Free chapter · Read without an account
Chapter 10
Page 10
*~reeeyarh~*
Suna tafiya du’a tace yaya ba kyau, me yiwa mutane rashi mutunci, du’a kinsan me, aa bana son shashan ci ne, haushi ta bani, dan uban ta ni zata ce tana so, dariya du’a ta fara, sosai take dariya, ke zaki tara mana mutane, yaya wallahi kun dace, du’a stop it banson wasa, kai yaya, shikenan, amma, du’a Nace ki mini shiru, da dan karfi, bata sake mishi magana ba har suka je shashen baffa.
Suna zana suka gaida shi, bayan ya amsa, sukayi hira da du’a, baffa, na’am babana, bayan bikin su hauwa zanje china, wani aiki, okay Allah ya taimaka, Ameen baffa, du’a ni zan tafi, ko zaki zauna ne, bata bashi amsa ba tayiwa baffa sallama, mamana, du’a baffa na magana, na’am baffa, sai yaushe zaki kara zuwa, sai ranar da Allah yayi, ki gaida mamaki, tam baffa.
Suka tafi ita har yanzu haushi take ji, shi kuma girman kai ya hana shi mata magana.
Tsintar kashi yayi da rike hannun, juyowa tayi tace nika sake mini, hannu na, marairaicewa yayi yace du’a fushi kike dani, turo baki tayi tace aa, gashi nan kinki kula ni, ni ka sake mini hannu na.
Sakin ta yayi, ko shashen mami bai komai ba, ya huce nashi, ita kuwa tana shiga mami na zaune ita da fatiha, du’a har kun dawo, eh mami ina yake, ya tafi shashen sa.
Fatiha zoki kai mishi abinci, tam.
Shi kuma yana shiga ya zauna ya jingi kanshi da kujera, me yasa koda yaushe yaga du’a yake kasa control din kanshi, yana tunanin nan fatiha ta shigo, yaya ga abinci mami tace na kawo maka, fatiha I’m okay banjin yunwa, ki tafi dashi, yaya wani abuna damun ka, aa me kika gani, ba komai. Tafiya tayi.
Ya nagan ki da abinci kin dawo, mami wallahi ku binciki yaya, wani abua damun sa, wai yace bazai ci abincin ba, mami kiran shi tayi a waya, yana dagawa tace yazo, mami nasan akan abinci ne wallahi na koshi, nace kazo.
Yana zuwa ya zauna a kusa da ita, mami bata kiran sunan shi sai abu mai mahinmanci meke damun ka, mami ba komai, okay indai akoi abinda bazaka iya fada mini ba nasan akan wata ce, wacece, haba mami ni wallahi, okay du’a, fatiha ku tashi ku tafi daki zamuyi magana.
Tunda ta tashi kallon ta yake ji yake kamar yace ta dawo ta zauna, ya za’ayi ya fadawa mami abinda yake ji, dan shi har yanzu bai yarda soyayya bace.
Ina jinka wacece, mami nifa ba komai kai kaina ke ciwo, aa fa ka fada mini gaskiyya.
mami da gaske ba komai. Okay tashi kage kaci abinci, su fatiha sunci aa, mami suzo muci tare banson cin abinci ni kadai, mami bata kawo komai a ranta ba.
A waya ta kira fatiha tace su sauko, suna sauko wa mami tace kuje kuci abinci, lokacin shi harya ge ya zauna, du’a tace mami na koshi, haba du’a yanzu fa is already 2:00 koma me kika ci aiya zazzage. Kije maza.
Suna zuwa fatiha tace yaya, wani kallo ya mata dan yasan ita tazo tace wa mami wani abuna damun shi.
Zama sukayi , wata tazo ta zuba musu abincin, fatiha idan ta daga kanta saita hada ido da yarima , dan haka dole tasa tace ta koshi, du’a ma tashi tayi zata tafi, ina zaki, nima na koshi, ai idan ta tafi ta barmu cinye ki zanyi, zauna ki cinye abinci nan.
Zama tayi tana juya abinci, tana daga kai suka hada ido, tayi kasa da kanta.
Sai kuma tace yaya meke damun ka, kina son sani, eh, okay dawo nan zan fada miki, tashi tayi ta koma kusa dashi, abincin fa, na koshi, aa dauko shi,
Abincin ta dauko ta zauna, kasa tayi da kanta, shi kuma sai kallon ta yake.
Du’a, dagowa tayi tace na’am, idan na fada miki bazaki fadawa kowa bah, eh yaya, kamar ya fada mata abinda yake ji akan ta, amma bazai iyaba.
Aljana ta dan Allah kina zuwa gidan mu kinji, mai yasa, kawai, mamma ba zata barni ba, hannun ta ya rike yace zan mata magana, kuma zata barki, saidai ke kika ce bazaki zo ba.
Toh ai mutane zasu ce nacewa kullun saina zo gidan ku, ai ba wurin su kika zo ba.
Toh yaya baka fada mini meke damun ka ba, ba komai du’a, zan jure wata rana zan fada miki.
Amma, matsa hannun ta yayi yace karki ce komai, ci abinci ki, na koshi, please kinji.
Tana ciki ci yace du’a, na’am, I’m sorry.
for what, dazu ita sai yanzu ta tuna yayi mata laifi, toh yaya ka daina mini fada, tam amma karki sake hada ni da kowacce mace kinji, in sha Allah.
Ya gama cin abincin amma ya kasa tashi dama su dawwama a haka.
Yaya muje nina raka ka asibitin, murmushi yayi yace du’a cuta ta bata asibiti bace, wai har yanzu tunanin abinda ziyada ta fada mini kake, aa du’a wani abune daban, amma ai, shiiiiiiiiit, aljana ta, emmm , kinyi tunanin akan abinda na fada miki, wanne, wanda kika ce idan kin dawo gida zakiyi.
Aa mai yasa, kawai okay inaso kiyi tunanin yanzu ki bani amsa, yaya bazan iya ba, yanzu ace baffa brother mamma ne, zaki kulani. Yaya karka yi wannan tunanin, me yasa, girgiza mishi kai tayi .
Du’a kalle ni, kin kallon shi tayi, hannun yasa ya daga fuskar ta, suka hada ido, yaya menene haka mami fa na palo, okay idan bata nan fa, yaja hancin ta. Yayi murmushi.
Tashi tayi zata tafi ya yi saurin tashi ya janyo ta, gurin yana da duhu kuma labulen gurin a sake yake, idan yarima nanan babu yar aikin da take zuwa gurin.
Hannu shi yasa a wrist ta ya janyo ta jikin shi, yaya ka sake ni bana so, kiyi shiru magana zamuyi, yaya mami na palo, hannun sa yasa ya toshe bakin ta, sai kuma yayi saurin sakin ta jin takun mutun.
Juyawa tayi ta fuce daga gurin, shi kuma ya koma ya zauna, tana fitoh wa palon ba kowa, sama ta tafi dakin fatiha.
Shi kuma tunda ya zauna ya dafe kanshi, me yake damu na, me yasa na mata haka, Allah yasa ba fadawa mami zatayi ba, mami ce ta karaso wurin , sannu da sauri ya daga kanshi ya kalle ta, har yanzu kana nan a zaune, ga alamu ya nuna akoi abinda yake damun ka amma kace ba komai.
Zama tayi tace nice mahaifiyar ka idan baka fada mini damuwar ka ba wa zaka fadawa, kodan zan kira adam na tambaye shi. Ta tashi, mami baisan komai ba, bata tanka mishi ba ta huce warta dan ya bata haushi, kenan akoi damuwar fada ne bazai ba.
Mami na kitchen lokacin da du’a ta tafi sama, du’a tunda ta shiga dakin fatiha ta kwanta, fatiha waya take bata lura da yace ta shigo ba, tana son control din kanta amma ta kasa, fatiha da tun dazu take waya da adam har ta fada mishi yarima na cikin damuwa yanzu ma a kasa ta taso ta barshi shi da du’a.
Kukan du’a ne yasa tayi saurin juyowa, besting lafiya, ba komai kaina ne yake ciwo, adam ne ya tambayi fatiha meke faruwa, du’a ce ta shigo tana kuka, kuka kuma bata wayar, mika mata wayar tayi, du’a mai ya faru, ba komai, they is something just tell me, wallahi ba komai kawai kaina ke ciwo, okay Allah ya sawake Ameen, ta mikawa fatiha wayar, teema kika ce ita da junaid kika bari, a okay shikenan ki lallashe ta, idan anjima zamuyi waya.
Tana kashe wayar ta juyo tana kallon ta, du’a wanine ya miki wani abu, girgiza mata kai tayi, yaya ne ko, aa fatiha kaina ke ciwo, bari na karbo miki magani, amma karki cewa mami nayi kuka, okay.
Anya kuwa abun da ziyada ta fada akan yarima ba gaskiyya ba ne, ita tasan ko su yaya Ibrahim da suke yan uwan ta basu taba kokarin rike mata hannu ba, amma shi yayi ta taba ta, taya zata fadawa fatiha abinda yarima yake mata, kenan yarima da adam duk halinsu daya.
Fatiha kuma tana sakko wa tace mami kina da maganin ciwon kai, lokacin ya dawo palo, ciwon kai kuma, eh du’a ce zata sha kanta na ciwo, okay ki je daki na ki duba. Allah ya du’a karta fadawa fatiha abinda ya faru, yanzu ya zaiyi.
Wayar shice tayi kara, ya tashi ya tafi shashen sa. Hello Adam, hello ya kake, lafiya, lafiya yaji muryar ka haka, lafiya lau, Junaid wallahi kayi wani abuba daidai ba, me zanyi kuwa, okay shikenan dama kira nayi mu gaisa, okay yaushe zaka zo, ina tunanin gobe zan shigo in sha Allah.
Du’a ga maganin karba tayi tasha, tace bari tayi bacci ko zata ji sauki kan nata, tana kwance tana tunanin har tayi bacci.
Bayan sun gama waya da adam shima kwonciya yayi.
Sai bayan la’asar ta tashi tana tashi tayi sallah, ta sakko kasa, suna zaune danshi ya dade da tashi.
Du’a kin farka, eh mami, ya jikin, da sauki, zoki zauna, aa mami tafiya zanyi, tun yanzu, akoi aikin da zanyi a gida, okay bari yayan ku ya kaiki, zuciyar ta kamar zata fashe, sai yace mami driver ya kaita ni ina da aiki. kana da aikin kazo ka zauna anan, kaje ka kaita ka dawo, mami ya bashi tunda yana aiki.
Driver ne ya kaita har gida, koda ta koma gida sister dinta basu dawo daga school ba.
Mamma ta lura kamar akoi abinda yake damun ta, du’a lafiya, lafiya lau mamma me kika gani ba komai.
Sai dare abbah ya dawo bayan ya dawo suka ci abinci, suna palo suna hira amma du’a wani tunanin take abbah ya lura da hakan har saida ya tambaye ko lafiya, abbah bacci nake ji ne, okay kije ki kwanta saida safe, du’a ku tafi da dee, mamma ta kwana tare da teema, okay saida safe.
Tana shiga daki taga miss call din yarima amma ko takan shi bata bi ba ta rufe daki ta kwanta, kiran ta aka sake yi, tana dubawa taga mami, a tunanin ta fatiha ce.
Hello besting, shiru, hello baki jina ne, du’a da sauri ta cire wayar taga dai sunan mami ne, kashe wa tayi, ya kara kira, tana daga yace ga mami zakuyi magana, okay shiru yayi sai kuma yace du’a dan Allah karki kashe wayar, ina mamin tana part dinta.
Shiru tayi tana tunanin me ya kawo wayar mami hannun shi, mai yasa dana kira ki baki daga ba, ina palo wayar kuma na daki, okay gobe inaso mu hadu, dawa,ke.
Dan Allah ni bacci zanyi saida safe, du’a karki sake ki kashe mini waya kinji ni.
Toh me kake sona maka, ina da abun yi, murmushi takaici yayi yace wana tsautsayi ne yasa yayi wannan abu, du’a kina jina, bata bashi amsa ba yace nasan yanzu kina mini kallon dan iska, a fusace tace wai daga an fara magana kuce baku aikata ba, ai yau gashi na gani da ido na kuma a kaina, karka damu bazan fadawa mami ba bama wanda zan fadawa.
Amma ka canza halinka, inalillahi , kaga you should end your call tun kafin nayi da kaina, okay I will but du’a dan Allah ki fahimce ni ajiye wayar tayi a gefen ta harya gaji ya kashe, kuka du’a tayi har bacci yayi gabada ita.
Shi yama rasa me zaiyi kodai ya kira adam ya fada mishi, aa ko ya fadawa fatiha, ya rasa yace zaiyi sai kusan 2:00 yayi bacci.
Washe gari du’a bata wani fita ba sosai.
Yau alhamis su fatiha sun fara bikin su, henna day sukayi, du’a bata zoba. Yarima yayi ta baza ido ya ganta amma bata zoba.
Washe gari saida fatiha taje har gida ta dauko ta, dan jiya ba yacce batayi ba da ita ba akan taje amma taki yau kuma kamu zasuyi.
Suna tafiya fatiha tace du’a kinyi kyau, kema haka amma mai yasa bakiyi makeup ba, ba komai, kinfi kyau ba makeup dama, da gaske, eh, ni wallahi bana son shiga cikin mutane, mai yasa, bakiga duk na rame ba, toh ai gara ke baki ga yaya yacce ya dawo ba.
Wai har yanzu baya jin dadi, eh wallahi.
Suna isa suka shiga lokacin 7:00 tayi amarya bata zoba, yarima ma baizo ba.
Suna zaune fatiha tace du’a zo muje mu gaida mami, suna zuwa suka gaisa, du’a kinyi kyau sosai, ai nazata bata kai miki aukon ba, aa mami sai yau ta kawo mini, okay. Fita sukayi daga event din, suna fita du’a take cewa me zasuyi a waje, ba komai.
Amarya ce tazo, nan akace azo a shiga da amarya, du’a kizo muje, aa ba zanje ba kije idan sun shiga zan shigo. Tafiya tayi,
Du’a na tsaye baki wata mota, bude motar akayi aka janyo ta cikin, ta matukar
tsora ta amma ganin wanda ya janyo ta ne yasa ta hade rai, me haka, murmushi yayi yace du’a ba gaisuwa, ban iya ba, ta sa hannu zata bude motar ta fita, yarima tun dazu yana zaune a mota yana kallon su dan ko shirya wa baiba, kawai yazo da ya ganta ne sai gashi kuwa Allah ya hada su.
Ya riga yasawa motar key, ka bude mini kofar, bai bata amsa ba, har saida ta juyo ta kalle shi. Ki tsaya muyi magana sai na bude miki ki fita, amma wallahi idan baki tsaya ba, ba inda zakije. bata mishi magana ba.
Du’a sai yayi shiru danshi baisan me zaice mata ba, karfin hali yayi ya ruko hannun ta, da sauri ta warce hannun ta karka sake taba ni, yarima ya saba shi a gurin shi rike hannu da hugs ba wani abu bane, rike hannun ya sake yi da karfi yace bazata iya kwacewa ba, kuka ta fara ni ka sake mini hannu na.
Du’a dan Allah karki yi kuka wallahi ni bayi hakan danna bata miki rai ba, ni ka sake mini hanu na, idan na sakeki baza ki kara kuka ba, daga mishi kai tayi.
Sakin ta yayi yace du’a wallahi ni ba, sai yayi shiru, baka aikata ba, na sani,
du’a I’m serious, wallahi ban taba, taba wata mace ba, saini murmushi takaici tayi, irin wannan ya raina mini hankali.
Du’a me kike sona miki ki yarda dani, ka rabu dani please I said i will not tell anyone, toh ka kale ni dan Allah. Okay shikenan bari naje na shirya.
You can go danni bansan me zance miki ba, amma zan fadawa adam ko shi zaiya ganar dake, adam adam, wana adam indai adam saurayi fatiha kake nufi to bazan yarda dashi ba, fatiha, eh fatiha kanwar ka ita, kayi mamaki ko, Allah sarki baka sani ba ko, dama bazai fada maka ba saboda yasan halinka kasan nashi.
Du’a me kike nufi, abinda kake tunanin, ta fice daga motar.
Fatiha da ta fitoh neman ta , ta ganta ta fitoh daga mota, da sauri ta karaso wurin tace du’a keda wa, I’m not in a good mood, mu tafi, fatiha bata san yarima bane dan bata sanshi da wannan motar ba.
Shi kuma suna tafiya ya dawo driver sit ya zauna, gida ya tafi yana tunanin shi bama tunanin adam da fatiha yake, tunanin shi kenan du’a kallon yan iska take musu, taya zai fadawa adam, yasan lallai sai ranshi ya baci, kuma hukunci harshi zai yiwa , da wannan tunanin yaje gida.
Du’a duk ta kasa suku ni ita me ya kaita fadawa yarima fatiha budurwar adam ce, kodan ai gara ta fada mishi saboda kar adam ya lalatawa fatiha rayuwa.
Adam ne ya kira yarima dan yaji yana ina, ina gida, okay mu hadu a event, tam.
Koda yarima yaje event din adam na event din yana jiran shi a mota,
Tare suka shiga event din nan akayi sanar war yayan amarya ya shigo, aka daiyi hotuna, amma hankalin shi na kan du’a.
Kiran ta akayi a waya ta fita, shima tashi yayi ya fita duk akan idon mami.
Kusa da wata mota ta tsaya tana waya, bata san yazo wurin ba, tana gama wa ta juyo zata bar wurin. Ganin shi tayi a tsaye a wurin, lafiya tana mishi wani irin kallo,
du’a adam baisan komai ba. baisan ina wannan abun ba dan Allah ki kara rufa mini asiri karki fada mishi.
Da gaske amma taya hakan zata kasan ce, du’a adam aboki nane ba amma ai ba gida daya muke rayuwa ba.
Du’a dan Allah ki rufa mini asiri, daga baya yaji ance wani abun ka sake yi, juyowa yayi, yayi murmushi yace, eh laifi nayi, ka tayani bada hakuri, du’a zomu tafi baza mu hakura ba. Ka bata hanya ta huce, tafiya sukayi suna tafiya tace yaya adam, na’am du’a na sake yanke wa wani hukunci ba tare da tunanin ba.
Du’a nace miki kina tunanin kafin ki yanke hukunci, yaya adam wallahi banyi ba kuma ina jin nauhi mutumin, badai junaid bane, ba shi bane, amma karka tambayeni waye, okay du’a Allah yasa idan kun hadu ya fahimce ki Ameen.
Yarima har suka shiga event din yana kallon su, a ranshi yana cewa Allah yasa du’a ba fadawa adam tayi ba. kodan bazata fada mishi ba tunda yace adam bai san komai ba. hukunci daya yanke yayi amfani tunda ta daina zargin adam.
Yana shigowa da ita ya fara karo sai dariya take, ita da fatiha da samha sai sultana, suna hira, tana daga kai suka hada ido, tamke fuska tayi kamar ba’a halici dariya a fuskar taba.
Du’a duk abinda take tana duba lokaci , tana ganin 9:00 tayi tace fatiha gida zan tafi. Mami taje tayiwa sallama, du’a ina zuwa, fatiha tasa ta kira mata yarima yana zuwa mami tace kasa a kai du’a gida, okay mami dama nima tafiya zanyi bari muje idan aka ajiye ta saina tafi, yawwa ni dai amana na baka, tam mami, fatiha saida ta raka su har gaban mota.
Yaya adam kaima tafiya zakayi, eh fatiha, sai gobe. Yarima a zuciya yake cewa lallai ma wallahi adam ya raina mini wayo, besting sai gobe, Allah ya kaimu,
Ki shirya da wuri, hmmm sai kiyi ai nace miki bazan zoba ko, adam ne yace mai yasa, kawai banson zuwa, akoi fuskokin da banson gani. du’a su waye, kar wanda ya tambaye ni, basai kun sani ba, mota ta shiga shima ya shiga, suka tafi.
Adam kuwa sundan jima da fatiha kafin ya tafi.
Suna tafiya a hanya yace kina kyau idan kina dariya, kokin hade fuska kina kyau, bata tanka mishi ba, Yallabai gida zamu tafi, aa hausawa zamu je zamu kai aljana gida, musa baiji karshe maganar badan yace yarima yayi maganar su biyu zasu ji.
Du’a badai ki fadawa adam ba, sai’a lokacin ta juyo ta kalle shi, mai yasa ka zabi wannan rayuwa, kaddara tace, amma ai zaka iya canza ta ba, a inason hakan amma na kasa, baka so canza waba, kasan babu kyau amma kake yi, du’a lokaci ne wata rana sai labari.
Amma idan baka canza ba wata ranar ka baza tayi kyau ba. Allah zai hada ni da mata ta gari in sha Allah.
Allah ba azzalumin bawan sa bane, bazai hada ka da wacce zaka cutar ba, du’a ina aure zan daina in sha Allah, toh mai yasa bazaka yi aure ba, lokaci, shiru tayi bata kara cewa komai ba.
Allah sarki rayuwa wai yau shi akewa kallon fasiki, kuma ya amsa, kai indai haka so yake so balai ne. Har gida suka kaita, ki gaida mamma, ka canza hali, ta fucewar ta.
Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️
Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.
Nagode
*~Book by Reeeyarh~*