Free chapter · Read without an account

Babi na Biyu

by Yasmeen · Kowa Ya Daka Ta Bado


2012

Malam Shu'aibu ne tsaya a ƙofar gidan maƙocinsa ya dafe bangon gidan da hannunsa na dama yana addu'ar samun abunda ya kawo shi. Tunani yake yi kala kala na neman mafita idan wannan bai yi aiki ba.

"Ah Malam Shu'aibu kai ne? Shigo daga ciki mana" ya jiyo muryar maƙocinsa Sani direba wanda ya saka shi ɗagowa shi ma yana miƙa masa hannu

"Ba sai na shigo ba Malam Sani. Maganar ba wata mai tsayi bace"

"Toh toh" ya faɗa yana bashi damar faɗin maganar da ta kawo shi

"Ka san Firdausi ta samu admission a nan makaranta a Zaria..."

"Eh haka na ji mai ɗakin nawa tana gaya min" Sani ya katseshi "Allah ya sa ma karatun albarka

"Ameen ameen. To kasancewar na san gobe baka aiki, na ce dan Allah ko zaka ara min motarka na kaita Zaria da kai na?"

Sani direban golf ya yi ɗan jim yana tunani. Tunda ya mallaki sabuwar motarnan shekaru bakwai kenan bai taɓa barin kowa ya tuƙa ta ba kuma bashi da niyya. Amma ta yaya zai kalli Malam Shu'aibu ya ce masa a'a? Mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata wanda yake zaune da kowa lafiya.

Da ace zai fita aiki ne sai ya kawo masa uzuri amma kowa ya san ranar juma'a ranar hutawarsa ce. Kaya yake ɗauka daga garinsu ya kai garuruwa na kusa a biya shi kuɗaɗensa.

"Ƙarfe nawa ne tafiyar sai na kai ku?"

"Na'am?" Malam Shu'aibu ya tambaya cike da mamaki saboda yanda ya ga Sani ya ɗan jima bai ce komai ba kuma kamar ya haɗe rai.

"Duk lokacin da ka shirya Malam Sani. Duk lokacin da ka shirya"

"To mu tafi bayan asuba mana yanda zamu je mu juyo da wuri har mu samu sallar juma'a a nan"

"Na gode Malam Sani, na gode" Malam Shu'aibu ya yi zuba godiya

"Ba komai. Allah ya tashe mu lafiya"

Sani direba ya koma cikin gida shi kuma Malam Shu'aibu ya juya ya nufi gidansa cike da farin ciki. Ya shiga da sallama ya tarar da iyalansa suna tsakar gida a kan ƙatuwar tabarma ana ta haɗa kayan Firdausi.

"Wannan kaya da ban samu aron mota ba ya zamu yi da su?"

Yaran sai suka hau murnar samun mota. Isma'il wanda da shi za'a tafi idan an samu motar ya miƙe da sauri ya shige cikin ɗaki dan zaɓo kayan da zai tafi da su.

Matar Malam Shu'aibu mai suna Zainab ta ƙara faɗaɗa murmushinta ta ce da Firdausi "ki ɗauko man gyaɗar ki ɗura a robar ki zo a zuge jakar"

Ta kalli mai gidanta "Kana fita aka kawo ƙuli ƙulin. A ɗibar maka?"

"In dai bata da yawa ki haɗa mata ta tafi da shi tunda dan ita aka yi"

"Kai dai a ɗibar maka saboda ƙurmusun dare. Kuma ma tana da yawa gaskiya" bata jira ba ta janyo ledar kusa da ita wata yaluwa da baƙa ta kunce ta soma ɗiba.

Bayan ɗan wani lokaci an haɗe kayan Firdausi tsaf an ajiyesu a ƙarƙashin rumfa da ke kusa da ɗakin samarin gidan. Sai a lokacin jama'ar gidan suka samu nutsuwar zama su ci abincin dare. Suna ci suna ƴan hirarrakinsu. Ba'a ɓata lokaci ba kowa ya shiga ya kwanta saboda tashin asubahi za'a yi.

**

"Ke ma kin kasa bacci ko?" Cewar Malam Shu'aibu bayan matarsa ta yi juyi sau babu adadi bayan kwanciyarsu

"Na kasa. Ka san Firdausi ko makarantar kwana bata yi ba. Ta yaya zata yi rayuwa a can?"

Malam Shu'aibu ya nisa. Shi ba nan tunaninsa ya tafi ba gaskiya. Yana jin ƴaƴansa a ransa musamman ma matan. Ya shaƙu da su sosai baya so su yi nisa da shi. A shekarun Firdausi goma sha takwas, sau uku kawai ta taɓa zuwa wani wajen ta kwana. Sau biyu ƙanwarsa ta takura sai ta je mata hutu Gombe inda take aure sai sau ɗaya da ta tafi biki da mahaifiyarta Jos.

Kwata kwata gidan duhu yake yi masa idan ya shigo bai ganta ba. Dama Amina babu inda ta taɓa zuwa ta kwana. Yanzu gashi Firdausi zata tafi tai wata da watanni na tsawon shekaru.

"Ban san nacin yarinyar nan na tafiya wata Kaduna ba" muryar matarsa ta katse shi

"Allah ya sa hakan ne mafi alheri garemu baki ɗaya"

"Ameen"

**

Tun kiran farko, Zainab matar Malam Shu'aibu ta fito ta ɗora musu ɗumamen tuwo saboda su samu su ci kafin su kama hanya. Gabaɗaya jikinta a sanyaye yake, baccin da ta yi ma rabi da rabi ne.

A ɗayar rishonta mai ci sosai ta ɗora musu ruwan da zasu yi amfani da shi su kashe sanyin ruwa su watsa. Zuwa lokacin kowa ya tashi banda auta Amina da ko juyin farko bata yi ba.

Kafin a shiga masallaci Malam Shu'aibu da Isma'il har sun yi wanka tunda da su za'a yi tafiyar.

"Yi sauri Firdausi ki yi wankan a gurguje ki yi sallah kar a fito sallah baki shirya ba" cewar Zainab tana sauke tukunyar ɗumame "Na haɗa miki shayi?"

Firdausi ta girgiza kai, bata son yin magana dan sai yanzu take jin kuka yana neman zuwar mata. Duk zumuɗin tafiyar da take sai take jin gabanta yana faɗuwa. Ta yi maza ta shiga banɗaki.

Sallamar Sani direba ya sa su Isma'il suka fara fitar da kaya dan a shiryasu cikin motar. Firdausi ta miƙe ta saka hijabinta kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki. Mahaifiyarta ta riƙe hannunta ta ce

" Ki kula da kan ki Firdausi. Ki kare mutuncinki da namu. Abunda ya kai ki ki yi shi. Babu ruwanki da kule kulen samari. Kin ji?"

Kai Firdausi ta gyaɗa mata dan idanunta sun cika da ƙwalla, da ta buɗe baki ta san hawaye ne zasu zubo.

Malam Shu'aibu na tsaye yana kallonsu. Matar tashi kamar ta kuma faɗawa tsakanin jiya da yau. Dama ba mai jiki bace. A inda yake namiji mai tsayi, ita mace ce gajera kuma ƙarama. Yanda take tsaye da Firdausi ba zaka ce ita ta haifeta ba. Balle kuma ka gan ta da Abubakar, Isma'il ko Mukhtar da yake shekarunsa na goma sha shida. Baƙa ce amma fatarta ta fi tashi haske.

"Baba mun gama saka kayan, wai ku fito" Abubakar ya leƙo yana gaya mishi.

Ya kalli ƴar tasa ya ce da ita su tafi ita kuma matarsa ya ce mata sai sun dawo ya juya ya fice. Ta saki hannun Firdausi tana mata rakiya zuwa ƙofar gida tana ta zuba addu'o'i. Sai yaƙe take yi na ƙarfin hali dan ita kaɗai ta san yanda take ji.

Ta san dole wata rana zasu rabu, amma bata taɓa tunanin ta silar karatu bane. Ta ɗauka aure ne kaɗai zai saka su ɗau watanni basu saka junansu a ido ba. Ta ji kamar ta saki ƴar jinjira mai tatata a cikin gari ne ita kuma ta koma gida. Idan lokacin Amina ne, ko ta fi ƙuda naci ba zata bar garin Kano da sunan karatu ba.

A cikin mota kuma muryar Sani da Malam Shu'aibu kawai ake ji da suke ta hira. Firdausi da yayanta Isma'il da take bi kuwa suna baya suna kallon wani film ɗin India mai fassara a ƙasansa. Basu samu sakewa ba sosai saboda katifarta da bokiti da bargo da ke zaune a gefensu a bayan motar. Suka tsaya a gidan mai Malam Shu'aibu ya bada kuɗi aka cika motar da mai suka hau titi.

Ko da suka shiga garin Zaria, Malam Shu'aibu shi ya dinga nuna ma Sani direba hanya tiryan tiryan har bakin ƙofar hostel ɗinsu da ta samu. Babu inda bai sani ba da ya danganci Firdausi tunda shi da ita suka dinga zirga zirgar registration. Sau ɗaya ne ta zo da Abubakar shi ma ƙarashe ne.

Sani ya samu gefen hanya ya ajiye mota ya kashe. Su kuma suka fito aka soma fiddo kaya. Maƙullin ɗakinsu yana hannunta dan haka kai tsaye ta ɗauki bokiti da su tsuntsiya da buta da robar wanka ke ciki ta shiga domin kaiwa.

Ɗakin nasu a buɗe yake dan haka ta shiga da sallama. Wata ta gani zaune kan gadon ƙasa wanda shi kaɗai aka saka ma katifa ta gaisheta ita kuma ta amsa. Ta ajiye katifarta a tsakiyar ɗakin ta kalli wacca ta samu a ɗakin ta tambayeta inda zata ajiye kayanta.

"Wannan na sama na wata ta kama. Ki zaɓi kowanne a nan".

Da sauri ta ce ta zaɓi na ƙasan. Tana ta tunanin dama ta ina mutum zai fara hayewa sama? Ita bata ga tsani ba balle ta ce. Ta ce mata zata ɗauko sauran kayanta.

Sai da ta kai dukka kayan ɗakinsu da ke hawa na farko sannan ta sauko domin yi musu sallama.

Mahaifinta ya yi mata nasiha da addu'o'i sannan ya shiga mota ya barta da ƙwalla fal idanu har guda ɗaya na saukowa ta yi saurin sharewa. Isma'il kuwa ya mata gwalo yana ɗaga mata hannu. Ta yi murmushi shi ma ta ɗaga masa hannu.

Zuwa azahar har ta saba da Deborah da ta tarar a ɗakin. Ta bata aron marker ta rubuta F. S. bayan ta taimaka mata ta karta wadannan harrufan a jikin bokitin. Ita Deborah shekararta ta biyu kenan a makarantar.

"In kin yi sallah ki zo sai na raka ki ki sayo kero ki haɗa rishonki ki sayi kayan miya"

Kwatancen masallaci Deborah ta yi mata da ke nan cikin hostel ɗin Queen Amina kasancewar bata zo da abun sallah ba balle ta yi a ɗaki.

Suka kulle ɗakin suka tafi kasuwa da ƙuɗaɗen da Abbanta ya bata kafin ya tafi. Akwai kuɗi a account ɗinta da Abubakar ya rakata ta buɗe. Wannan sai kuɗin hannunta sun kusa ƙarewa zata ɗebo. Akwai wanda Mama ta bata ma.

Kalanzir kawai ta saya sai ganyen salak da tumatir dan tana da soyayyar miyar da aka yi mata aka saka mata a ƙaramin bokiti.

Ko da suka koma ɗaki, wata suka tarar a ciki tayi ɗare ɗare a gadon saman Firdausi. Suka yi mata sannu.

Kafin su kwanta bacci, zaka rantse cewar dama Firdausi, Deborah da Kaltume sun san junansu tuntuni. Ita ma Kaltume sabuwar shigowa jami'ar Baba Ahmadu Bello ce. Zuwa lokacin ta yi waya da ƴan gidansu tana ta basu labarin ƴan ɗakinsu.

A nan hankalin iyayen ya ɗan kwanta jin babu wata damuwa.

*

Mahaifin Malam Shafi'u mai suna Abubakar haifaffen ɗan garin wudil ne. Inda ya fito daga gidan sarkin ruwa na garin Wudil. Matarsu Amina ita ma asalin ƴar garin ce. A nan garin Wudil ɗin suka yi rayuwarsu inda ta yi haihuwa ɗai ɗai har guda goma sha uku. Mijin nata ya mutu ya barta da ƴaƴa bakwai.

Bata zauna ba, ta shiga saye da sayarwa dan ta ga ta riƙe marayun ƴaƴan duk da kuwa danginta da na mijin nata basu yada ita da yaran ba. Kowa yana yin iyakacin bakin ƙoƙarinsa.

Ɗaya bayan ɗaya ƴaƴan Amina guda bakwan nan suka dinga mutuwa sai da suka rage ƙwaya biyu tak! Malam Shu'aibu shi ya fara wuce shekaru goma sha shida a cikinsu. Sai ƙanwarsa Maimuna da ya ba shekaru kusan shida.

Idanun Amina suka mutu saboda kukan rashin da ta sha a rayuwarta. Bata yi zaton zata tsira da ƴaƴan da zasu binneta ba saboda yanda suka dinga tafiya babu ciwo. Sai dai a wayi gari a ga rai ya yi halinsa.

Bata damu da maganganun da ke ta yawo a garin nasu ba. Wasu sun ce tsafi take yi da su, wasu sun ce ita mayya, maganganu kala kala harda wanda hankali bazai iya ɗauka ba.

Shu'aibu na kammala karatun secondary ya haƙura. Ya maida hankali wajen taimaka ma mahaifiyarsa da kuma ƙanwarsa.

Maimuna na kammala karatunta ta auri wani saurayinta ɗan Bauchi. Suka haɗa mata abunda zasu haɗa mata suka kaita gidan miji.

Sai da Maimuna ta haifi Musa (Amir) da Shu'aib (Yaaya) sannan Shu'aibu ya yi aure ya auri Zainab ƴar Gwarzo. Ya ɗauke mahaifiyarsa daga garin Wudil ya dawo da ita gidanshi da ke Sabon titi saboda raunin ganinta, tana buƙatar mai kulawa da ita.

Auren bai shekara ba suka samu ƙaruwa, ɗa namiji da ya maida sunan mahaifinshi Abubakar. A tsarin Malam Shu'aibu shi baya ɓoye suna, saboda haka kai tsaye dukka ƴaƴansa ake kiransu da sunyensu na yanka.

Bayan Abubakar suka samu Isma'il, Firdausi, Mukhtar sai auta Amina. Mahaifiyar Malam Shu'aibu takwararta ce kawai bata gani ba a ƴaƴan ɗan nata.

A rayuwar Malam Shu'aibu, ya yi sana'o'i da ɗan dama. Amma wanda ya daɗe yana yi shi ne aikin kamfani. A yanzu haka a wani kamfanin shinkafa yake aiki. Daga safe zuwa la'asar yake yin aikin nashi ya koma gida. Sai kuma sana'ar fata da yake ɗan taɓawa.

Abubakar ya yi diploma ɗinsa a matan fada inda ya karanci lissafi amma yanzu kasuwar wambai yake zuwa yana shagon wani Alhaji Aminu a unguwarsu wanda yake dealer ne na atamfofi musamman na inyamurai da kuma na cotonou. Yana samun alheri babu laifi, ɗan kuɗin da zai kashe basa gagararsa sannan yakan ɗan rage ma mahaifinsa wasu abubuwan. Yana son ƙara karatu ya samu degree amma admission din ne bai samu ba.

Isma'il kuma yana level two a jami'ar da ke wudil yana karantar Computer. Idan baya makaranta to yana nan wata Internet cafe da ke unguwarsu yana aiki.

Firdausi ita ta samu gurbin karatu a jami'ar Ahmadu Bello zata karanci Biology Education.

Mai bi mata kuma Mukhtar yana SS1 yana bangaren Arts dai auta Amina da ke da shekaru 6 tana primary 1.

*

Ko da suka kashe fitila domin yin bacci, Firdausi sai ta ji kewar gidansu. Yanzu haka da suna kwance a ɗaki ita da Amina a kan gadonsu. Ta ji ƙwalla ta cika mata idanu ya gangara gefe zuwa kunnenta. Ta yi sauri ta share hawayenta ta ja mani. Kar ƴan ɗakin su ji tana kuka ƙila basu kai ga baccin ba su ma.

Tana nan bacci na shirin kwasheta ta ji wayarta da ke ƙarƙashi pillow ta yi vibrating. Ta ɗauki wayar wacca ta Mamansu ce aka bata ta taho da shi tunda tana browsing ko ba komai ta yi ɗan amfani da ita idan an basu assignment.

Saƙo ne daga masoyinta

"Ki yi haƙuri ban kira ki ba throughout. Ina shirin dawowa ne. See you soon. I love you"


Assalamualaikum makaranta littafin Kowa ya daka ta bado... Wannan ne karo na farko da nake amfani da manhajar arewa books, a hankali nake gane yanayinsa 😅 Da fatan labarin zai samu karɓuwa a wajenku har ku dinga danna min like kuna commenting. 

Mabuɗin labarin ya fara a shekarar 2024 ne. Na yi ƙoƙarin editing na saka sai ban gane yanda ake yi ba. 


Na gode 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol