Free chapter · Read without an account
BABI NA ƊAYA
BA NI DA IKO...
©Fareeda Abdallah
Bismillahir rahmanirraheem
In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.
Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages daga page 1 zuwa 10 in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting a nan Whatsapp.
1)
A tausashe yake kallon fuskarta, da idanu masu bayyana matsananciyar ƙauna da Soyayya. A hankali ya fara sauke idanunsa ƙasa-ƙasa har ya dire su akan tsohon cikin da yake jikinta, haihuwa ko yau ko gobe. Lokaci ɗaya wani matsanancin farin ciki ya ƙara yalwata a zuciyarsa, farin cikin da bai tsaya a nan ba, sai da ya bayyana akan kyakkyawar fuskarsa. Kyawun da duk da shekaru sun ja a tare da shi, har yau bai gushe a cikin jerin kyawawan dattijan da suka yi tashe a zamanin samartakarsu ba.
Kamar ko wane lokaci in dai za ta shiga turakarsa, ranar girkinta ko ba ranar girkinta ba. Hannunsa ya ɗaga ya shafo ritsetsen cikin da bai ɓoyu a cikin zumbulelen hijabin da yake jikinta ba.
A kunyace, da yanayin shagwaɓa a sassanyar muryarta ta ce
"Kai Malam...!"
Ƙaƙƙarfan dariyar da ya kwashe da ita shi ne ya katse ƙorafin da ta fara yi mishi. Dariyar da dirar sautinta a kunnuwan Inna Ramatu da ke can waje a madafa tana dama kunu, ya zama tamkar saukar ruwan dalma a kunnuwanta. Runtse idanu tayi da sauri, cikin ƙanƙanin lokaci wasu zafafan hawaye suka fara tseren sauka daga idanuwanta.
A can cikin turakar Malam kuwa, kasa haƙuri yayi, daga shafa tsinin cikinta yana murmushi sai da yasa hannu ya janyo ta zuwa jikinsa. Saboda tsinin cikinta ta baya ya rungumeta. Hannayensa duk biyu suna kan cikin da ya ƙwallafa rai, shafawa yake sannu a hankali cikin lallaɓa kamar mai shafa ɗanyen ƙwai da bai gama shan iska ba.
Kansa ya ɗora a kafaɗarta saboda ya fi ta tsawo. Kasancewarsa cikin jerin mutanen da Allah ya huwace musu ƙatuwar murya yasa sai da ya rage muryarsa sosai ya raɗa mata
"Haba Amaryata. Me nayi miki da zafi kike neman hana ni gaisawa da farin cikina?"
Kafin ta amsa sai ya juyo da ita suna fuskantar juna. Kan kujera ya zauna, ba tare da jin nauyinta ko na cikin da yake jikinta ba ya zaunar da ita akan cinyarsa. Hijabin jikinta ya tattare zuwa sama, ya ɗage rigar jikinta, turtsetsen cikin ya bayyana a fili.
Bakinsa ya sa ya sumbaci daidai cibiyarta. Kamar ɗan cikin ya san abinda ke faruwa a lokacin sai kawai yayi ƙwaƙƙwaran motsi. Motsin da har Malam sai da ya ji a bakinsa da ke kan fatar cikin. A karo na biyu ya sake kecewa da dariyar farin ciki, kamar ƙaramin yaro sai ya fara magana da jaririn da ke cikin cikin.
"Abdullahi, ka ga Innarka tana so ta hana ni gaisawa da kai ko?"
Sai kuma ya ɗauke bakinsa ya kara kunnensa a cikin, kamar dai yana sauraren abinda Jaririn da ke cikin cikin yake cewa.
Can kuma sai ya cire kunnen ya mayar da bakinsa yana cewa
"To! Ba damuwa Abdullahi. Shi kenan, na haƙura. Ah ai dole, kaima ka san dole Innarka za ta cigaba da cin tabarrakinka mai babban suna. Allah dai ya nuna min ranar da za ka fito duniya in ɗauke ka da hannaye na..."
"Amin thumma Amin."
Ta amsa a hankali. Fuskarta cike da murmushin jin hiran Malam da jaririn da bai san abinda Duniya take ciki ba. Duk da wani ɓangare na zuciyarta cike take da fargabar tsawon lokacin da take ƙara ɗauka a cikin ɗakin, bayan gagarumin kashaidin da Inna Ramatu tayi mata akan hakan, kwanaki uku da suka wuce.
Domin katse ƙara yawaitar cin lokacin yasa ta fara yunƙurin faɗa masa abinda ya shigo da ita turakarsa a daidai lokacin
"Malam..."
Yatsarsa manuniya ya ɗora mata a baki, har lokacin murmushin fuskarsa bai ɓace ba ya ce
"Amma fa Binta tunda aka yi hoton cikin nan aka tabbatar namiji ne a ciki na ce ki dinga ce min Baban Abdullahi. Me yasa kike mantawa?
Murmushi tayi, a kunyace ta ɗaga hannu ta shafi gefen kumatunsa.
"Kayi haƙuri Mal... Au! Baban Abdallah!"
Ta kira sunan Abdullahi da yanayin gayu tana dariya.
"Na ji, na haƙura. Yanzu dai tunda na gaisa da Yaro na faɗa min abinda ke tafe da ke."
Yayi maganar idanunsa na kanta.
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi, zuciyarta cike da taraddadi da addu'ar Allah yasa kar ya sake ce mata a'a a wannan karon ta ce
"Daman zan tuna maka gobe ne za'ayi addu'ar ukun Baffan Hauwa Bafulata. Idan ka amince bayan mun idar da sallar asubahin gobe sai muyi sammakon tafiya ni da Hajiya muyi musu gaisuwa..."
Ganin yadda yanayin fuskarsa ya sauya cikin ƙanƙanin lokaci yasa jikinta yayi sanyi, har ta kasa ƙarasa maganar da take yi. Idanunta ta saukar ƙasa, kamar baza ta cigaba da magana ba, sai kuma ta ce
"Shi kenan! Allah ya baka haƙuri Baban Abdallah! Na haƙura da zuwa gaisuwar, tunda zuciyarka ba ta so. Daman dai na duba ƙaunar da ke tsakanina da ita Hauwan ne shi yasa na nace in je mata gaisuwar rashin mahaifinta. Amma tunda ba ka so na haƙura..."
"Kin tabbata? Kin haƙura har zuciyarki Binta?"
Ya katse ta da tambayoyin tun kafin ta aje numfashin maganarta.
Fuskarta da murmushin yaƙe ta ɗaga mishi kai alamun eh! Ta haɗiye wani dunƙulallen miyau mai kauri a maƙoshinta, zuciyarta cike da baƙin cikin yadda a mafiyawancin lokuta yake hana ta fita har akan abubuwa masu muhimmanci, amma ko kusa bata bari ɓacin ran ya bayyana ba.
Domin ta ƙara share masa tantama a karo na biyu sai ta sake shafo ɓangaren kumatunsa na dama.
"Duk da dai na so zuwa da farko... Amma da gaske a yanzu na haƙura. Farin cikinka ya fiye min komai Baban Abdallah..."
"Shi kenan. Allah ya miki albarka Binta."
Ya faɗa fuskarsa cike da yalwataccen fara'a. Kafin ta amsa ya cigaba da cewa
"Shi yasa fa a kullum nake ƙara ƙaunarki a zuciyata, ba don komai ba sai don wannan ladabi da biyayyar taki."
"Amin ya Allah. Na gode Malam."
Ta amsa tana murmushi.
Shiru ya ratsa tsakaninsu na tsawon daƙiƙu sittin. Ita kanta yana ƙasa tana wasa da yatsun hannayenta, shi kuma idanunsa yana kallon kyakkyawar fuskarta da fara'a a fuskarsa.
Yunƙurin miƙewa tsaye tayi, a lokaci ɗaya kuma tana cewa
"Bari in je, kar in shiga cikin lokacin Yaya sosai. Sai ka fito Malam."
Baiyi yunƙurin hana ta fita ba, bai ce komai ba, yana kallonta zuciyarsa cike da saƙe-saƙe har ta isa bakin ƙofar ɗakin tana daf da ficewa.
"Binta?"
Ya kira ta a tausashe.
"Na'am! Malam"
Ta amsa a ladabce.
"Goben idan Allah ya kaimu ku shirya ke da Hajiya kuje gaisuwar ku dawo. Zan yi magana da Yaron nan Haladu, ya samu abokinsa ɗaya sai su zo da Baburansu su kai ku kuyi gaisuwar ku dawo. Amma don Allah kar ku je ku daɗe."
Tun kafin ya ƙarasa maganar da yake yi fara'ar gaske ya mamaye fuskarta, sassanyar kallo mai bayyana ƙauna take aika mishi har ta taka ta koma inda yake zaune, ƙasa tayi niyyar zubewa bisa gwuiyawunta kamar yadda ta saba domin tayi mishi godiya bisa faranta mata da yayi amma sai yayi saurin riƙo kafaɗunta.
"Na faɗa miki ki daina garajen durƙusawar nan da kike yi Binta, a yanzu cikinki ya yi nauyin da bazai jure duk ire-iren waɗannan abubuwan ba."
"Kayi haƙuri Baban Abdallah. Zan kiyaye in sha Allahu."
Sai ta ɗanyi shiru tana mayar da numfashi.
"Wallahi farin ciki ne yayi min yawa sanadiyyar amincewarka. Na gode. Kai kanka ka sani Malam a cikin shekaru biyu na haɗuwarmu da Hauwa a dalilinka tana yi min kara a duk wani al'amari da ya shafe ni."
"Uhmmm! Haka ne Binta. Nima abinda na tuna kenan shi yasa na barki kije mata gaisuwa."
Ya amsa yana wani irin murmushi mai kama da ta ƙasaita.
Tsabar farin ciki yasa Binta karkace kai ta fara jera mishi kirarin da yake fasa mishi kai kamar yadda take mishi idan tana son koɗa shi.
"Allah dai ya ƙara maka lafiya da nisan kwana Baban Abdallah... Alhaji Balarabe Sarkin Noman Kasuwar Magani, Uba a gurin Zainab da Zakiyya, Baba a gurin Hasiya da Ruƙayya, tsayayyan mahaifi a gurin Hadiza da Aliya, Na Yaya Ramatu uwargida sarautar mata, Ango a gurin Binta ba da kanka a sare ka je gida ka ce ma Hajiya ya faɗi."
Saboda tsananin daɗi da girman da kansa yake yi idan tana yi mishi ire-iren waɗannan kirarin bai san sa'adda ya sake kwashewa da wata ƙaƙƙarfan dariya ba. Dariyar da sai da ya ɗauki tsawon minti ɗaya yana yi, daƙyar ya iya tsagaitawa yana kallonta da murmushi, a zuciyarsa yake jin yadda ako wane lokaci yake ƙara son Binta. Shekaru biyu da rabi kenan da ya aure ta, amma a kullum sake zuwa mishi take yi da wasu ire-iren salo na tarairaya da girmamawa da kambamawa, ɗabi'ar da yake saka shi ƙara jin ta a ko wane lungu da saƙo na zuciyarsa. A yadda yake ji kamar jiya ya auro ta.
A tausashe da girmamawa da salon iya magana ta ce
"Ammm na ce Baban Abdallah ina nan ina Rugar Na Bello saboda Allah? Duka-duka tafiyar babu nisa fa, kuma ka manta na faɗa maka a Asibiti sun ce in dinga yawaita zurga-zurga masu ɗan nisa saboda samun sauƙi gurin haifo Abdallah? Muna wuce Gonar Malam Musa fa, muka wuce Gida mai Rijiya, shi kenan sai Rugar Na Bello. Duka-duka tafiyar baza ta wuce ta mintuna talatin ba. Kuma muna tafe a hankali muna hira da Hajiya nan da nan za mu isa in sha Allahu. Don Allah ka bari mu taka sayyadarmu."
"Shi kenan. Tunda haka kike so. Ni dai ina sake jaddada miki kar ku daɗe, idan kuwa kika bari kuka daɗe ke da sake fita sai bayan kin haifi Abdallah ya yi watanni shidda cur...!"
"In Allah ya yarda ma baza mu daɗe ba."
Ta katse shi tana dariya.
Ya buɗe baki zaiyi magana sai ga sallamar Uwargidansa Inna Ramatu a ƙofar turakarsa. Ko kafin su amsa mata, har ta saka hannu ta yaye labulen ƙofar ɗakin ta cuso kanta cikin ɗakin, fuskar nan nata a ɗaure tamau, kamar wacce bata taɓa sanin yadda ake dariya ba.
Zumbur! Binta tayi gaggawar miƙewa tsaye tana zazzare idanu. Sai dai kuma ta riga ta makara, abinda take gudun Inna Ramatu ta gani ta riga ta gani, zaman da tayi akan cinyoyin Malam ɗare-ɗare kamar ta samu kujera Innar ta riga ta gani. Wani abu da bata sani ba ma shi ne, tun kafin Innar ta shigo daman ta daɗe tana laɓe a ƙofar ɗakin, kuma tana laɓen tana ɗan leƙo gefen labulen a dabarance don ta gani kuma ta ji abinda suke tattaunawa.
Fakar idanun Malam Inna Ramatu tayi, ta aika ma Binta wani mummunan kallo da lokaci ɗaya yasa yaron cikinta takurewa ya dunƙule guri ɗaya. A tsorace, kuma a gaggauce ta kawar da idanunta gefe ɗaya. Domin Allah ya sani tana tsoron Inna Ramatu, saboda mace ce mai makircin tsiya, kuma masifaffiya ce ta bugawa a jarida a bayan idanun Malam.
Da sassarfa ta kama hanyar ficewa daga turakar tana cewa da Malam da Inna Ramatu a lokaci ɗaya.
"Malam na tafi, sai ka fito. Sannu da aiki Yaya."
Bata jira amsawar ɗaya daga cikinsu ba tayi gaggawar ficewa daga ɗakin.
"Ramatu?"
Malam Balarabe ya kira sunanta a ɗan kausashe bayan ya tabbatar Binta ta yi nisa da turakarshi.
"Na'am Malam"
Inna ta amsa, bayan ta ƙaƙalo murmushin yaƙe da ya fi kuka ciwo ta yaɓa a fuskarta.
"Ramatu sau nawa ina yi miki kashaidi akan kina yin sallama kafin a amsa miki ki faɗo min cikin turaka kamar an hankaɗo ki?"
Ya tambayeta bayan ya ƙara ɗaure fuska tamau.
Kwanon shan kunun da yake hannunta ta ajiye a tsakar ɗakin, sai kuma ta zauna a ƙasa tayi kalar ban tausayi da fuskarta ta fara bashi haƙuri tana matsar idanu da hanci kamar mai kuka.
"Uhmmm! Ramatu kenan! Ina raba ki da kiwon awaki kina kyalla ta haihu. Wannan mummunar ɗabi'ar da kike neman tsira a cikin kwanakinnan ina tabbatar miki bazai haifar miki da ɗa mai ido ba. Binta dai matata ce, ko ranar girkinta ko ba ranar girkinta ba igiyar aure ya bani damar keɓewa da ita a duk sadda nake so. Ko ba don wannan ba ma Binta tsohon ciki take ɗauke da shi, cikin ma na ɗa namiji, irin cikin da aka tabbatar ya cika zuwa da tsarabe-tsarabe da laulaye-laulaye ba kamar na ƴaƴa mata da kika saba ɗauka kina haifa a sauƙaƙe ba. Da wannan dalili kuwa Binta ta cancanci in ninka kulawa ta a kanta. Don haka idan sa'ido za kiyi ki cigaba da yi. Kaza dai garin tone-tone take tono wuƙar yanka kanta."
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na daƙiƙu sittin. A ɗazu matsar idanun ƙarya Inna Ramatu take yi, amma a yanzu bata san sadda hawayen gaske suka fara sauka daga idanunta ba.
Ta buɗe baki za tayi magana Malam Balarabe yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu.
"Ban tambaye ki wani ƙarin bayani ko ƙoƙarin kare kanki ba. Nasiha ce nayi miki, ko ki ɗauka, ko kar ki ɗauka matsalarki ce. Je ki kaimin ruwan wanka."
Sau uku tana yunƙurin miƙewa sannan Allah ya bata sa'a ta ciɓa da ƙyar, saboda tsananin damuwar da yayi ma zuciya da gangar jikinta ɗaurin huhun goro. Ta taka a hankali ta fice daga cikin ɗakin, jikinta sanyi ƙalau kamar wacce aka sheƙawa ruwan ƙanƙara.