Free chapter 路 Read without an account
PAGE 24
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671
FREE-BOOK
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel 蓷inmu na tafe in sha Allahu zamu ri茩a yi muku posting gaba 蓷aya free books 蓷inmu wa蓷anda babu algus....
PAGE 24
Yana saka mini numbern ba 蓳ata lokaci na kira Ya Jafaru cike da farin ciki na kara a kunnena.
Ina jin ya 蓷aga na buga wani irin ihu tamkar zan fasa masa dodon kunne na ce.
"Ya Jafaru na yi Wayaaa! Yaya Ashiru ya siya mini waya"
Zaune yake akan gadon sa a hostel da tarin Handout a gabansa, daman kuma already an wuce shi a lectures na tsawon sati biyu sannan ya yi joining na su.
Lokaci 蓷aya ya mi茩e tsaye tamkar wanda aka tsikara da allura jin wata irin mummunar magana...
"Hallo! Ya Jafaru kana jina??"
Cikin wani irin 蓳acin ran da har yasa ya kasa controlling kansa ya buga mini tsawa da fa蓷in.
"Akan me to zai saya miki Waya? Ban ce kada ki tsaya saurarar kowane shashasha ba Beenafah?"
Cike da mamaki na ce.
"Ya Jafaru Yaya Ashiru fa na ce maka..."
"And so! Akan mi zai saya miki Waya? Akan wane dalili?"
"Ya Jafaru ba fa wani abu ba ne, Kano zai wuce shiyasa ya siya mini..."
"Uhm! To na ji!"
Daga haka ya katse kiran wanda ni a tunanina network ne, hakan yasa na sake gwada kiran numbern tasa amma kuma sai aka ce mini wayar a kashe take.
Kallon Ya Hamza na yi sai kuma na kalli Ammie wacce gaba蓷aya hankalinta ya 蓷auku yana kan Bahrain da Farisa suna magana. Ganin hakan yasa na kalli Ya Hamza na ce.
"Ya Jafaru fa fa蓷a yake akan Wayar nan. Daga jin yanda yake magana bai ji da蓷in ta ba. Ko kuma dai akwai abin da yake damuna? Saboda ba haka yake ba."
Mi茩ewa ya yi bayan ya gama cin abincinsa ya jinjina kansa yana fa蓷in.
"Wata 茩ila akwai abin da yake damunsa dai kam.....Ni na wuce sai da safe."
Game muka shiga bugawa a wayar ni da Bahrain, bayan kuma wani 蓳angaren na zuciyata cike yake da tunanin abin da ya Jafaru ya yi. Muna nan daga nan na 蓷an yi wasu aikace-aikace sai muka je muka kwanta domin Yaya Ashiru bai kirani ba, nima kuma 蓷in ban yi tunanin kiran sa ba. Washe gari ina tashi na yi Sallah na 蓷auko wayar na yi 蓷an latse-latsena wanda ko Azhkar ban samu na yi ba akan 蓷oki saboda dannar wayar, bayan na ga lokaci ya tafi na ajiye na je wurin shirin tafiyata bayan na kambala duk aikinda ya kamata na fice zuwa gidan aikina.
****
Misalin 茩arfe biyu saura na rana, Mamansu Fakiha na zaune tana zuba musu girkin da ta sauke kawai sai Jafaru ya yi sallama ya shigo gidan.
Ajiye serving spoon 蓷inda yake hannunta ta yi cike da tashin hankali ta dafe 茩irji ta ce.
"Jafaru! Lafiya? Miye yasa ka dawo? Miye ya faru?"
茒an guntun tsaki ya ja tare da janyo kujerar tsugunno ya zauna akai yana mai yasar da 茩aramar school bag 蓷insa wacce ke 蓷auke kala uku ta kayansa gefe ya kalle ta ya ce.
"Ba bu abinda ya faru... Kawai dai na zo ne inji dalilin da yasa wannan Ashirun ya sayawa Beenafah waya.."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Jafaru! Kana da hankali kuwa?"
Yana gunguni 茩asa-茩asa ya ce.
"To ai hakan ba daidai bane,fisabilillahi Mama kuma ace kuna gani ku bari wani 茩aton banza ya siya mata waya ya bata, wannan hanyar lalacewa ce aka bi蓷ar mata, idan ba shi ba dan Allah Mama Ina Beenafah ina Way..."
Kafin ma ya iyarda rufe bakin sa tuni ta rotsa masa Cokalin miyar da yake Cikin tukunyar gabanta a hasale tana fa蓷in.
"Ka ci ubanka da kai da dalilin naka.."
Saurin Mi茩ewa ya yi ya matsa gaba can nesa da ita domin Cokalin ya sauka a daidai, hakan ne ya haddasa masa jin zafi a gefen bakin shi shiyasa ya tashi ba shiri.
Cikin nuna tsantsar 蓳acin rai ta kalle shi taci gaba da fa蓷a tana cewa.
" Yanzu Jafaru saboda baka san ciwon kanka ba, Alhaji ya kashe ku蓷i ya saka ka a makaranta amma shi ne zaka wani 蓷ebo 茩afa sati 蓷aya ka dawo gida akan wani dalilinka na banza na wofi? Ina ruwanka don Ashiru ya saya mata waya? Na ce ina ruwanka? Can wan can lokacin baya da ta ta蓳a yin wayar don ubanka kasan ma da zancen? Inda tana da niyyar lalacewa da tun can bata lalace ba... "
Mi茩ewa tayi tare da nuna shi da yatsa ta ce.
" To wallahi bari kaji in yi maka rantsuwar Musulmi.. Wallahi tallahi kar in ji kar in gani wai ka yi musu zancen wayar nan da sunan 蓳acin rai,ban amince ba ka ji na fa蓷a maka, kuma wallahi yanda ka 蓷auko 茩afa a yau 蓷innan ka zo a yau 蓷in nan zaka koma ba sai gobe ba. Sannan mags Garin nan kuma; idan har ba hutu aka yi ba ban amince da ka zo shi ba. Domin baka isa ka zubar mini da mutuncina ba a wurin Alhaji ka ji na fa蓷a maka.. "
Daga haka ta 茩wala kiran Fakiha akan ta zo taci gaba da raba abincin ita kuma ta shige 蓷aki rai a matu茩ar 蓳ace.
Tsaye ya yi kawai yana mai jin wani irin tashin hankalin da bai san ma yanda zai fasalta shi ba. Wai Mama ko tasan miye yake ji akan Beenafah? Jiya sam bai samu ya runtsa ba tunda ta yi nasarar shaida masa wannan mummunar maganar.Wallahi tallahi zai iya 蓷aukar mummunan mataki akan koma waye akan Beenafah. Shi kenan kawai don ya ta蓳a taimaka musu sai a bar shi da ita yayi ta abin da ya ga dama. Idan ba iskancin banza ba akan me zai saya mata waya to?
Ya jima a tsaye tsawon lokaci yana karanta wasi茩ar Jaki. Ya sa茩a ya warware ya sa茩a ya warware ya rasa ma tudun dafawa. Yana nan a haka sai ga babansu ya yi sallama ya shigo. Daga ganin irin kallon da yake bin shi dashi kasan cewa labari ya riga da ya gama kai masa. Cikin nuna 蓳acin ransa 茩arara shima yace.
"Mutumin banza mutumin 蓷an magori!"
Cike da fatan Allah yasa baban ya Fahimce shi a wannan maganar ya yi 茩asa da murya ya ce.
"Yanzu kai ma Baba laifina za ka gani kenan? Beenafah fa amana ce a garemu bai kamata mu bar ta tana rayuwa kara zube ba a duk yanda taga dama..."
"Beenafahr ce take rayuwar kara zube?? Miye ka ta蓳a gani ko ka ta蓳a ji ance tana yi wanda ba daidai ba? Ka fa蓷a mini shi ni kuma na yi maka al茩awarin 蓷aukar mata mataki da kaina"
茦asa ya yi da kansa ya na wani turo baki yace.
"To amma dai ai wannan wayar bata kamata ba, idan ma magana yake so yayi da ita ya kira ta wayar Mama man..."
"Kai.. Kai.. Dan Allah banson shirme ka ji ko! 茒auki jakarka ja juya yanzu-yanzu ba sai anjima ba ka koma..."
Wani irin shock ne ya ji ya ziyarcesa a lokaci 蓷aya wanda har bai san sanda ya 蓷ago ya kalle shi ba yana fa蓷in.
"Haba Baba! Dan Allah ku bari zuwa gobe..."
"Wallahi yau za ka juyi ka koma Jafaru ka ji na fa蓷a maka. Idan kuma karatun ne baka so sai ka fa蓷awa Alhaji Usman 蓷in ya daina asarar ku蓷insa a kanka.."
"To ai ni yanzu bani da isassun ku蓷inda zan iya komawa yau 蓷in..."
"Au! Yanzu ashe ma ba kada isassun ku蓷i amma ka yi 茩unar ba茩in Wake ka wanko 茩afa ka zo?"
Fitowa Mama tayi daga can varender ta watso mishi dubu biyar tana fa蓷in.
"Ga su nan ka 蓷auka maza da zafi ka juya ka koma ka ji na fa蓷a maka....Hmm!"
Ta fa蓷a daga 茩arshe tana mai ri茩o daga cikin 茩arfen turakunda suka ri茩e verander 蓷in ta ci gaba da fa蓷in.
"Aikin banza aikin wofi! Wannan ai isar baka isa bace kake nunawa. Idan har so kake ka nuna isa to ka je ka fara zama wata tsiya tukunna."
Tsince ku蓷in ya yi ransa na yi masa wata irin suya tamkar ya fashe haka ya ke ji.
Yana gama tattare ku蓷in ya 蓷auki jakar sa ya fice.
Hanya ya kama wanda sai da ya yi nisa sannan ya juyo kuma ya dawo, ya so ya yi zuciya ya tafi amma kuma ba zai juyawa ya koma bai ganta ba.
Yana dawowa sai gani ni kuma na iso 茩ofar gidan...wani irin mamaki ne ya ziyarce ni a lokaci 蓷aya na wani hangame baki ina zare ido na ce.
"Ya Jafaru??"
Fuska ba yabo ba fallasa ya kalle ni ya ce.
"Beenafah! Kin dawo?"
"Miye ya dawo da kai kuma? Ba kace sai kun yi jarabawa ba?"
Ga dai bikin zuwa amma babu Zanen 蓷aurawa. Ga dai Beenafah yana gani amma kuma bai isa ya yi mata zancen waya ba tunda Mama ta hana, sannan uwa uba ga maganganun da Mamar ta yi masa na 茩arshe sun yi matu茩ar 茩ona masa zuciya. Wato ga mari ga tsinka jaka! Tuna wannan yasa ya 蓷an 茩ir茩iro wani murmushin dole ya 蓷aura akan fuskar sa ya ce.
"Wani 蓷an abu ne ya kawo ni kuma ma na kambala yanzu zan juya in koma..."
"To amma ko shigowa ba za ka yi ba Ya Jafaru??"
Girgiza kansa ya yi ya ce.
"A'a. Ni na wuce sai an jima."
Tsaye nake yayin da fuskata ta cika da ma蓷aukakin mamaki ina kallon sa har ya 蓳acewa ganina. Ajiyar zuciya na sauke tare da girgiza kaina kawai na juya na shige gida ina fa蓷awa Ammie cewa yanzu naga Ya Jafaru ashe ya zo har ya juya ya koma kuma.
Itama da mamaki a fuskarta ta kalleni ta ce.
"Jafarun?"
"茦warai kuwa Ammie. Wallahi na ganshi yanzu. Amma kuma har ya koma."
茒an Jim tayi ka蓷an tana nazari, sai daga baya kuma ta jinjina kai ta ce.
"To wata 茩ila akwai abin da ya dawo da shi, amma zan shiga gidan na ji."
Da ta je gidan ta tambayi Mama, ce mata tayi wasu takardun makarantarsa ne ya manta wanda dole ana da bu茩atarsu shi ne ya zo ya 蓷auka ya koma.
****
Gefen su Hassana kuwa;Tun bayan da su Ammar suka zo suka gansu da wata uku aka kawo kayan gaisuwa tamkar za'a bu蓷e wani super market. Mummy wacce ta ji kamar ta yi hauka akan tsananin farin cikin da take ciki, babu abinda take in ba alfahari ba tana 蓷aga shoulder musamman da taga an 蓷ora ku蓷i sama har 5M. Wai ku蓷in gaisuwa kawai. Hakan yasa ta 茩ara jaddadawa su Hassana cewa gwanda ma ta bada kai bori ya hau, domin kuwa wallahi tallahi aure tsakanin su da '拼a'拼an Alhaji Mansur Anka babu fashi sai idan mutuwa ce ta shiga tsakani.
Hassana tasan Mummy ta san me take iya yi hakan yasa dole ta shafawa kanta ruwa, duk cewa Aunty Aysha sa saurin en uwa sun yi lallashin duk a banza, domin kuwa ba don ta ha茩ura ba.
Yau ma a makaranta tun da suka fito morning lecture take tare da sabon saurayinta Salman a school cafeteria.
Suna zaune Husaina ta iso wurin a hankali ta yi musu sallama sannan ta tsaya akan Hassana ta ce.
"What you are doing is not right Hassana..."
Mi茩ewa ta yi cikin azama ta janyo hannunta da 茩arfi suka bar wurin, cikin nuna 蓳acin ranta ta ce.
"Hussy miye haka? A gaban Salman 蓷in za ki fara yi mini maganganun haukar na ki??"
Girgiza kai ta yi itama ranta a 蓳acen tana mai nuna ta da yatsa ta ce.
"Ke ce kike abin da bai kamata ba Hassana... Akan me za ki zo da maganar wani akanki amma kuma ki fara soyayya da wani! Ina jiye miki abin da ke bakya hangowa Hassana..."
"Ina ruwan ki? Na ce miye abin da ya shafeki da abin da nake yi? Salman shi nake so kuma shi zan aura...Wallahi tallahi ni babu wani Ameer 蓷inda zan aura..."
Hannunta Husaina ta kama hankalinta a tashe ta girgiza kanta ta ce.
" Please listen to me Hassy... Ka da ki bari hakan ya girmama. Mummy ba za ta amince ba... "
" Dole sai ta amince? Ko kuma ita ce za ta zauna mini a gidan aurena?"
Girgiza kanta Husaina ta yi still ta ce.
"Hassy ina jiye miki kada..."
Hanya ta nuna mata cike da hargagi tana wani girgiza mata kai alamar bata ma son maganar ta ce.
"Kinga Malama dan Allah, ki wuce kije wurin abin da ya shafeki.."
"Hassy! Gaba蓷aya yinin yau only morning lecture kika yi attending...Tun da aka tsaida maganarki da Ameer ko sau 蓷aya baki ta蓳a bashi lokacin ki ba, haka zai zo ya zauna 茩arshe ya kakka蓳e rigar sa ya tashi ba tare da kin kula sa ba, sannan yanzu gaba蓷aya karatunki ya fara samun matsala duk ta dalilin Salman... Ina shawartar ki da kuma garga蓷in ki; kada ki bari Mummy ta gano duk wannan abubuwan da kike a bayan idonta. "
Daga haka ta juya ta koma class. Mamaki take ta rasa mike damun Hassana, duk abubuwan nan da take tsawon lokaci Hussaina ba ta ta蓳a yi mata magana akai ba sai yau. Kuma da ace ita ce take wannan da yanzu ta da蓷e da kaiwa Mummy labari. Tun da ta ha蓷u da Salman shikenan komai na ta ya 茩ara komawa baya, bata ji bata gani idan ba Salman ba. Ita kuma tana jiye mata masifar da za ta janyowa kanta domin tasan Mummy ba 茩yale ta za ta yi ba.
****
Tun da Hajiya ta yiwa Aunty Ziza garga蓷i akaina tun daga wannan lokacin na samu sassauci. Ba ruwanta da ni irin haka muddin dai ba wani aikin take so ba, kuma shima ba na irin takurawar nan ba kamar na da.
Sai da ta cika wata uku da haihuwa a gidan cif sannan ta shirya ta koma gidanta. Hakan ya 茩ara bani wata damar samun kwanciyar hankali wanda bani da wata matsala a yanzu. Shi ma Mijinta ni dai tun bayan sunan da na ganshi sau 蓷aya ban sake ganin shi ba har yau.
A duk lokacin da ta zo gidan ta ganni a zaune bana aikin komai, hakan ba 茩aramin ba茩in ciki yake bata ba. Da wannan ta yi nasarar shawo kan Hajiya akan dole ya kamata ace na koyi girki ko don yau da gobe. Ta hakan tayi amfani da 茩arfin ikonta tasa Oga Sule ya 蓷aukeni ya kai ni Ziza Eatry and more inda na du茩ufa koyon girke-girke ba kama hannun yaro.
Babban wurin abinci ne dake titin bypass mai sassa daban-daban da ake gabatar da abubuwa a ciki, wanda aka 茩awata shi da kayan girke-girke na zamani wanda babu abun da babu.
Manyan hotunan ta ne kakkafe a babban reception 蓷in, sai hoton wani daban wanda ban san wanene shi ba sannan hoton mijinta yana sanye da kaki.
Ma'aikatan dake wurin kuwa, ganin Oga Sule ke kawoni akodayaushe yasa suka saki jiki dani sosai muna harakar mutunci da su yayinda na 茩ara kwantar da kai ina 茩ara samun ilmi.
A wurin wata Aunty Subai'a ce na tambaya cewa wace ce Ziza wai? Domin ganin irin yanda take hul蓷a da mutane daban-daban a wurin yana matu茩ar bani mamaki.
Cike da alfahari ta fara mini bayanin ta da cewa; ita 蓷in ta yi karatu a 茩asar France inda ta karanci Culinary Arts a Le Cordon Bleu University. A nan ta yi degree 蓷inta a fannin girke-girke, ta koyi abincin 茩asashe daban-daban tare da samun gogewa daga manyan chefs na duniya.
Ziza ta kasance Mace mai baiwa ta musamman wadda Allah ya horewa hikima da fasaha a harakar girki.
Bayan ta dawo 茩asarta Nigeria da taimakon Daddy Ashraf shaharren 蓷an kasuwa wanda ya kasance zaman mahafinta domin tun tana '拼ar 茩arama ya 蓷auko ta ya dawo da ita hannun shi a nan Potarcourt inda a nan ne bayan ta dawo ta samu damar cike mafarkinta na bu蓷e babban gidan girke-girke na Ziza Eatry. A hankali ta fara suna har ta zama cikin manyan gwanayen da ake ji da su a duniyar girke-girke a Nigeria. Sannan daga baya a hankali tana 茩ara girma har ta fara samun gayyata daga 茩asashen waje, Dubai, Turkey, France da Kuma Saudi Arabia inda take yawan halarta domin gabatar da gasanni da kuma shirye-shirye a fannin girki. Ta samu awards na African Female Chef Wanda aka gudanar a 茩asar Ghana, sannan ta samu award na Best traditional Cuisine Innovator a Dubai food Expo Sannan kuma da award na Taste of Excellence a Paris International food festival.
A Kaduna suka ha蓷u da Emraan, bayan sun yi aure aka kawo ta Gusau, inda Emraan ya cika mata al茩awarinta na bu蓷e mata reshen ta na Ziza Eatry a nan bayan wancan dake gudana a portacourt 蓷in.
Har la茩ani gareta akan 茩wazonta wanda ake kiranta da shi wato Queen Ziza the Flavour Master, wannan Sunan ya samo asali ne ta dalilin yadda ta iya ha蓷a aroma, texture da Kuma presentation na abinci gwanin burgewa akodayaushe.
Suna yawan yabon halayenta na kirki da kuma son mutanen da take da shi amma kuma ni Sam ban gani ba, domin ko sau 蓷aya bata nuna mini kirkinta ba sai ba茩in hali da mummunar fuska wacce a duk sanda na kalle ta, to bana hango komai sai tsantsar tsanata wanda har yau na rasa dalili.
Haka na ci gaba, kullum idan gari ya waye Oga Sule ko Lawan har 茩ofar gidanmu suke zuwa su 蓷aukeni su kaini, idan 茩arfe uku ta buga na rana su dawo dani har na tsawon wata uku. Wanda ban sani ba ko ita gani take kamar mugunta ce ta mini,bayan bata san cewa wannan abun da ta yi mini ba tayi matu茩ar taimaka min kuma har abada ba zan daina gode mata ba domin ta 茩ara inganta mini rayuwata.
A haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar damu yau da蓷i gobe akasinta,inda yanzu na doshi tsawon shekara ta biyu ina aiki a gidan Hajiyar. A gefe 蓷aya kuma ina nan ina zuwa Islamiyya, Alhamdulillah na samu na kambala sauke Al-Kur'ani kuma ina ci gaba da litattafaina. Ina nan ina ta 茩ara samun gogewa a rayuwa ta gefen 茩awayena su Hafsa da kuma su Munira. Gefen Ya Jafaru kuma;yana nan sannu a hankali ya kambala aji 蓷aya ya shiga aji na biyu. A kullum kwanan duniya sai ya kirani a wayar Mama sau 蓷aya ya ce a kirani yana so mu gaisa,baya dawowa sai 茩arshen Semester idan ya kambala exam ko kuma idan wani wani uzuri ya ta so. Wani abun da yake 蓷auremin kai kuma ya tsaya a raina shi ne, yanzu kwata-kwata ya daina matse mini kamar yanda yake yi ada. Kuma tun ranar na kira shi da wayar nan bai ta蓳a kirana da ita ba, idan ma na kira shi baya 蓷agawa sai dai ya kirani ta wayar Mama muyi magana wanda a yanzu na daina kiran sa ma da ita, kuma ko ya zo bai ta蓳a cewa yana so ya ga wayar ba. Sai dai maganarsa guda ce kullum, na kula da kaina kamar yanda yake kulawa da kansa.
Gefen Yaya Ashiru shima yana Kano abinsa, amma dai shi baya shafe cikakken wata 蓷aya bai zo ba, sai dai kuma, baya wuce kwana 蓷aya ko biyu yake juyawa ya koma, shiyasa na 茩ara samun kusanci da kuma sha茩uwa da shi sosai. Dokar Ammie tana nan wacce ta sanya mini akan waya, bana fita ko'ina da wayar nan, amfaninta a gareni kawai sai idan ina gida, wanda shima daga zaran Yaya Ashiru ya kirani sau 蓷aya da magariba, baya 茩ara kirana sai kuma wata goben amma kuma muna 蓷aukar lokaci akan wayar muna magana wacce duk yawanci hirarrakin duniya ne.
Gefen Daddy kuwa, babu wani labari tsakaninmu da su, bamu da nasu haka zalika suma ba su da namu labarin. Komai tamkar a mafarki haka yake tafiya tsakaninmu da su Daddy tamkar bamu rayu da su ba.
Alhamdulillah! Ubangiji duk inda yake so yaga bawansa a nan zai barshi, duk abinda ya rubuta maka ya nufeka za ka samu to tabbas babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa. Ga shi dai muna raye kuma cikin rayuwa mai da蓷i ba tare da su ba. Idan ka dogara ga Allah ha茩i茩a ya isar maka da komai.
Uncle Isma'ila sau biyu ya ta蓳a zuwa gidanmu, ganin gidan yana nan tsab hakan yasa ya 蓷auke 茩afarsa, kuma ni duk zuwa biyun da yayi ban ta蓳a ha蓷uwa da shi ba, sai dai daga baya Ammie ta bani labari. Rayuwa tayi mana komai Alhamdulillah, muci mai kyau musha kyau sannan mu gabatar da sauran bu茩atocin rayuwa duk a cikin inuwar Aunty Labiba da kuma Ahlinta wanda babu komai tsakaninmu da su sai fatan alheri.
****
Misalin 茩arfe biyar na yammar ranar Talata. Ashiru yana zaune a bakin 茩ofar 蓷akin Ayya suna magana kwatsam sai ga Yaya Nura ya shigo.
Wata irin zabura Ashirun ya yi ya mi茩e tsaye yana wani rarraba ido alamun rashin gaskiya.
Kallon shi Yaya Nuran ya yi calmly yana girgiza kai ya ce.
"A'a! Zauna abin ka, ni indon ganina ma bari wata razana."
Wuri ya samu ya zauna yayinda har yanzu Ashirun yake a tsaye. kallon Ayya ya yi suka gaisa sannan ya tambayeta Umma ta ce ta fita anguwa. 茒aya daga cikin 茩annen na su ne wata ta zo ta 蓷auki jakar Yaya Nuran ta shigar masa da ita 蓷akin Umma daga nan shi kuma ya mi茩e ya ce idan sun yi sallar Isha yana so su zo a zauna yana da maganar da yake so su tattauna akai.
Tun da Ashiru yaga shigowar Yaya Nura bai sake samun nutsuwa ba, musamman idan Umma ta dawo ya fa蓷a mata cewa sai da yace masa kar yazo amma ya 茩etare maganar sa ya yi tahowar sa.
Sannan yanzu bai san wane kalar hukuncin Yaya Nuran zai yanke masa ba, domin abin da har ya 蓷auko shi a wannan lokacin daga Kano ya kawo shi Gusau to tabbas abin nan ba 茩ara mi ne ba.
Da wannan tunane-tunanen ne ya samu jiki sanyaye ya gabatar da sallar Magriba da Isha sannan ya tattaro ya dawo gidan.
Bai 茩ara shiga tashin hankali ba sai da yaga Yaya Kamal da kuma Aunties 蓷insa guda biyu, Nasma da kuma Nusaiba.
A bakin 茩ofar 蓷akin Ummar ya tsaya ya togace domin ya kasa 茩arasowa ciki.
Wani kallon Umma ta jefa mishi sannan ta ce.
"Ai sai ka 茩ara so ciki kai ake jira mutumin banza kawai!"
A hankali ya sa蓷a蓷o ya zauna a gefen Nusaiba tare da fa蓷in ina wuninku.
Babu wanda ya amsa daga cikinsu tsawon lokaci sannan daga 茩arshe Yaya Nura ya sauke wata ajiyar zuciya ya ce.
"To! Alhamdulillah! Ni dai ma茩asudin tara ku a nan shi ne; Ashiru dai 茩anina ne kamar yanda yake a gare ku kuma, bani da wani buri a raina face inga na gina shi kamar yanda nima na ginu. Shiyasa na tsaya na 蓳ata lokacina da kuma ku蓷ina wurin ganin ya samu ilmi ya kuma samu hanyar dogaro da kansa. Mutumin kirki ne, domin gaskiya idan na ce ga kuskurensa da ya ta蓳a yi wurin sa蓳a mini to na shiga ha茩茩insa. Yana nan yana karatunsa lafiya lau ba wata matsala kasuwancinsa ma haka, komai na tafiya yanda ya kamata kuma ana kan samun alheri babu laifi,to amma yanzu matsala 蓷aya ce wacce ku kanku nasan kun san da ita kawai dai kun yi shiru kun zuba masa ido ne bama kamar ke Umma da Ayya. Tun da yarinyar nan ta dawo rayuwar sa shikenan ya rasa sukunin rayuwa, bai da wani aiki sai nata bai da wata magana sai tata, yanzu a wata sai ya zo Gusau sau biyu ko sau uku kullum cikin zarya yake akan 茩arfe, Maman Nabil har da magana ta yi masa kwanaki akan ya sararawa hanya amma bai saurareta ba, sannan ni kaina a wannan karon sai da na fa蓷a masa cewa kada ya zo, amma haka ya shure maganata ya 蓷auko 茩afa ya dawo... "
Cike da jin haushi Yaya Kamal ya maka masa wata uwar harara ya ce.
" To tun da har ya nuna ba'a isa da shi ba ai shikenan, sai yaje ya yi ta abunda ya ga ya fiye mish... "
Girgiza kai Yaya Nura ya yi ya ce.
" A'a, duk batun hakan bai taso ba. Ku kanku kun sani, an yi fa蓷an an yi mi amma kuma bata sauya zani ba..."
Kallon sa Umma ta yi ta ce.
" Nura ka daina cewa wai ba zai canza ba! shi ne ya haifi kansa ko kuma haifar sa akayi da zai ce yafi 茩arfin mutane... "
" To ai ni Umma ina da wata shawara wacce nake tunani da kuma ganin ita ce maslaha a wannan al'amarin. Kawai aje a nema masa aurenta. Idan akayi auren sai ya tattara ta su dawo Kano gaba蓷aya kinga shikenan an huta an yi maganin abun... "
Wata irin zabura Ayya ta yi ta ce.
" Kai Ina! Gaskiya Nura wannan magana ba za ta yiyu ba, mutanen nan fa ni har yanzu ban yarda da su ba, hatta ku蓷in da Uwar ta ta kawo wai a siyawa Zulfa Tsintsiya suna nan na ma茩ale su a kusurwar 蓷akina... "
Girgiza Kai Nasmatu ta yi tana fa蓷in.
"Haba Ayya! Dan Allah ki daina wannan maganar. Hasashen fa da kike akan mutanen nan sam ba gaskiya ba ne, tashi suka yi daga gidan da suke suka canza wuri ba tare da kowa yasan inda 蓷an uwansa yake ba. Sannan tun da ya samo inda suke har yau kin 茩ara jin cewa sun 蓳ata?.....Ni dai Yaya Nura Ina goyon bayan wannan maganar kawai a nema masa aurenta kowa ma ya huta, domin zaryar hanyar nan da yake ta yi yawa..."
Jinjina kai Yaya Kamal Ya yi, ya ce.
" Tabbas nima na goyi da baya, tsawon lokacin nan da aka share yana bibiyarta, komai za'a yi ba zai daina ba, saboda haka a saka lokaci kawai mu shirya muje a nema masa aurenta."
Nusaiba itama ta ce.
" Ni ma na amince da wannan shawarar, kuma wallahi Beenafah yarinya ce mai nutsuwa da hankali, daga ita har mahaifiyarta suna da kirki sosai, ko haihuwar nan da na yi kwanakin baya sai da suka zo mini barka."
Ido ya juya ya kalli Umma ya ce.
"Umma ke baki ce komai ba??"
Girgiza kai ta yi ta ce.
"Bani da matsala domin ba ni ce zan zauna masa zaman auren sa ba, Allah yasa alheri yasa albarka."
"Ke fa Ayya?"
"Hmm! To! Ni dai gaskiya na so ya Auri Sabila tun da dai ita ce wacce muka sani, amma kuma 蓷an yau nasan baka isa ka shiga gaba da al'amarin shi ba,saboda haka nima na amince amma dai ba don raina ya so ba."
Babu wanda bai dara ba a wannan amsar ta 茩arshe da Ayya ta bada, sannan daga 茩arshe Yaya Nura ya ce.
" To abu yayi kyau, kuma In Sha Allahu zan tattauna da su Alhaji Nasiru suma (cewa da sauran yuyyunsu da kuma en uwan su) nan da sati biyu zamu kai 茩arshe, gaba蓷aya zuwa wata 蓷aya, sai mu zo muje gidan wurin nema masa ita. Saboda haka gobe a tare zamu koma da kai 茩afata 茩afarka, ina so zan tafi 蓷auko kaya, dole za ka tsaya a Shago.... "
Wata Hararar Umma ta sake jefa mishi sannan ta ce.
" To yanzu sai na gani kuma idan ha茩urin wata 蓷aya ne ba za ka iya ba, tunda har an yi wannan maganar ina so ka tsaya ka fuskanci kasuwancinka."
Tamkar wanda aka zarewa lakka haka ya gya蓷a mata kai a hankali ya tashi ya bar 蓷akin.
Can wajen 茩ofar gidan ya fice gaba蓷aya yana nazari. Shifa wallahi notukan kanshi ma sun kwance a halin yanzu, ya kasa rarrabe cewa shin a yanzu farin ciki yake ciki ko kuwa. Auren Beenafah fa akace za'a nema masa amma kuma bai ta蓳a furta mata cewa yana sonta ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Abin da ya shiga nanatawa kenan yana mai samun wani 蓳aragurbin tunane daga wani 蓳angare na zuciyarsa cewa to idan ta ce ita bata son shi da aure fa?? Tambayar kan shi ya fara na cewa to shi 蓷in yana sonta kuwa? Duk da tsoro ne fal a cikin zuciyar sa amma hakan bai hana mishi murmusawa ba a lokacinda ya tsinci kanshi da yiwa kansa tambayar.
Tabbas yana sonta yana yi mata wani son da baki ma ba zai fasalta shi ba.
Wayarshi ya zaro daga Aljihu ya duba agogo. 茦arfe goma sha 蓷aya saura na dare, saboda haka lokacin kiranta ya wuce a gareshi amma kuma magana ta gaskiya ba zai iya kai wa Magribar gobe ba tare da ya bayyana mata halin da ake ciki ba. Hakan yasa ya tura mata text da cewa dan Allah gobe ta yi ha茩uri ta tafi da wayar wurin aikinta yana so ya yi wata magana da ita mai matu茩ar muhimmanci.
*****
Tun a daren jiya, da mamakin rashin kiran Yaya Ashiru na kwana a raina har gari ya waye.
Ina yin sallah na janyo wayar da sunan yin azkhar 蓷inda nake yi wanda yake Application ne mai zaman 茩anshi a wayar kwatsam sai ga text 蓷in Yaya Ashiru na gani.
Na da蓷e tsawon lokaci ina jujjuya maganar a 茩wa茩walwata sannan daga 茩arshe kawai na yi murmushi na tashi na yi duk abin da zan yi sannan da zan tafi na ma茩ale wayar a hijabina abin da ban ta蓳a yi ba. Wato yi wa Ammie rashin gaskiya da kuma sa蓳a maganarta, wanda ni har ga Allah ban yi hakan da wata manufa ba, kawai dai na 茩osa ne in ji shin wacce magana ce yake so ya furta a gare ni,domin ba zan iya jira har Magrib 蓷inba.
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍