Free chapter · Read without an account
Page 3
•••SANADIN MAHAIFINA•••
Wattpad@SaNaz_deeyah
Arewabooks@sanazty
Facebook@Habibtyn Habibi
YouTube: ***
Tiktok: ***
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
```Shafi na 3```
Tun ƙarfe 10 na safe ta gama shiryawa cikin wata atamfarta exculusive holland, red color, sannan ta ya fa gyalenta red, ta ɗauki pause. Duk da cewan light makeup tayi amma tayi kyau sosai kasancewarta kyakykyawa fatarta mai kyau da sheƙi, kuma komai ta saka yana mata kyau.
Farhan dake rubutu a jotter, ɗagowa tayi tana kallonta kawai. Safina kuwa tana kan gado a kwance tana waya da Ahmad ɗinta.
"Safina ki bani key zan fita" Jannat tayi magana tana kallon Safina.
"Yau fa bamu da lecture wai ina zakije?" Farhan ta jefo mata tambayar. "Zanje gidan su Sa'ad. Safina ki bani key please mana, sauri nake" "Excuse me, i will call later, zanyi magana da Jannat" tana faɗa ta katse. "Me zakiyi a gidan su Sa'ad?" "Safina zan miki bayani idan na dawo please sauri nake"
"Wai ba jiya kuka je ba?" Farhan ta sake magana. "Mtsww i dont have ur time, ina ruwanki" "Uhmm babu kam, ai ni kin saba gwasileni" Dariya tayi tare da girgiza kai. Safina kuwa janyo side drawer tayi ta miƙa mata key.
"Thanks you sai na dawo"
"Inzo inyi rakiya?" Farhan ta faɗa cikin tsokana. "Ba buƙata" "Nima dama ba zuwa zanyi ba dan inji me zaki ce ne" "Yanzu ai kinji" tana faɗa ta fice. Safina ta kalli Farhan tace "Ke dai Allah shiryeki da tsokana" "Gaskiya zanyi missing Jannat idan kukayi aure ko dan tsokana" ta faɗa tana cigaba da abinda take. Itama Safina girgiza kai tayi tana murmushi.
******
A ƙofar gidansu Sa'ad tayi parking mota. Da sauri ta fita ta ƙarasa cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama. Hannatu dake shara ta ɗago kai ta kalleta. "A'ah Jannat kece? Sannu da zuwa" "Yawwa Hannatu. Kawo na tayaki" Dariya tayi, tare da faɗin "Ah haba dai ki barshi ma"
"Umma na nan kuwa?" "A'a ta ɗan fita nan maƙota anyi haihuwa, amma yanzu zata dawo,Yaya yana ciki ki shiga"
"To" ta furta tare da wucewa cikin parlon.
A zaune ta ganshi ya luna duniyar tunani bai ma san ta shigo ba. Zama tayi ɗan nesa dashi sannan tayi gyaran murya. Aikuwa da sauri ya ɗago ya kalleta. Ɗan murmushi yayi wanda bai kai har zuci ba. "Jannat yaushe kikazo?" "Lokacin daka lula duniyar tunani mana. Ai dama na san tabbas kana da damuwa amma kake ɓoyemin"
"Tayaya kika san ina da damuwa?" "Saboda nima na damu da kai. Yanzu dai ba wannan ba, wacece wannan yarinyar? Ni ka faɗa min zanje na sameta" Ta tambaya tana kallon cikin idanunsa.
Duk sanda ta ƙara tambayar ka wacece to ka faɗa mata itace kake so, idan har tana sonka dole ta haƙura da wancan auren ta aureka, idan kuma baka faɗa ba zan ɗauki fushi da kai tunda kana nema so ya halaka ka. ya tuna furucin Umma a daren jiya.
"Sa'ad nima ka sakani a damuwa dan Allah ka faɗa min wai wacece wannan"
"Kece....!" kawai suka ji an faɗa. Dukkansu suka juya suna kallonta. Shigowa tayi ɗakin ta ajje tsintsiyar a gefe sannan ta zauna tare da dafa cinyar Jannat.
"Hanne mene ya shigo dake ɗakin nan? Tashi ki fita" ya faɗa cikin tsawa.
Ita kuwa Hannatu cewa tayi "Wallahi bazan bari ka salwantar da rayuwarka ba dan haka sai na faɗa mata"
Tasowa yayi da niyyar ya doketa, Jannat ta ɗaga masa hannu. "A'a Sa'ad tunda kai ka ƙi faɗa ka bari ta faɗa min" Jannat ta faɗa cikin sanyin murya.
"Duk abinda zai fito daga bakinta ƙarya ne, kada ki saurareta" Ya faɗa yana mai lafewa jikin bango kamar wani ƙadangare.
"Naji! Ina jinki Hannatu"
"Jannat kece Yaya yake so, kuma wallahi ya fara sonki tun ranar daya fara ganinki, sai dai kasancewarki ƴar masu kuɗi shiyasa ya kasa faɗa miki yayi ta dakon soyayyarki. Har abin ya kai shi ga kwanciya a asibiti. Umma tayi faɗa sosai domin dukkanmu muna sonki, tace lallai ya sameki ya faɗa miki. Ranar da yaje zai faɗa miki ya ganki da wani sai ya kasa faɗa, anan ma ya sha faɗan Umma, sai yace idan kinzo zai faɗa miki to zuwan da kikayi kuma sai gashi kin kawo mana I.V na bikin ki. Gaskiya Yaya yana cikin wani hali kuma komai zai iya faruwa" tana faɗa ta tashi da sauri ta fita gudun kar ya doketa.
Shiru tayi haka shima. Ɗakin tamkar babu mutane kusan minti biyu sannan ta ɗago kai ta kalleshi.
Ga mamakinta kawai taga hawaye a idanunsa. Ta miƙe tsaye a hankali ta ƙarasa kusa dashi.
"Kenan abinda ta faɗa gaskiya ne?" bai ɗago ya kalleta. Dafe goshi tayi tare da girgiza kai. "Kai fa namiji ne, ya nake ganin hawaye a idanunka?" Hannu ya sa ya goge har lokacin yaƙi ya kalleta.
"Wannan kaɗai ya isa ya gaskata min da cewa lallai abinda Hannatu ta faɗa gaskiya ne"
"Wannan hawayen na rashinki ne Jannat, na san bazan taɓa samunki ba, masu kuɗi bazasu taɓa bar mana kyawawa masu kyawawan halaye irin ki. Jannat na san nayi babban rashi. Na fara sonki ne duk da na san bazaki iya auren talaka kamar ni ba, wanda baya da wani tsayayyen aiki sai buga-buga"
Sai lokacin kuka ya kubce mata. Ta kalleshi tace "Waya faɗa maka haka? Ni ban taɓa zaɓi akan mijin aure ba ko talaka ko mai kuɗi ni dai fatana kawai in samu nagari. Kuma kai shaida ne kasan kuɗi basu gabana, meyasa baka faɗa min kana sona tun ranar da muka haɗu? da ban bari zuciyarka ta saba da tawa ba dan tun lokacin da muka haɗu akwai baiko a kaina na Khalil. Wallahi Sa'ad ban san kana sona ba da ban bari kayi nisa haka ba"
"Kada ki damu ba laifinki bane tunda ke baki sani ba"
"Ya ilahi" ta faɗa tare da zama kan tsohon carpet ɗin dake shimfiɗe a tsakar ɗakin.
Ta daɗe kanta a sunkuye, hannunta riƙe da goshinta.
Sallamar Umma ce ta saka suka ɗago tare. "Dan Allah karki nuna damuwa Jannat" ya faɗa yana kallonta.
Da sauri ta goge hawayen idonta tana gyaɗa kai.
Umma na shigowa ya fara faɗin "To shikenan Jannat insha Allahu zanyi ƙoƙarin kawo miki shi kafin ranar kamun" Ya faɗa yana murmushin yaƙe.
Sai kuma ya ɗaga kai yace "Umma kin dawo? sannu da zuwa"
"Yawwa. Jannat ashe kinzo ai da kin aika an kirani"
Jannat da ta saki baki tana kallon Sa'ad sai lokacin ta ɗago ta kalli Umma. "Umma ina yini? Ai ance min ba daɗewa zakiyi ba" ta faɗa itama tana murmushin da iyakacin shi leɓe.
"Sannu da zuwa. Ya ba'a kawo mata ruwa ba ina Hannatun"
"Ba ta tsakar gida?" Sa'ad ya tambaya..
"Ba ta nan" Ita dai Jannat kanta na ƙasa har lokacin zuciyarta zafi take.
"Bara na kawo miki ruwa Jannat"
"A'a Umma tafiya zanyi ma, dama kawai nazo mu ƙara gaisawa ne" ta faɗa tana miƙewa. "Wato yanzu dai baki son cin abu na gidan nan"
"Laaa ba haka bane Umma zanci next time idan na dawo" tana faɗa ta buɗe labule ta fita.
"Ka rakata mana" Umma ta faɗa tana kallonshi.
"Umma barta kawai." ya faɗa cike da damuwa.
Ganin haka ne ya saka ta zauna gefensa tare da faɗin "Ya kukayi da ita?"
Ta ɓangaren Jannat kuwa tana fita taci karo da Hannatu zata shigo. "A'ah ba dai tafiya ba?"
"Eh wallahi ana jira na ne"
"To ki gaida gida" bata samu damar bata amsa ba ta wuce ita kuma ta shige ciki.
Tafi minti biyar a tsaye tana jira ya fito amma shiru. Ganin haka ne ya saka ta tabbatar da bazai fito ba, dan haka ta shiga mota ta figeta da gudu.
*****
"Lallai yarinyar nan bata da mutumci kenan bazata iya aurenka ba? Bata ga halin da kake ciki ba" Umma ta faɗa cikin faɗa.
"Umma taya zata ajje aure lokaci guda kuma har an gama komai, gaskiya ni dama na san abu ne mai wuya, kawai na faɗa mata ne saboda naga ta damu tasan meke damun Yaya" Hannatu ta faɗa a sanyaye.
"Dalla gafara shashasha kawai, ke me kika sani? Da yaushe kika zo duniyar?" Umma ta faɗa sannan ta juya kan Sa'ad "Ka fita a harkarta kuma ka fidda ta a ranka ba kai ba ita bikin nata ma bazamu je ba. Wallahi duk yadda ake cewa masu kuɗi basu da mutumci, ban san abin haka yake ba sai yau. Lallai Jannat ta bani mamaki"
"Umma karki ce haka dan Allah, ita bata da laifi, kuma kamar yadda Hanne ta faɗa dama abu ne mai wuya ace Jannat ta ajje soyayyar da ta daɗe tana ginawa kuma fa har an kusa bikinta sati biyu kacal bai ma ƙarasa ba. Ko da tace zata aureni iyayenta bazasu yarda ba"
"Sa'ad bana son maganar banza. Ban san maloho na haifa ba sai yau. Ƴaƴan masu kuɗi nawa ne aka zo ɗaurin auren su suka ce basu so kuma aka fasa ɗin. Ita dai bata da mutumci kuma da kun faɗa min wallahi da tun kafin ta tafi zan mata raddi"
Ganin Umma na ta faɗa ya saka duk sukayi shiru. Cikin ɓacin rai ta janyo waya tace bara na kirata. "Umma dan Allah kiyi haƙuri" "To ubana sai ka hanani kiran" ta faɗa rai a ɓace. Hannatu ce ta masa nuni da yayi shiru.
Ta ɓangaren Jannat kuwa tana yin parking taga kiran Umma ya shigo. Gabanta ya faɗi dan ta ɗauka wani abu ne ya samu Sa'ad. Da sauri ta fita ta kulle motar ta nufi cikin gidan a dai-dai lokacin kira ya ƙara shigowa bata ɗaga ba har sai da shiga ɗakinsu. Farhan na kwance tana barci ita kuma Safina tana jikin mirror tana gyaran gashi.
"Kin dawo"
"Eh..." ta faɗa tare da zubewa kan gado. A lokacin kira na huɗu ya sake shigowa. Kallon wayar tayi ta kasa ɗagawa.
"Daddy yace yana neman mu da yamma" Safina ta faɗa. Bata amsa ba, kawai ta ɗaga kiran tare da karawa a kunne.
"Munafukar yarinya dole ki ƙi ɗaga kirana" shine abinda taji Umma ta faɗa.
Miƙewa tsaye tayi gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba.
"Umma...."
"kada ki ƙara ce min Umma dan ni ba uwarki bace ko nina haifeki?" jin haka ne ya sa hawaye masu zafi sauka kan kuncinta.
Safina kuwa cewa tayi "lafiya?"
Da hannu Jannat tayi mata nuni alamun tazo. Tasowa tayi ta ƙaraso Jannat ta saka wayar a handsfree dai-dai lokacin Umma ke faɗin "Jannat kin cucemu kin shigo rayuwarmu kin ruguzata, kin san mu talakawa ne shiyasa kikayi amfani da talaucinmu kika shiga rayuwarmu dan ki ruguza."
"Umma ni wa....."
"Na faɗa miki ki daina kirana da wannan sunan tunda bani da daraja a idonki" Farhan ta miƙe tana kallonsu daga inda ta ke zaune kan gadonta.
"Sai da kika saka masa sonki a zuciyarshi sannan zaki ce wai an miki miji, baki da tausayi da imani, Allah ya isa tsakaninmu dake Jannat, kuma bikinki bazaki ganmu ba kizo ki ɗauki kayan da kika kawo idan ma baki ɗauka ba zamu aiko miki amma ba dai ki ganmu ba sai dai wasu. Kuma duk abinda ya samu ɗana tabbas kece" bata bawa Jannat damar furta ko da sentence ɗaya ne haka ta katse wayar.
Jannat ta ɗora kanta a kafaɗar Safina ta fashe da kuka. Da sauri Farhan ta taso tana tambayar wace ce?.
"Maman Sa'ad" "Taɓɗijam shine take faɗin maganganu haka, su fa talakawan nan basu iya samun guri ba, ki bani number ɗin mayar mata da raddi"
Safina tayi saurin cewa "A'a kefa Farhan baki da kai wani zubin, duk wanda ya girmeka ya girmeka, zafin zuciya ne ya saka ta faɗi haka kuma ko ita Jannat ai bazata so hakan ba"
"Ni fa shiyasa bani son raɓar talaka domin wallahi basu san halacci ba, ga baƙaƙen magana kamar a bakinsu aka halitta"
Sai lokacin Jannat ta ɗago cikin kuka tace "Safina wallahi ban taɓa sanin yana sona ba da na faɗa masa an min miji, ke kanki kin sani bani da son kai, ban san yana sona ba sai yau" ta ƙara fashewa da kuka. Safina da Farhan zama sukayi suna ta bata haƙuri.
Ta ɓangaren Umma kuwa tana katse kiran taja dogon tsaki.
Hannatu kuwa ta riƙe baki tana mamakin irin baƙaƙen kalaman da Umma ta faɗawa Jannat, lallai ta ɗau zafi shiyasa ta manta kirki irin na Jannat.
Sa'ad kuwa tashi yayi ransa a ɓace yana ƙoƙarin fita yaji Umma tace "Idan kuma kaje gidan su Allah ya isa.....!" Maganar ta girgirza shi sosai. Ya tsaya cak ya kasa motsawa daga inda yake.
"Kaji na faɗa maka, kuma anjima zaka rakani da yamma gidan nasu zan je in nayar mata da kayan da ta bamu bama so"
Jikinsa a sanyaye ya juyo ya kalli Umma tare da faɗin "Umma dan Allah kiyiwa Jannat kyakykyawan zato please"
"Bazan mata ba, Sa'ad ka fice ka bar gurin nan kafin raina ya ɓaci. Bana son maganar banza" bai ƙara cewa komai ba ya fita ya bar gidan.
Kallon Hannatu tayi tace "Ke kuma meye kika ƙura min idanu kamar yau kika fara ganina?"
Sauke ƙwayar idonta tayi ƙasa ba tare da cewa komai ba.
******
03:15pm
Tana kwance kan gadonta tayi lamo. Ta lula duniyar tunani, mamakin irin munanan kalaman da Umma tayi mata take. Da ta san yadda ta ɗauke su, da bata mata wannan wulaƙancin ba.
Jin ana knocking ya saka ta ɗago kai ta goge hawaye tare da cewa "shigo"
Ɗaya daga cikin masu aikinsu ta shigo ɗakin ta tsugunna har ƙasa.
"Salame ya dai?" "Dama kinyi baƙi ne shine Hajiya tace na kiraki"
"Suna ina?" "Suna ƙaramin falo." "To kice gani nan zuwa"
Salame ta miƙe ta fita ita kuwa ƙara goge fuska tayi, sannan ta zura hula a kanta ta fita.
Ganin Umma zaune ya saka ta jin faɗuwar gaba. Hannatu na gefen Umma da alamun damuwa a tattare da ita.
Jannat kallon Mommy tayi tace "Mommy gani..." "Baƙi ne kika yi gasu nan" ta nuna su Umma.
Jannat kuwa sai da ta haɗiyi yawu sannan ta zauna zuciyarta sai duka take da sauri.
"Ina yini..." ta furta lokacin data zauna. Tsaki Umma taja sannan ta kalli Hanne tace "Bani ledar nan" miƙawa mata tayi ta taso ta direta akan cinyar Jannat "Ga tsiyarki nan bamu so, kuma har in mutu ina miki Allah ya isa, domin mun daɗe bamu shiga matsala ba in ba ta talauci ba, sai da kika shigo rayuwarmu"
Kuka Jannat ta fashe dashi. Mommy ta fara tambayar lafiya. "Mommy Maman Sa'ad ce" Jannat ta faɗa tana goge hawayen da basu bar zuba ba.
"To mene ya faru ne haka, da har kuka mai do kaya? Jannat tana sonku kullum maganarku take. Idan wani laifi tayi ku faɗa min sai a sasanta"
Hannatu ma hawaye take yayinda Umma ta fara magana cikin faɗa "Ashe yarinyar nan ta san an mata miji, amma ta fara soyayya da ɗana. Yanzu gashi can kwance ciwon shi ya tashi, ta saka masa ciwo wallahi bamu yafe ba, kin san ba aurenshi zaki yi ba amma kika fara sonshi"
"Jannat ya akai haka?" Mommy ta faɗa tana kallonta, ita kuwa kuka kawai take.
"Dan Allah ku zauna mu warware matsalar" Mommy tayi maganar cikin roƙo.
"Bazan zauna ba. Tunda ba maganin matsalar zakuyi ba, sai dai ku bamu haƙuri, ai dama ku masu kuɗi haka kuke baku da amana, ku da Allah"
Tana gama faɗa taja hannun Hannatu suka fita.
Mommy juyowa tayi ta kalli Jannat ranta a ɓace. Jannat kuwa ta kasa cewa komai sai hawaye kawai take. Hannunta Mommy ta fuzga tana cewa "Bara muje ai Mahaifinku na nan sai kiyi masa bayani" Jin haka yasa Jannat ta fara ƙoƙarin zamewa tana kuka tana faɗin ta saketa zata mata bayani, amma ina ai bata direta a ko ina ba sai a falon Daddynta. Yana duba jarida ya ɗago ya kallesu tare da zare glass ɗin idonshi.
A gabansa Mommy ta dire Jannat tare da faɗin "Gata nan tayi maka bayani, yanzun nan wata mata tazo ta gama wulaƙanta mu, wai Jannat tayi soyayya da ɗanta bayan ta san ba aurenshi zatayi ba"
"Daddy wallahi ba haka bane, hasalima ni ban san yana sona ba, Daddy zanyi maka bayani"
"To inajinki yi bayani" Hawayen idanunta ta goge sannan ta bashi labari komai.
"Ƙarya kike duk zumuɗin zuwa gidan su da kike yi da kuma yawan zuwa da yake yi duk ba so bane?"
"Mommy wallahi gaskiya na faɗa muku, ni ban san yana sona ba sai yau ɗin nan"
"Shikenan ƴata share hawayenki, amma ki sani bazan lamunci wani talaka yazo har cikin gidana ya wulaƙanta iyalina ba, kuje zan ɗauki mataki a kansu"
"A'a Daddy ni dai dan Allah kada ka ce zakayi wani abu, please Daddy please"
Cikin ɓacin rai Mommy tace "Kaji ko? Wallahi idan ka bibiya zancen waccan matar gaskiya ne"
Daddy ya dafa kafaɗar Jannat yace "Meyasa baki so a hukuntasu?"
"Daddy nima ya taɓa taimaka ta, kuma kasan talaka basu fiye fahimtar abu ba, sai dai kawai su yanke hukunci dan Allah Daddy ka ƙyalesu kawai"
"Shikenan, amma next time idan suka yi wani cin mutumci tabbas zan hukuntasu."
Ɗaga masa kai tayi alamar ta yarda.
"Tashi kije" kallon Mommy tayi sannan ta miƙe ta fita, jikinta a sanyaye.
Ɗakinsu ta koma ta haye kan gadonta tare da fashewa da wani kukan. Ga Farhan da Safina basu nan bare su rarrasheta.
Ta ɗauki kusan awa guda tana abu ɗaya kafin kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. A haka bacci ya ɗauketa.
Ringing ɗin wayarta ne ya tasheta taji idanunta duk sun mata nauyi ga kuma ciwon kai da take fama dashi.
Ɗago wayar tayi dan ganin wa ke kiranta. Sunan Sa'ad ne ya saka ta saurin tashi zaune. Ɗaga wayar tayi tare da karata a kunnenta ba tare da tace komai ba.
"Jannat....!" ya ambaci sunanta a sanyaye.
Bata ce komai ba sai a jiyar zuciya da ta sauke.
Shi kuma ya cigaba da faɗin "Umma tayi Allah ya isa idan har nazo gidan ku, shiyasa ban zo ba. Jannat dan Allah kiyi haƙuri akan abinda Umma tazo tayi miki, Hannatu ta faɗa min komai, a gaskiya banji daɗi ba kiyi haƙuri laifina ne"
"Baka da laifi Sa'ad, ni ce mai laifi dana kasa fahimtarka, dan Allah kayi haƙuri Sa'ad ban san kana sona ba, da ace ba'a kusa bikina ba wallahi da na aureka Sa'ad, domin babu macen da zata ƙi ka, ka yafemin ina ji a jikina kamar na zalunceka"
"Baki da laifi Jannat, tunda bama ki san ina sonki ba"
"Dan Allah ina so ka bawa Umma haƙuri please, kuma ina fatan wannan ba zai zamo sanadiyyar rugujewar zumuncinmu ba, idan na samu dama zan ƙara zuwa in bata haƙuri"
"Kada kizo dan Allah"
"Meyasa?" "Saboda komai zai iya faruwa domin Umma ta ɗauki zafin da ni kaina ban taɓa tunani ba"
"Kana nufin yanzu shikenan ba zan ganku a bikina ba?"
"Idan mun samu dama zamu zo, amma dai kada ki saka ran ganin Umma"
"Shikenan to kayi min alƙawari" ta faɗa muryarta da alamun kuka.
"Wane iri?"
"Ba zan faɗa ba har sai kayi ɗin"
"To nayi miki"
"Kayi min alƙawarin ko kowa bai zo bikina ba kai zaka zo, idan har baka zo to nima bazan zauna ba wallahi saina fita daga hall ɗin"
"Kada ki damu insha Allahu zanzo"
"Nagode"
"Ni ne da godiya" sun ɗan taɓa hira kaɗan har ta manta da damuwarta.
******
A wannan ranar kuwa Sa'ad bai yi bacci ba. Da sassafe suka tafi asibiti ciwon zuciya ya kamashi. Umma kuwa yini tayi tana surfawa Jannat zagi.
Satinsu ɗaya aka sallamesu. Tare da magunguna da aka bashi. Tun daga lokacin kuwa ya kasance yau yana da lafiya gobe babu shiyasa ya daina zuwa kasuwa kullum yana gida.
Jannat kuwa data kirashi ta tambayeshi meya samu wayarshi tsawon sati ɗaya idan ta kira a kashe sai cewa yayi ai matsala ta samu. Nan kuwa Hannatu ce ta kashe tun ranar da ya fara ciwo gudun kar ta kira Umma ta gani.
Ranar Kamu
Suna zaune a ɗakinsu an kira mai makeup tana yi masu. Farhan aka fara yiwa ta shirya kasancewar su zasu yi gaba saboda tarar baƙi.
Tana saka takalminta Jannat ta ɗago ta kalleta. "Farhan dan Allah ki ajje gate pass guda biyar saboda su Sa'ad zasu zo" "To mai Sa'ad ki dai nutsu kar makeup ɗin ya ɓaci"
"Na san halinki ne dan Allah ki ajje mishi, na tura masa numberki idan yazo zai sameki ki basu ko su nawa ne"
"To Hajiya ta" ta faɗa sannan ta miƙe tana shirin fita Jidda ta shigo "Ke fa muke jira Farhan motoci sun zo"
"Gani nan... Ta faɗa tare da kallon Safina "To brides sai kunzo,brides sister dai tayi gaba"
Dariya Safina tayi tana girgiza kai.
Ta ɓangaren Sa'ad kuwa yana fitowa daga wanka ya shirya sai dai bai saka kaya masu kyau ba, gudun kar Umma ta gane.
"Wai ina zakaje ne naga kana ta shiri kana tangaɗi kamar zaka faɗi."
Ɗan kallonta yayi duk da jiri na ɗibarsa amma ya daure yace "Umma zanje gidan su Saminu ne babarshi ce ba lafiya"
"Babu inda zakaje, bayan baka da lafiya"
"Umma Saminu fa, dan Allah ki barni inje"
"Saminun shima ai ya san larura bara in kirashi in sanar masa ni zamuje da Hanne mu dabata amma kai kam babu inda zakaje bayan har yanzu kana fama"
Gabanshi yaji ya faɗi, ya zaiyi idan har baije kamu ba, tabbas Jannat zata iya aikata abinda ta faɗa. Kuma gashi Umma ta tafi ɗaukar waya domin ta kira Saminu, kuma tana kiransa zai ce lafiyar Ummanshi ƙalau.
Ƙame wa yayi a gun dan ya rasa tudun dafawa.
SaNaz Ce✌️