Free chapter 路 Read without an account
Chapter 55-56
by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...
馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮
_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Page 55&56
____________Mamaki Umma take yi na ganin 茩ofar gidan a bu蓷e, ta san babu mai makullin gidan sai Haidai, 蓳oye mamakinta ta yi suka shiga gidan, Haidar na 茩o茩arin fitowa da ga 蓷akinsa, ya ji sallamar Umma, wani irin juyi ya ji hanjin cikinsa sun yi, nan take ya ji fitsari na 茩o茩arin zubo masa, da mugun gudu ya nufi katifarsa ya kwanta, ya ja bargon dake gefe ya rufe jikinsa gaba 蓷aya.
Umma tsaye ta yi tana bin 茩ofar 蓷akin Haidar da kallo, nufar 蓷akin ta yi da niyyar shiga, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, 蓷akinta ta bu蓷e.
Sannan ta kalli Afnan da ta yi tsaye a guri 蓷aya, ta ce "Afnan shigo ciki mana" ta yi maganar a hankali, shiga 蓷akin ta yi ta zauna a 茩asa, Umma ta ce "Haba ya ki ka zauna a 茩asa? Ki hau saman kujera mana, ki saki jikinki nan fa gidanku ne".
Umma ta mi茩e ta fita waje, ta 蓷ebowa Afnan ruwa masu sanyi ta kawo mata, sannan ta fara tunanin 蓷ora musu girki.
Haidar kuwa ya na can cikin bargo ya tara uban gumi, ban da nadama da da nasanin zuwan da ya yi gidan, babu abin da yake yi, sai da Faruk ya yi masa gudun haka, yanzu ya zai yi? Me zai cewa Umma ya kare kansa? Bayan ga 茩aryar da suka kuma yi mata yanzu.
Afnan bayan ta sha ruwan da Umma ta kawo mata, wani bacci ta ji ya na ta so mata, kashingi蓷a ta yi a saman kujera ta fara lumshe idonta. Ganin haka ya sa Umma ta ce "Afnan idan bacci ki ke ji ki je kan shimfi蓷a ki kwanta".
Afnan ta ce "A'a Umma nan ma ya isa".
茦yaleta Umma ta yi, sannan ta fita waje dan sama musu abin da za su ci.
Kallon 蓷akin Haidar ta kuma yi, tana mamakin me yake yi a ciki ne da ya ji shigowarta kuma ya kasa fitowa, nufar 蓷akin ta yi tana shiga ta ga mutum cikin bargo.
Ta ce "Waye a 蓷akin nan?".
Sha茩e murya ya yi da 茩yar ya ce "Umma ni ne"
Umma ta ce "Haidar ya a ka yi na ganka a gida? Bayan ban da蓷e da gama waya da Faruk ba, ya ce mini kuna wurin mai magani".
Haidar 茩iri 茩iri ya karkace baki ya ce "Umma ko da ki ka yi waya da Faruk duk muna gidan nan, dawowarmu kenan, abin da ya sa ya ce miki muna wurin mai magani, saboda munga ba kya nan ne, kuma ba mu san uzurinki ba, idan ki ka ji ina gida za ki iya dawowa ba tare da kin kammala abin da ya fitar da ke ba, shi ne na ce abari sai kin gama idan ki ka zo sai na yi miki baya ni". Ya 茩arasa maganar ya na nishi ka蓷an ka蓷an.
Umma mutuwar tsaye ta yi, tana tambayar kanta yaushe Haidar ya koyi 茩arya? Amma dai ta yi masa kamar ba ta fahimci komai ba ta ce "Ok to ya jikin naka? Ina fatan ka samu sau茩i".
Ya ce "Eh da sau茩i, sai dai Umma ina jin jiri na 蓷ibata idan na ce zan yi tafiya, yanzu haka ina so na 蓷an ji 茩warin jikina ne zuwa gobe sai na yi tafiyar da ki ka ce".
Umma ta ce "Wai to me yake damunka ne? Ni Faruk ya fa蓷a mini baka da lafiya, kuma rashin lafiyar da ya yi mini baya ni, ai ba irin wannan ce ba, yanzu kuma na ganka a kwance".
"Eh Umma yau ne na tashi da wannan zazza蓳in, ai shi ya sa ma da ba za ki iske ni a gidan nan ba, saboda niyyata ina dawowa zan wuce abin na raina".
Wani kallo Umma ta yi masa, sannan ta ce "To Allah ya sauwwa茩e ya baka lafiya, ai ma ba sai ka yi tafiyar ba, tun jiya ba na nan, na je 茩auye ne". Ya ce "茦auye kuma? Me ki ka je yi a 茩auye?".
"To Haidar ba ka nan, gashi ban samun wayarka, Yaya ya uzzura mini da kansa ya zo gidan nan, shi ya sa kawai na je na taho da yarinyar".
Ai da mugun sauri ya tashi zaune Haidar ya ce "Umma ki ka taho da ita nan garin? Umma me za ta yi a nan 蓷in? Ai da kin bar ta a can 蓷in, sai na je, amma nan me za ta yi wa mutane, ban da 茩auyanci".
Sakin baki ta yi tana kallon shi, sannan ta ce "Zuwan da na yi na taho da ita ne laifi Haidar? Wai Haidar yaushe ka koyi wannan halin ne? Ina magana ka na yi mini musu, to shikenan ai sai ka san yadda za ka yi da ita gata can 蓷akina tana bacci". Ta yi maganar tana dubansa ta ji me zai ce.
"Haba Umma ni dai ban ji da蓷in zuwan nan da ita ba, ni ba abin da za ta 茩are ni da shi a gidan nan, yanzu Umma duk wanda bai san da auren nan ba, zuwanta gidan nan zai sa ya sani". 茦arara Haidar ya nunawa Umma rashin jin da蓷insa, da 茩yan茩yamin yarinyar.
Kasa magana Umma ta yi, tana kallon ikon Allah.
Juyawa ta yi za ta bar 蓷akin, ta juyo ta ce masa "Tunda na ga ka fara jin dama, bari na turo maka ita ku gaisa da ga nan sai ta gyara muku 蓷akin, ta kwaso kayanta, ta dawo nan 蓷akin". Da gangan Umma ta yi masa wannan maganar dan kawai ta 茩ara fahimtar me yake nufi, dan ko da ya nuna mata ya ji da蓷in zuwan da ta yi da ita, sai ya gane bashi da wayo.
"Don Allah Umma ka da ki turo ta 蓷akin nan, ki bari idan na fito sai mu gaisa, sannan ta yi zamanta a 蓷akinki ba sai ta dawo nan 蓷akin ba".
Fita Umma ta yi tana jinjina kai.
*******
Mami ganin ciwon na Huda sai gaba yake yi, ya sa ta kira dr Nura ya zo ya duba jikinta, tunda ta ce ba za a kaita asibiti, zama ta yi a falo tana jiran isowarsa dan ya ce mata gashi nan zuwa yanzu.
Mudan ya shigo falon babu sallama, zama ya yi bai ce 茩ala ba
Mami ta ce "Mudan ba za ka daina shigo mini falo babu sallama ba ko?". Shiru ya yi ya na 蓳ata fuska dan shi ba wannan ne a gabansa ba.
Ta kuma cewa "Wai lafiya za ka zo ka tsare ni ka na mini yi ba茩in rai? Ko kuma saboda na ce ba za ka auri Hasina ba ne? To ka sani ko mutuwa za ka yi ba za ka aure ta ba, mara hankali kawai, an ce maka ni mahaukaciya ce da zan bari ka auri 蓷iyar Turai, to wallahi tun wuri ka daina wannan tunanin, Sharifa nake so ka aura".
Cikin rashin 蓷a'a Mudan ya ce "Mami wallahi ba wanda ya isa ya hanani auren Hasina tunda ita nake so, babu wata Sharifa da zan aura. Hasina ce kawai nake gani a matsayin mace a idona, kuma sai na aureta".
"Mudan an ya kana cikin hankalinka kuwa?"
"Ni Mami lafiya 茩alau nake, kawai idan ana son zaman lafiya a gidan nan a aura mini Hasina, idan kuma ke ba za ki yarda ba, zan je na samu Abba na gaya masa. Ai nasan shi zai fahimci ni, kuma ya amince". Daga haka Mudan ya bar falon kai tsaye sashen Ammi ya nufa.
Bayansa Mami ta bi da kallo tana nazari da tambayar kanta an ya Mudan na cikin hankalinsa kuwa?.
Da sallama Mudan ya shiga falon Ammi, sai dai shiru babu kowa a falon zama ya yi ya na jiran fitowarsu, dan baya jin zai iya ha茩ura, ya yi wa Mami biyayya.
Dr Nura ya zo Mami ta yi masa jagora har 蓷akin Huda, tana kwance Mami ta ce "Huda tashi ga likita nan ya zo zai duba ki".
Huda ta ce "Mami ba na ce bana so ba..." Ba ta 茩arasa ba, Mami ta ce "Ba na son iskanci Huda. Dr zo ka yi aikin ka".
Ba yadda ta iya haka ta 茩yaleshi ya fara yi mata duk wani gwajin da ya kamata, bayan ya kammala ne ya dubi Mami ya ce "Yaushe a ka yi mata aure ban sani ba?".
Mami ta ce "Aure kuma? Huda ai ba ta da aure".
Da sauri ya kalli Mami, sannan ya mai da dubansa ga Huda, da ta tsareshi da ido. Ya ce "Ba ta da aure?".
Mami ta ce "Eh likita me yake damunta ne wai?".
Shiru ya yi, sannan ya ce "Maganar gaskiya ba zan 蓳oye miki ba, tana da juna biyu har na tsawon wata biyu da sati 蓷aya, sai ulcer da ke damunta, a kan rashin cin abinci da ba ta yi".
Cikin ka蓷uwa Mami ta ce "Likata ka san me ka ce kuwa? Hudan ce ke 蓷auke da juna biyu?".
"Eh hajiya, haka binciken da na yi ya nuna mini, sai ta kula da cin abinci, zan rubuta mata maganin da za ta ri茩a sha, wanda zai taimaka mata ta samu 茩warin jikinta". Ya rubuta mata maganin ya a ji ye takardar, sannan ya kwashe kayansa ya fita.
Har ya gama surutunsa ya bar 蓷akin Mami ba ta kuma yi masa magana ba, kallon Huda take yi kamar yau ta fara ganinta.
*******
Haidar Umma na fita ya 蓷akko wayarsa ya kunna ya kira Faruk, ya na 蓷auka Haidar ya ce "Kai abin da ka yi gudu shi ya faru fa, ina shigowa gidan sai ga Umma ta dawo".
Mi茩ewa zaune Faruk ya yi da ga kwancen da yake ya ce "Da gaske ka ke ko dai wasa ka ke yi mini?".
Haidar ya ce "Wallahi da gaske nake" nan ya fa蓷a masa duk yadda suka yi da Umma da zuwan da ta yi da yarinyar da aka aura masa.
Dariya Faruk ya yi ya ce "Haidar yaushe ka iya 茩arya haka ne? Ah lallai ka ce dai yau kai ango ne, anjima za mu zo siyan baki".
"Kai banza ne, me zan yi da wata 拼ar 茩auye? Ni bari ka ji bama zan bari na ha蓷u da ita ba, wasan 蓳uya za mu yi da ita a gidan nan, ai ni a gurina babu wadda nake wa kallon mace sai Afnan".
Faruk ya ce "Haidar ka daina ambatar matar mutane, hakan babu kyau, kuma bai kamata ba, sannan ina so ka yi ha茩uri tunda har Umma ta zo da ita ka rungume 茩addararka Haidar, ka tsaya ku gaisa wata 茩ila sai ka ga Allah ya gyara maka ita a rayuwa".
Tsaki Haidar ya yi ya kashe wayarsa, tashi ya yi ya li茩a ta taga, ya ga babu kowa a waje dan haka cikin san蓷a ya fito ya yi waje abinsa.
Umma ko jolof 蓷in taliya ta yi musu, bayan ta gama ne a lokacin Afnan ta farka da ga baccin da take yi.
Umma ta ce "Afnan kin tashi?".
Ta ce "Eh Umma"
"To sai ki tashi ki yi wanka, sannan ki ci abinci".
Tashi ta yi Umma ta kai mata ruwan wanka, Afnan duk kunya ta isheta, saboda ita ya kamata a ce ta yi mata hakan, wanka ta yi ta zo ta zauna Umma ta zuba mata abinci, sannan ta zuba wa Haidar nasa, ko da ta je 蓷akinsa wayam baya nan, a je ye masa abincin ta yi ta fito.
****
"Huda ya a ka yi hakan ta faru? Huda ciki fa ciki a ka ce kina da. Don Allah wa ya yi miki wannan aikin? Huda yanzu ni za ki kunyata? Ni za ki tozarta a idon duniya? Me narage ki da shi da har za ki aikata irin wannan 蓷anyen aikin?". Mami ta 茩arasa maganar muryarta ko fita ba ta yi saboda 蓳acin rai
Kuka Huda take yi sosai, ta kasa yi wa Mami magana
Cikin tsawa Mami ta ce "Ba magana nake yi miki ba ne? Uban wa ya yi miki wannan cikin?"
"Don Allah Mami ki yi ha茩uri, wallahi ba laifina ba ne".
"Huda za ki fa蓷a mini wanda ya yi miki cikin nan ko sai na sha茩e ki a gurin nan". Shiru ta yi ta 茩i cewa 茩ala. Ganin Mami ta yo kanta ya sa cikin kuka ta ce "Ya Mudan ne".
茒iff Mami ta yi jin maganar ta yi tamkar an saukar mata da aradu, jinta da ganinta suka 蓷an bar jikinta na wucin gadi, fa蓷uwa ta yi kasa da蓳as, ta yi zaman 拼an bori, tana kallon Huda kamar wata sabuwar halitta. Kuka Huda take yi sosai, tana bawa Mami ha茩uri, a hankali Mami ta mi茩e da 茩yar ta fita daga 蓷akin, bedroom 蓷in ta ta shige ta kulle kanta, kwanciya ta yi, tana jin kamar ba a duniya take ba, haka take ganin kamar mafarki take yi ba gaskiya ba ne.
Mudan ganin ya da蓷e a falon ba su fito ba, ya sa shi mi茩ewa ya bar falon, da niyyar zai sake dawowa motarsa ya shiga ya ja bar gidan.
*****
Afnan fitowa ta yi ta share gidan tsaf, ta yi wa Umma wanke-wanke, ta gyara mata 蓷akinta, har lokacin Haidar bai dawo gidan ba.
Da yamma Umma na zaune ita da Afnan a tsakar gidan, suna hira duk da Afnan ba wani sakin jikinta take yi ba. Haidar ya shigo gidan da sallama. Bai 茩arasa sallamar ba. Ya fara murzar idonsa ya na son tabbatarwa da kansa cewar ba gizau idonsa ke yi masa ba, cikin rawar murya ya ce "Afnan ki ce, na ke gani ko dai gizau ne idona ke yi mini?"
Ita ma Afnan cikin mamaki ta ce "Ya Haidar" tana cewa haka ta yi shiru.
Umma ta ce "Kin san shi ne Afnan?".
Kafin Afnan ta yi magana Haidar ya ce "Umma ita ce yarinyar da muka yi maganarta da ke kwanaki".
Da sauri Afnan ta kalle shi, gaba 蓷aya kanta ya kulle, ta kasa fahimtar komai.
Umma ko murmushi ta yi ta ce "Alhamdulillah Allah an zo gurin".
Amanar cool ce 鉁嶏笍
***