Free chapter 路 Read without an account

PAGE 02.

by Sumaiya M Tukur 路 RASHIN SANI

馃挮馃挮RASHIN SANI 馃挮馃挮

STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).

Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).

Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.

Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.

PAGE 02

CIGABAN LABARI...

Aimana tana nan kwance a dakin Dada har dare,duk cinyoyinta sunyi tsami suna mata ciwo, dakyar ta lallaba tayi sallan magariba da isha, ko abinci ma a nan Dada ta kawo mata,shima dakyar taci, ga kanta dake mata ciwo dalilin kukan da tayi,magani Dada ta bata tasha bayan ta gama cin abinci ta kwanta, Dada tayi sababi da mita kamar zata ari baki,haka dai ta gaji ta hakura ta kwanta itama bacci ya dauke ta.

Baba kuwa sanin yau ya tabo Dada yasa yayi shiru kamar baya gidan,duk sababin da Dada take yana ji,dalilin haka yau ko sai da Safe baije yiwa Dada ba sanin zai sha fada, Mama sai dariya take masa, ya bari in tayi bacci yaje ya leka ta.

Haka kuwa akayi,saida yaji shiru tukun ya leka duk sunyi bacci, murmushi yayi yace " Dadata kenan, Allah ya kara tsawon rai mai anfani, ke kuma Aimana Allah ya shirya min ke" kashe musu wuta yayi hade da rage musu gudun AC sannan ya fice.

Duk da Baba ba mai tsananin wadata bane amma yana da rufin asiri daidai gwargwado,ya wadata gidansa da abubuwan more rayuwa iya karfin shi, gida ne madaidaici 3 bedroom flat nashi, sai na Dada dake gefe ciki da falo sai madaidaicin kicin nasu a tsakar gida da kuma wani karami a falon Mama, sai filin tsakar gida mai dan girma, shima an zuba masa broken tiles yayi kyau, gashi ko yaushe zaka ganshi fess dashi kamar ba tsakar gida ba.

Tun asuba Dada ta tashi,ta tashi Aimana don gabatar da sallan, kasancewar Dada macece mai riko da addini,bata barin lokacin salla ya wuce ta ko yaya ne sai dai kuma in ciwo,shima in zata iya ko a kwance sai tayi,don takan ce bata san ko Allah zai sa ta tashi har ta rama ba, ba kuma tason mutuwa da bashin sallah a manta.

suna idarwa Aimana ta fito taje ta gaishe da su mama kafin tafara sharan tsakar gida hade da kicin kasancewar taji sauki Alhamdulillahi, kuma tasan in ma batayi ba Mama ba barin ta zata yi ba ko zatayi latti sai tayi, shiyasa ma yanzu bata jiran sai ance tayi, don bata son makara saboda dukan latti.

Tana kammalawa tayi wanka ta shirya kafin tazo ta karya da alalen da Mama tayi da safen nan,ta sabi jakanta tare da musu sallama, Baba ya bata kudin break hade da mata kashedin ba ruwanta da yaran jama'a.

Yau ita kadai zata tafi don Abdul baya nan a gida daddy ya kwana duk wannan wainar da ake toyawa ma bai sani ba.

Tana fita ta hango Kamal shima ya fito da shirin tafiya, hannu ya daga mata, da sauri kuwa tazo tana yake masa hakwara.

"Ya Kamal ina kwana"

"Lafiya kalau Aiman Dada"ya amsa tare da mayar mata murmushi, suka fara tafiya a tare kasancewar makaranta daya suke zuwa.

Kamal yaron makwabcin sune, gida biyu ne a tsakanin su, sosai jininshi ya hadu da Aimana, bata jin maganan kowa a unguwar sai na kamal, kuma bata magana da duk wani saurayi a unguwar inba Kamal ba.

Malam Mohammad shine mahaifin Kamal,matarsa daya Hauwa wacce suke kira umma, sai yaransu hudu, Kamal shine babba, sai Umar, sai kuma Yan biyu Hamida da Humaida, sune suke sa'a da Aimana,kuma kawaye ne sosai, ajinsu daya a makaranta, sai dai su sarakan latti ne, Kamal bai jiransu kasancewar shi prefect ne,da wuri yake tafiya,dake Aimana ma bata latti yawanci tare suke tafiya.

Suna tafiya suna hira har suka isa makaranta,dayake makarantan ba nisa a kafa suke tafiya, suna isa Aimana ta masa sallama ta nufi site nasu na primary, shima yayi site nasu na yan secondary, Aimana sune masu yin command Bana, a yayinda kamal kuma su zasuyi candy bana.

Shiganta aji ba dadewa su Hamida suka iso Suma, zama sukayi dake sit nasu daya kowa ta ajiye jakanta.

Hamida ce tace,"to sarakan hanzari muma Allah ya kawo mu"

Aimana ta amshe da cewar" ku kuma sarakan latti ba, hala yau ma kopur ya zane Ku"

Hamida tace" ai kuwa munyi sa'a bai fara taran latti ba tukun"

Gyara zama Aimana tayi tace"yau akwai labarin, amma dai bari sai anjima"

Humaida tace "don Allah ni ki gaya mana kar kija mana rai"

Aimana tace" Ku dai kuyi hakuri nafi so ku gani kafin kuji labarin".

Hamida tace "ki gaya mana kawai malama"

Tace to shikenan, ta bude baki da niyar fada musu kenan malaminsu ya shigo dole suka hakura,yana fita kuma wani na shiga, basu samu kansu ba sai da aka fita break.

Suna fita kuwa Humaida tace "bamu musha," tace to kuzo in Baku, wuri suka samu suka zauna.

Aimana tace "kudai wallahi ba daga nan ba wurin jin gulma" suka ce eh munji.

Gyara zama tayi ta tace "ina yaron nan Shamsu na ajin su ya Abdul yayan su fiddausi, suka ce eh, "to jiya Allah ya bani sa'a na samu na targade masa 'yan yatsu"suka hau shewa suna tafi, "kai Aimana garin yaya?, labarin duk abunda ya faru ta basu, har punishment da Baba ya mata, suka jajanta mata

Mikewa sukayi suka je sukayi break suka koma aji aka ci gaba da darasi har zuwa lokacin tashi suka fito, suna riga su Kamal tashi, wani lokacin suna jiranshi yauma hakance ta faru, Aimana tace sai ta jira Abdul, shiyasa suma su Hamida suka tsaya.

Minti talatin tsakani suma aka tashe su,sun fara fitowa ba jimawa su Abdul ma suka fito tare da Kamal suka kama hanyan gida.

A hanya take ba Abdul labarin abunda ya faru jiya, mai zaiyi inba dariya ba, yace"yanzu duk cika bakin Shamsu shine ya tsaya har kika targada shi"

Wani doro tayi tace"nidin aka ce ma ta wasa ce"

Kamal da yake jinsu yace"sannu da kokari kinji Aimana,ashe bance ki daina fada da maza ba?, wato kin daina jin magana ko, to shikenan ba ruwana dake, kai kuma dube ka wai kanwarka ce mai amsan ma fada maimakon kai zaka tare mata, zanga randa zakayi zuciya Abdul.

Narai narai Aimana tayi da ido tace" kayi hakuri ya Kamal bazan sake ba wannan dinma haushi naji shiyasa,kasan fa biron nan Daddy ne ya ban,shine na ara masa ya kai aka karya amma daga wannan bazan sake ba.

Yace "da dai yafi miki"

Haka suka cigaba da hira har suka iso kofar gidan su Kamal suka rabu suka karasa gida suma.

Suna shiga suka gaida iyayesu tare da kintsawa sukayi salla sannan suka ci abinci suka wuce islamiya.

Haka rayuwarsu take gwanin ban sha'awa don Baba tsaye yake akan yaranshi, basu rasa komai ba a rayuwa,ga uwa uba tarbiyya don Mama ma tana nata kokarin,ga kuma Dada a gefe, don itama ba mace bace mai wasa a fannin tarbiyar yaro,tana da tsanani tanan, shiyasa duk tsiyan Aimana akwai tarbiyya.

Kwanci tashi ba wuya har su Aimana sunyi command, yayinda Abdul yake, jss 3 yanxu, Kamal ma sun kammala sauran jiran sakamako, yanzu Abdul ne kadai ke zuwa makaranta, abun Sam baya masa dadi, su Aimana kam sai zaman gida daga islamiya sai hadda, rashin ji kuma sai abunda yayi gaba.

Yau tana tashi tace wa Mama gidan Daddy zata,tace "to sai ki shirya in anjima, ina da sako ma da zaki kaiwa mommyn taki", cike da farin ciki ta tashi ta hau shiri, kafin karfe goma ta kammala komai,taje tayi wanka ta shirya.

Direct wurin mama ta wuce tace "Mama na shirya", "oh su Aimana sarkin zumudi, to gashi turaren wuta ne ki kai mata,amma ki fara biyawa gidan Abbanku ki bawa ummi wannan tukun sai ki wuce,kuma kice ina gaishe su,don Allah Aimana banda tsokana da fada,kuma ki kula da hanyan"

Ta karba tace to Mama insha'Allah, amma don Allah in kwana tunda gobe jumma'a ba islamiya, sai in dawo goben.

Tace "wannan kuma sai na fadawa babanku,duk da dai nasan ba hanaki zaiyi ba,kije ki sallami Dada kafin ki tafi,kuma karki manta da addu'an fita gida, Allah ya tsare min ku.

"Ameen Mamata ta kaina insha'Allah bazan manta ba, Allah ya barmin ke ki dade kiyi lasting hajiya ta," ta fita tana dariya.

Murmushi Mama tayi tana jin tsananin kaunar yar diyarta tilo da Allah ya bata,tace Allah ya shiryamin ke Aimana da dukkan 'ya'yan musulmi baki daya.

"Dada! Dada! Wai ni kam tsohuwar nan bacci kikeyi ne" ta fada tare da leka falon Dada.

can ta hangota tana sallan walaha,tace ho su Dada 'yan aljanna Allah yasa mu a danshinku,in kin idar dai ni na tafi sai kuma gobe in Allah ya kaimu,zance kina gaishe su duk da baki fada ba," tana gama magana ta saki labule ta nufi kofar fita,ta tsaya ta karanto addu'arta kafin ta fita.

(BISMILLAHI TAWAKKALTU ALALLAHI WALAHAULA WALAKUWWATA ILLA BILLAH, Annabi SAW tace duk wanda ya karanta wannan addu'ar yayin fita dag gida, to yana cikin kariyar Ubangiji har zuwa lokacin da zai dawo, Allah ya bamu ikon yi a koda yaushe)

Tana fita ta tare abun hawa ya kaita unguwar su Abba, wato Sulaiman yayan Baba, da sallama ta shiga gidan,daga ciki ummi ta amsa,tace shigo.

Shigowa tayi ta same ta a falo,Abba baya nan,ya tafi kasuwa,don shima ya watsar da aikin gwamnati ya koma kasuwa, kuma Alhamdulillahi ya samu budi sosai, don shaguna uku ne dashi yanzu a kasuwa.

"Wa nake gani kamar Aimana" cewar ummi dake zaune rike da autan ta dan shekara uku.

"Ita din ce dai ummi, nace dai yau kam bara na kawo muku ziyara, ina kwana"

"Lafiya qalau Aimana ya su Dada da Mama,kwana biyu nima bamu gaisa ba"

"Lafiyan su qalau ummi sunce a gaishe Ku"

"Muna amsawa,kuna Shan hutu abinku ko?

"Eh wallahi ummi sai islamiya,ga wannan ma inji Mama in kawo miki" ta fada hade da mika mata sakon mama.

"Ai ko nagode kaman ta San ina son turaren kuwa, don wanda nake dashi saura kadan, sauran kuma basa min dadi sai dai insa kawai don ba yanda zanyi"

Dariya tayi tace" ummie tamu kenan, ina su Afrah?

"Suna cikin dakinsu,ai basu san kinzo ba da yanzu kin gansu,tashi kije suna ciki"

"To ummie bara na shiga", ta mike tare da nufar hanyan dakin su Afrah.

karo taci da ya Munnir a hanyan,da wuri ta sunkuya ta gaishe shi, don tasan yanzu sai ya rankwasheta a banza, don baya daukan rauni ko kadan, ya mugu suke kiranshi don tsaban cin zalinshi,har iyayen fada suke masa akan ya rage zafin rai.

Amsa mata yayi kamar baya so ya wuce,hamdala tayi itama ta shige wurin su Afrah.

Anan ta samu adda Amal ma suna hira, nan ta shige cikin su aka ci gaba da gashi,dama zani ce ta tadda muje, Afrah da Ruma sune kusan sa'o'inta a gidan, Afrah ta bata shekara daya ita kuma ta ba Ruma shekara, Adda Amal kam barin musu dakin tayi ta tafi nata.

Nan suka baje koli, sai da tayi azahar kafin ta wuce gidan Daddy, kwankwasa tayi Baba Habu mai gadinsu yazo ya bude,ganin Aimana ne ya washe baki yace..

"A'a, su Aimana ne yau a gidan,lallai yau anyi babban kamu"

Dariya tayi tace" Baba Habu Allah da abun dariya kake, babban kamu sai kace wata kifi? Kaidai baka rabo da abun dariya,to yanxu dai ina yini"

"Lafiya qalau diyar albarka,ya gidan naku?

"Alhamdulillahi Baba,bari na shiga ciki"

"To a fito lafiya"

"Allah yasa", daga haka tayi cikin.

Sa sallama ta shiga falon, saidai ba kowa sai sanyin AC da kamshin turare hade da room fresh ne kawai ke tashi,wani kofa ta nufa tayi sallama ta shiga,wani madaidaicin sitting room ne, daga ciki aka amsa mata,shiga tayi,ai da gudu ta karasa ta fada a kanta tana mai farin cikin ganinta.

"Adda Nana yaushe kika zo" ta tambaya fuskanta dauke da farin cikin ganin addan nata.

"Jiya nazo my sweet Aima,yau nake gayawa mommy zanje in ganki don nayi missing naki,sai ga kiran Mama tana tambaya ko kin iso.

"Oh Adda Nana ai na tsaya gidan Abba ne, da nasan kina nan ai da na taho da wuri"

"Aiko nima kamar naje na dauko ki da naga baki zo ba tun dazu"

"Kai Adda Nana, yanxu dai bara na gaida mommy tukun,kar mu zauna surutu in manta", tana gama magana ta mike tayi daki wurin mommy.

Sallama tayi ta shiga, tarar da ita tayi tana jera kayan wankinta da aka kawo, ta gaishe ta sannan ta bata sakon Mama, ta karba tana jin dadi sosai.

Ta mike tace"mommy bari naje falo" murmushi mommy tayi tace "ai tunda naga kina ta hanzari nasan mutuniyar ki kika gani a can", "aikuwa dai mommy kin dago ni da wur"i.

Fita tayi ta samu Adda Nana a falo, anan suka baje hiran su, tana ta bata labarin school,dayake Adda Nana tana makaranta ne a Nile University Abuja, yanzu ma sun dan samu break ne na sati biyu shine tazo gida.

"Adda Nana muna ta hira ina tsaraban school"

"Wani tsaraba ne a school Aimana in banda na karatu, kuma dai Allah ya kaiku wannan matakin kuji yanda yake"

Kyalkyala dariya tayi tace"Adda Nana yaushe kuma kika zama raguwa, kece mai cewa karatu akwai wahala,tabdi"

"Hmmm Aima bazaki gane ba sai kinje can, amma jami'a ba kamar primary da secondary bane, sai kinkai lokacin zaki gane abunda nake nufi"

"To Adda Nana, Allah ya taimaka,muma dai yanzu sai jss, girma yazo"

"Uhumm yan jss manya, muje in nuna miki wani abu" suka mike sukayi dakin Nana, cirowa tayi daga jakanta ta mika mata.

Wani tsallen murna tayi tare da rungume Nana tana mai jin dadi, ganin abunda ta dade tana so........

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol