Free chapter · Read without an account

Page 24

by SaNaz deeyah · SUMAYYA

SUMAYYA

Wattpad@SaNazdeeyah_

Arewabooks@sanazty

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[tushen mu'amula tagari]

Free

Page 24

Goggo faɗa sosai tayi akan abinda suka yi, ta kira Daddy tayi masa tas sannan ta ce kuma Sadeeq ba zai ƙara komawa gidansu ba sau dai da sunan ziyara

ɓangaren Hafsat ma tasha kuka sosai akan abinda Mommy tayi mata, sai da har ta ce ta daina zuwa, sai Mami ce ta bata haƙuri tare da nasiha. Jin Sadeeq ya koma gidan Goggo itama kawai ta ce can zata koma, kuma ta kafe a haka har sai da ta koma dan dama ita da Sadeeq duk a gidan Goggo suka taso, da suka san kansu ne ko wanne ya gudu gidansu.

***********

Kallonta ya yi da mamaki sannan ya kalli trolley ɗin da kayan dake ƙasa, "Ya naga haka? Meyasa naga kamar babu farin ciki a fuskarki?"

"Yaya Jamilu! Ina mamaki yadda ka samu kuɗi har haka, kuma naga baka fita aikin ma"

"Allah yasa hakan da kika gani bai ɗarsa miki zargi a zuciyarki ba"

"Eh to, naga duk kayan nan masu tsada ne, gasu da uban yawa, sai nake ganin kamar ƙarfinmu bai kai ace ka sayi kaya haka ba"

"Sumayya kamar dai zargi na kike?"

"Ni bana zarginka"

"To idan ba zargi ba mene wannan? Sumayya bani da ikon yi wa ɗiyar da zan haifa abu sai kin saka zargi a ciki?"

"Dan Allah kayi haƙuri wallahi ba da wani abu na faɗi haka ba"

Miƙewa ya yi tare da faɗin "To koma dai mene ke kika sani, idan har kika ce zargi za ki fara abin ba zai mana daɗi ba" Bata tanka masa ba, ya saka kai ya fice rai a ɓace. Ajiyar zuciya Sumayya ta sauke bata iya cewa komai ba.

Ko mintuna biyar bata yi da jin tashin napep ɗinsa ba kawai taji sallama. Da ƙyar ta iya miƙewa daga kan katifar. "Za a fito ne ko mu shigo"

Murmushin ƙarfin hali Sumayya tayi sannan ta buɗe labule.

"Bismilla ki shigo mana"

"Jamilu yana nan?"

"A'a yanzu ya fita, amma wacece ban ganeki ba"

"Karuwarsa ce, ko kin manta nazo kwanaki"

"Subhanallahi, baiwar Allah wace irin magana ce haka babu daɗin ji"

"Oh dole kice haka, aike gashi ya ɗirka miki ciki har ya girma kin kusa haife shi ni kuma da yake nawa shege ne ai an saka na zubar, wallahi Jamilu ƙungurmin macuci ne"

Ɗan lumshe ido Sumayya tayi cikin ƙunar rai ta ce "Dan Alah kiyi haƙuri baya nan, idan ya dawo sai ki dawo"

"Oh wai korata kike? Ya naga kina magana ma kamar irin haushi kike ji, wai kema har kishi ne dake?" "Hmmm!" Kawai ta iya faɗa sannan ta juya ta koma ɗaki.

"Za ki gane kin share ni, wallahi sai na shigo gidan nan na buga kishi dake sai kin gwammace kiɗa da karatu." Juyawa tayi ta tafi ta bar gidan cikin ɓacin rai.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta faɗa cikin tashin hankali sannan ta jingina bayanta da bango, ta lumshe idanunta da taji suna barazanar tarwatsewa, a hankali ta zame ta zauna a ƙasa tana mai jin wani irin zugi a zuciyarta, ita ta kasa gane shin gaskiya ne ko ƙarya abinda waccan yarinyar ke faɗa.

*********

Ƙarewa gidan kallo take a lokacin da shi kuma ya shigo mata da kayanta, mutane sai kai da kawo suke a tsakar gidan babu wanda ya lura da lamuranta. "Ina ne nan Alhaji?" Ta furta cikin tashin hankali.

"Ba daɗewa za mu yi ba"

"Ni dai hankalina bai kwanta da gidan nan b..." Bata ƙarasa ba taga wasu mata sun tamƙeta, wani ƙara ta kurma sai dai bata sake sanin inda kanta yake ba.

A hankali ta fara buɗe idanunta da suka mata nauyi, ɗakin da take babu wani haske sosai a cikinsa, sai ɗan kaɗan wanda bama ka iya tantance komai na cikin ɗakin. Ta dai hango wasu ƙwarare masu ƙurzunu-ƙurzunu an jere su guri guda. A hankali ta fara ƙoƙarin tashi a lokacin ne ta fara jiyo sound na shashsheƙar kuka a hankali. Wata matashiyar mace ta gani zaune a gefenta wadda a ƙalla za tayi shekaru ashirin da 29, ganta an askeshi ƙwal an shafe shi da wani farin abu mai kama da farar hoda, babu ɗan kunne a kunnenta ɓular kunnen ce kaɗai ta tabbatar mata da macece ba namiji ba.

"Ina ne nan?" Ta furta a gigice, matar ta kalleta sannan ta kauda kai gefe.

"Baiwar Allah ki faɗa min ina ne nan?"

"Nan? Ke dai kawai ki cigaba da addu'ar neman gafarar ubangiji, cikin biyu ne za a samu ɗaya ko dai a kashe ki anan ayi kuɗi da gangar jikinki ko kuma Allah ya kuɓutar dake" "Kenan Alhaji ɗan yankan kaine kawo ni nan ya yi a yanka?"

"Koma waye hakane"

"Na shiga uku, wayyo Allah na cuci kaina" Ta fashe da kuka. "Kiyi haƙuri, amma ko wane tabbas ya bayar da jininki" Sam ta kasa salati ta kasa addua sai zancen zuci tun daga lokacin da ta fara haɗuwa da Alhaji Garba.

**********

Tana hamma ta zauna a kujera tare da kallon Goggo "Ina kwana Goggo?"

"Sarkin bacci har ƙarfe 11 sannan za ki tashi"

"To Goggo in ina gidan nan aini 'yar hutu ce, gashi kin ga babu school gabaɗaya zaman banza ne"

"Kece dai baki so aiki ba, amma ai da kin min tausa"

"Goggo idan ina yi cewa kike ina matsa miki ƙafa da ƙarfi"

"Ai dama dan ki fake da haka shiyasa tun farko baki son yi min a hankali"Murmushi tayi sannan ta ce "Yanzu dai ba wannan ba, breakfast fa?"

"Ai har ya gama yin sanyi kije kici a haka waye ya saka kiyi bacci"

"A'a ni kam sai an yi warming ɗinsa" Ta faɗa tare da kaɗawa Suwaiba kira, ɗaya daga cikin 'yan aikin gidan. Tana zuwa ta bata umarnin ta ɗauke kayan ta mata warming "Ba ki san ko mene ba"

"Ni kam Goggo koma mene" Ta faɗa tana ɗaukar wayarta.

"Sadeeq ya fita ne?"

"Yana nan, ai Sadeeq yanzu kam zai daɗe bai fita ba, ko parlour dai kina gani sai kece in kin takura yake fitowa, ban san sai yaushe zai haƙura da komai ba"

"Goggo dama sai a hankali ai, bari na kirawo shi" "To wataƙila ke yaji take maganar dan ni da kaina naje na buga masa bai buɗe ba."

Miƙewa Hafsat tayi ta nufi side ɗin da Sadeeq yake.

Yana kwance a kan gado ya baje yana zuƙar shisha daga kwance ya ji knockong. Kallon ƙofar ya yi sai dai bai yi yunƙurin buɗewa ba. Jin an takura da bugun ya saka ya ce "Waye?"

"Sadeeq nice" Jin haka ya sakashi saurin miƙewa "Ina zuwa" Ya furta sannan ya ɗauki kwalbar shishar ya ksi toilet ya kashe wutar ya barta anan. Yana fitowa ya ɗauki freshner kan mirrow ya feshe ko ina, sannan ya ƙarasa gaban ƙofar ya buɗe mata. Kallonshi tayi sannan ta ce "Ya naga ka toge anan ka matsa min in shiga mana"

"Okay" Ya furta kamar wanda a lokacin ya tashi a barshi sannan ya matsa ta shiga.

Juyowa tayi tana kallonsa "What?"

"Ka sha wani abun ko?"

"No babu abinda na sha"

"Ɗakin ya sauya haka voice ɗinka ma"

"Am so sorry Hafsat, na kasa jurewa ne ina cikin damuwa"

"Shaye-shaye ba shi ne abinda ya dace da kai ba Sadeeq yanzu kana tunanin idan Goggo ta sani ko taji warin za taji daɗi?"

"Na rasa nafita Hafsat?" Ya faɗa yana zama kan sofa.

"Na san Goggo ba zata jiyo ba saboda na rufe ɗakin kuma Ac ma na kai ƙarfinta ƙarshe" Sh9ru tayi bata ce komai "Kiyi haƙuri" Ya sake furtawa.

"A buge fa kake?"

"No"

"Wallahi a buge kake"

"Ni fa ba a buge nake ba, ya ina magana da hankalina kina min maganar a buge nake, ni ban sha wadda zata bugar dani ba, sai dare nake shanta"

"Oh kana sha kenan?"

"Bani da mafitar da tafi wannan" "Okay" Ta furta tare da miƙewa "To ka sani san tattara na koma gida tunda zamana anan baya da wani amfani dama dan na ɗebe ma kewa ne amma tunda akwai abinda ya fini shikenan kawai"

"Babu Hafsat"Ya furta yana tarar gabanta.

"Idan kika tafi ya zan yi waye zai bani shawara?"

"Su kayan mayen ai sai su baka shawara" Tana gama faɗa ta wuce.

"Ina cikin wata masifar Hafsat" Ya furta a dai-dai lokacin da taje bakin ƙofa. Cak ta tsaya dan furucin nashi ya doketa.

"Mommy za ta ƙara tsanata ƙila ma ta tsine min Hafsat" Ya faɗa lokacin wasu zafafan hawaye suka sauka a fuskarsa.

Ku yi manage please, insha Allah saura shafo ɗaya mu gama free page, zaku riƙa samun dogon page tare da posting a lokacin daya dace.

Sannan a goben dai promo ɗinmu zai ƙare duk wanda zai sayi book zai saya akan ₦500 vip kuma ₦1000 amma daga yau har zuwa daren gobe in Allah ya kaimu a ₦300 kacal zaku saya.

Halima Adamu Salahu

***

Opay

Katin waya da kuma shaidar biya ta wannan number ***

SaNazdeeyah_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol