Free chapter 路 Read without an account
PAGE 10
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
FREE-BOOK
PAGE 10
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta jinjina kanta ta ce.
"Shikenan. Allah yasa a dace."
"Amin..."
"To amma kin san gidan ne?"
"Eh, bayan gidanmu ne fa wanda muka taso, wannan Layin baya 蓷innan. Amma dai zan hau Mashin ga 蓷ari hu蓷u nan a hannuna yanda zai mini sau茩in ganewa."
"OK to, Allah ya tsare."
"Amin."
Har na mi茩e tsaye sai kuma ta kalleni ta ce.
"Yau ni zan yi girki kenan Beenafah?"
Da sauri na 蓷aga yatsata na ce.
"A'a Ammie...."
"Zan iya fa, ba abinda zai faru..."
"A'a ni dai Ammie dan Allah. Kada ki yi, ga sauran 蓷umame nan zai isa kuci da ranar nan har na dawo..."
Murmushi ta yi ta ce.
"To na ji, idan ni an yi mini dole to shi 茒a na fa? Shima tuwon zai ci? Kin san fa hali..."
Dariya na yi sannan na ce.
"Kai Ammie wane irin an yi miki dole magana ba da蓷in ji haka..."
"Eh mana,..."
"Ammie shima idan ya dawo ya ci tuwon kawai, kisha masa toka dole zai ci ya wuce. Ban yarda a kunna wuta idan bana nan ba, 茩arshen magana. Na wuce sai na dawo."
Dariya ta yi tace.
"To Uwa, Allah ya tsare."
Ni ma dariyar nake har na fice daga gidan zuciyata fal da farin cikin samuwar sau茩in Ammiena. Sai yanzu ma na gane cewa akwai hikima cikin tashin Daddy zuwa Abuja da kuma korarmu da ya yi. Na sani akwai ciwo har abada a rayuwarmu amma kuma nisantar su da mukayi ya sauya mana rayuwa daga ba茩in ciki da 茩unci zuwa farin ciki na dai-dai rayuwar da Ubangiji ya za蓳a mana. Da ace har yanxu muna tare da su da yanzu ciwon Ammie yana nan yana 茩ara hauhawa da yin barazana ga rayuwarta.
Daga gidanmu zuwa titi akwai tazara sosai, ga uwar rana yau ana 茩walawa, hakan yasa na samu wata inuwa na zauna ina hutawa. Duk wata Keke-Napep 蓷inda za ta wuce haka zan 茩ura mata ido ina kallon mammallakinta har sai ta 蓳acewa ganina. Tun bayan da muka rabu da Yaya Ashiru haka nake akoda yaushe na fito daga gida sai in ri茩a jin kamar zan gansa a ciki,zuciyata ta kasa mantawa da shi ko na rana 蓷aya.
Ni 蓷in yarinya ce 茩arama mai 茩aramin tunani, a shekarun rayuwata da irin rayuwar da nake fuskanta bana tunanin na san ma miye soyayya take nufi. Kawai dai ina jin tsananin kewar shi wanda wasu lokutan har kuka nake yi da fatan Allah ya ha蓷ani da shi watarana. Rashin Yaya Ashiru ya bar mini wani tabon da ba zai ta蓳a goguwa ba a zuciyata.
Bayan na gama hutun jakin na mi茩e na 茩arasa titin na tare abun hawa na yi masa kwatancen inda zai kai ni. Unguwar dama can sananne wuri ne ba yanka za ka sami mutumin da zai ce bai san wurin ba.
Muna isowa kan corner na sauka daga nan don kada ma na hango tsohon gidanmu na sharce daga nan kawai na wuce gidan.
Ban san cewa na yi kato蓳ara ba sai da na iso bakin gate 蓷in gidan mai gadin su ya tsareni yana min tambayoyin wai wace ce ni kuma daga ina nake?
Jiki a sanyaye na ce.
"Wurin matar da ke 蓳angaren can na dama na zo..."
Wani irin kallon sama da 茩asa ya yi mini sannan ya ce.
"Gaskiya yanzu an daina barin ma su neman taimako suna shiga gidan nan saboda haka ki yi ha茩uri kawai ki wuce..."
Gabana ne ya yanke ya fa蓷i jin yana neman lalata mini shirina wanda shine last hope 蓷ina a yanzu. Cike da magiya na fara ro茩onsa na ce.
"Dan Allah ka taimaka mini mana...Allah fa na ce!"
"Ahf! Komai fa za ki ce ba zan barki ki shiga ba tunda mai gidan da kansa ya umurceni.."
"Haba malam dan Allah! Kayi ha茩uri ka ce mata mai aikinda Biba ta kawo mata ce."
"To kinga sai yanzu kikayi magana...Bari na sanar mata a waya in ji."
Daga haka ya ciro '拼ar 茩aramar wayarsa daga aljihu ya daddana ya kira. Bayan sun gama magana ya kalle ni ya ce.
"An ce ki shiga."
Da sauri na tura kaina gidan ina fa蓷in na gode. Ina shiga na 茩wan茩wasa sai ga wata matashiya ta zo ta bu蓷e rungume da blender a hannunta ta ce mini na shigo.
Wuri na samu cikin ha蓷a蓷蓷en parlurn da ya amsa sunan sa parlour na zauna tsawon lokaci ina ta kallo a TV can sai ga ta ta sauko.
Gyara zamana na yi da kyau bayan ta zo ta zauna, na ce.
"Ina wuni?"
"Lafiya 茩alau.....Sai yanzu ki ka zo?"
Da sauri na girgiza kaina na ce.
"Ki yi ha茩uri, mahaifiyata ce ta yi rashin lafiya sai da muka yi jinya a Sokoto."
"OK.. Ya ma kika ce sunan ki?"
"Sunana Beenafah."
Jinjina kanta ta yi sannan ta ce.
"Beenafah! Kin ganni nan? Bana son 茩azanta,bana son kwa蓷ayi, bana son sata, sannan uwa uba bana son shisshigi da kuma 茩eta. Akan wa蓷annan shara蓷o蓷an ne yasa na kasa zama da masu aiki da yawa, sai Hajjo ka蓷ai wacce kika ga tazo ta bu蓷e miki 茩ofa. Mahaifiyar Biba ta yi aiki a gidanmu tsawon lokaci kuma munyi zama na mutunci da ita shiyasa da ta kawo ki ta ro茩eni na ji ba zan 茩i yi mata alfarma ba hakan yasa na amince. Allah yasa za ki iya kiyayewa da duk abinda na fa蓷a miki."
Gya蓷a kaina nayi a hankali na ce.
" In sha Allahu zan kiyaye."
"Sunana Labiba Attahiru Araam, ni 蓷in nan Lauya ce ta gwamnati a 茩ar茩ashinsu nake aiki. Nan shi ne gidana, na haifi yara Uku, Raudah ita ce ta farko amma ta rasu ba jimawa, sai Adeel, da kuma Hanan."
Ban san dalilin hawayen ta ba, ko kuma don ta tuna da '拼ar ta tace da ta rasu Allah masani, hakan sai yasa na ji tausayin ta sosai a raina, a hankali na ce.
" Allah ya gafarta mata yasa tana aljanna."
Jinjina kai tayi sannan ta ce.
" Amin. Yanzu ya kike so ayi?"
Cikin rashin fahimtar tambayar ta na ce.
"Ki yi ha茩uri, amma ban fahimci tambayar ba."
Shiru ta yi na 蓷an lokaci sannan daga 茩arshe naga ta danna wani abu can sai ga Hajjo ta shigo ta zauna a gabanta cike da ladabi ta ce.
"Ga ni Aunty Labiba."
Kallona ta yi ta ce.
"Wannan sunanta Beenafah, kije da ita, duk wani aikin shara da goge-gogen da kika san kina yi daga yau itace za ta koma yinsa, ki nuna mata komai yanda yake. Ke kuma sai ki ci gaba da wanke-wanke da girki kamar yanda kika saba."
"Tau yayi Aunty Labiba, In Sha Allah."
A tare muka ratsa babban parlourn da ita muka mi茩a wata doguwar 茩ofa haka, sannan ta kai ni wani parlourn wanda ya fi wancan da muka baro ha蓷uwa da tsaruwa.
Nan ta shiga nuna mini duk inda zan ri茩a sharewa da gogewa har da 蓷akunan dake sama guda biyu da wani parlourn. Tana gama nuna mini ta bani kayan aiki ni kuma ba 蓳ata lokaci na 蓷aure hijabina na yi na gama. Ko da na kambala 茩arfe biyu na rana ta yi. A can baya na zagaya inda na 蓷ebo ruwan mopping a famfo nayo alwala na zo kan verandar 蓷in 茩ofar baya na yi sallah sannan na dawo wurin Hajjo na ce mata na kambala.
Nan na jira ta ta shiga ta fito 蓷auke da kula a hannunta ta ce mini ga shi in ji Aunty Labiba ta ce sai gobe na dawo. Godiya na yi mata na kamo hanyar fitowa daga gidan. A harabar gidan na tarar da wata ha蓷a蓷蓷iyar mota an wangale 茩ofofinta yara na fitowa kimanin su shida, manya da 茩anana. Da alama wannan kam driver ne don ya yi kama da driver 蓷in musamman yanayin yanda ya yi shiga.
Tsaye na yi hangame da baki ina kallon su har suka nufi 茩ofafin uwayensu wanda da alama wa蓷annan da suka nufi gidan Aunty Labibar su ne Adeel da Hanan 蓷inda ta fa蓷a mini 蓷azu.
Kallona drivern ya yi ya ce.
"Malama Lafiya?"
Girgiza masa kaina na yi na ce.
"Ba komai."
"To ki wuce zuwa inda za ki mana."
Ta蓳e baki nayi sannan na sa kai na wuce a raina ina mita wai driver da shi zai ri茩a wani iskanci kamar shi ne da gidan,aikin banza kawai.
****
Maple Crescent,
Notting Hill,
London,
United Kingdom.
Misalan 茩arfe shida na yamma Ahlan ya shigo gidan bayan ya dawo daga wurin aikinsa. Tun da ya shigo yake 茩wala kiran Aysha amma baiji ta amsa ba. Duk wani lungu da sa茩o dake gidan sai da ya duba amma bai ganta ba sai da ya kewaya garden sannan ya tarar da ita tana zaune tana darza kuka gwanin tausayi kamar ko yaushe idan abin ya ciciyeta.
Cikin tashin hankali ya isa gareta yana mai janyo ta jikin sa cike da nuna tsantsar tausayi ya ce.
"Aysha! Mummy ce ba?"
Sai yanzu ta 蓷ago idanuwanta da suka rine sosai tsabar yanda tasha kuka cike da karyewar zuciya ta ce.
"Ahlan shekara uku! Shekara uku ban ha蓷a fuska da iyayena ba. Me naiwa Mummy da zafi haka? Me nai mata dan Allah? Ahlan Wai har Daddy ya ce mini ita ce ta haifeni..."
茦ara sassauta muryar sa ya yi sosai cikin 茩wararawa ya ce.
"Haba Ayshan Ahlan! Kada zuciya ta saka ki aikata abin da za ki dawo daga baya kina dana sani. Mummy ita ce wacce ta haife ki kawai dai akasi ne aka samu, ba komai bane wannan illa sharrin shai蓷an. saboda haka ki ci gaba da ha茩uri ki ci gaba addu'a..."
"Ahlan har yaushe?.."
"Kai...Haba Aysha! Kin ta蓳a jin an ce ha茩uri ya 茩are a duniya? Duk wanda kika ji an ce wai ya yi ha茩uri bai ci riba ba to ka蓷an ya yi...."
"Ahlan wallahi ina cikin tsantsar ba茩in ciki da 茩unci. Akan abin da bai taka kara ya karya ba wai Mummy ta ce mini na yi nesa da ita, idan na sake tako inda take bata yafe mini ba duniya da lahira. Abu kamar wasa...Ah.. Ahlan.."
Rungumeta ya 茩ara yi sosai ya shiga lallashinta kamar yanda ya saba har sai da yaji sautin kukan ta ya ragu sosai. Shi kansa bai ta蓳a ji ba kuma ya da蓷e ko yace har yanzu yana kan mamakin rayuwa irinta surukar sa Mummy Zaliha. 茒anka! Ka ce wai yayi nesa da kai, idan ya sake takowa sai ka tsine masa albarka. Wannan wace irin uwa ce..
"Ahlan..muje ka ci abinci.."
Da sauri ya dakatar da ita da fa蓷in.
"No Aysha... Zauna abin ki, bari naje sai na fara yin wanka tukun. Ina Baffa?"
"Baffa yana gun Salma yana bacci."
Mi茩ewa ya yi ya nufi ciki, bayan ya yi wanka ya shirya, ya yi sallar magrib sannan ya 蓷auko wayarsa ya kira Daddy, bayan sun gaisa cike da girmamawa ya ce.
"Ahm! Daddy daman dangane da zancen Aysha ne, a matsayina na Mijinta kai kuma a matsayin Uba a gareta. Ya kamata ace an kai 茩arshen wannan abun, koma minene Mummy take ji ta yi ha茩uri ta yafe mata. Yanzu ga auren 茩anwata Firdausi ya tashi, dole muna da bu茩atar zuwa gida amma ta ce matu茩ar Mummy ba ta amince da ta zo gida ba ita ba za ta je Nigeria ba. Daddy tun Baffa yana zanin goyo rabonmu da gida gashi yanzu har ya yi shekara uku. Aysha bata cikin walwala, kullum cikin kuka da damuwa. Kai kanka Daddy idan na kiraka kullum magana 蓷aya ce cewa ta 茩i ta ha茩ura..... "
" To yanzu mi kake so Ahlan?"
" Eh.. Daman cewa na yi dan Allah ka 茩ara bai wa Mummy ha茩uri ko Allah zai sa ta sauko ta janye furucinta."
Daga can 蓳angaren Daddyn ya ce.
" In sha Allahu zan 茩ara 茩o茩artawa in gani. Zalihar ce ta cika kafiya wallahi."
"To daddy na gode, Allah ya bamu alheri."
****
Hayin malam Ibrahim.
Gusau, Zamfara State.
Nigeria.
Ina shiga na zauna kusa da Ammie tare da dire kular da ke hannuna ina murmushi na ce.
"Ammie sannu da gida."
Kallona take kallo mai cike da alamar tambaya ta ce.
"Yauwa. Wannan fa?"
"Ammie har na gane gidan har na yi aikina na yau na kambala sai kuma gobe..."
"Wannan kular fa?"
"Bayan na kambala aikina na fa蓷awa Hajjo, shine taje ta sanar mata sai gashi Hajjon ta kawo mini wannan kular ta ce Hajiyar tace na tafi sai gobe."
Jinjina kai ta yi alamar gamsuwa sannan ta ce.
"Miye tsarin aikin?"
"Shara ce da goge-goge kawai. Idan Mijinta yana sashenta sai sha 蓷aya na safe zan tafi, idan kuma ba sashenta yake ba 茩arfe tara na safe ta yi min a can."
"Ta fa蓷a miki nawa za ta baki a wata?"
"A'a Ammie. Ba muyi maganar ku蓷i ba gaskiya. Amma dai da gani matar tana da kirki.."
"Duk da haka ki kula Beenafah."
"In sha Allah Ammie. Kin san me ma..."
Nan na yi ta zuba ina fa蓷a mata duk yanda muka yi da mai gadin gidan da kuma bayanin da Aunty Labibar ta yi mini. Muna nan muna fira sai ga Bahrain ya shigo. Bayan ya gaishemu ya hau rarraba ido yana kallon kyakkyawar kular da ke gabanmu...
"Ka je ka 蓷auko plate ka zo in zuba maka Bahrain."
Kyakkyawar Jallop rice ce wacce ta ji wake lafiyayye da koren ganyen da namomi a ciki. Rabonmu da irin wannan kyakkyawan ha蓷in tunda muka baro Sokoto.
Yanda Bahrain ke cin abinci hakan sai ya sanyani jin hawaye saboda yanda yake yaba da蓷in abincin.
A tare muka ci da Ammie, sauran da ta rage kuma na rufe masa idan ya dawo daga islamiyya da dare ya 茩arasa cinye saura.
Washe gari da wuri na tashi na nema mana abin kari muka ci Bahrain ya shirya ya wuce makaranta,ni kuma na yi shara da wanke-wanke na shirya na wuce.
Haka na ci gaba da aikina gidan Aunty Labiba. Idan na tafi sha 蓷aya na safe kwana biyu bayan kwana biyu kuma in tafi 茩arfe tara na safe.
Yau ma, ina shiga na ci karo da su Adeel sun fito za su je islamiyya kasancewar Asabar ce.
Muhsin wanda shi ne babba cikin su gaba 蓷aya da alama zai yi irin shekara sha biyar haka na ji yanata kiran.
"Ke.. Ke.. Ke bakya ji ne?"
"Aunty Beenafah."
Na jiyo muryar Adeel ya kira sunana.
Waigowa na yi na ce.
"Na'am Adeel, ya akayi?"
"Ba Adeel ke kiran ki ba nike kiran ki."
Cike da mamaki na dawo baya na ce.
"Ya akayi?"
Basket 蓷in 茩anwar sa Tima ya nuna mini yana fa蓷in.
"Tea ya zube a basket 蓷inta, ki amsa kije ki wanke mata ki gyara ki kawo."
Ba musu na amsa naje na cire kayan ciki a bakin famfon da ke harabar gidan na wanke sannan na 茩ara 蓷aure bakin bottle 蓷in da kyau na saka a ciki na kawo musu suka shiga mota suka wuce.
Ina shiga na tarar da Aunty Labiba zaune a parlournta da kayan break fast a gaban ta da alama yanzu suka 茩arasa karyawa tare da su Adeel 蓷in.
Du茩awa na yi na gaisheta kamar yanda na saba a duk lokacin da na tarar da ita gida, saboda tunda na fara aikin nan na kan share kwana biyar ko fiye ma da haka ban sanyata a ido na ba.
Bayan mun gaisa na mi茩e da nufin tafiya wurin aikina sai na ji ta kira sunana.
"Beenafah."
Waigowa na yi na ce.
"Na'am Aunty Labiba..."
Please ki zo ki shigar da kayan nan kitchen, sannan dan Allah ina neman alfarma da ki 蓷an wanke mini uniform 蓷in su Adeel saboda Hajjo bata da lafiya, daman ita ke wanke musu uniform ta goge kasancewar bamu da mai wanki a gida sai dai idan kaya sun taru mu ha蓷a akai waje.
"Haba Aunty! Miye na neman alfarma. Kawai cewa zaki yi na yi."
Murmushin jinda蓷i ta yi tare da jinjina kanta ta ce.
"Allah sarki, to na gode."
"Ki je ki fara karyawa tukun kafin ki fara."
Girgiza kaina na yi na ce.
"Na gode Aunty, amma na 茩oshi."
"Haba Beenafah! Miyasa kike yin haka? Hajjo ta sanar mini duk kika zo gidan nan ko ruwa bakya sha."
"To ai na 茩oshi ne Aunty."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Shikenan! Ta shi kije."
Kayan na kwashe na kai kitchen sannan na fito da kayan na wanke tas! Sannan na hau aikina kamar yanda na saba. Ina cikin yi sai ga Hajjo ta shigo 蓷auke da sallama a bakinta. Kallonta na yi na ce.
"Sannu Aunty Hajjo."
"Yauwa Beenafah."
"Ashe ba kiji sarai ba? Allah ya baki lafiya."
"Amin Ya Allah, na gode sosai."
Bayan na gama aikina wuraren 茩arfe 蓷aya da wani abu na 蓷auko kayan da na wanke na shiga 蓷akinda muke zama idan mun zo ni da Hajjo na shimfi蓷a guga kamar yanda naga Hajjo tana yi.
茒akin Hajjo ta shigo ta kalleni ta ce.
"Ke dai Beenafah shikenan ba ruwan ki da kowa, kullum tamkar wata sabuwar ba茩uwa haka kike rayuwa da mu."
Murnushi na yi ina girgiza kaina ce.
"Ba haka bane Aunty Hajjo."
"To yanzu ki ta so ki kaiwa driver abincin su Adeel in ji Aunty Labiba."
"To,yanzu kuwa, In Sha Allahu."
Hijabina na janyo daga inda na sagale na sanya sannan na fito naje kitchen 蓷in na 蓷auko babban basket wanda aka cika da abin Ci da Sha na kai bakin motar na ajiye wanda a dai-dai lokacin ne itama wata mata ta fito daga 蓳angaren hagu ta ajiye basket guda biyu. Cike da nuna isa da 茩asaita ta kalleni ta ce.
"Ke kuma wace ce?"
Cikin ladabi na 蓷an rusuna ka蓷an na ce.
"Ina wuni?"
"Ba shi na tambaye ki ba, cewa na yi ke wace ce?"
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍