Free chapter 路 Read without an account

Chapter 59-60

by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮



_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 59&60



____________Afnan 茩o茩arin janye jikinta ta yi, sai dai ta kasa samun damar yin hakan, soboda ba 茩aramar runguma Haidar ya yi mata. 

"Haidar tashi ka bar 蓷akin nan tun muna shaida juna". Umma ta yi maganar cikin dakiya, dan ba 茩aramar kunya ta ji ba, da ta san abin da za ta gani kenan da ba ta zo 蓷akin nan ba. Duk da tana ban蓷aki zuciyarta ke raya mata zai iya shiga 蓷akin tunda ya ga ta shiga wanka, shi ya sa ta yi saurin watsa ruwan ta fito, saboda ko magana ba ta son ya yi da ita, sai gashi ta ga abin da ya girmi tunaninta, ita ma dai Afnan 蓷in an yi sakara marar wayo. Duk irin jan kunnen da ta yi mata, shi ne za ta biye masa.

A hankali ya fara 茩o茩arin raba ta da jikinsa

Hakan ya ba ta damar mi茩ewa da sauri tana mayar da numfashi dan ba 茩aramin tsoro ta ji ba.

Tashi Haidar ya yi jiki ba 茩wari kamar wanda 茩wai ya fashewa a ciki ya ra蓳a ta gefen Umma ya bar 蓷akin. Ya na shiga 蓷akinsa kwanciya ya yi ya lumshe idonsa, wani ba茩on yanayi na ziyartarsa, ba abin da yake gani a idonsa sai surar jikin Afnan da yanayin kwanciyar da ya ga ta yi. 


Afnan ko bayan fitar Haidar ji ta yi kamar 茩asa ta bu蓷e ta shige, wata matsananciyar kunya ce ta kamata, ta kasa yin 茩wa茩waran motsi, sai gabanta da ke dukan uku uku tana mamakin wai yau ita ce namiji ya rungume ta har ya na ha蓷a jikinsa da na ta.

Umma kuwa 茩ala ba ta cewa Afnan ba, ta ci gaba da sabgar gabanta, domin ta lura da yanayin Afnan 蓷in kamar a firgice take, shi ya sa za ta 茩yaleta sai da safe. Duk da ta san ba laifin ta ba ne, amma za ta 茩ara ja mata kunne. Afnan na jiran ta ji me Umma za ta ce mata, sai dai ta ji ta yi mata shiru, hakan ya sa hankalinta ya 蓷an kwanta, har Umma za ta kwanta ta tuna da ledar da Haidar ya zo da ita, tashi ta yi ta fita waje ta 蓷akko ledar gasashen nama ne, ta ce wa Afnan ta tashi gashi nan ta ci, tashi ta yi saboda ba ta son yin musu da ita, ta 蓷an 蓷auki ka蓷an ta ci sannan ta kwanta.


Gaba 蓷aya Haidar ya kasa samun nutsuwa, sai da ya gwammaci bai shiga 蓷akin nan ba, a daren nan dai bacci gagararsa ya yi, ban da juyi ba abin da yake yi. "Kai gaskiya ban yi wa kaina adalci ba, me ya sa na kasa ha茩uri tun farko wai? Yanzu gashi na rasa me zance wa Umma ta yarda da ni". Ya yi maganar a fili, a wannan daren dai Haidar kwanan zaune ya yi.

Washe gari sallar asuba ma sai a gida ya yi ta. 

Ya kasa fitowa daga cikin 蓷akinsa, saboda ya na jin kunyar ha蓷a idanu da Umma, sai yanzu yake jin kunyar abin da ya aikata jiyan. 

Afnan ma haka sai sunkuyar da kai take yi. Umma da ta gama ha蓷a musu abin kari, ganin har lokacin Haidar bai fito ba ya sa ta fara tunanin ko lafiya yake. 

Zama suka yi nan waje suna karyawa

Haidar na jin duk abin da suke yi, kasancewar 蓷akinsa da toilet a ciki, ya sa sai da ya gama shirin sa tsaf na fita, sannan ya fito, suna ha蓷a ido da Umma da sauri ya kauda kansa gefe, 茩arasowa ya yi, ya tsuguna ya gaishe da Umma, ta amsa masa fuskarta ba yabo ba fallasa. 

茦uri ya yi da ido ya na kallon Afnan, ganin haka ya sa ta ce "Ina kwana ya Haidar"

"Lafiya 茩alau Alhamdulillah fatan kin tashi lafiya?"

Ta ce "Alhamdulillah"


Umma ta ce "Afnan ban hanaki yi masa magana ba ko shiga harkarsa ba?".

Shiri ta yi, ta sunkuyar da kai 茩asa

Haidar ya ce "Umma kamar ya? Ban gane kar ta yi mini magana ba? Matata ce fa Umma" ya 茩are maganar ya na kallonta.

Umma ta ce "Au haba ashe matarka ce fa, to sannu mai mata"

"Umma wai dan Allah me ki ke nufi dani ne? Na baki ha茩uri fa Umma"

"Haidar ba na son damuwa, idan ka tashi ga abin karin ka nan".

Kasa magana ya yi ya na bin Afnan da kallo

Umma na ankare da shi, dan haka ta ce "Afnan tashi wucewar ki 蓷aki ki 茩arasa karin a can"

Tashi ta yi ta 蓷auki abincin ta ta shige 蓷aki. Umma ta ci gaba da karin ta

Haidar ya gane dan shi ne Umma ta yi hakan, tashi ya yi bai ko tsaya karyawa ba, ya yi mata sallama ya fice daga gidan.

Umma ta ce "Tukuna baka ga komai ba, sai ka gane kuskurenka, dan rainin hankali yaron".


Mama ta damu sosai na rashin jin Afnan da kuma sanin halin da take ciki, shi kansa Baba ya na jin babu da蓷i a ransa amma ya kasa magana da nuna damuwarsa a kan hakan.

"Maryam"

"Na'am Mama"

"Ni ko ina ta so in fa蓷a miki wannan yarinyar ta zo lokacin da ba kya nan".

Maryam ta ce "Wace yarinya Mama?"

"Wannan yarinyar da ta ta蓳a zuwa nan gidan, a lokacin da ta rage muku hanya"

"Au wai Sharifa ki ke nufi?"

Mama ta ce "Eh ita, ta zo hadda tsaraba ta kawo mana, ta ce na bata lambarki na ce ai ba ki da waya, shi ne ta kar蓳i tawa lambar, sannan ta saka ta ta a wayata".

Maryam ta ce "Allah sarki, ta kyauta"

Zaliha ce ta shigo da sallama, ko amsa mata ba ta tsaya a ka yi ba, ta ce "Ke Maryam ki zo Innata tana son ganinki" daga haka ta juya ba ta ce wa Mama 茩ala ba.

Maryam ta 蓷aga muryarta da 茩arfi yadda Zalihan za ta ji ta, ta ce "Ki je ki ce mata ba zanzo ba, in ta isa ta zo ta jani da 茩arfin tsiya...." "Ke Maryam ba na son rashin kunya, Hajara 蓷in ce za ta aiko kiranki ki ce ba za ki je ba? Ba matar Babanki ba ce? Maza tashi ki je ki ji kiran da ta ke yi miki".


Tashi ta yi tana 茩un茩uni ta bi bayan Zaliha, ko da ta je kawu Sanusi na zaune, zama ta yi ta gaishesu, ya amsa ya na fa蓷in "To mara kunyar yarinya, wato kin 蓷auka Hajara ce ke kiranki shi ne ki ka ce ba za ki zo ba?"

Shiru Maryam ta yi. 

Hajara ta ce "Ta za ta ni ce kashin namalkonsu ita da uwarta, to ba ni ba ce ubanki ne gashi nan".

Zaliha ta ce "Hadda zaginki ta so yi fa"

"Ai za ta aikata in dai ita ce" cewar kawu ya na kallonta.

Maryam dai 茩ala ba ta ce musu ba, sai dai ta 茩uduri aniyar sai ta ci uwar Zaliha idan ta kamata.

Kawu ya ce "Dama abin da ya sa nake nemanki, jiya Malam Almu ma茩ocinmu ya tare ni da maganar 蓷ansa Daudu ya ganki kuma ya na sonki da aure, shi ne kafin na fitar da maganar na fara gaya miki dan ki san da zancen".

Da wani irin sauri ta kalli kawu ta ce "Wane Daudu kuma kawu?"

"Bangane ba Daudun ne ba ki sani ba ma茩ocin namu? wai me ya sa ki ka raina mutane ne Maryam?".

Shiru ta yi bata kuma magana ba, in da shi ne ya zo mata da zancen wannan yaron ba da sai ta zage shi wallahi.

"Kin yi shiru ba ki ce komai ba?"

"To Kawu me zance?" . Ta yi maganar cikin hasala.

Ya ce "To shikenan tashi ki tafi, dama dan ki san da zancenne"

Tashi ta yi, tana 茩o茩arin barin wajan 

Hajara ta ce "Ji mini yarinya ana 茩o茩arin yi miki gata ki na yi wa mutane iskanci"

Maryam ta dube ta ta ce "Ko ba gata ba? Ai naga kema ki na da 拼ar sai ki aura masa ita, ba dole sai ni 蓷in ba" tana cewa haka ta yi wucewar ta.

Hajara ta ce "Mara kunyar banza, wannan yarinyar fa magana ce ta fa蓷a maka a fakaice".

Kawu ya ce "Rabu da ita zan yi maganinta ne"

Zaliha ko ban da dariya babu abin da take yi, jin wai Daudu ne ke son Maryam.

Da kuka Maryam ta 茩arasa Mama ta ce "Ke lafiya me ya faru ne?"

Cikin kuka ta ce "Wallahi Mama ba wanda ya isa ya yi mini abin da a ka yi wa Aunty Afnan".

"Wai me ya faru ne? Wani abin a ka yi miki ne?"

"Mama wai kawu ne ya ce an zo nema wa Daudu aurena"

Dafe 茩irji Mama ta yi ta ce "Daudu kuma wane Daudun?"

"Mama Daudun da ki ka sani na unguwar nan mana, wannan gigiwagaga 蓷in nan, wallahi Mama ko za a kashe ne ba zan aure wannan 蓷an iskan 蓳arawo ba, Mama bai da isashen hankali fa, idan gaskiya ne ai ya na da 拼a, me ya sa ba zai aura mata shi ba?".

Wani irin 蓳acin rai ne ya turni茩e zuciyar Mama, nan take ta ji ba za ta lamunta ba, a wannan karon ko me zai faru ba za ta yarda da wannan maganar ba, wace irin 茩iyayyace a ke nuna mata 茩arara haka? lallai wannan karon za a sha mamakin ta.

*******

Kasancewar yau Abba a 蓳angarin Mami yake, ya sa shi yin amfani da wannan damar wurin yi mata magana a kan zancen da Mudan ya zo masa da shi. 

"Mamin yara"

"Na'am Alhaji" 

"Magana nake son yi dake. Duk da naga yanayin ki ya sauya, tun jiya da na zo kamar akwai abin da ke damunki?"

"Babu komai Alhaji me ka gani ne?"

Ya ce "To shikenan tun da babu komai, yanzu dai ina Mudan? Tashi mu je falo a yi komai a gabansa"

Gabanta ne ya fa蓷i, amma sai ta dake ta ce "To mu je"

Tashi suka yi zuwa falon. Abba ya kira Mudan a waya, babu 蓳ata lokaci ya zo falon. Mami sai bin sa take da kallo tana mamakin yadda ya iya aikata wannan aikin.

Abba ya dubi Mudan ya ce "Mudan"

"Na'am Abba"

"Sake maimaita abin da ka fa蓷a mini"

Ba tare da shakkun komai ba. Mudan ya sake maimaita abin da ya fa蓷awa Abba 

Abba ya dubi Mami ya ce "Saratu me cece hujjar ki na hana shi auren yarinyar da yake so? Kuma yarinyar ma 拼ar aminiyarki, ai sai nake ganin kamar hakan bai da ce ba?"


Mami ta ce "Au 茩arata ya kai kenan? Alhaji ni ba ni da hujjar komai, kawai dai auren ne ba na bu茩ata, idan ma auren zai yi ya je ya nemi wata yarinyar ya aura, amma ba Hasina ba, ko kuma ka yi ha茩uri a mai da maganar aurensa da Sharifa".


"Saratu ba na ce kar a sake tayar da zancen auren sa da Sharifa?"

Ta ce "Allah ya ba ka Ha茩uri, to ya nemi wata yarinyar ba Hasina ba"

Abba ya ce "Ba ki da hujjar hana shi auren Hasina Saratu, wai ke wace irin mace ce? Hasinar nan 拼a take a gurinki, to bari ki ji ko ki yarda ko kar ki yarda, ni zan shige masa gaba wurin ganin na aura masa ita". 

Ya dubi Mudan ya ce "Ba dai ka na sonta ba ko? Tashi ka yi tafiyar ka, zan san abin yi".

Tashi ya yi ya fita. Duk abin da a ke yi Huda na la蓳e ta ji komai, da sauri ta shiga kitchen ta bi ta 茩aramar 茩ofar da za ta sada ta da 蓳angaren Mudan.

Ganin Huda ya yi kamar wadda a ka jefo

"Ke lafiya za ki shigo mini haka ko sallama babu?"

"Ai sallama ana yinta ne a in da ya da ce. Mudan ni za ka ci wa amana? Ni za ka yaudara ka 蓳ata mini rayuwa sannan kuma ka guje ni? Lallai ka cika babban mara jin tsaron Allah. A tunanina ko mai yi mini hakan ka gani kai mai tsaya mini ne, sai gashi kai da kanka ka aikata mini haka. Mudan wallahi na yi da na sanin biye maka da na yi".

"Huda ni ki ke gaya wa magana haka?"

Cikin tsiwa ta ce "To hell with you" ta fa蓷a tana yi masa mugun kallon.

"Huda fice mini a 蓷aki"

"Ai dama ba zama na zo yi ba, sannan ka shirya amsar da za ka ba Mami domin ta san da zancen cikin nan". Daga haka ta fice 

Mudan ko ba 茩aramar razana ya yi ba, wai da gaske Huda ciki ne da ita? Kai anya ba 茩arya ce take yi ba? To Mami ta san da zance ne za ta yi masa shiru, tuna irin kallon da ya ga Mamin na yi masa 蓷azu ya sa shi shan jinin jikinsa. "Lallai in dai cikin nan ya tabbata a kwai matsala"

*****

Afnan ta yi wa Umma sharar gida ta wanke kwanuka. Umma sai da蓷i take ji, tana 茩ara yi wa Allah godiya. Bayan Afnan ta kammala aikin ta yi wanka, sannan ta koma 蓷aki ta yi kwanciyar ta, tunanin Mama take yi da halin da take ciki. Umma ta zo ta zauna kusa da ita, ta ce "Afnan wai ni ko iyayenki sun san kin dawo garin nan kuwa?".

Tashi ta yi zaune ta ce "Wallahi Umma ban sani ba ko an sanar da su".

"Gashi ke ba waya ce da ke ba balle ki kira su, ko kina da lambar su ne, sai ki kira a waya ta".

Cikin zumu蓷i Afnan ta ce "Eh ina da lambar Mama"

Ba ta wayar Umma ta yi Afnan ta kar蓳a da murna ta saka lambar Mama ta kira

Mama na tare da Maryam dake ta cika tana batsewa, kira ya shigo wayar ta, ba茩uwar lamba ta gani ta 蓷auka tare da yin sallama 

"Afnan ta ce "Mama ina kwana"

"Afnan ke ce? Lafiya 茩alau Alhamdulillah, Afnan ina ki ka koma ne? an ce surukar ki ta zo ta tafi da ke?"

Afnan ta ce "Mama ina cikin garin nan"

"Wane gari kuma?" Mama ta yi tambayar da mamaki

Afnan ta tabbatar mata da nan dai garin nasu, dama ashe nan suke da zama shida Ummanshi

Da sauri Maryam ta ce "Mama ba ni ita, mu yi magana"

Mi茩awa Maryam ta yi tana mamakin wannan lamari 

Maryam ta ce "Aunty da gaske kina nan garin? To wace unguwa ce kuke?"

"Maryam ni ma ban san sunan unguwar ba, amma ki kira ya Haidar ki tambaye shi, zai fa蓷a miki, ya san har gidan da muke"

Maryam ta ce "Ya Haidar kuma? To ya a ka yi ya sani?"

"Ke dai ki tambaye shi kawai, idan ki ka zo sai ki ji koma mi ye" hira suka yi sosai gaba 蓷aya Maryam ta nemi damuwarta ta rasa, Mama ma haka wata nutsuwa da kwanciyar hankali ta ji suna shigarta, sai godiya take yi wa Allah a zuciyarta

Umma ta ce "Afnan zan 蓷ora girki sai ki kular mana da shi, ina so zan je gaisuwa ne, sannan dan Allah Afnan ina ro茩on ki da ka da ki sake biye wa Haidar. Duk wannan abin da ki ka ga ina yi miki ba wai dan ba na son zaman ki da shi ba ne, incinki na ke 茩o茩arin 茩watar miki a wajansa, ina so ko da ba na gidan nan ya zo ka da ki kula shi. Duk da na san da wuya ya dawo 蓷in"

Du茩ar da kai 茩asa ta yi ta ce "To Umma in sha Allah, ba ma sai kin 蓷ora girkin ba, ki bari ba 蓷ora da kaina".

Umma ta shirya ta tafi, da yake unguwar akwai nisa, ta so tasa Haidar ya kai ta, sai kuma ta 茩yale shi.

Haidar kuwa ya na can gurin aikinsa, bayan ya sauke fasinja ne ya ji ya na son komawa gida. Duk da ya na jin haushin abin da Umma ke yi masa, kai tsaye gida ya nufa, a lokacin Afnan ta 蓷ora girkin, tana 蓷aki ta ji sallamar Haidar sai da gabanta ya fa蓷i, da 茩yar ta amsa sallamar, ya nufin 蓷akin na Umma, sannu da zuwa ta yi masa ya amsa ya na fa蓷in "Ina Umma?"

"Ta tafi unguwa" ta bashi amsa 

Shiru ya yi ya na 茩are mata kallo, ganin duk a tsorace take, ga hijabi a hannunta tana son sakawa ta kasa.

Hannu ya sa ya kar蓳i hijabin ya ajiye, jikinta ne ya 蓷auki rawa, ta mi茩e tsaye, tashi tsaye ya yi shi ma, ya janyo ta ya koma kan kujera da ita, a kan cinyarsa ya zaunar da ita, ya saka hannuwanshi ya zagaye 茩ugunta, 茩o茩arin tashi ta yi amma ya 茩i ba ta damar yin hakan.

A hankali ya ce 

"Haba Bab ya ki ke gudana ne? Ni fa mijinki ne, yanzu da ke za a ha蓷a baki a wahalar da ni" ya yi maganar ya na wasa da jigidar da ya ji a 茩ugunta.


Amanar cool ce 鉁嶏笍 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol