Free chapter 路 Read without an account

Chapter 81-82

by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮



_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 81&82 


_________Gabanta ne ya tsananta bugawa a lokacin da ta 茩araso 茩ofar gidansu, tuna halin mahaifinta ya sa lokaci 蓷aya hanjin cikinta suka ka蓷a. Sai a yanzu ne wani irin razani da tsoron arangamar da za ta yi da iyayenta ya 茩ara shigar ta, musamman mahaifinta da yake da mugun tsanani. 


Kasa shiga gidan ta yi, ta tsaya a soron gidan tana rarraba ido kamar wadda ta yi wa Sarki 茩arya, ta da蓷e tsaye a gurin, da ta ga babu Sarki sai Allah, ya sa ta yi 茩unar ba茩in wake ta afka cikin gidan, ciki-ciki ta yi sallama kamar Akuyar da ruwan sama ya yi wa tsinannen duka.

Gidan shiru, da alama salla suke yi, jiki ba 茩wari ta shiga 蓷akin Babarta, ta tatar tana salla, ajiye akwatin ta ta yi ta fita waje alwala ta yi ta zo ta ta da salla. Babar Amina rikicewa ta yi, sallar da take yi ma ba ta san ya ta idar da ita ba, saboda jin muryar Amina da ta yi kamar a mafarki. Jikinta har rawa yake yi ta sallame salla.


"Amina ke ce nake gani ko gizau idona ke yi mini?". Sai da ta gama maganar sannan ta fahimci cewar salla take yi. Zama ta yi tana bin 拼ar ta ta da kallo cike da mamaki.


Bayan Amina ta 茩are sallan, da 茩yar bakinta har rawa yake yi, cikin jin nauyi ta ce "Barka da yini".

Kasa amsawa ta yi sai ma kuka da ta fashe da shi tare fa蓷in "Amina ina ki ka shiga ne tsawon wannan lokacin? Mun nemeki sama da 茩asa mun rasa, ina ki ka je ne? Sace ki aka yi ne?".

Cikin kuka Amina ta ce "Dan Allah Inna ku yi ha茩uri ku yafe mini, wallahi sharrin shai蓷an ne, da kuma sharrin zuciya ya sa na kasa ha茩uri da hukuncin da kuka zartar a gare ni, nabi...." Sai kuma ta kasa 茩arasa maganar saboda kukan da ya ce 茩arfinta.


"Amina saurayi ki ka biya saboda 蓷ai an hanaki aurensa? Amma dai ba ki kyauta wa kanki ba, muma baki kyauta mana ba, kin jawo mana abin fa蓷a a garin nan, sai surutu ake yi akan ki". Gyaran muryar da suka ji ne ya tabbatar musu da mai gidan ne. 

Inna ta ce ''Sai ki shirya amsar da za ki bashi, idan ya tambaye ki, shashashar banza wadda ba ta san abin da ya dace da ita ba".


Ya shigo 蓷akin da sallama, turus ya tsaya jin sautin kukan da ke tashi a 蓷akin, da kuma muryar da ya ji tana yin kukan.


"Muryarwa yi nake ji a 蓷akin nan?". Ya yi tambayar ya na kallon inda Amina ke zaune a takure. Shiru da ya ji anyi mai ne, ya sa shi kuma yin tambayar cikin 蓷aga murya.

"Baba ni ce"

"Kece wa?".

"Amina ce"

"Me ya dawo dake nan gidan?".

Shiru ta yi taka sa magana, cikin tsawa ya ce "Tambayar ki nake, me ki ka dawo yi a gidana?".


Jikinta har tsuma yake yi tsabar firgita ta ce "Dan Allah Baba ka yi ha茩uri, ka yi mini afuwa, wallahi ba a son raina...." Ai bai bari ta 茩arasa maganar ba, ya ce "Rufe mini baki, ba na bu茩atar sake jin komai daga gare ki. Duk abin da ki ka fa蓷awa mahaifiyarki na ji, dan haka ba za ki zauna mini a gida ba, ki tashi maza ki koma inda ki ka fito, ki je can mun yafe masa ke, tunda shi ki ka za蓳a akan".


Kuka sosai take tana bashi ha茩uri, amma ya 茩i ya saurare ta, Inna da ta ga iyakar gaskiyar yake maganar sai ta bar gidan, ya sa ta ce ''Haba Malam ka yi ha茩uri mana, ai baya ru蓳ewa ka yanke shi ka yada. Tunda har Allah ya ganar da ita, ta yi tunanin dawowa gida ai shikenan sai mu ha茩ura mu rungumi 茩addara.." Tsawar da ya buga mata ne ya sa ta yin shiru da bakinta.


Fafur Malam ya murje ido ya fatattaki Amina a gidan, tana kuka mahaifiyarta ma kuka take yi, hankalin ma茩ota ne ya fara dawowa kansu, nan aka fara bashi ha茩uri, amma 茩ememe ya 茩i saurarar kowa, hakan ya sa aka yi saurin sanar da mai gari abin da ke faruwa. Amina na kuka tana sake bashi ha茩uri, ya 茩i kulata ma bari ta saka ran zai ji kukanta, daga 茩arshe ma 茩aton icce ya 蓷auko ya na 茩o茩arin buga mata shi, sai da aka ri茩e shi. Ana cikin haka mai gari ya aiko da dogarawa ya zo yanzu ya na son ganin sa kuma ya zo tare da Aminar. Ji ya yi kamar ya kurma ihu dan babu yadda zai yi ne, dole suka nufi gidan mai gari gaba 蓷ayansu.


Suna zuwa fada, cikin damuwa mai gari ya dubi shi ya ce "Ka bani mamaki, ina hankalin ka? Ina tunanin naka yake? Da har za ka yi wa 拼arka irin wannan tozarcin, kai da ya kamata ka yi wa Allah godiya da dawowarta, ina jin nan fadar ka yi kukan 蓳atan da ta yi, kuma Allah ya dawo da itan za ka kore ta? So ka ke yi ta shiga duniya? Maganar gaskiya ban ji da蓷in abin da ka yi ba".


"Ranka ya da蓷e yarinyar nan fa ba sace ta aka yi ba, da kanta ta bi saurayin nan, to akan me yanzu za ta dawo na kar蓳e ta? Tunda shi ta za蓳a ai sai ta koma gurin sa" . Baban Amina ya yi maganar cike da 蓷acin rai da takaicin abin da 拼ar tasa ta aika ta.


"Koka dai mene ne, bai kamata ka kore ta ba, dan haka ina mai baka ha茩uri da ka barta ta zauna a gidan, tunda har ta yi tunanin dawowa gida, ka 蓷auki hakan a matsayin 茩addara, ina fatan Allah ya huci zuciyarka".


Malam ya ce "Ta ce darajarka, na ha茩ura, sai dai da shara蓷in duk naga wani abin da ban san da shi ba, wallahi ba zan lamunta ba".

Mai gari ya ce "In sha Allah babu komai ma sai alkhairi". Ya dubi Amina ya ce ta tashi ta je gida, godiya ta yi masa sosai, sannan ta tashi a gurin. Nan mai gari da sauran jama'a suka 茩ara rarrashin Malam 蓷in.


Tunda Amina ta dawo, babu abin da ke ha蓷a ta da mahaifinta, baya shiga sabgar ta, ko gaisheshi ta yi baya amsawa, abin ba 茩ara min damunta yake yi ba, gefe 蓷aya ga tunanin Munir da ya addabi zuciyarta. Ga laulayin da take fama da shi, wanda a gidan ba wanda ya san halin da ta ke ciki, hasalima basu san da cewar ta yi aure ba. Dan ba ta fa蓷awa kowa ba, akan babu wanda ke saurarar ta a gidan, gara ma Inna wani lokacin tana 蓷an kulata.


A haka har ta yi sati 蓷aya da dawowa ba mai shiga lamarin ta, sai dai tana lura da yadda Inna ke yawan tsare ta da ido tana kallon ta, har sai ta ji ta tsargo.


Satin Amina biyu da dawowa, ciwon laulayi ya fara kaita kwance, ga rashin Munir dake mugun damunta. Hankalin Inna ya fara tashi, domin ganin hasashenta na neman zama gaskiya, idan ko haka ne da sun shiga uku.


Zama ta yi ta dubi Amina da ke kwance ta ce "Amina me yake damunki kwana biyun nan naga kamar ba daidai ki ke ba? Ba ki da lafiya ne?".

Cikin yanayi na rashin jin da蓷in jiki ta ce "Inna ba na jin da蓷i ne".

"Ba kya jin da蓷i to me yake damunki?".

Kafin ta bawa Inna amsa wani irin amai ya taso mata, tana 茩o茩arin mi茩ewa ta bar 蓷akin, sai dai ina ya riga ya kawo nan ta shiga kwara shi akan ledar dake shinfi蓷e a tsakar 蓷akin. Hankalin Inna ba 茩ara min tashi ya yi ba, nan take ta ri茩a fa蓷ar "Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un, Amina me zan gani? Dan Allah ki ce mini ba gaskiya ba ne, innalillahi wa'inna ilaihim raji'un, innalillahi wa'inna ilaihim raji'un".


A wahalce Amina ta kwanta a gurin tana mayarda numfashi, Inna sai magana take yi mata, amma ta kasa ce mata uffan.

"Amina dan Allah ki yi mini magana, ba dai ciki ne dake ba?".


Hawaye taga suna zuba daga idon 拼ar ta ta

Cikin 茩ullewar ciki Inna ta kuma cewa "Shikenan Amina kin kashe mu, kin janyo maba abin fa蓷a, amma dai ba ki kyauta mana ba, kin cuce mu, kuma kin cuci kan ki". Kuka sosai Inna ke yi, Amina son fa蓷a mata yadda abin yake, sai dai ta kasa magana, sannan ta san ba yarda za a yi da abin da za ta fa蓷a ba 蓷in, saboda ba ta da wata shaida.


Ganin Amina ta kasa 茩wa茩waran motsi, ya sa Inna tashi ta gyara gurin da ta 蓳ata 蓷in, bayan ta gyara ta dawo 蓷akin tana ci gaba da tambayar Amina, amma ta yi mata shiru. A haka Malam ya shigo ya ga Inna na kuka har idonta sun kumbura.


"Lafiya me yake faruwa ne?" Ya yi tambayar ya na kallonta.


"Malam akwai matsala" .


"Wace irin matsala?".


"Malam yarinyar nan fa ciki ne da ita". 


Shiru ya yi ya na duban Amina da ke ta aikin zubar da hawaye.


"Ke abin da ta fa蓷a haka ne?" Ya tambayi Amina, ai da sauri da mi茩e zaune tana fashewa da kuka, ta ce "Eh Baba haka ne, sai dai wallahi ba ta..." Yi mini shiru, wato abin da ki ka aikata kenan shi ya sa ki ka dawo mini gida? To ba a nan gidan ba, ba zan iya ci gaba da kallon ki a cikin gidan ba. Sa'adu ne ya yi sallama, jin muryar wanda ya yi sallamar ne ya sa Inna cewar ya shigo, ya na shiga kallo 蓷aya ya yi wa fuskokinsu ya san cewar akwai damuwa.


"Inna me yake faruwa ne kuma?".


Babu 蓳oyon komai ta fa蓷a masa halin da ake ciki, zaro ido ya yi ya na kallon Amina. Kafin ya yi magana ya ji Baba ya ce "Ki tattara kayanki tun muna sheda juna, ba tare da kowa ya sani ba ki koma inda ki ka fito, wallahi Amina ba za ki zauna mini da cikin shege a cikin gidan nan ba".


Da sauri Sa'adu ya ce "A'a Baba ba za a yi haka ba, dan Allah ka yi ha茩uri kar ka yi mata haka, ka bari abi komai a sannu". "Sa'adu ba fa za ta zauna mini a gida ba, na riga na gama magana".


Ganin haka ya sa Sa'adu cewa "Amina tashi muje gidana ki zauna a can". Da sauri Baba ya ce "Ban yarda ba, ba za ta zauna a gidan ka ba. Sai dai ta je can inda ta 蓷akko abin ta ta rena sa a can".


"A'a Baba, dan Allah ka yi ha茩uri, Amina fa tamu ce ba yadda za mu yi, gaskiya ba zan bari ta koma inda ta fito ba". Daga haka ya saka Amina gaba ya bar gidan da ita, ko kayanta ma bai tsaya 蓷auka ba.

Gidansa ya wuce da ita, matarsa Atika ta kar蓳e ta hannu biyu, aka bata 蓷aki 蓷aya a gidan. Sannan ya koma ya 蓷auko mata kayanta ya kawo. 


Inna ta yi kuka, ta yi ba茩in cikin da abin da Amina ta aikata, bayan kwana biyu sai magana ta fara fita abin da ya 茩ara tunzura zuciyar Malam kenan, ya ji gaba 蓷aya ba ya son ko sunan Amina ya ji.


Munir kuwa ya na can kwata kwata ya manta da wata Amina a rayuwarsa, sai dai ya na jin damuwar rashin wani abu a zuciyarsa, idan Musa ya ya masa zancenta sai ya nuna masa kwata kwata bai san wace ce wannan 蓷in ba. Daga 茩arshe ma ya nuna masa baya son zancen ya daina, Musa abin ya bashi mamaki sosai, to ko dai Hajiya ta raba shi da Amina ne? Amma ai da ya kamata ya fa蓷a masa. Daga nan shima ya tattara zancen ya watsar.


Gari ya fara 蓷aukar Amina ta yi cikin shege, har Babanta ya kore ta daga gidansa, Amina ta shiga 茩uncin rayuwa, tana jin zagin da ake yi mata a garin ga iyayen ta sun yi fushi da ita sosai, sauran danginta ma sun nuna mata tsana 茩arara, gurin Yaya Sa'adu 蓷ai da matarsa take samun sau茩i. Tun tana saka ran ganin Munir har ta ha茩ura ta ci gaba da rainon cikinta.


Kwance tashi babu wuya a gurin Allah, cikin Amina ya isa haihuwa, ranar wata Alhamis Amina ta haiho 蓷anta namiji. Sai dai kaf dangi babu wanda ya zo yi mata barka, abin ya yi mugun 蓳ata mata rai, mahaifiyarta ta so ta zo amma fafur Malam ya hanata, ya ce idan ta je gidan nan da sunan ganin Amina da abin da ta haifa a bakin aurenta. 


Sa'adu ya tambaye ta, sunan da za a saka wa yaron? Ta ce duk sunan da ya ga ya dace. 

Ya ce "Bari a saka masa Aliyu Haidar".


Ta amsa da "To shikenan Allah". Yaya Sa'adu ya yi wa yaro hu蓷uba da suna Aliyu sai suke kiransa da Haidar. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, dangin Amina da iyayenta gaba 蓷aya ba sa shiga harkar ta, ko biki ake yi a gidan Sa'adu idan suka zo ba sa kulata ita da yaronta, hakan ba 茩ara min 茩ular da Amina ya yi ba. Haidar ya taso cikin tsangwama da hantara mutanen gari, ana kiransa da shege, tun abin baya damunsa har ya fara saka abin a ransa, 茩iri-茩iri yara ke tare shi, su yi masa wa茩ar bashi da uba. Ya zo wa Amina ya na kuka, makaranta ma idan ya je basa 茩yale shi, daga 茩arshe ma ya daina fita, kullum ya na gida zaune.

Amina na da burin son Haidar ya yi karatu, dan haka ta samu Yayanta da maganar, nuna mata ya yi indai a cikin garin nan ne Haidar ba zai samu wannan damar ba. Saboda tsangwamar da ake yi masa.

Ta ce "To Yaya babu yadda za a yi ne, ni da akwai wada za a yi sai na bar garin nan da shi, na je can wani gari, na nemi ko da aikin wankaune, shi kuma sai na saka shi makaranta".

Tana cewa haka ya tuna da wani abokinsa dake zama a Katsina amma yanzu ya dawo garin Kano da zama, kuma Malamin makaranta ne.

Kiran sa ya yi bayan sun gaisa ne, ya ce "Abokina dama wani yaro nake da shi, 蓷an 茩anwata ne, nake so ya yi karatu a nan Kano 蓷in, sai dai ban san ya za a yi ba?".


Ya ce "Ai ba damuwa sai na baka address 蓷in gidana ka zo da shi nan 蓷in na ha蓷a shi da yarana ko".


Sa'adu ya ce "Yaron 茩arami ne bai fi shekara hu蓷u zuwa biyar ba".

"Ok ai ba damuwa, ka kawo shi kwai, ai shi ma 蓷in kamar 蓷a yake a gurina. Yawwa Sa'adu dan Allah a garin nan naku ba za ka samo mana wadda za ta ri茩a kula mana da 茩ananun yara a makaranta ba. Duk wata sai mu ri茩a biyanta". 

Ya ce "Anya za a samu a garin nan kuwa? Amma bari na bincika idan an samu zan kira ka" . Sallama suka yi. Ya dubi Amina ya ce "Ai kinji yadda muka yi da shi ko? Me ki ka ce? Kin amince akai shi 蓷in?".


"Eh Yaya na amince, sai dai me zai hana na kar蓳e aikin da na ji suna so a nemomusu wadda za ta yi, kaga zai fi jin da蓷in sakin jiki ya yi karatu idan ya na gani na". 


"To kina ga za ki iya kuwa? Sannan Baba zai yarda da hakan? Ki yi tunani Amina".

"Yaya kaima kasan Baba ba zai haba ba, babu ruwansa da ni ba, kawai amincewarka na ke nema, ai ni yanzu ba ni da kowa a garin sai kai".

"Amina ba na son irin wannan maganar. Duk da haka zan yi wa Baba maganar".


Ya je ya samu Baba dan zancen, sai dai Baba ya yi masa fata-fata ya kore sa, Yaya ya kira abokinsa ya gaya masa an samu wadda za ta yi aikin. Babar yaron ce. Nan suka yi magana ya ce zuwa jibi idan ta shirya sai ta zo. Godiya sosai.


Ya ce "Amina sai ki shirya jibi ki tafi" ba 茩ara min da蓷e Amina ta ji ba, nan take ta 茩udiri aniyar idan ta bar 茩auyen nan ta barshi kenan har abada. Bayan kwana biyu Amina ta shirya, Yaya ya ba ta 茩aramar waya, ya saka mata lambar abokin na sa, idan ta isa ta kira shi. 


Shigar Amina a garin ya tada mata da mugun mikin da ke dan茩are a zuciyarta, sai dai tana addu'ar kar Allah ya ha蓷a ta da ko da wanda ya san Munir ne har 茩arshen rayuwarta, kamar yadda ya manta da ita da cikin jikin sa da ta ke 蓷auke da shi, haka itama ta manta da shi kenan.


Amina ta isa gidan lafiya, washe garin zuwan ta ta fara zuwa makarantar, kuma a ranar aka saka Haidar shi ma, tana jin da蓷e sosai gani Haidar ya fara karatu, sannan tana 茩o茩ari sosai wajan kula da yaran. Sai dai tana fuskantar 茩alubale wajan matan da ta ke zama a gidansu, 茩iri-茩iri suke nuna mata tsana. Tun mai gidan baya fahimta har ya fahimce su. Amina ganin abin na neman zama rigima ya sa ta ce masa za ta bar gidan, ha茩uri ya ba ta.


Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya, Amina tunda ta zo kano kusan shekara 蓷aya kenan ba ta je 茩auye ba. 

Babu za to Kamilu wato abokin Yaya Sa'adu, uzurin barin garin Kano gaba 蓷aya ya kama shi, Amina ba ta jin da蓷in hakan ba, saboda ba ta san inda za ta zauna ba. 

茦o茩ari ya yi ya kama mata gidan haya ya biya mata ku蓷in shekara uku, sannan ya ba ta jari a hannunta ya ce ta samu sana'ar da za ta ri茩a yi, domin rage wasu bu茩atun, sannan ya siya mata abinci mai yawa. Godiya ta yi masa sosai 


Amina ta ci gaba da aikinta na kula da yara a makaranta, sannan kuma tana sana'o'inta, a gida, Alhamdulillah tana samun ciniki. A haka har Haidar ya gama primary ya shiga makarantar gaba da primary. Bata zuwa 茩auye sai dai Sa'adu ya kawo mata ziyara, idan ya zo ya yi ta mitar rashin zuwanta, sai dai ta bashi ha茩uri. 


Haidar ya fara girma, sai yake kiran Amina da Umma, idan ya tambaye ta ina Baban shi sai ta ce masa ya rasu. Sai dai duk zafin da Umma ta 蓷auka da Munir, hakan bai hana saka masa sunan Munir a makaranta ba. Haidar Munir ake kiransa, saboda sanin darajar kiran yaro da sunan mahaifinsa.


Bayan wasu shekaru Haidar ya girma, ya kammala karatunsa, a lokacin Umma ta daina akin da ta ke yi a makarantar, yanzu sana'arta take yi. Haidar bashi da sana'ar yi ganin haka ya sa Yaya Sa'adu da yanzu shi ne Sarkin fada a garinsu, yi wa wani Alhaji magana dake nan Kano 蓷in ya san shi sosai suna mutunci, da ya taimaka ya bawa yaron shi mashin saboda zaman da yake yi na rashin sana'ar. Dama aikin da bawan Allah ke yi kenan na taimakon marasa 茩arfi.


Bayan kwana biyu aka bawa Haidar napep ya fara aiki, ganin Haidar 蓷in na da amana ya sa Alhajin jan Haidar jikinsa, ya na saka shi cikin wasu harkoki nasa.


Sauke ajiyar zuciya Umma ta yi bayan da ta gama tunanin rayuwar ta ta ba, wani 蓷aci take ji a zuciyarta. Abubuwan da suka faru gani take kamar yanzu abin ya faru.


Maryam ganin yanayin da Umma ta shigo gidan ya sa ta yi wa su Afnan sallama ta yi gida. Haidar ya shiga 蓷akin da sallama Afnan na biye da shi. Umma na ganin su ta ce "Haidar ba na bu茩atar kowa a kusa da ni yanzu, ku yi tafiyar ku zanne meku" .


Hannun Afnan ya ri茩e suka bar 蓷akin, ya nufi nasa 蓷akin ri茩e da Afnan 蓷in.



Amanar cool ce鉁嶏笍
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol