Free chapter · Read without an account

Page 10

by SaNaz deeyah · SANADIN MAHAIFINA

•••SANADIN MAHAIFINA•••

Wattpad@SaNaz_deeyah

Arewabooks@sanazty

Facebook@Habibtyn Habibi

YouTube: ***

Tiktok: ***

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula ta gari]

                    '''Shafi na 10'''

________________📲 04:30pm

A hankali ta buɗe idonta da suka mata nauyi sosai, har lokacin kasala take ji da bacci, lumshe idon tayi, ta fi mintuna biyu kafin ta buɗe ido, miƙewa tayi zaune, sai jin wani mugun zugi tayi daga private part na ta. kallon jikinta tayi. Yaushe har na cire bra nawa na kuma zage zip ɗin rigana?. shine tambayar da ta fara yi wa kanta kafin ta bi jinkinta da kallo.

Sai lokacin ta ga jini kwance, ya bi ƙafarta, zabura tayi tare da zunduma ihu. Abu biyu ga zafin da taji na yunƙurin tashi da kuma kaɗuwa da yanayin da ta tsinci kanta.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,mene ya faru dani" ta faɗa tare da rufe bakin ta da hannu tana kuka.

Cikin barf ta shiga tana gasa jikinta da gaba ɗaya ya ke ciwo. Kuka kawai take duk da cewar har lokacin bata tabbatar da abinda ya faru da ita ba.

Ta fi mintuna talatin a toilet kafin ta fito tana ɗangyasa ƙafarta.

Jikin mirror ta tsaya tana kallon fuskarta da ta ɗan kumbura. Ya Allah ka raba ni da jin kunya duniya da lahira. ta faɗa tana ƙara goge hawaye. Bedsheet ɗin ta yaye ta kai toilet ta ajje sannan ta shimfiɗa wani.

Bayan ta shirya kuwa gado ta kwanta ta rufe jikinta saboda zazzaɓin da ta ji yana neman rufeta. Allah ka sa ba aljani bane ya aureni. ta sake furtawa tana zubda hawaye mai zafi.

Taso faɗawa Safina abinda ya faru amma sai ta fasa saboda gudun kar ta jefata a damuwa, dan ko da ta tambayeta da taga yanayin tafoyarta kawai sai ce wa tayi a toilet ta faɗi.

4 days later

Tana zaune tana yanke farcen ƙafarta, Safina na kitchen tana haɗa abincin lunch, saboda friday ne Ahmad baya dawowa gida sai an fito daga masallaci.

Knocking da akayi ne ya saka Jannat tashi ta zura hijab sannan ta nufi ƙofar da buɗe. Wani mayen kallo ya bita dashi, ta juya kawai ta wuce ciki.

Tana zaune kan gado ta tanƙwashe ƙafafunta ta lula duniyar tunani.  Safina ta turo ƙofar ta shigo cikin sallama. Kallonta tayi ta amsa mata sannan ta kawar da kanta gefe.

"Ki taso muyi lunch."

"Na ƙoshi" ta bata amsa a taƙaice.

Zama tayi a gefen gadon ta kalleta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Na kasa gane kanki Jannat, meke faruwa ne?"

Hawaye ne suka zubo daga idanunta ta kalli Safina tace "Har tsawon wane lokaci zan yi kafin Daddy ya ya fe min? Safina ta ya zaki gane kaina bayan har yanzu ina cikin fushin mahaifi, ba zan taɓa samun sukuni ba matuƙar Daddy bai yafemin ba"

"Kada ki damu insha Allahu Daddy zai yafe miki"

"Sai yaushe? Gaskiya akwai takura zamana a wannan gida"

Ɓangaren Ahmad kuwa Safina na tafiya kiran Aiman ya nufi dinning. Zoɓon da ta haɗa ya buɗe jug ɗin ya zuba ƙwayoyin bacci ya saka spoon ya juya sosai har ya narke sannan ya mayar ya rufe.

Komawa yayi falon ya zauna. Ta ɓangaren Safina kuwa, Jannat take ta rarrashi da ƙyar ta tashi suka fita falon suka zauna domin yin lunch.

Suna ci suna hira amma Jannat bata saka masu baki sosai,shi kuwa Ahmad sai ƙara jan ta yake da hira. Kowa shi yayi serving kan shi.

Jannat kallon Safina tayi ta ce "Aunty zoɓo yayi daɗi fa, kamar kar na daina sha"

"To ai ga ki ga zoɓon nan, kina ganin nawan kurɓa ɗaya yayi wai bai masa ba."

"A'a Yaya Ahmad wannan zoɓo kuwa ya yi sosai ba ƙarya"

"Ai nima ba kushewa nayi ba ƙanwata, kawai dai wannan ɗin ne bai min ba."

Zuɓura baki Safina tayi ta miƙe ta bar gurin. Daga shi har Jannat da dariya suka bi ta.

"Ƙanwata bari naje na lallaɓa princess"

Tana hamma tana gyaɗa masa kai alamar to. Ɗan murmushin mugunta yayi sannan ya wuce.

Miƙewa tayi tana son komawa ɗakinta amma taji ina, bacci ya ci ƙarfinta akan carpet ɗin dining anan ta zube tana bacci.

Ta ɓangaren Safina kuwa tana shiga ɗakinta ta kwanta kan gado tun kafin ya ƙarasa har bacci mai ƙarfi yayi awon gaba da ita.

Falon ya koma ya tarar da Jannat a kwance kan carpet. Tallabota yayi ya shafo fuskarta yace "Ina sonki Jannat, na so ace kece matata ba Safina ba, gaskiya ba zan iya rabuwa dake ba, dan haka a duk lokacin dana buƙaceki zan baku magani kuyi bacci sannan inyi sha'anina"

Tashi yayi ya jefa wasu ƙwayoyi guda biyu a bakinsa ya kora da ruwa. Cikin seconds talatin ya fara fita hayyacinsa. Tun anan ya fara kissing ɗin ta kafin ya saɓeta zuwa bedroom ɗin ta. Abinda ya yi mata a wannan karon ya fi wanda yayi mata a farko saboda ƙwayoyin da yayi amfani dasu. Yayi mata kaca-kaca har jini ya ɓalle mata.

A nan shima ya zube yan bacci.

07:30pm

A hankali ta buɗe idanunta da suka mata nauyi. Kallon agogon hannunta ta fara yi ta ga lokaci. Zubur ta miƙe tana salati.

Meyasa Jannat bata tasheni ba, ko La'asar banyi ba, gashi Magriba ta wuce. ta faɗa tare da jan tsaki.

Tashi tayi ta shiga toilet tayi alwallah, ta rama sallolinta tare da yin istigfari, tana mamakin wane irin bacci tayi haka.

Ko da ta fita falo, ɗankwalin Jannat ta fara cin karo dashi a ƙasan carpet. Meke faruwa? ta faɗa tana ƙoƙarin yin side ɗin Jannat sai ganin Ahmad tayi ya fito daga corridor ɗin ƙasan jallabiyar jikinsa jini, ga kuma boxer ɗinsa a hannu.

Zaro idanu tayi tana kallonsa, haka shima ya tsorata da ganinta sosai.

"Me ka aikata Ahmad, ba...ba...dai ƙanwata Jan...." bata ƙarasa ba saboda yadda bakinta ke rawa.

"Zan maki bayani ki saurare ni dan Allah Saf...." hankaɗeshi tayi ta nufi ɗakin Safina da gudu.

Tana shiga tayi turo ta tsaya, runtse ido tayi tare da sakin razanannen ƙara. A take a gurin ta suma.

1 hour later

Da kuka ta farka tare da miƙewa zaune. Yana tsaye yana share zuffa duk da cewar ba zafi ake ba.

"Ina Jannat ina ƙanwata?" ta furta cikin matsanancin kuka tare da dira daga kan gadon asibitin.

Nurse ɗin ce ta riƙeta, aikuwa ta fincike "Baki da cikakkiyar lafiya fa, kina ɗauke da juna biyu bai kamata ki riƙa wasa da lafiyarki ba."

Kallon Ahmad tayi, ya sunkuyar da kanshi ƙasa. Gabansa ta ƙarasa tace "Ka faɗa min ina Jannat?"

"Safi......."

"Jannat na tambayeka Malam" tayi maganar cikin tsawa.

"Tana emergency"

Da gudu ta fita daga ɗakin bata ma san wane asibiti bane dan idonta ya rufe.

Sai da ta tambaya sannan aka nuna mata, kai tsaye ta faɗa. Aikuwa bata ƙarasa ba akayo waje da ita.

"Likita ƙanwata ce, dan Allah karki hanani ganin ta"

Riƙo hannunta tayi tace "Kiyi haƙuri likito ci na kanta, zaki ganta amma ba yanzu ba."

"Dan Allah ku ceto min rayuwar ƙanwata idan har na rasata nima mutuwa zanyi" cikin kuka take wannan maganar.

Ahmad kuwa daga can nesa da ita sosai ya tsaya domin ya san idan har ya ƙaraso inda take to za a iya samun matsala.

09:00pm

Fitowar likita ya saka ta miƙe daga kujerar da take zaune, ta ƙarasa gabanshi da sauri.

"Doctor ya ƙanwata?"

Cikin tausayawa ya kalleta yace "Koyi haƙuri zata samu lafiya insha Allahu, amma dai for now ba zaki iya ganin ta ba,ki biyoni office zan miki bayani.

Da sauri ta bi bayan shi, a office ma bata zauna ba. Har sai da yace ta zauna sannan ta zauna tana kallon shi cikin tashin hankali.

"Amma garin ya ya hakan ta faru?"

Cikin kuka ta ce "Doctor a bar tone-tone dan Allah, kawai ka faɗa min abinda ke damun Jannat.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Sakamakon Fyaɗe da aka yi mata, anyi amfani da ƙarfi, da kuma ƙwayoyin ƙarin feelings, sannan wanda yayi mata yayi sa ne cikin forcing, hakan ya saka ya ji mata ciwo sosai har ta kamu da cutar VVF"

"Me...hak...hakan ke nufi, ka...na...nu..fin..kace min Jan...nat ta kamu da cutar yoyon fitsari?"

"Ƙwarai haka nake nufi, amma zata iya warkewa idan har aka yi mata aiki, zamu tura ku can asibitin masu wannan larurar a can ne zaku ji ƙarin bayani"

Miƙewa tsaye Safina tayi ta buga table ɗin tare da cewa "Ba zai wuyu ba wallahi ƙarya kake"

Hannu ta ɗora a ka tayi salati da ƙarfinta tare da cewa "Ahmad ka cucemu Allah ya isa, Ahmad meyasa, me muka maka, wannan itace ribar son dana nuna maka...meyasa sai Jannat?" A take a gurin ta zube ta sake suma.

Ahmad kuwa yana laɓe, yanajin ance yoyon fitsari ya arce. Gidan ya fara komawa ya ɗebi kaya a trolley ya saka a jaka. Abuja ya tafi ba tare daya sanarwa kowa ba, daga csn kuwa ya ɗauki alwashin wucewa wata ƙasar har sai komai ya lafa.

2 days later

Safina ita take jinyar Jannat, daga ita har Jannat ɗin kuma cikin kuka suke da tashin hankali. Sam Safina taƙi sanarwa gida abinda ke faruwa gudun kar ya zama surutu. Sai dai ta kira Sa'ad ta sanar dashi abinda ya faru, sai dai Jannat ɗin ts roƙeta da tace ɓarayi ne suka shiga gidan amma kar ta faɗi wannan abin kunyar.

               *******

Ummu, Hannatu da Sa'ad yau sune suka zo dubiyar Jannat a asibitin Nassarawa.

Tana zaune akan gadon an saka mata ledar fitsari, idan ta cika Safina ke juyewa ta zubar.

Suna zaune Umma tana ta fama toshe hanci da gyalenta duk da cewar akwai turaren wuta kuma ɗakin baya zarni sosai.

"Gaskiya sun cutar da ke Jannat sannu"

Hannu ta saka ta goge hawaye ba tare da tace komai ba.

"Jannat naso aurenki da Sa'ad kuma naso zama dake sai dai ba abu ne mai yuwu wa ba"

Gaba ɗaya suka kalli Umma. Sa'ad ne ya fara cewa "Umma kamar ya? Ni ai so nake zuwa jibi a saka ranar mu, hakan zai iya rage mata jin raɗaɗin abinda aka mata"

"A saka maka rana kai dawa? Yarinyar da aka yiwa fyaɗe har da yoyon fitsari, wama ya sani ko wanda yayi mata yana da cutar ƙanjamau ko kuma ciwon sanyi?"

Dirowa Safina tayi daga kan gado ta nuna Umma da ɗan yatsa. "Ka da ki ƙara jifan ƴar uwata da muna nan kalamai"

"Ka da ki ƙara nuna uwata da yatsa" Hannatu ta faɗa tana nuna Safina.

"Safina dan Allah ki bari" Jannat ta faɗa tana shashsheƙar kuka.

"In bar me? Wai bakya jin abinda matar nan ke faɗa a kanki"

"Mahaifiyar Sa'ad ce"

"Ko ma wacece, ita bata duba irin halaccin da kika mata ba, shine take faɗar haka"

"Na shiga uku" Jannat ta furta tare da rufe fuskarta da hannayenta.

"Ban yiwa Jannat dole a kan sai tayi tarayya da ɗana, dan haka Sa'ad ka zaɓa ko ni ko Jannat dan ba zan taɓa yarda ka auro mana annoba ka kawo min gida ba" tana gama faɗa ta wuce ta bar ɗakin.

Hannatu ma kuka ta fashe dashi, ta ƙarasa jikin gadon ta riƙo Jannat tare da cewa "Wane irin mutane ne mu? Muddin muka gujeki ba zamu taɓa wanyewa lafiya ba, ki saka a ranki, zan yi duk iya iyawa dan ganin na ganar da Umma." Juyawa tayi ta kalli Sa'ad tace "Kace wani abu Yaya"

Juyawa yayi kawai ya fita Hannatu a fili ta saki kukanta sannan tace "Kiyi haƙuri Jannat" itama juyawa tayi ta fita.

Safina ta ruƙo Jannat tana kuka mai taɓa zuciya. "Idan da na san haka zata faru, da ban janyo ki gidan ba, Ahmad ya cuceni, ya gudu ban ma san ina yayi ba, ba zan taɓa yafe mi shi. Ki yafe ni Jannat"

Itama cikin kukan tace "Wannan shi ake kira ana zaton wuta a maƙera sai ga ta a masaƙa. Safina baki da laifi domin kin jawo ni ne saboda kar na shiga wani halin" shashsheƙar da ta fara ne ya saka ta ɗan tsaya kafin tace "Yau an wayi gari na rasa budurcina ba ta hanyar aure ba, wanda naso yayi aure, wanda na tausayawa yana neman tafiya ya barni, ban taɓa dana sanin zuwana duniya ba sai yau, wace ƙaddarace wannan? Mijin yayata ya lalata rayuwata, ki kirawo min Mommy dan Allah ki kirowata mutuwa zanyi."

"Ina tsoro ina tsoro Jannat."

"Safina kar sai bayan na mutu ki fara dana sanin rashin faɗawa Mommy halin da nake ciki"

"Shikenan zan kirata" ta faɗa tana kuka. Janyo wayarta tayi ta kira number Mommy ta faɗa mata cewar Jannat ba lafiya yau kwanan su biyu a asibiti. Hankalin Mommy ya tashi kuwa, tace gata nan zuwa. Safina ta faɗa mata asibiti da kuma ɗakin da suke.

Tana gama faɗa ta miƙe ta durƙusa har ƙasa tace "Jannat ina jin kunyarki, Jannat ki yafe min, gani nake kamar ni ce Sanadi"

"Ko kaɗan baki da laifi Safina, wannan itace ƙaddararmu"

"Zan bar asibiti har sai su Mommy sun tafi, ni ba zan iya haɗa ido dasu ba, ace mijina ne yayi miki fyaɗe, matuƙar Umma zata zauna anan, to ni kuwa bazan dawo ba?

Karki tafi ki barni dan Allah Safina" janye hannunta tayi ta fita kawai daga cikin asibitin ta lula duniya tunanin irin yadda Ahmad ya so ta amma wannan shine sakamako.

Kan titi tahau domin bata cikin hayyacinta a lokacin,aikuwa mota ta banketa, a take a gurin ta zube jini ya ɓalle mata, ga kanta ya fashe.

Ta mutu ne?

Me zai faru a gaba?

Ya makomar Jannat? Kuna ganin Sanadin ta ne ko na mahaifinta?

Ina Khalil?

#Vote

#Comment

#Share

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol