Free chapter · Read without an account
Page 1
•••SANADIN MAHAIFINA•••
Wattpad@SaNaz_deeyah
Arewabooks@sanazty
Facebook@Habibtyn Habibi
YouTube: ***
Tiktok: ***
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
GARGAƊI: Ban yarda wani ko wata su ɗauki wannan littafi ko wani ɓangare na littafi su saka a wata kafa ko a canja masa fasali ko a mayar audio ba tare da iznina ba. A kiyaye⚠️
Shafi na 1
*Ƙofar Nassarawa*
Maitama Sule University
Su uku suka fito daga cikin hall ɗin, suna bin steps suna sauka ƙasa. Dukkansu ukun fuskokinsu cike da murmushi, a haka suka sauka ƙasa sannan suka tsaya. Safina ce ta fara rufe fuskarta da handout, sannan ta sauke ta kalli ƴammata biyun da suke tare tace "To yanzu mun fito a cigaba daga inda aka tsaya" Farhan tayi dariya tace "Ni fa bazan sake cewa komai ba dan naga ke da Jannat musu baya ƙare maku, sai dai a sakar maku. Jannat sai a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Ni fa yunwa nakeji, gaskiya mu tafi gida tunda mun gama lectures" "Ai dama aikin kenan ci, acici kawai. Wannan ko bamu gama lecture ba ai dole a samo miki abinci kafin ki sume mana anan" Farhan ta faɗa cikin tsokana.
"Ni dai koma me zaki ce na yarda da ulcer ta kamani gara ace min acici" Duk sukayi dariya.
Asalinsu
Alhaji Mu'azu wani shahararren mai kuɗi ne wanda a duk faɗin Nigeria ake ji dashi, saboda irin dukiyar daya tara da kuma taimakon mararsa ƙarfi da yakeyi. Cikakken ɗan kasuwa ne, wanda ya jiƙu da naira. Mutum ne da baya da ganin ƙyashi, sannan mutum ne mai tsare gida. Matan shi biyu Hajiya Falmata itace uwargida ƴar asalin garin maiduguri ce, aure ne ya kawota Kano, sun haɗu da Alhaji Ma'azu a wani biki na ƴan uwanta da tazo, to daga nan kuma soyayya ta ƙullu tsakaninsu har ta kaisu ga yin aure, Ƴaƴanta biyu Safina da Jannat. Sai Hajiya Bilki ita kuma ƴar asalin kano ce, kuma auren zumunci sukayi da ita, domin ɗiyar yayan babanshi ce, ƴarta ɗaya Farhan. Ƴaƴan Alhaji Ma'azu uku kuma dukkansu mata. Safina itace babba, sannan Jannat sai Farhan da ta kasance itace auta a cikinsu. Tare suka taso kasancewar tsakanin Jannat da Farhan shekara ɗaya ne, ita kuma Safina itace ta bawa Jannat Shekara biyu Farhan kuma uku.Zaman lafiya ne ke wanzuwa a wannan gida,domin yaran ma ɗakinsu ɗaya sai dai kowa da gadonta. Tun Safina na jss2 Alhaji Ma'azu yayiwa Farhan da Jannat Jumping suka dawo tare. Kuma ko bayan da suka gama secondary school sai duk suka nuna cewar sunfi ƙaunar suyi course ɗaya, dan haka dukkansu tare suke a fannin Accountancy. A yanzu haka suna L200 ne.
Cigaban Labari
Tare suka ƙarasa har jikin motar tasu, Safina ce ta shiga driver seat, sai Farhan a gefenta, yayinda Jannat ta koma baya, ta kwanta kan kujera. Hira suke har suka isa gida. Gidansu mantion ne mai masifaffan kyau ya haɗu iya haɗuwa idan kana cikinsa baza kace a kano kake ba. Babu kowa a duka faluka biyu da suka wuce. Ɗakinsu suka nufa kai tsaye. Suna shiga Jannat ta nufi fridge ta buɗe ta ɗauki fresh milk ta kafa a baki. "Uhmmm acici kenan, gaskiya ina tausayin Khalil dan gaba ɗaya sai kin taƙaitashi" Safina ta furta tana cire kayanta. "Shi yaga zai iya ko sis" Farhan ta faɗa tana zama kan gadonta. "Wallahi kuwa faɗa mata dai, kuma shi wannan arziƙi ya masa yawa babu abinda zai ji" Dariya Safina tayi sannan tace "Bari dai na fito daga wanka ki bani labarin wannan Sa'ad ɗin da kika ce ya taimakeki" Ta faɗa lokacin tuni ta ɗora towel ta nufi hanyar bathroom. "Ni yau ma zamu shirya da yamma muje gidan nasu please" "Gaskiya ni dai kin san Assignment ne dani" "Assignment ɗin ba dukkanmu ne ke dashi ba, ni fa bani son wannan iyeyin naki" "Babu wani iyeyi wataƙila ma ni zan maku" "Naji idan bazaki ba, Safina ta rakani" Dariya Farhan tayi tana faɗin "Taɓ Safina ce zata bi ki" "In tayi niyya sai ki hanata ai" Dariya Farhan tayi tana jan ƙatuwar tedy ɗinta.
Suna zaune sai ga ɗaya daga cikin masu aikin ta shigo. Har ƙasa ta tsugunna duk da cewar ta girmesu. "Sannunku da dawowa, dama naji kun shigo tun ɗazu, to sai nace bari na bari ku gama kintsawa sannan in shigo inji shin a kawo abincin nan ko kuma a barshi a dinning?" Kafin Jannat tayi magana har Farhan tace "Wannan wane irin shashanci ne? Ba nace idan kinyi knocking ki tsaya a inda kike har sai mun miki iso, kuma nace idan mun dawo kada kizo side ɗinmu sai munyi kamar awa da dawowa. Da yaushe muka dawo da har zaki zo ki damemu, dalla malama ɓace min da gani" Sunkuyar da kai tayi tare da faɗin "Allah ya huci zuciyarki wallahi da nayi knocking sai dana tsaya" "Mtsw aikin banza." Ta faɗa tare da kwanciya.
Jannat ta miƙe tsaye tare da faɗin "A'a Farhan ba'ayin haka, kinga ki kawo mana abincin nan sai ku jera kan table, ni dama da yunwa na dawo" Tashi tayi ta fita. Jannat ta dawo da kallonta ga Farhan tace "Haba Farhan ta girmemu fa" Cikin tsiwa Farhan ta ce "To ni ina ruwana, matuƙar tana aiki a ƙarƙashinmu dole ne ta girmama mu, kema fa kina wulaƙancin nan dan har kin fini" "Ni bana yiwa ƴan aiki ai" "Amma kina yiwa ƴan gari ko" "Calm down naga duk kin ɗau zafi" A dai-dai lokacin Safina ta fito daga wanka. Jikin ƙaton mirror ɗinsu ta tsaya tana tsane ruwan jikinta kafin tace "Nake ta jiyo hayaniyarku mene ke faruwa?" "Wannan banzar Lami ta shigo mana ɗaki" Farhan ta faɗa rai a ɓace. "Ai bata kama kanta wallahi, shegen gulma wato tazo taga me ake" Jannat ta ajje wayarta tayi, tare da miƙewa ta fita daga ɗakin. Safina ta bita da kallo. "Wane ya taɓota?" "Wai dan na yiwa Lami faɗa shine taji haushi" "Iko sai Allah."
Yamma
Suna zaune su uku a babban falon gidan sai musu suke. Safina na faɗin Ahmad ɗinta yafi Khalil kyau, itama Jannat na faɗin ai Khalil yafi kyau. Farhan kuwa sai dariya take. "Ki daina dariya Farhan ki faɗi gaskiya. Khalil ga kyau ga kuɗi ga iya soyayya" Farhan tayi dariya tace "Ga kuma tsokana ba, Yaya Khalil ba dai tsokana ba, shi kuma Yaya Ahmad matsalar baya da fara'a shiyasa kyaunsa bai fitowa" Safina ta wulla mata cushion tace "Oh kawai cewa zakiyi Ahmad kike kushewa, to ta ina zai sakar muku fuska ku renashi" "To ai Khalil shi ya kamata yaƙi sakin fuska ma, domin shi ɗan uwa ne idan ya saki fuska zamu renashi, amma kuma still ya saki ranshi kuma babu wani raini tsakaninmu" "To naji a wuce wannan maganar, Farhan meyasa bazaki fito da miji ba kema ai bikinmu gaba ɗaya?" "Safina yanzu idan na fidda miji inyi ya ya da karatu? Ni fa bazan iya haɗa biyu ba,kin sanni dai akan boko" "Alhuda huda ba. To muma ai tare muke amma kuma gashi zamuyi auren, yanzu nan da wata biyu fa duk muna ɗakin miji, ke kuma kina nan ko?" "Eh mana a barmin mota sai yadda naga dama da ita. Amma fa zanyi missing ɗinku, musamman Jannat sarkin musu" "Kanki akeji monga park." Dukkansu dariya sukayi. Safina ta gyara zama tace "Jannat waye Sa'ad ɗin nan?" Itama gyara zaman tayi sannan tace "Wani bawan Allah ne daya taimakeni wallahi, ina ranar da nace muku ina da test a school wadda nayi missing Shu'aib zaiyi min" "Inajinki?" Safina ta faɗa tana kallonta "Wallahi tsautsayi kawai na tafi a napep, muna cikin tafiya ruwa ya ɓalle, kinsan napep ba ƙofa haka ruwa yayi min duka duk da a cikin napep nake, material ɗin jikina nylon gaba ɗaya ya kwanta min, ina sauka fa har zan shiga school kawai yayi min magana, yace inje gidansu a bani hijab in saka bai kamata in shiga school a haka ba, nayi masa godiya na bishi gidan nasu, wallahi muna shiga ruwa ya ƙara zugewa, kinsan mutumcin da suka min? aka bani kayan ƙanwarshi na saka, sannan mamanshi da kanta ta matse kayana ta shanya, shi da ƙanwar tashi suka rakoni school abin haushinma lecturer'n bai zo ba, wallahi cewa sukayi ba damuwa in tafi da kayan kuma suka saka min nawa a leda sai dana dawo sai washe gari na mayar masu" "Okay nasan ranar inajin last week ne, lokacin Safina kin je shopping ta dawo" Farhan tayi maganar. Jannat ta cigaba da faɗin "To kunga kuwa duk wanda yayi maka wannan halaccin ai bazaka manta ba" Dariya Farhan tayi kafin ta sake cewa "Yanzu ɗan wannan abin ne zaki wani ɗauka babba" "Farhan ke kike ganin sa a ɗan amma ni a babban na ɗauka" "Gaskiya kam yayi mutumci sosai kar a fara musu" Dariya Jannat tayi kafin tace "Ku dai kun liƙan abu" "Sanin hali mukayi ai" "Kefa baki da kunya" "Oh kaji babba" "Eh faɗi ki ƙara,ni dai anjima zaku rakani ko?" "Ni dai ina da Assignment" "Safina zaki rakani?" "Rakiyar ƙanwa?" "To shikenan ko bakuje ba ni zanje ai" ta faɗa tare da miƙewa tayi side ɗinsu. Dariya suka bita dashi.
Tana shiga ɗaki ta cigaba da game a wayarta. Biyar dai-dai ta tashi ta ƙara gyara fuskarta sannan ta canza kaya. Doguwar riga ta saka maroon color. As usual ta ɗauki ƙaramin mayafi black tayi rolling sannan ta feshe jikinta da turare. Tana ƙoƙarin saka takalmi Safina ta turo ƙofar ta shigo. "Sai yanzu zaki fita?" "Eh naso na fita tun ɗazu sai kuma game ya ɗauke min hankali" Lokacin ta ɗauki jaka tana shirin fita. "Ga key ɗin mota." Safina ta miƙa mata, karɓa tayi tana ƙoƙarin wucewa Safina tace "Allah yasa dai baki fushi damu" Juyowa tayi tana smiling ta ce "Haba Aunty fushi dai? Allah kiyaye, aini bani fushi daku, Ina Farhan tayi?" "Tana side ɗin Ummu(Wato mahaifiyarta) Jannat ni kuwa kin haɗu da Mommy yau?" "Bamu haɗu ba, amma idan na dawo zanje mu gaisa" "To shikenan a dawo lafiya" "Allah yasa" ta faɗa lokacin tuni ta kai bakin ƙofa.
Tana fita falo ta tarar da Mommy a zaune tana yiwa ɗayan daga cikin ma'aikatan bayani. Da sauri Jannat ta ƙarasa gurin tare da zama ta ɗanyi hugging Mommyn sannan tace "Mommy baki nemana yau throughout ban saka ki a idanuna ba" tayi maganar cikin shagwaɓa."
Mommy ta kalleta cikin so da ƙauna tace "Ɗazu nake tambayar Safina kina ina tace kina ɗaki wai fushi kike" "Haba dai wallahi babu fushin da nake, kawai game ne ya ɗauke min hankalina. Sai da Mommy ta sallami Hajjo mai aiki sannan tace "Jannat ina zuwa naga kamar kin fito da shirin fita?" "Wallahi kuwa zanje gidan su Sa'ad ne" Kallon agogon hannunta tayi kafin tace "Gaskiya da kin haƙura sai zuwa gobe, kin ga sai ki tafi ma Mamansu da anko na iyaye" "To amma Mommy ai yayi tsadar da bazasu iya ba, na ƴammata ma cewa nayi zanyiwa ƙanwarsa. Kinga basu san da bikin ba, so nake sai na kai masu anko tare da I.V, to shi Khalil har yanzu bai kawo min ba, amma dai yace zuwa jibi zai kawo" "To ki dai haƙura da fita yau, domin magriba tayi, kuma naji Safina na cewa bayan magrib za'a kayo I.V ɗinta da kuɗin party, kinga dole ku zaku tsaya keda Farhan ku karɓa" "A'a Mommy sai dai ta kira Sakna ai itace ƙawarta sai su haɗu da Farhan su karɓa, nima fa Khalil yace zai zo" "To shikenan sai a kira Sakna" "Mommy bara naje na cire kayan tunda na fasa fita." "To shikenan."
******
Hannatu na tsakar gida tana wanki sai ga Sa'ad ɗin ya shigo hannunsa ɗauke da ƙatuwar leda baƙa. "Yaya sannu da zuwa." ta furta tare da karɓar ledar hannunshi, shi kam da "Yawwa" ya bita. Har ɗaki ta kai, Umma na kan abin sallah tana jan carbi bayan ta idar da sallar magrib. Zama sukayi har ta idar sannan suka shafa tare. "Sa'ad har ka dawo daga kasuwar?" "Eh Umma na dawo" ya faɗa tare da ajje mata ledar. "Umma atamfofine na sayowa Jannat zan kai mata" Ɗan murmushi tayi sannan tace "To Allah ya tabbatar mana da alkhairi, sai dai har yanzu ɗan nawa matsoraci ne" Hannatu tayi dariya tace "Wallahi Umma nace ni ya barni na faɗa mata amma yaƙi yarda." "Umma yanzu dan Allah sai aje kawai a samu Jannat ace ina sonta" Umma ce tace "Amma Sa'ad dan me bazaka faɗa mata kana son ta ba?" "Umma ina tunanin kar na faɗa tace bata sona" "Amma kuma ai gara ka faɗa ɗin, meyasa zaka bar sonta a ranka, ka bayyana mata, idan tana sonka shikenan idan kuma bata sonka sai ka fidda ita a ranka" Ɗan sosa kai yayi. Hannatu ta sake cewa "Kuma wallahi itama a yadda na lura tana son shi fa" Umma ma ta ƙara da cewa "Ina so ace Jannat ta zama suraka ta domin tana da tarbiyya, hankali da kuma nutsuwa." "Umma insha Allahu zanyi ƙoƙarin bayyana mata yadda nake ƙaunarta da kuma yadda muke son zamanta tare da mu, Ina fatan Allah yasa ta amince" "Amin ya rabbi" "Zanje gidan nasu da anyi sallar isha'i" "To Allah ya taimaka."
*******
Jannat na zaune a falon baƙi ita da Khalil suna zance, wanda rabin hirar duk akan yadda zasu tsara bikinsu. Shigowar Farhan ne ya saka sukayi shiru. "To kizo ga Sa'ad nan yazo" "Yana ina?" "Yana waje" "Kice ya shigo sai su gaisa da Khalil ma" "To shikenan" Bata daɗe da fita ba sai ga Sa'ad ɗin ya shigo. Cikin jindaɗin tace "Sa'ad zauna mana, ɗazu naso zuwa sai yamma tayi" Zama yayi jikinsa a sanyaye dan yadda yaga Jannat suna hira da Khalil babu shakka saurayinta ne. "Ina yini ya gida yasu Mama?" "Suna gaida ki" "Wai ina Hannatu wato bazata zo gidanmu ba, fushi nake da ita ka faɗa mata indai bata zo ba, to ko naje bazan kulata ba" Murmushin yaƙe kawai yake. Kallon Fancy bags ɗin dake gefe yayi kusan guda shidda ne, duk da chocolates wasu kuwa yaga atamfofine masu kyau ɗayar kuwa laces. Kada ka bada naka domin ko ka bata babu abinda zataji dan tafi ƙarfin atamfar dubu uku. wata zuciyar tashi ce ke faɗa masa hakan. "Khalil wannan shine Sa'ad wanda na faɗa maka ya taimakeni" Sa'ad ya tsinkayi muryar Jannat. Khalil kuwa cewa yayi "Mungode sosai Sa'ad Allah ya saka" "Amin..." yace sannan ya miƙe "Jannat zan tafi sai da safe" "Tun yanzu nayi tunanin kazo muyi hira ne" "To ai kina tare da baƙo kinga kada na takura maku" Kallon Khalil tayi tace "Zan taka masa, yanzu zan dawo" "Okay" shine abinda ya faɗa yana cigaba da danna wayanshi. Suna fita farfajir gidan Sa'ad ya kalleta yace "To Jannat ki koma kada ki barshi shi kaɗai, ni zan wuce gida" "Nagode sosai da wannan ziyarar ka faɗa wa Mama zanzo jibi in Allah ya kaimu" "To Allah ya nuna mana" "Amin ya rabbi."
*****
Kayan bacci Farhan ta saka sannan ta koma kan gadon Safina suka cigaba da haɗa I.V da kuma ware mutanen da za'a bawa. Jannat ta turo ƙofar ta shigo hannunta ɗauke da bowl cike da kankana da madara a ciki. "Kada a manta a ajje min na ƙawayena" "Kinji ki, wallahi ba zamu baki gate pass ba, Farhan da Sakna zasu riƙe" "Taɓɗijan,To ni kuma babu ƙawata ko ɗaya,salon in sunzo a hanasu shiga" "Kinga mu fa I.V muke haɗawa yanzu muna fidda mutanen daya dace a bawa,gate pass kuma ai sai biki ya matso sosai sannan" "Zama tayi gefen Farhan sannan tace "Gaskiya Safina ni fa bazan iya yawon rabon I.V ba,sannan kuma inyi na gate pass" "To ai shine aka ce za'a bamu domin mun san wanda zamu bawa idan lokaci yayi ko?" "A'a ni kam baku san ƙawayena ba dan haka nima na wakilta Jidda ku bata guda hamsin ta riƙe" Dariya Safina tayi sannan tace "Idan ma kika ce ɗari kike so ai sai a bata ɗin" "Ƙawayen nata da basu wuce goma" Farhan ta faɗa tana dariya."Eh naji ai dai yafi taron yuyuyu" Duk sukayi dariya.
Ta ɓangaren Sa'ad kuwa yana zuwa ya faɗawa Umma yadda sukayi da Jannat. Umma faɗa tayi masa kuma tace idan har bai faɗa mata ba to zata fara fushi dashi. "Yaya wai mene a ciki dan ka faɗa mata? Wataƙila ma jira take ka faɗa domin ai ita bazata taɓa cewa tana sonka ba, a matsayinta na mace" Umma ta ɗora da faɗin "Kuma ma banda abin Sa'ad kawai dan ka ganta da wani sai aka ce maka saurayinta ne?" "Umma a yadda naga suna hira jikina ya bani hakan, kuma daga ganinsa ɗan masu hali ne" "To sai me a ciki? Idan ma saurayin nata ne ai ba aibu bane, dan mace kamar Jannat ai baza'a rabata da samari ba, sai dai kawai muce mai rabo ne zai ɗauka" "Umma kinsan ƴaƴan masu kuɗin nan basu auren talaka, yanzu ba'a wannan soyayyar" "Sarewar da kake shine ke ƙara ɓata min rai, na faɗa maka ka jarraba" "Shikenan, zatazo jibi in Allah ya kaimu, idan tazo kafin ta bar gidan nan zan bayyana mata abinda ke raina" "Allah yasa ka iya" Kallon Hannatu yayi yace "Ke....! Yaushe na fara wasa dake" "Allah ya baka haƙuri" ƙwafa kawai yayi, sannan yayiwa Umma sai da safe ya nufi ɗakinshi.
Juyi yake tayi kan katifarsa amma sam ya kasa bacci, ya akai son ta ya shigesa sosai haka? Mene dalilin dayasa ya fara son ɗiyar masu kuɗi kamar Jannat. Sauro sai cizonsa yake, ga dai magani ya saka amma kamar bai saka ba. Anya Jannat zata iya sona kuwa? Zata iya rayuwa cikin talauci kamar yadda mukeyi?. tashi yayi zaune yana ɗan sosa hannun da sauro ya cije.
Ni fa ko, ban damu da dukiya ba, shiyasa bana nuna ni ƴar wani ce, domin zan iya rayuwa a duk inda na tsinci kaina, dan haka ka daina min kallon ɗiyar masu kuɗi. Furucin Jannat ya tuna a lokacin daya fara sanin waye mahaifinta.
"Tabbas zata soni, ko ma ince tana sona" shine abinda ya faɗa a fili yana smiling cike da jindaɗi. A haka dai ya kwanta yana ta tunanin irin rayuwar da zasuyi da Jannat idan ta kasance mata a gareshi. A haka har bacci ya sace shi.
Bayan kwana biyu
Jannat ɗin na zaune a kan tabarmar dake shimfiɗe a falon Umma. Hira suke taɓawa sama-sama da Hannatu yayin da Umma ta kan saka baki amma ba sosai ba.
Sa'ad yayi sallama ya shigo. Suka amsa "Ashe ma kana kusa" Jannat ta faɗa tana kallonshi "A'a ina kasuwa kika kirani shine kawai na hayo napep na dawo" "Amma banji daɗi ba na taso ka kana aiki" "A'a kada ki damu" Ɗan murmushi tayi tana faɗin "Ina nan ina ma Hannatu faɗa taƙi zuwa" "Ai gara dai kiyi mata bata son zumunci" Umma ta faɗa. "Sa'ad a samo mata ruwa ko?" "To Umma..." Har ya miƙe Jannat tayi saurin cewa "Laaaa Mama wallahi na ƙoshi na gode sauri nake ma" Janyo ledar gefenta tayi ta fito da kayan ciki ta kalli Umma tace "Mama dama ankon bikina na kawo muku" Umma da Sa'ad suka haɗa ido ko wanne sai dayaji bugun zuciya.
SaNaz is back, hope littafin ya bada citta? Da zafi-zafi nazo, littafin nan gaba ɗayanshi free book ne, comments nake biɗa, sannan duk wanda ya gani ya tayani yaɗawa, fatan zai samu karɓuwa, idan ina samun comments sosai to posting zai ƙaru.
SaNaz Ce✌️