Free chapter · Read without an account
31
by Kansa'u Bello · MATAR MANYA
💓MATAR MANYA💓
By
OUM FATIMA
GAJEREN LABARI
PAGE 31
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
******* A ɓangaren Alhaji Murtala dala kuwa sosai rayuwarsa ta sauya, ya daina auri sakin da yake ya tsaya ya maida hankali wurin kula da tarbiyyar yaransa tare da taimakon Matar ƙwarai daya samu wacce bata duba rashin kunyar da yaran ke mata. Ƙoƙari tayi ta jasu a jiki take kyautata musu, yau da gobe har suka fara sakewa da ita.
Ƴanmatan kam sai a hankali domin kuwa Babarsu tayi musu wata irin tarbiyya wacce sai a hankali zata canza. A wannan lokacin ne Allah ya amshi ran Mahaifin Alhaji wanda ya mutu yana farin cikin shiriyar da babban ɗansa yayi ya gyara rayuwarsa.
Sati huɗu tsakani itama Hajiya Fatsuma ta koma ga Allah bayan doguwar jinyar data sha ba tare da zuciyarta ta rusuna ba, ta mutu ne zuciyarta cike da baƙin cikin faɗuwar da tayi. Babban Abinda yafi ƙona mata rai shine ƴan uban data tsani a haifawa yaranta su, sai dai aka haifesu bayan duk irin shige da ficen da tayi don ganin ta hana faruwar hakan, wanda a sanadiyar hakan ne ta haɗu da hatsarin da shine yayi ajalinta.
(Allah kenan mai yin yanda yaso a kuma lokacin da yaso ba wanda ya isa ya hana shi yin abinda yayi niyya. Allah ka tsare mana imaninmu).
___________★
Hanifah ta kammala karatunta ta dawo aka yi shagalin biki ta tare a madai-daicin gidan da mijinta ya sama mata, ba wani kantameme bane ginin flat ne mai kyau daya tsaru sosai aka zuba masa kayan da suka ƙara ƙawata shi. Sosai na danni zuciyata na kwantar da hankalina aka yi hidima lafiya aka kammala, inda ita kuma Aliya ta dasa shirmen da tayi a nawa bikin.
Sosai abinda nayi ya ƙara kankaro min mutunci a wurin Mijina da Iyayensa suka yi tasa min albarka.
Alhamdulillah rayuwa taci gaba ta tafiya mana cikin kwanciyar hankali sai larurori irin na yau da kullum da ba za'a rasa ba, sosai Suhail yake ƙara samun ci gaba a aikinsa da kuma Kasuwancinsa da yake yi a gefe, kofofin arziƙi buɗe masa suke yi sosai Kasuwancinsa ke ja yana kawo masa kuɗi.
A cikin sheƙara biyu ya sayi ƙaton fili a wata haɗaɗɗiyar unguwa ya gina Mansion ɗinsa mai ɗauke da part huɗu. Tsayawa bayyana tsaruwar ginin ma abin ba zai yiwu ba, domin komai daka sani da ake ƙawata gida an zuba shi. Duka ya haɗe kan Matansa a sabon gininsa inda ko wacce ta ɗauki part ɗaya, sauran ɗayan kuma ya bawa ƙaninsa da zai yi aure yace ya tare a ciki.
Zuwa lokacin na haifi yarona na farko a gidan domin nina fara haihuwa inda yaron yaci sunan Babansu Suhail Umar muke kiransa da (Abee). Shekara ɗaya tsakani na ƙara haifar ƴa Mace wanda a lokacin ne muka haihu tare da Hanifah da itama ta haifi ƴa Macen, rana ɗaya aka yi suna saboda kwana ɗaya ne tskaninmu, ni na fara haihuwa da dare kafin da safe Hanifah itama ta haifi tata ƴar.
A wannan lokacin Bestie nayiwa takwara aka sawa yarinya Kairiyya nake ce mata ( Little Bestie). Ƴar Hanifah kuwa Suhaila aka saka mata, sosai aka yi hidima wacce ta ƙayatar.
A ɓangaren Aliya shiru ita har yanzu Allah bai bata haihuwar ba wanda ita da Mahaifiyarta suke ganin kishiyoyinta ne suka hana ta haihuwar don haka suke ta asarar kuɗinsu wurin neman magani, abinda bata sani ba shine ita ce keda matsala a mahaifa ba zata iya ɗaukar ciki ba. Lokacin data takurawa Suhail da fitina shine ya ɗauketa ya kaita asibiti aka duba ta wanda ta jiyo mummunan labarin daya saka ta sume.
Sosai Suhail ya tausaya mata saboda kowa na son yaga ƙwansa a duniya sai dai idan Allah bai nufeka da samu ba sai kayi haƙuri ka rungumi ƙaddara.
An sha fama da ita sosai kafin a samu ta haƙura inda Suhail ya samu jari mai kauri ya bata yace tayi sana'a saboda ta ɗebe mata kewa tunda ita kaɗai ce bata yi karatu ba bata fita aiki.
Alhamdulillah komai ya wuce tayi haƙuri ta rungumi ƙaddara inda ta buɗe shagon sayar da suturu na yara komai daya dangance su, Alhamdulillah kuma kasuwancin ya amsheta don haka itama take ficewarta wurin kasuwancinta.
Bayan wani lokaci....
Sosai kawunan Matan Suhail daya zama baban mutum a yanzu suka haɗu wuri ɗaya, tuni muka haɗa kanmu muna zamanmu lafiya kuma muna zumuncinmu, inda zuwa yanzu na ƙara haifar yara biyu Namiji ɗaya Mace ɗaya inda Hanifah ta tsaya gayu bata ƙara ba. Da kaina na ɗauki yarinyata ta uku mai sunan Mamy wato Zaliha da muke kira da (Mamy) na bawa Aliya ta riƙe saboda zuwa yanzu na gamsu da sauyawarta na san ba zata cutar min da yarinya ba. Ai kuwa harda kukanta tana min godiya, hakan kuma ya kara soyayyata da ƙauna mai zafi a zuciyar Mijina wanda ko wacce daga cikin Matansa sun san soyayyarsa ga Salma ta da bance saboda babu wanda bai san labarin irin soyayyar da ya mata ba, kuma yake kan mata har abada.
Sai dai da yake mutum ne shi mai ƙoƙarin ganin ya kiyaye haƙkin kowa yasa ya iya tafiyar da gidansa cikin tsari ba tare daya tauye kowa ba, sai dai ya bar abin a zuciyarsa da kuma motsinsa da yake fallasa shi a wasu lokutan. Har gida Babar Suhail tazo ta min godiya ta saka min albarka akan abinda nayi na bawa Aliya kyautar ƴa, nuna mata nayi ba komai ai mun zama ɗaya. Kuma har cikin zuciyata da niyar alkairi na bata tamkar yanda na bawa Aunty su Ameerah da suka girma sosai abinsu.
Alhamdulillah babu abinda zan cewa Allah da ya wuce godiya domin kuwa farin ciki ya gama zagayeni tako ina a rayuwata, tun daga kan Iyayena, Iyayen riƙona da kuma ƴan'uwana da muka shirya muke zumunci tamkar bamu taba samun saɓani ba, sosai kuma nake ƙoƙarin taimaka musu da abinda Allah ya hore min.
Yaya Habu ma Suhail bai barshi haka ba sai da ya kaishi inda ake kula da masu shaye shaye-shaye irinsu aka ɗora shi a kan magani wanda yaci matuƙar azaba tamkar zai rasa ranshi a karshe Allah ya taimake shi ya warke tas sannan ya jashi a jiki ya bashi jari yace yayi kasuwanci. Baba Mari harda kukanta tana godiya da jin kunyar abinda ta rinƙa yi, gashi dai Hadizar data tsana ita da ƴaƴanta a gidan arziƙinsu take ci ita da nata ƴaƴan.
"Allah kenan." Malam Shehu yake faɗa mata lokacin da take kuka tana neman gafara. Mama tace mata babu komai ai tuni sun yafi juna komai ya wuce sai fatan Allah ya ƙara haɗa kansu ya basu zaman lafiya mai ɗorewa.
****** Yau Abban Abee a wurina yake don haka da wuri na tashi daga wurin aiki na dawo gida na ɗaura girki na kammala, mai tayani aiki da aka sama min saboda fita wurin aiki tuni ta gyara ko ina tsaf ta saka ƙamshi ta kama yara da suka dawo daga Makaranta tayi musu wanka ta shiryasu ta basu abinci, Malamim islamiyyarsu yazo ta jasu suka wuce domim har ita ake yiwa karatun.
Ina gama girki na kimtsa komai wanka nayi na tsara kwalliya ta mara hayaniya, wani sassauƙan leshi na ɗauko wanda kana kallonsa zaka san ya lashi kuɗaɗe wurin mallakarsa. Ɗinkin doguwar riga ne straight don haka ya zauna ɗas a jikina kai ba zaka ce na haife yara har shida ba, domin masha Allah ina da kyan jiki kuma ya haɗu da gyara.
Kusan ƙarfe 3:00pm ya shigo a gajiye don haka na tare shi na amshi jakar hannunsa ina masa sannu da zuwa, amsa min yayi a kasalance yana bina da ƙananun kallon da nasan me yake nufi da hakan. Murmushi nayi ina duƙar da kaina a hankali nace "Muje kayi wanka first your lunch is ready." Kallon ashe kin ganoni ya min yana hayewa sama na take masa baya ina murmushi.
Ruwan wanka na haɗa masa na raka shi bathroom ɗin sannan na fito na fitar masa da ƙananan kayan shan iska, zama nayi a bakin gadon na jira sa ya fito, taimaka masa nayi ya shirya kafin na riƙe hannunsu muka sauka ƙasa na haɗa mana abinci. Tun a wurin cin abincin yake bina da ƙananun kiss har muka kammala a shiririce, ko bari bai yi na tattare wurin ba ya ɗaga ni sama muka shige ɗaki ya maida ƙyaure ya rufe......
TAMMAAT BI HAMDULILLAH, INA MATUƘAR GODIYA GA ALLAH DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LABARIN DANA SAKA WA SUNA MATAR MANYA. INA ROƘON ALLAH YA YAFE MIN KUSKUREN DA NAYI A CIKIN WANNAN LABARIN, ABINDA NA RUBUTA DAI-DAI INA ROƘON ALLAH YASA YA AMFANI AL'UMMAR MUSULMI. DA HAKA NAKE CEWA BISSALAM SAI MUN SAKE HAƊUWA A WANI SABON LABARIN.
TAKU KANSA'U BELLO (OUM FATIMA)