Free chapter · Read without an account

Page 3

by Hafsat Abdullahi sani · Qauna

Page 3

By Hafsat Abdullahi

A kan me zaku turke yarinya har haka ta faɗa muku bata sani ba cewar Hajiya sameera ke nan wato qanwace ga Abba mahaifin Ameera kuma ita ce auta a ɗakin su, isowar ta ke nan ta iske maman Ameera sai faɗa take wai a tambayi Maryam ko mai tunda tare suke kwana, jin hakan ne yasa ta da ka tar dasu tare da bawa Maryam umarni da ta tafi ɗaki.

Jin sallamar baqi yasa Maryam da ka tawa daga inda take, dawowa tayi ganin ƴan sanda duk a tsammanin ta za su ce sun tsinci Xulaihah ne,, ji tayi suna tambayar tana ina hakan yasa ta ɗan shork to wa ke nan kar dae a ce sun zo kama ni ne ta tambayi kanta aikuwa bata ankara ba taga abba qarami yana nunata mamaki ne yasa ta kasa motsi daga inda take gani tayi macen ƴar sanda ta tunkaro ta tambayar kanta take wai ysanar da suke mata har ta kai haka ita to ina ta san inda Xulaihah take, "ku da kata" a cewar Hajiya sameera sannan ta ɗora da ni zan kawo ta. Bayan fitar ƴan sandan ne Hajiya sameera ta fara faɗan me zabe sa a kawo musu ƴan sanda har cikin gida kuma da biyar kama ƴar cikin gidan, abban Ameera ne ya dakatar da ita yana cewa Ni na kira ƴan sanda sbd dole ta san inda take, ta ya za ai suna kwana tare su tashi tare ta ce bata san inda take ba, saboda haka ka kira ƴan sanda? Abban Ruqayyah da duk abinda ake bai saka baki ba ya tambaya sannan ya ɗora da cewa wannan ba hujja bace don haka ka kira jami'an ka ba su haquri don ba za'a tafi da ita ba, ta shi yayi zai bar wajen sannan ya bawa mahaifiyar Ruqayyah ta tafi da ita ɗakin ta sannan shima ya tafi.

Kama ta umma tayi suka nufi ɗakin ta, bayan sun shiga ta zaunar da ita a falo sannan ta shiga keching ta haɗo mata abincin kari sannan ta zauna kusa da ita tana bata baki, ganin taqi ci sai sheshsheqar kuka da take yi, rasa abin yi tayi kawai sai ta zura mata ido tana kallon ta abban Ruqayyah ne da ya shigo sai ya ci gaba da bata baki a haka har ta ɗauki tea ta fara sha bayan gama karin ne Abba ya ke tambayar ta da ina daina suke zuwa ita da Xulaihah? Shiru ta ɗanyi sannan ta amsa mashi da gidan su maimuna qawarta sai ..... Shiru tayi Abba ya sake tambayar ta sai ina? ganin ba yanda ta iya dole ta faɗa hakan yasa ta cewa "ina raka ta wani restorent tana haɗuwa da saurayin ta.

Bayan jin abinda Maryam ta faɗa ne ya ta shi da kanshi suka nufi gidan su saurayin Xulaihah wato Khalil, bayan sun je gidan sai Maryam ta shiga cikin gidan shi kuma ya tsaya a bakin gate ɗin, bata jima ba ta fito tare da mai gidan, bayan gaisuwa da sukayi ma junan su ne Abba ya ke faɗa mashi abinda ya kawo shi, shiru mahaifin Khalil yayi sannan yace ina mai baka haquri Alhaji muma yau da alhinin da muka tashi ke nan, mun kwanta da shi mun tashi babu shi kuma mun kira wayar shi a kashe.

Haqiqa ran Abba ya ɓaci sosae don tun bayan jin abinda mahaifin Khalil ya faɗa masa hankalin sa ya ɓaci ya rasa mai zaiyi don da alama duk inda Xulaihah take tana tare da khalil, duk ma ba wannan ba taya zai faɗa ma ɗan uwansa cewar ƴar sa guduwa tayi tare da saurayin ta? Waigo wa yayi inda Maryam ke zaune a motar tare da yi mata kashedin karda ta faɗa ma kowa abin da ya faru.

Bayan sun dawo ne suka tarar da duka mutanen gidan a falo hankali tashe ɗaya bayan ɗaya yake kallon su har ya kai kallon sa kan jamila wato mahaifiyar Xulaihah hakan ya qara tayar masa da hankali, idanun da suka zuba masa ne yasa shi faɗin na miqa rahoton gurin ƴan sanda sannan ya wuce ɓangaren sa.

Cikin sheshsheqar kuka ta shige ɗakin ta sannan ta ɗauki waya ta kira yayan ta bayan ya ɗaga ma kuka tasa masa rarrashin ta ya fara yi sannan ya tambaye abinda ke damunta zayyana mashi duk abinda ya faru tayi daga ciki kuwa harda kashedin da Abba yayi mata, tabbas yaji ba daɗi duk da ba qaunar su yake ba amma saboda ya kwantar mata da hankali yace kiyi haquri zanyi wani abu kai kinji yanzu ki turo Mani da hoton ta. Kashe wayar yayi tare da juyawa ya kalli abokin sa da ya shigo yanzu, zama yayi a kujerar da ke kusa da shi tare da buɗe computer da abokin ya ajiye akan table ɗin wajen "duka bayanan suna ciki" abokin ya faɗa sannan yace kuma yana yawan zuwa babban hotel da ke a garin, ɗagowa yayi yace masa ka shirya mana mutum biyar da su za mu yi tafiyar, sannan ya rufe computer ya nufi wani ɗaki dake a gurin, bayan shigar da kai tsaye gurin window ya nufa tare da qare ma jejin kallo.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol