Free chapter 路 Read without an account

Chapter 45-46

by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮





_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Page 45&46



__________瞥an kai amarya ma sun samu tarba ta mutunci da karramawa a wajen Atika da ma茩ota da ta gayyato, nasiha aka 茩ara yi mata sosai kafin suka bar gidan, ba yadda Afnan ba ta yi ba akan Maryam ta zauna, amma 茩ememe Asabe ta 茩i barin ta, ta tasa 茩eyarta gaba, ta ce "Yo hauka muke yi da za a bar miki ita, shi angon na ki ki kai shi ina?".


Afnan na ji na gani aka watse gaba 蓷aya, aka barta ita ka蓷ai, tsoro ta rin茩a ji, ga damuwa tayi mata yawa, hakan ya sa ta fashe da kuka. Tunanin Mamanta da ya addabi zuciyarta, ya 茩ara bijiro mata, tasan Mama na cikin damuwa ita ma.


Sarkin fada ne ri茩e da waya a hannunsa, wata lamba ya kira ana 蓷auka.

Ya ce "Wai ya aka yi haka ta faru ne? Tun蓷azu nake saka ran ganin yaron nan ya zo amma shiru bai zo ba, ya ku ke so na yi da 拼ar mutane ne? Ko so ku ke ku nuna mini ban isa ba ne? Yanzu gashi an kawo 蓷iyar mutane babu shi ba alamar shi, shin hakan dai-dai ne? A kawo 蓷iyar mutane a 蓷aki a ajiyeta ita ka蓷ai kamar mayya? Gaskiya ban ji da蓷in wannan abin ba, yanzu da bai zo ba ya kuke so na cewa iyayen yarinyar nan? ko 蓷azu sai da mai gari ya tambaye ni, na ce masa ai yana hanya yau zai 茩ara so. Shin ko so ku ke dangi suyi mini dariya? dama suna jin haushin shiga lamarin ku da na ke yi".


Shiru ya yi ya na sauraran abin da ake gaya masa a cikin wayar


Daga baya ya ce "To shikenan, amma ya tabbatar da gobe ya zo garin nan, in ma zaman ne ba zai iyaye a nan ba, sai ya 蓷auki matar tasa". Da ga haka ya kashe wayar ya na cigaba da masifa. Dan ba 茩aramin 蓳ata masa rai suka yi ba.


Atika ta dube shi ta ce "Ka yi ha茩uri mai gida, gaskiya bai kyauta ba, ni kaina banji da蓷in wannan abin ba, wallahi da na kalli yarinyar sai da ta ba ni tausayi, yarinya kyakkyawa da ita, kuma da alamu akwai nutsuwa a tattare da ita".


Sarkin fada ya ce "Ni ma ina jin tausayin yarinyar, musamman yanzu sai Allah yaron nan in ba kunyata ni zai yi ba".


"Ka yi ha茩uri in sha Allah hakan ba za ta faru ba, ni yanzu damuwata yadda za ta kwana ita ka蓷ai a 蓷akin nan, gashi yanzu mu ba yara ne damu ba, balle ace su taya ta kwana, 蓷azun ba yadda ba ta so a bar mata 拼ar uwarta ba, aka 茩i, na so na saka bakina akan a barta 蓷in. To ina gudun su gane mijin baya nan".


Tsaki ya yi, ya na fa蓷in "Yara basu a je komai sai shirme da shiririta, ana yi musu gata ba sa gani". 

Ha茩uri Atika ta shiga bashi, da 茩yar ya yi shiru ya daina mitar da yake.


Allah sarki Mama tun jiya cikin damuwa take, tunanin yaranta ya saka ta a gaba, ga Baba ya yi halin ko in kula da ita, ta na son ko da muryarsu ne ta ji, tana son sanin halin da suke ciki. Duk da tasan inda suke ba za a cutar da su ba.

Sai dai idan ta tuna da rashin sanin wane irin miji Afnan ta aura abin na 蓷aga mata hankali, da 茩ara saka ta a damuwa. Duk da ta na yi mata addu'a da fatan Ubangiji ya ha蓷a ta da miji na gari mai tsoron Allah, haka dai ta kasance cikin damuwa, komai cikin sanyi jiki take yinsa.


Afnan ta da蓷e ta na kuka sai da ta ji kanta ya yi ciwo kamar zai rabe mata gida biyu, sannan tayi shiru ta daina kuka. Tun ta na baza ido, da jiran tsammanin ganin wanene mijin da Allah ya ha蓷a ta zama da shi a matsayin abokin rayuwa, amma shiru babu shi babu alamar shi, tsoro ne ya 茩ara kamata, ta du茩un茩une guri 蓷aya, ta fara tunanin to kodai mijin baya sonta ne? Shi ma auren dole ne aka yi masa.

Ta na nan zaune tayi jugum idan ta gama wannan tunanin sai wannan a haka har bacci ya 蓷auke ta.


Kiran sallar farko a kan kunneta a ka yi shi, a hankali ta mi茩e zaune, ta kunna filitar hannun da ta gani a 蓷akin, can gefe ta hango buta, mi茩ewa tayi ta 蓷auki butar tayi waje, dudubawa tayi har ta ga inda ban蓷akin yake, bayan ta fito alwala tayi ta koma 蓷aki, 蓷ankwalinta ta shimfi蓷a tayi nafila sannan ta zauna ta na lazimi, sai da aka yi assalatu ta mi茩e tayi raka'atanin fijir, sannan ta gabatar da sallan asuba.


Zama tayi ta na addu'a tare da yi wa Allah ki rari, ta na kai masa kukanta, ta na nan zaune ta ji ana sallama.


Amsawa tayi, ta tashi tsaye fitowa tayi, haske har ya fara bayyana.


Atika ce ta shigo domin ta duba ya ta tashi

Afnan a murya ta gane ta, saboda jiya da aka je da ita wurinta fuskarta a rufe take.


Du茩awa tayi har 茩asa ta ce "Ina kwana Inna"

"Lafiya 茩alau Alhamdulillah, fatan kin tashi lafiya? Ya ba茩unta da kuma ka蓷ai ce?"


"Alhamdulillah"


"Ki yi ha茩uri na rashin ganin mijin na ki, jiya abin hawa ne, ya lalace musu a hanya, da yake baya gari, kin san 茩arfen nasara bashi da tabbas".

Sunkuyar da kai tayi ta ce "Babu komai".


Atika ta ce "To ma sha Allah, dama zuwa ne nayi na duba ki, bari na je a ha蓷a abin kari sai aka kawo miki".


"To" ta amsa

Atika ta juya ta bar gurin, Afnan bin gidan da kallo tayi, a fili ta ce "Alhamdulillah Allah na gode ma da wannan ni'imar da ka yi mini".

茒aki ta koma tayi zaune, tare da yin tagumi


Kamar kullum yau ma Haidar bayan ya dawo daga masallaci, ya shiga 蓷akin Umma domin ya gaisheta, zama ya yi ya ce "Umma barka da safiya, fatan kin tashi lafiya?"

Shiru tayi ba ta ce masa 茩ala ba, ta ci gaba da jan carbi

Gyaran murya ya kuma yi, ya ce "Umma barka da safiya...." "Dakata ri茩i gaisuwarka ba na bu茩ata, kuma ka tashi ka fitar mini a 蓷aki".

"Subhanallah! Umma fushi ki ke da ni har haka? Please Umma dan Allah kiyi ha茩uri, ki fahimce ni, Umma ba zan iya jure ganin fushinki a gareni ba, da wanne zanji?".


"Haidar tunda nake da kai ban ta蓳a baka umarni ka bijire mini ba sai jiya, ka ba ni mamaki Haidar, a tunanina duk hukuncin da zan yanke a kanka batare da sanin ka ba, kuma ka kar蓳a ka yi mini biyayya a kai. To 蓷an uwana ma ya isa ya yanke shi akan ka, amma sai kanuna mini bai isa ba, ni ma 蓷in da na ke ganin na isa na tursasaka ka nuna mini a wannan karon ban isa da kai ba. Tunda nake da 蓷an uwana ban ta蓳a jin shi kin tsananin fushi irin na jiya ba. Kuma duk a dalilin abin da kayi, ai ko ya ya ne ya kamata tunda na ce ka je, ka je 蓷in. Haidar ina ilimin ka yake? Ina tunanin ka? Da har zaka kasa kar蓳ar 茩addararka da hannun biyu, ka yi tunanin hakan baya cikin tsarina a yanzu, amma da Allah ya 茩addari lokacin yinsa ya yi ai na ha茩ura na kar蓳a. Idan baka sani ba, wannan abin ta wani fannin gata a kayi maka, amma tunda ka nuna ba ka so, zaka iya yanke duk hukuncin da ka ke ganin ya dace, wu茩a da nama a hannunka suke".


Shiru Haidar ya yi, tabbas maganganu Umman shi sun ratsa shi, sai dai ba ya jin zai iya zuwa wannan garin ya yi zama ko da na kwana biyu ne, sannan Umma da take maganar gata aka yi masa, shi babu wani gata da aka yi masa, a auren dolen da aka 茩a茩aba masa, kuma auren ma wai a 茩auye, shi bayan takurawa da 茩ara jefa shi cikin damuwa da aka yi, a halin yanzu yadda yake ji, tunda ya rasa Afnan, babu wata macen da zata 茩ara burge shi. Gyara zama ya yi, ya ce


"Umma dan Allah ki yi ha茩uri na 蓳ata miki ran da na yi. Duk abin da ki ka gani ban yi dan na 蓳ata miki rai ba, Umma ni ba 茩in kar蓳a nayi ba, zuwa canne ba zan iya ba, me yasa ba a zo nan 蓷in ba?".


"A ta茩aice dai ko yau 蓷in ba zuwa zaka yi ba Haidar? Wato kunyata ni ka ke son yi ko? Haidar kasan illar abin da ka ke shirin aikatawa kuwa? Abin da nake ganin yafi 茩arfin yinka a yanzu, amma cikin hukuncin Ubangiji ka same shi a 蓳agas shi ka ke wula茩antawa? Haidar ina nusar da kai amma ka 茩i ka fahimta, yanzu mahaifar tawa ce ba za ka iya zuwa ba? To shikenan tunda baka so zan yi magana da shi, na bashi ha茩uri, sai ka sauwwa茩ewa 蓷iyar mutane, ta kama gabanta, kai kuma ka tsaya jiran wadda ka ke son 蓷in, tashi ka ba ni guri tun raina bai 茩ara 蓳aci ba".


Haidar zai kuma yin magana, Umma ta hana shi, tare da umartar ya bar mata 蓷akin ta.

Tashi ya yi ya fita jiki ba 茩wari, ya na jin sai dai Umma tayi ha茩uri ba zai ta蓳a zuwa gurin wata kucakar mace ba a 茩auye, to ya je me zai yi mata? Idan suka gaji da jiransa dole su nemi mafita.


Da kallo Umma ta bishi, ta na mamakin 茩arfi hali irin na Haidar, tunda take bai ta蓳a nuna mata kafiya ba, sai wannan karon. A fili ta ce "Lallai barewa ba ta yi gudu 蓷anta ya yi rarrafe ba, ba za ta manta kafiya irin ta mahaifinshi ba, Allah Sarki rayuwa kenan".


Umma ba tayi aune ba sai jin zubar hawaye tayi a kan fuskarta, a duk lokacin da zata tuna Baban Haidar takan shiga damuwa marar misaltuwa. Goge hayen tayi, ta na tunanin irin hukuncin da zata 蓷auka akan Haidar, dan ta san ba 茩aramin ya茩i za ta yi dashi ba, a yadda ta ga ya dage 蓷in nan, yanzu ya za ta yi da Yaya? Me zata ce masa? Haka dai ta shiga zancen zuci daga 茩arshe ta yanke shawarar abin da zata yi.


Da sanyi safiyar nan, wasu hadda abin kari basu 蓷ora ba, Gwaggo ta saka Sanusi ya kira mata Yaya Bala, Baba na zaune shi dai bai ce 茩ala ba. 


Mai gari na zaune Maryam na kusa da shi, ta ba shan koko da 茩osai, ya ji ana kiran wayarsa, dubawa ya yi ya ga Sanusi ne, 蓷aga wayar ya yi tare da yin sallama.


Amsawa Gwaggo tayi tare da fa蓷in "Antashi lafiya Yaya ya mutan gidan?"


"Alhamdulillah Halima fatan kuna lafiya kuma?" .


Ta ce "Lafiya lau Alhamdulillah Yaya".

"To ma sha Allah, jiya dai A'isha a 蓷akinta ta kwana".

Gwaggo ta ce "Ma sha Allah, ashe ma abin bai da蓷e ba, sannu da 茩o茩ari Yaya Allah ya bar zumunci, ya 茩ara girma" . Ya amsa da Amin 

Sannan ta ce "To ita wannan mara kunyar me take nufi? Ko ba za ta dawo ba ne? Can zata zauna a gidan mutane ta ri茩a yi musu rashin kunyar da ta saba yi, ko kuma ta kashe mata auren ma gaba 蓷aya, idan kuma can 蓷in take muradin zama ita ma sai a nemamata mijin a can".

Mai gari ya ce "Halima wai yaushe zaki daina wannan masifar ne? Shin babu inda zata zauna ne sai gidan A'isha? Da ki ke ta ha茩ilon zata kashe mata aure, ba na son irin wannan halin naki, ki rabu da ita duk lokacin da tayi ra'ayin komawa gida, sai ta tafi, yarinya mai hankali ki na kiranta da mara kunya".

"Allah ya baka ha茩uri Yaya, ina godiya sosai a gaishe mini da mutan gidan".

Ya ce "To zasu ji" daga haka Gwaggo ta kashe kiran, ta ci gaba da masifa, ba gaira babu dalili. 


Mai gari ko dariya ya yi ya ce "Halima Allah ya kyauta". Maryam dai bata ce komai ba 


Bayan hantsi ya fara fitowa Maryam ta ce gidan Afnan zata je, aka saka yaro ya rakata.


Afnan na zaune bayan ta gama karyawa, ta nemi guri 蓷aya ta zauna, ta zuba uban tagumi, sallamar Maryam ta ji. Cikin farin ciki ta nufi Maryam ta rungumeta.



Amanar cool ce 鉁嶏笍 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.