Free chapter 路 Read without an account
PAGE 27
by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO
GANIN IDO 馃馃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671
FREE-BOOK
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel 蓷inmu na tafe in sha Allahu zamu ri茩a yi muku posting gaba 蓷aya free books 蓷inmu wa蓷anda babu algus....
PAGE 27
Cikin rashin 蓷aukar zancen na wa da muhimmanci yasa shi murmusawa yana mai jinjina kansa a hankali ya lumshe idanunsa ya bu蓷e su a kaina ya ce.
"Lokaci ne ka蓷ai zai tabbatar da hakan Lady B.....kuma In Sha Allahu dani za a yi shi matu茩ar dai ba ke ce za ki ce a'a ba..."
Juyawa na yi na bar wurin na wuce kai tsaye 蓷akinmu na jefa ledar wayar a kan katifa na koma na ci gaba da abunda nake.
*********
Tudun Wada,
Zamfara State,
Gusau, Nigeria.
" Look Ziza! Ni fa ko ka蓷an bana nufin 茩untatawa a gareki.... "
Cikin gunjin Kuka ta katse shi da fa蓷in.
"Baka nufin 茩untatawa a gare ni amma kake neman auren House Maid Emraan...Wannan wane irin 茩as茩anci ne da rashin daraja... Yanzu kai baka ji kunyar hakan ba? Miye na yi maka? Auren namu kwata-kwatansa kwana nawa ne? Ni za ka wu茩alanta? a gabana fa ka bu蓷e bakinka ka ce wai ka samu matar aure, alhali an ce ko mutuwa tana kunya idon mahaifi...Amma haka ka nuna bani da wata daraja ko wata 茩ima kenan..... "
" No..no..please Ziza,wallahi that's not what I meant...ko ka蓷an ban fa蓷i haka wai don in tozarta ki ba ko kuma wula茩anci... I love you... I love you so much Ziza kuma hakan ba zai ta蓳a canza wa ba, ke 蓷in matar rufin asiri na ce kuma ina matu茩ar alfahari da hakan domin tsawon zamanmu ban ga wani babban kuskurenki da zan ce Allah wadai ba...please try to understand me Ko ka蓷an ban da nufin wu茩alanci a gare ki.. In fact gidanki daban na ta daban...Babu wacce zan wula茩anta kuma ba zan bari wata ta wula茩anta wata ba a cikinku,... And kasancewar ki babba, dan Allah let's peace and harmony reigns between us...... "
Cike da jin wani irin sabon ba茩in cikin ta girgiza kanta ta katse shi da fa蓷in.
" Emraan ko a 茩ar茩ashin 茩asa za ka sakata wannan duk a banza domin ba'a canzawa tuwo suna, muddin ka aureta ta riga ta zama kishiya ta kuma wallahi tallahi na rantse da Allah hakan ba zai faru ba domin baka isa ba wallahi!!!"
Jinjina kansa ya yi yana mai jin wani irin 蓳acin rai ya ce.
" Haka ki ka ce ko?"
" Eh haka na ce Emraan!"
Mi茩ewa ya yi tsaye kamar yanda ta tsaya a kansa suna fuskantar juna ya ce.
" To bari ki ji Aziza...Tun da har na biki da lalama kuma baki saurare ni ba, shikenan! Zan yi aure, kuma zan auri Beenafah, dan Allah idan kin isa ki hana. Zaman lafiya akace ya fi zama 蓷an sarki... Da wannan yasa nake so mu yi komai cikin ilmi da wayewa..."
Wani irin matsanancin kuka ne ta sake fashewa da shi tana fa蓷in.
" Haka ka ce? Haka ka ce ko? Wallahi tallahi za ka gani! Matu茩ar dai na amsa sunana ni Ziza Ashraf wallahi tallahi ba za ka aureta ba... "
Zaunawa ya yi a hankali ya janyo glass cup 蓷inda ta kawo masa ya tsiyaya lemu da nufin sha amma cikin zafin nama ta saka hannu ta ture kayan gaba蓷aya suka watse a 茩asa suka tarwatse.
Mi茩ewa ya yi kurum ba tare ya ce mata komai ba yasa kai ya fice daga gidan gaba蓷aya.
Wayarta ta 蓷auko hankali a tashe ta kira wayar Mummy Raliya. Tana jin ta 蓷auka a gigice ta ce.
"Mummy na shiga uku na lalace Mummy.... Wai Emraan kishiya zai mini kuma kishiyarma '拼ar aiki..."
Daga can 蓳angaren Mummy Raliyar ta ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!....Please cool your mind...Samu wuri ki zauna ki kur蓳a ruwan sanyi sannan ki yi wannan addu'ar; ki ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirni fiy-musibati-Wa Akhlufni khairan minha...please ki yi yanda na ce miki yanzu, idan kin kambala sai ki kirawo ni muyi magana. "
A gaggauce ta aikata duk abinda ta ce mata exactly sannan ta sake 蓷aukar wayar ta kira ta ta ce.
" Mummy na yi duk abin da kika ce...."
A hankali ta jinjina kanta ta ce.
" Masha Allah, In Sha Allahu ko mine ne zai zo miki da sau茩i... "
" Mummy kishiya fa na ce miki Emraan zai mini kuma da mai aiki..."
"Duk na ji! Amma ki sani, tashin hankali ko wani barazanar ki ba zai sa ya sauya ba, in dai ma namiji ne sai da ya 茩ara miki ba茩in ciki akan ba茩in ciki muddin kika ce ba za ki shafawa kan ki ruwa ba.....Hajiyarsa ta sani?"
Ido cike da ruwan hawaye ta ce.
" Hajiya bata sani ba, na tabbata bai isa ya fa蓷a mata wannan abun kunyar ba...."
"To Labiba fa?"
Cikin jin wata irin tsanar Labibar a lokaci 蓷aya ta ce.
"Ya sanar mata, dole ita zai sanarwa tunda ita ce babbar munafukar da ta kawo yarinyar gidan na su wai da sunan mai aiki, wallahi tallahi wannan munafukar yarinya daman ba ta yi kama da mai aiki ba kawai dai munafurci suka shirya wanda tun farko ban gane ba ma sai yanzu... "
" Duk da haka dai, ki bari abi komai a sannu Ziza, tashin hankali babu abinda zai haifar idan ba 茩arin matsala da 蓳acin rai ba... "
Cikin wani irin kuka ta shiga girgiza kanta tana fa蓷in.
" Ai na san haka za ki ce Mummy....daman nasan haka za ki ceee... "
Daga haka ta yanke wayar tare da jifa da ita a 蓷ayan kujerar da take zaune.
********
Sai da Mummy ta share kusan kwana uku a asibiti, ta suma ta farfa蓷o ta suma ta farfa蓷o haka ta dinga yi sai daga 茩arshe suka samu aka samo kanta da 茩yar sannan suka tattara suka dawo gida.
Gaba蓷aya ta susuce ta gigice ta fita hayyacinta, ko ka蓷an ko a mafarkinta bata ta蓳a zaton cewa wai Hassana za ta iya bijire mata ba har da ha蓷a kayanta ta tsere. Wannan wane irin tozarci ne da abun kunya?
Tana zaune Aysha na ta aikin ba ta baki ta 蓷ago idanuwanta da suka rine sosai suka yi sasul akan kuka ta kalli Ayshar ta ce.
"Aysha duk an bincika ko'ina ba'a ga Hassanar ba har yanzu? Ko ba'a je neman ta ba ne? Ina Alhajin yake?"
Cikin tausasawa Aysha ta ce.
"Mummy ki kwantar hankalinki In Sha Allahu za a ganta..."
Hannu ta saka da 茩arfi ta ture kofin shayin da Husaina take bata tamkar wata mai ta蓳in 茩wa茩walwa ta shiga kallon su tana fa蓷in.
"In kwantar da hankalina kike cewa Aysha?? Miyasa kike yin wasu abubuwan da yasa nake jin kamar bakya 茩aunata? Kin san irin kalar al茩awarurrukan da ke tsakaninmu da gidan Alhaji Mansur 蓷in idan har wannan auren ya tabbata? Ni karan kaina akwai wani kamfaninsa da ya yi al茩awarin mallakamin, suma su Hassana akwai abubuwa da dama da za su mallaka na manyan kadarori,...waccan jibgegiyar motar da kika gani fa sabuwa tare da lefen nan aka kawo Alhaji ita kyauta, an ce ta amaren da tawa suna hanya...sannan har cikin shares 蓷insa ya yi al茩awarin mallakawa Alhajin da kuma Hafiz wasu daga ciki da zaran an yi auren kafin nan kuma Hafiz ya iyarda kambala karatun sa ya dawo..."
"To Mummy idan ban ce ki yi ha茩uri ba mi zan ce? tun fa ranar Daddy ya aika har garin su Salman 蓷in amma ba'a samu labarinta ba, har kulle Salman 蓷in akayi sai jiya aka sake sa amma kuma shi kan shi an yi duk binciken da za'a yi amma bai san inda take ba. Gida ma duk su Alhaji Baba su Uncle Isma'il kowa ya ce bata je wurin sa ba... "
Girgiza kanta take tamkar wata mahaukaciya tana fa蓷in.
" A'a, wallahi tallahi wannan 茩arye ne... Wayyo Allah na! Wayyo ni Zaliha! Hassana ta tona mini asiri, na shiga uku na lalace..."
"Innalillahi! Dan Allah mummy ki yi ha茩uri. In sha Allahu za a gano inda take..."
"Ina Alhaji yake??"
"Daddy tun safe ya hau jirgi zuwa Australia an yi mishi kiran gaggawa daga makarantar su Hafiz."
Komawa ta yi luf ta kwanta jikin kujera kamar wata marainiya tana mai share hawaye akai-akai abin duniya duk ya bi ya isheta.
*******
Tun da Daddy ya kar蓳i sa茩on gayyata ta gaggawa through Email 蓷insa daga makarantar su Hafiz hankalinsa ya tashi, gaba蓷aya ko baccin kirki ya kasa yi akan wannan dalilin, kwana ya yi yana tambayar kansa miye ya faru da har ta kai aka aiko masa da official letter of misconduct? Miye Hafiz 蓷in zai aikata haka da zafi? Yaron kirki mai matu茩ar basira miye zai faru haka?
Tambayoyinda ya yi ta jerawa kansa kenan daga cikin zuciyarsa wa蓷anda yasan tabbas ba shi da amsar su sai dai idan ya isa makarantar ya gani ya kuma jiye ma kunnen sa.
A hankali ya taka ya shiga Main Admin block 蓷insu Wanda daga nan reception aka dangana shi da office 蓷in vice Chancellor Mai suna Professor Dean Michael inda a nan ya tarar da Head of academic, Register, Discipline committee, sauran head of department da kuma sauran lecturers wanda daga cikin su akwai Mr. Collins.
Gefe 蓷aya kuwa, Hafiz ne tare da sauran 蓷alibai en uwansa su takwas.
A hankali Daddy ta taka ya je ya samu 蓳angaren inda sauran iyayen yaran suka zauna shima ya zauna ri茩e da file 蓷inda aka bashi tun daga Reception 蓷in.
Vice Chancellor 蓷in ne ya fara magana cikin harshen turanci cike da girmamawa ya ce.
" Good afternoon all, muna yi muku barka da zuwa kuma mun gode muku sosai da har kuka iya amsa gayyatarmu akan lokaci kuka halarta daga sasassa daban-daban na fa蓷in duniya. Muna fata kuma za ku bamu ha蓷in kai domin gudanar da abin da ya tara mu a nan cikin girmamawa da mutuntuwa....."
Bayan sun gama gudanar da duk wasu bayanai da tsare-tsaren su sannan Mr. Anderson daga Discipline committee ya janyo file 蓷inda ke gaban sa ya bu蓷e shi ya fara bayani da cewa.
" Mun kira ku nan ne akan manyan laifukan da aka kama yaranku sun aikata, wa蓷annan laifuka ne da suka shafi both academic and moral standards na wannan makarantar."
Tsit 蓷akin ya yi tamkar ba kowa a ciki tsabar yanda daga yaran har iyayensu suka sha jinin jikinsu, ba ma kamar Hafiz 蓷in.
A hankali ya ci gaba da cewa.
"Wa蓷an nan laifukan su ne wa蓷anda muka same su da su bayan yin 茩wa茩w茩waran bincike yanda ya kamata tare da tuhumar yaranku akan laifin kuma suka amsa ba tare da sun musa mana ba, Hafiz Mudassir Wazeer; Laifinsa na farko akwai academic fraud. Hafiz ya ha蓷a baki da Mr. Collins ya biya sa ku蓷i masu yawa ya shirya masa false academic records na fake result 蓷in semesters shida, wanda ya nuna yana da high scores amma kuma bayan biyar diddi茩i na ainahin result 蓷insa mun gano ko wace semester GPA 蓷insa is below 1.50 GPA. Laifi na biyu kuma shine;Bribery and corruption. Ma'ana mun samu 茩wararan shaidu da suka nuna cewa Hafiz yana turawa Mr. Collins ma茩udan ku蓷a蓷e akan ya ri茩a canja masa result 蓷insa a kowace semester. Sai kuma na uku, wanda dukkan su ne ta shafa har da sauran wa蓷an nan 蓷aliban na Repeated misconduct, An sha kama su ana kawo mana 茩arar su daga security campus a wuraren da bai kamata ba, suna shaye-shaye,lalata da yaran mutane, da kuma gurbata rayuwar salihan 蓷alibai zuwa mutanen banza. Sun kasance suna yawan shirya abubuwa wa蓷anda suke taka mana dokar makaranta,sannan ga rashin girmama malamai da yi musu rashin 蓷a a. Na hu蓷u kuma;Akwai poor academic performances Wanda for the past four semesters Kowanne daga cikin su ya yi failing Registered courses da Kuma missing five official exams without any genuine reasons. Sai abu na 茩arshe kuma;Forgery of official document. Ma'ana, an gano cewa Hafiz yana printing fakes progress reports yana aikawa gida Nigeria yana yaudarar iyayensa da sunan shi 蓷in mai 茩o茩ari ne alhali ba haka bane."
Cikin tashin hankali kowa ya hau fa蓷in albarkacin bakin sa, cike da ba茩in cikin abin da yaran na su suka aikata musu bayan sun jima suna kashe musu ma茩udan ku蓷a蓷e.
Wasu irin hawayene masu matu茩ar 蓷aci da 茩una suka gangarowa Daddy wanda ya 茩ura ido kawai yana kallon Hafiz.
Wata envelope ce Head of academic ya bi dukkan iyayen na su ya rarraba musu bayan an ba su dama cewa idan akwai mai wani 茩orafi ya yi.
Bayan ya gama mi茩a musu a hankali ya ce.
"Wannan ita ce takardar official expulsion, ma'ana;an kore su daga wannan makaranta. Muna fata za ku yafe mana domin dole ce ta sa muka aikata hakan."
Waje suka dawo wanda har yanzu ya kasa bu蓷e baki ya furta masa wata magana kamar yanda shi ma Hafiz 蓷in ya yi tsamo-tsamo tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi. Kwata-kwata Hafiz bai tsammaci zuwan wannan ranar ba a rayuwar sa. Ya 蓷auka cewa salin asalin zai gama baza life 蓷insa ya amshi fake result 蓷insa ya koma gida, ashe-ashe rana dubu ce ta 蓳arawo rana 蓷aya ta mai kaya. Yanzu ga shi son zuciya da ganin ku蓷i yasa ya rushe rayuwar sa, bama kamar yanda Mr. Collins ya dinga kuka bayan shi ma an kore sa shi ne abinda ya tsaya masa a rai. Duk irin yanda Mr. Collins 蓷in ke ta baya-baya gashi sai da ya jefa shi a matsalar da yake gudu.
Suna nan tsaye sunyi cirko-cirko sai ga motar jami'ai ta iso wurin, a gaban iyayen na su aka 蓷auke su zuwa office 蓷in immigration domin a fitar da su daga 茩asar Australia cikin kwanaki uku da kuma izinin cewa kada su sake dawowa 茩asar har abada kamar yanda dokar ta su ta tanada.
*******
Jafaru kuwa, yana Zaria 茩aninsa Hamza ya kira shi yana 茩yan茩yasa masa halin da ake ciki na cewa, idan bai dawo ba wallahi sai an aurar da Beenafah ga Ashiru domin har sun zo shi da iyayensa wurin neman auren na ta.
A gigice ya baro Lectures ya juyo ya dawo gida.
Ita dai Mama tana zaune ita da Bahrain da Farisa suna 茩ulla guggurun da ta gama yi yanzu taga mutum ya shigo mata hankali ta she yana fa蓷in.
"Yanzu Mama Beenafahr tawa ce ake zancen a aurawa wani ita? Mama wai ko don ban ta蓳a fa蓷a muku bane ina sonta?Wallahi tallahi ina son ta, babu wacce nake so a cikin raina idan ba ita ba, dan Allah Mama ki fa蓷awa Baba wallahi ita nake so na aura..."
Hannu Mama ta mi茩a masa hankalinta kwance ta ce.
" Bani ku蓷in sadakin ka, lefe, sannan ka nuna mini gidanda zaka ajiye ta...."
Shiru ya yi tare da 茩ura mata ido domin ya rasa bakin magana. Kwata-kwata shi bai tsammaci wannan magana daga bakin ta ba.
"Ka yi shiru! Bani sadaki da lefe na ce, sannan ka nuna mini gidan da za ka sakata a ciki, da kuma sana'ar da kake wacce za ka iya ri茩e ta sannan kuma ka ci gaba da 蓷aukar nauyin karatun ka...."
Gunguni ya fara 茩asa-茩asa yana fa蓷in.
"To amma ai Mama komai na duniya 蓷an a hankali ne..."
Jinjina kanta ta yi tare da 茩ara tamke fuska ta ce.
"Allah ko! To ai tun kafin a haifeka na san cewa komai na duniya 蓷an a hankali ne.... Tabbas da ace kana da wa蓷annan abubuwan da na lissafa da dani da Malam ko sama da 茩asa za ta ha蓷e sai mun tsaya akan dugaduganmu mun tabbatar cewa ka same ta....amma yanzu Jafaru magana ta gaskiya ka yi tsaga da fa蓷i. Da ma ace itama karatu take kamar kai, da na san tabbas za ku iya yin daidai... "
" To Mama dan Allah a sakata makarantar mana, sai mu jira juna ni da ita... "
" Jafaru! Jafaru! Ka wuce ka mayarda hankali akan karatunka ko dan goben ka, ka sakawa kanka salama domin ba za ka ta蓳a samun Beenafah ba... "
Cike da wani irin 茩unci da damuwa ya ce.
" Dan Allah Mama ki fahimtar da su cewa su mayarda ita a makaranta wallahi na san zamu yi daidai.. "
Jinjina kai ta yi ta ce.
" To je ka ka fahimtar da su Jafaru."
A nan ya yasar da jakar sa da yazo da ita ya fito afujajan ya nufi gidan Ammie ransa na masa wata irin suya.
Ammie na tsaye tana shanya kayan Bahrain a igiya ya yi sallama ya shiga.
Kallo 蓷aya Ammie ta yi masa ta fahimci kwanan zancen, daman ta san tabbas za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya.
Ido a rufe ya fara masifa da fa蓷in.
"Ammie miyasa za a nemi bayar da Beenafah alhali ni 蓷in ina sonta?? Wannan ba adalci ba ne, babu wanda zai aure ta ya kula da ita fiye dani,..."
Jinjina kai tayi cikin tausasa murya ta ce.
"Na sani Jafaru....amma samu wuri ka zauna mu yi magana."
A nan inda yake tsaye a nan ya dar蓳e zaune yana mai 茩ure ta da kallo alamar yana jira ya ji mi za ta fa蓷a masa.
Kujera ta janyo ta zauna suna fuskantar juna cikin 茩ara tausasa maganarta ta ce.
"Na san cewa kana son Beenafah, na fi kowa sanin yanda kake sonta,kuma idan har Allah ya rubuta cewa Beenafah matar ka ce, to babu wani mahalu茩inda ya isa ya hana, idan kuma Allah ya rubuta cewa ba matarka ba ce duk yanda aka so ba za ka aure ta ba. Abubuwan sun juye fiye ma da yanda muka tsammata Jafaru. Kuma ina neman alfarma a gareka....kamar yadda ka ji tana cewa tana da matsayi a gareka na soyayya, to ina so ka sake bata wani 蓳angaren a zuciyarka na zamto wa 茩anwa a gareka, ka 蓷auketa tamkar Fakiha wacce duk rintsi za ka tsaya mata a matsayin Yayanta mai kare mata mutuncin ta. Idan har Allah ya nufe ka da aurenta ba ni da ja da hakan, idan kuma ya 茩addaro cewa wani daban ne za ta aura to za ka yafe mata ku ci gaba da zumunci. "
A hankali kukan da yake ri茩ewa ya kubce masa da 茩arfin gaske tamkar wata Macce.
Tashi ta yi taci gaba da abin da take ba tare da ta yi yun茩urin hana sa kukan ba. Sai da ya yi sosai wanda har sai da ya ji zuciyarsa ta 蓷an sanyaya sannan ya sassauta tare da mi茩ewa a tsaye ya kalle ta murya a dusashe ya ce.
"Na gode Ammie, idan Beenafah rabona ce ina fata Allah ya mallaka mini ita, idan kuma ba rabona ba ce ina yi mata fatan alheri da fatan farin ciki mai 蓷orewa har zuwa 茩arshen rayuwarta."
Daga haka ya juya ya fice ba tare da ya jira amsar ta ba.
Jikin gini ta tsaya shiruu! Tana jujjuya al'amarin a zuciyarta, wallahi tallahi ta yi matu茩ar tausaya masa a yau kamar yanda take tausayawa Ashiru. Duk irin amsar da shima ta bashi ya ce sam ba zai ha茩ura ba, 茩arshe ma cewa ya yi ta bashi numbern Daddy da address 蓷insa shi zai je har Abuja ya same shi. Jin ya matsa ya dage akan dole sai ta bashi yasa ta ce yaje tsohon gidanda suka taso wurin Uncle Isma'il ya bashi numbern Daddyn da address 蓷insa.
*********
Ziza kuwa, tun da Emraan ya sa 茩afa ya bar gidan bata sake sanya shi a idonta ba, kiran duniya ta yi kuma ya 茩i ya 蓷aga wayar ta. Gashi bata ma son ha蓷a fuska da Labiba ballantana taje ta koka mata halin da take ciki. Sannan ta yi tsammanin Hajiya za ta zo gidan ta sameta idan ta ganshi a gidan amma kuma ba ta yi hakan ba wanda shi ne abin da ya 茩ara tunzura ta. Shawara take na ta kira Baba Ustaz 茦anin Mahaifin Emraan 蓷in ko kuwa ta 蓷an 茩ara jira ta gani.
茦arshe dai haka ta mi茩e ido cike da ruwan hawaye ta 蓷auki Abeer ta je ta shiga motarta ta wuce gidan Hajiya.
Tana shiga gidan ta wuce har bedroom 蓷inta ta zauna a sofa ko gaisawa bata jira sun yi ba kawai ta fashe mata da kuka.
A hankali Hajiyar ta ajiye turarukan da take gyarawa ta zo ta zauna a edge 蓷in gadonta suna fuskantar juna ta ce.
"Subhanallah! Ziza Lafiya kuwa?..."
Cike da damuwa ta ce.
"Hajiya yanzu abin da Emraan zai mini kenan? Ga mari ga tsinka Jaka! Sannan Hajiya ace kina ganin sa amma ba za ki masa magana ba..."
"Bayani za ki yi mini yanda zan fahimta Ziza, go straight to the point please."
"Hajiya Emraan ne ya sameni da zancen wai zai 茩ara aure, kuma auren ma da Beenafah wanda na san bai fa蓷a miki ba, to wai don saboda na nuna rashin amincewa ta shi ne ya baro gidan ya dawo nan yau tsawon kwana biyu cikin na uku. Yanzu Hajiya dan Allah hakan adalci ne?"
Girgiza kai Hajiya ta yi tana mai kallon 茩wayar idanunta ta ce.
" Magana ta gaskiya, na san da zancen auren amma kuma ban san cewa yana gidan nan ya yi miki ya ji ba tsawon kwanaki... "
Wani iri dummm! Ta ji a 茩irjinta tamkar an soka mata Mashi jin furucin Hajiya a gareta...Yanzu kenan tasan da zancen auren na shi kuma shi ne take zaune hankalinta kwance?
" Ki yi ha茩uri, In Sha Allahu zan mi shi magana... "
Wata irin zabura ta yi ta mi茩e tsaye ranta na mata wata irin suya a gigice tana kallon Hajiyar ta ce.
"Yanzu Hajiya abin da ma za ki ce kenan, duk irin 茩untatamin da ya yi ya bar ni tsawon kwana biyu sannan ga zancen auren da ya yi duk baki ga wani laifin sa ba, abin da zaki ce kawai shi ne in yi ha茩uri za ki masa magana! Ba za ki kira sa a gabana gani ga shi ki yi mana hukunci ba? Ya rasa wacce zai aura sai Mai aiki? Wallahi tallahi ba zan yarda ba! Wallahi ba zan yarda ba... "
Daga haka ta juya ta bar gidan gaba蓷aya ta koma gida ta shiga ha蓷a kayan ta.
Hajiya kuwa, Wayarta ta janyo cike da al'ajabi ta shiga kiran Emraan 蓷in amma kuma bai 蓷aga ba. Mamaki take wai ace Emraan yana gidan tsawon kwana biyu ba tare da ta sani ba, jiya ya shigo da yamma, shekaranjiya ma ya shigo da dare amma kuma duk bai wani jima ba ya tafi.
Bayan ta yi ta kiran wayarsa bai 蓷aga ba, 茩arshe ta fito da kanta ta je 蓷akinsa amma kuma baya nan babu wata alama da ta nuna mata ma cewar yana gidan. To ko dai wani wurin ya je ba nan ba?
Da haka ta sake juyawa ta koma ciki ta ci gaba da ayyukanta. Tunani take a ranta cewa tun da har taji hatta Hairiyya bata kira ta akan wannan maganar ba to ta tabbata babu wacce ya sanarwa daga cikin su, daga Labiba har Nadeeya babu wacce ya sanar wa. Saboda haka so take sai ta fara magana da shi sannan ta san irin hukuncin da ya kamata ta yanke.
Ta na nan dai Misalin 茩arfe biyu da rabi na rana, ganin har yanzu bata samu magana da Emraan ba kuma shi bai zo ba yasa ta 蓷aga waya ta kira Haula ta ce mata ta fa蓷a mini cewa tana son ganina yanzu.
Ina zaune bayan na kambala sallah na yi shiru ina nazari. Baccin da na yi ne mai nauyi har yasa na makara wurin gabatar da sallar Zuhr 蓷in. Suna zaune a gefe suna cin abinci Hajiya ta kira ta ina ji ta ce tana son ganina.
Kallona Haula ta yi ta ce.
"To tunda kin 茩i kici abinci ta shi kije Hajiya tana neman ki."
Mi茩ewa kawai na yi na fito waje na samu wuri na zauna tsawon lokaci, sannan daga 茩arshe na tashi na shige cikin gidan ba tare da sanin dalilin kiran ba, sai dai kuma ban kawo komai a raina ba domin tun ina jin 蓷ar-蓷ar na cewa za ta yi mini magana akan Emraan, ko ita ko Aunty Labiba har na zo na daina damuwa domin a tunanina shi ka 蓷ai ne yake shirmensa ba tare da kowa ya sani ba. Sannan kuma sanin cewa Daddy ya ce zai aurar dani ga Ilyas yasa na daina damuwa da al'amarin Emraan 蓷in domin nasan Ihu ne kawai yake bayan hari, domin tun da Daddy ya furta, to kuwa nasan tabbas zai cika.
A hankali na tura 茩ofar tare da yin sallama na shiga na zauna a 茩asa ina fa蓷in gani. Sai dai kuma, ganin mutanen da ke zaune a 蓷akin ne ya yi matu茩ar 蓷aga mini hankali ganin babu mutum 茩waya 蓷aya da na sani a cikin su sai Hajiyar.
Wayarta dake gefe ce ta shiga 蓳urari ba 茩a茩茩autawa. Sai da tayi kamar ba za ta 蓷auka ba sannan kuma daga 茩arshe ta janyo ta duba,ganin sunan babbar 茩awarta Hajiya Samira dake zaune a Lagos, yasa ta yi saurin 蓷aga wayar tana fa蓷in.
"Ziza ta kawo 茩ara ko?"
Dariya matar ta yi daga can 蓳angaren ta ce.
"Kamar ko kin sani! Yanzu ta kirani tana shaida mini shi ne na ce ta jira zan kira ki yanzu..."
Mi茩ewa tayi tare da 蓷aukar excuse a wurinsa ta fice daga parlourn domin amsa kira.
Suna ganin ta fice suka juye baki suka yi ta magana da turanci wanda na san hakan ba ya rasa nasaba da wanzuwata a 蓷akin domin kada in ji mi suke fa蓷a.
Sun 蓷auki tsawon lokacin da yakai hour 蓷aya cikin ta biyu suna magana wanda ban san abinda ya tsayar da Hajiya waje ba har yasa bata dawo ba. Fira suke wacce ta gigitani da kuma 蓷ai蓷ai蓷aita tunanina, firar da ta shigar dani cikin tsananin duhu da ru蓷anin neman 茩arin bayani dangane da abubuwan da kunnuwana suka jiye mini, zuciyata ce ta tsinke! Tunanina ya juye! Hankalina ya yi tashin gwauron zabin da ban san ma miye ya kamata na yi ba. Miye wannan suke magana akai? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wai miyasa duniya ta dawo haka ne? Miyasa cin amana da zalunci ya zama kamar shan ruwa a wurin wa su?.
Mi茩ewa na yi jikina na rawa na sulale na bar 蓷akin, domin akan maganar ta yi masu da蓷i, dariya suke suna ta kekkewa hankalinsu kwance.
Tafiya nake amma a matu茩ar gigice nake, domin bana kallon ma inda nake jefa 茩afata tsabar tashin hankalin da nake ciki, har na kai gida na fa蓷a 蓷aki na kwanta ina mai rushe wa da kuka ban san miye yake damuna ba, jikina sai wata ciccira yake tamkar wata mai sabuwar cutar jijjiga.
Ammie da kambala sallar ta kenan tayo kaina da gudu tana mai janyoni jikinta hankali tashe tana fa蓷in.
"Lafiya Beenafah! Miye ya faru dake?"
Girgiza kaina na shiga yi ina kuka ina fa蓷in.
"Ba komai... Ba komai Ammie! zazza蓳i ne kawai nake ji... Zazza蓳i mai zafi sosai... Ta蓳a jikina ki ji ya yi zafi sosai Ammie.."
Da sauri ta kawo hannunta zuwa wuyana zuwa goshina. Cike da tashin hankali ta ce.
"Wai Beenafah dan Allah ba za ki tausayawa kanki ki 蓷au dangana ba? Ke ce fa kike mini nasiha akan kada in damu da komai in yi ha茩uri Allah yana sa ne da komai..."
Haka ta 蓷auki tsawon lokaci tana lallashina tare da bani baki a hankali har ta samu na natsa da kukan da nake yi ba tare da amsa mata ko da magana 蓷aya ba.
Duniya ta bani mamaki, matu茩ar mamaki wanda har yanzu ba ta daina ba, domin kullum kwanan duniya akan bani sabon darasi take kamar ko yaushe.
Yanda na ga rana haka na ga dare domin ko ka蓷an ban samu na runtsa ba, tunane-tunane kawai na ke da neman mafita. In sa茩a in warware in sa茩a in warware haka nai ta yi har gari ya waye.
Ina tashi na yi sallah na fito da nufin aiki sai Ammie ta hanani ta ce na koma na kwanta, ko gidan aikina ba zan je ba domin rashin lafiya ya kauda komai, sai da lafiyar ake iya yin wani kata蓳us saboda haka na koma na kwanta abina.
A yanzu, ba saurarar maganar ta ce a gabana na ba, domin ni sam ban ga ta zama ba. Hakan yasa ban ko bi takan wanka ba na ce mata dole sai na fita domin akwai ajiyar da Hajiya ta bani kuma nice ka蓷ai zan iya 蓷auko wa daga inda na ajiye, ga shi za ta yi asuba zuwa Kebbi, saboda haka dan Allah ta barni in tafi in bata sa茩on daga baya sai in dawo tunda babu wayar da zan kira in shelanta musu uzurina.
Ko makaho ya shafa yanayin da nake ciki yasan bana cikin hayyacina, ta dalilin damuwata da ta gauraya da wata gingimemiyar damuwar da ban san ma ta ina zan fara ba. Gidan Aunty Labiba na nufa ba tare da jin wani 茩iren tsoro ba na 茩wan茩wasa 茩ofar gate 蓷in.
Kallona Mai gadin na su yayi ba tare da ya gane ni ba ya ce.
"Malama ke wacece kuma wa kike nema?"
Kai tsaye na ce.
"Wurin Aunty Labiba na zo, dan Allah kira ta kace ta yi ba茩uwa..."
Agogon 茩aramar wayarshi ya duba yaga cewa bakwaice yanzu na safe da mintuna tara. Cike da zallar mamaki ya ce.
"Ina fata dai lafiya?"
"Lafiya lau, ka kirata ka ce mata Beenafah ce."
Wani irin kallon ne ya jefa mini, kamar zai yi magana sai kuma bai yi ba ya 蓷auki wayar ya kira ta kusan sau hu蓷u amma bata 蓷aga ba, mita ya fara akan bata tashi ba kuma 茩arshe ma in ja masa ayi masa fa蓷a.
Ni dai ina tsaye na yi shiru duk abin duniya yabi ya ishe ni. Ina nan ba tsammani daga 茩arshe na ji ya ce in shiga tana ciki ta ce in shigo.
Ina tura 茩ofar parlourn na sameta tsaye sanye da kayan baccin ta dogaye har 茩asa ta 茩ura mini ido cikin tashin hankali ta ce.
"Lafiya Beenafah?"
Hawayen da suka silalo mini ne na share sannan na jinjina kaina na ce.
"Shin zamu iya zaunawa muyi magana ta fahimta Aunty Labiba?"
Da sauri ta jinjina kanta tana fa蓷in.
"Of course dear...zo mu shiga wancan parlourn..."
Ta 茩arashe maganar tana jan hannuna da sauri muka shige parlourn ta rufe ruf da key muka zauna a kujera 蓷aya gab da gab ta 茩ura mini ido tana fa蓷in.
"Miye ya faru haka Beenafah?"
Still da ruwan hawaye a idona ina kallonta kamar yanda take Kallona na ce.
"Wane ne Muhammad Aunty Labiba???"
Wata irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali tare da lumshe idanunta ta bu蓷e sannan ta yi wani murmushi mai gauraye da ruwan hawaye a lokaci 蓷aya ta ce mini.
"Yaya MOHAA! Shi 蓷in Yayana ne, Shi ne babban Yayanmu..."
Kafin ta iyarda rufe bakinta na gya蓷a kaina na ce.
"To Ina so na aure shi!!!"
Wata irin zabura ta yi ta mi茩e tsaye har saida na 蓷an tsorata ta kalleni hankalinta a tashe ta ce.
"Kin san mi kike fa蓷a kuwa Beenafah???"
Gya蓷a kaina na yi ina kallonta na ce.
"Na sani!!..."
Girgixa kai ta shiga yi tana fa蓷in.
"A'a, baki sani ba Beenafah....gaskiya baki sani ba.."
"Aunty Labiba ina sane da komai, a hayyacina nake, kuma shi nake so shi zan aura..."
Wani irin kuka ne ta fashe da shi wanda ya sar茩afe zuciyata da matsanancin ru蓷ani da tsoro.
Shiru 蓷akin ya 蓷auka na tsawon lokaci wanda daga ni har ita babu wanda ya yi magana sannan daga 茩arshe ta 蓷ago idanunta wa蓷anda suka ji茩e da ruwan hawaye ta kalleni tana mai girgiza kanta ta ce.
"Na sani, you are doing all this things don Kawai ki faranta mini kamar yanda na taimake ki ko? Hmm! Kada ki sakawa ranki abin da ba zai ta蓳a yiyuwa ba Beenafah. Ko ma a ina kika jiyo tarihin Daddyn Raudah, wannan bai dame ni ba, domin ba abun 蓳oyo ba ne,amma kuma ki sani, ba za ki ta蓳a iya yin nasara ba..."
Wani kallon na yi mata na ce.
" Miyasa kika ce haka Aunty Labiba...Miyasa kike ganin kamar ba zan iya ba? A rashin tayi fa ake barin arha banza...ki barni na jaraba sa'a ta mana.!!!"
Wani irin murmushi ta yi mai sauti sannan ta girgiza kanta ta ce.
"Uhm! Beenafah kenan! neman aure sau ashirin da bakwai...goma sha uku daga ciki har ranar 蓷aura aure sai an kai amma kuma a fasa, uku daga ciki hour 蓷aya ce zuwa biyu yake ragewa a 蓷aura amma kuma a fasa. Manyan mata, manyan 'ya' yan attajirai, har 'ya' yan sarakuna ma an nema, amma kuma ba a yi nasara ba. 茦arshe kunya ce da ba茩in ciki da kuma nadama suke mamaye farin ciki da 蓷aukin da muke ciki a maimakon murnar auren. Mun ha茩ura, mun janye, idan har wannan ita ce 茩addararsa muna fata Allah yasa jinda蓷insa da farin cikinsa su riskesa a aljanna firdaus idan yana da rabo.... Dan Allah kada ki sa ciwon da ya wuce a wurinmu na tsawon lokaci ki ce za ki sake fama mana shi.... "
Hannunta na ri茩o cike da 茩warin gwiwa na ce.
" Aunty Labiba ki yarda dani, in sha Allahu rabbi da izinin ubangiji wannan karon zamuyi nasara...dan Allah ina ro茩on ki da ki amince kuma ki bani goyon baya dan Allah... "
" Beenaf... "
" Trust me.... In Sha Allah we are going to succeed.."
"But how??"
"Gobe za'a 蓷aura mana aure. Amma kuma da shara蓷i?"
Wani irin kallo ne ta bini da shi mai cike da tsananin ru蓷ani da neman 茩arin haske ta ce.
"Shara蓷i Beenafah? Wane irin shara蓷i ne wannan?"
鉁嶏笍 OUM-AMEER 鉁嶏笍