yana barci.
"Mai girma Shugaban kasa, baka ce kome na?"
Murmushi yayi domin idan Adamu yana son tsokanar shi haka yake gaya mishi, Nuhu kuma yace mishi Honorable.
"Bana sha'awar siyasa amma har yau zuciyata tana kwadaita min son haduwa da Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda."
"Kai Haba?"
"So nake nagan shi sosai na fahimci me yasa ake mishi butulci ne haka?"
Dariya suka saka mishi, sannan Nuhu yace mishi.
"Mutumina idan ka shiga siyasa wannan shegen fadin ranka da son mulkinka sai ya kara hauhawa kamar furashin Gwauron zabi."
Murmushi yayi sai da dimple point din shi ya lubba sannan yace musu.
"Allah yayi min tsari, ban hango hadiri ba, taya zan bata jikina da kashi? Ai wannan lamari sai na masu yanci. Ni da Unguwar mu ma dakyar nake iya tankwara yaran unguwar balle mulki baki daya kai ko siyasar bana fatar shigar ya ɓalle mulkin kai manta kawai."
Zuwan Zakaria ne yace mishi.
"Dan iska idan ka shiga siyasa wallahi Mantawa zaka yi da mun tab'a zama a kofar gidan ku, Umma ta girka mana abin karyawa. Domin kuwa yan siyasa ba daraja ce pda ku ba"
Ya fada tare da ɗaukar kofi ya cika da ruwan zafi, sannan ya jefa lipton ya dauko sugar me iyali yana zubawa yace.
"Dan Umma kai dai Allah ya baku lada, amma wallahi yau kwandala bana maganin shi, kai ma kenan da kayi karatun bokon baka zauna a banza ba, kana tafiya saro bakin mai, amma mu gashi bamu ga tsuntsu bamu ga tarko ga dan banzan tara iyalai da nayi kuma, wallahi yanzun haka Zinnirah ciki ne da ita bata yaye Takwaran ka ba, abin haushi yaron watan shi goma sha biyar fa. Umma Hani kuwa dama ita kam ba haihuwar take akai akai na, sai dai Murja itama ko yau ko gobe wallahi na rasa yadda zan yi da rayuwata,yadda kasan na gudu na bar garin....
#Mai_Dambu
#PaidBook
#Freepage
300₦ katin mtn ko shaida ta wannan Numbers👇🏽
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank! *** or ***
*Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:*** sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza -
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zum
a
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina ya rikice
Zazzogau
Haɗin gigita shi
Maƙale mata
#mai_Dambu...