Free chapter Β· Read without an account

Chapter 5

by Pinky Darling Mrs Jay Β· SHA'AWARATA NIKEYI

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*SHA'AWARTA NIKEYI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

(Romance and sxy)

πŸ”žβŒ
Writer Bey
Pinky Darling Mrs Jay ✍️
✨✨✨✨✨✨✨✨

Following this link to join my WhatsApp channel domin samun zafafan liltafaina sabbi da tsofaffi tare abubuwan k'aruwa 

***


BOOK ONE
PAGE 9οΈβƒ£β©πŸ”Ÿ
Sai da suka d'auke hanya yace"Barka da safiya Princess.". Wani murmushi tayi mai me kashe zuciya kana tace "yauwa barka ykk.?" "Alhamdulillahi ya fad'a tare da maida hankali kan tuk'i kar ya b'arar dasu kan titi, yace "Ina muka nufa.?" Tace "Gidanka zamuje inaso ka bani masauki a ciki ka gabatar dani wurin Matarka a matsayin wacce zaka aura wannan kawai nike buk'ata ka bar ni da sauran aikin."

k'irjinsa ne ya shiga dukan uku uku Marwa ai sai ta kona gidan saboda kishi tinani yake tayi har suka k'arasa makeken gidansa mai kyau da had'uwa, ya bud'e Mata gaban Motar ta fito tare da b'allo cingam ta saka a baki tana ci, kallonsa tayi kana tace"Muje ko." Gaba ya shiga tana bayansa, yana bud'e k'ofar parlou yaci karo da kwalin lemo da robar ice cream, 

tsallake su ya yi kana suka shiga ciki gaba d'aya parlon a hargitse yake ba gyara ga plate d'in da akaci abinci nan zube wasu har kan kujera, da gorinan ruwa, komai a haukace sai Tv dake k'ara shi kad'ai yastine fuska Ayma tayi tana k'arewa parlon kallo ba abinda beji ba na more rayuwa amma kazanta ta bata gidan, 

Alhaji Abubakar kuwa yace "Ayma ina zuwa nasan tana ciki bata falka ba." Ayma tace "rabuda ita tafiyar ka kawai saika dawo ina ne d'akin da zan sauka." sama suka haura wani babban parlou ne har yafi na farko had'uwa d'auke yake da 4 bedroom kitchen da sauransu kamar dai parlon k'asa d'aya daga cikin room's din ya yace ta zauna rakasa tayi har zuwa Mota kana ta dawo,

ta shiga gyaran gidan daga sama har k'asa, tayi wanke wanke ta feshen ko ina da turaruka gida, kana tayi wanka ta sauya kaya, wata riga ta saka, kamar ta bacci, me hannu d'aya iya cinya rigar ta tsaya, kana ta fito parlon k'asa ta kunna kid'a, ta shiga kitchen ya soma girki sakwara tayi da miyar ugusi da jalop d'in shinkafa da naman kaji,,

ta had'a zobo da kunun aya, tana jira kayan kan teburin cin abinci saiga Marwa ta sauko cikin kayan bacci tana k'arewa parlon kallo, ga wani mayen k'amshi daya dake hancinta, Ayma kuwa yi tayi kamar bata ganta ba sai kwasar rawa takeyi, Marwa tace "Ke wacece uban waye ya baki damar shigomin cikin gida har kina wannan iskanci.?"

dakatar da rawar tayi tana k'arewa Marwa kallo gata da kyau dai dai ita amma ba tsafta ta koma kucaka ballagazar mace, wacce batasan inda ke mata ciyo ba, Ayma tace "Kega Sakara ni d'in Amaryar Mijinki ce wacce ya auro saboda jin dad'in rayuwarsa, na d'auke mai takaici da bak'in ciki, so ki iya bakinki, 

Lamba d'aya muke bugu a gidan nan." Tana gama fad'ar haka ta cigaba da rawa tana karairaya jiki." Marwa kuwa Wani dum taji kamar saukar arado, jiri taji na neman kwasarta amma ta dake tace "k'arya kikeyi Wallahi Mijina bazai yimin kishiya ba saboda yana masifar sona." Dariyar rainin hankali Ayma tayi kana tace

"To ki dena yaudarar kanki saboda yanzu ni d'in Matarsa ce yau sati biyu da d'aura muna aure saboda mugun kishinki na banza ban samu damar tarewa ba sai yau, saboda haka yanzu mu Biyu yake masifar so." kukan kura Marwa tayi zuwa kan Ayma zata dake ta ai kuwa Ayma ta cafke ta tare da murd'e mata hannu tace "Ke mahaukaciya wallahi raba kanki da cewa,

zaki dake ni nan da kike ganina tsohuwar y'ar jagaliya ce ajen K'arshe Wallahi karairayaki abu ne mai sauk'i a wurina, saboda haka ke dena wannan sakarce don Wallahi dukan tsiya zanyi miki y'ar daud'a har wani tsami ke tashi a jikinki ai dole Baby ya k'ara aure." Ayma ta fad'a tana wulla Marwa kan kujera kamar tsumma,

sama ta haura tana rera wak'a." Marwa kuwa bak'in ciki ne ya kamata ta jima zaune kafin ta haura sama tana d'aukar wayarta ta kira, Hida baby buga d'aya ta d'aga tace "Hida kina ina ne na shiga uku na lalace ashe Alhaji aure ya yi har tsawon sati biyu sai yau Amaryar ta tare, gashi nan sai rahsin mutunci takeyi min dan Allah kizo muci uban shegiya mu korata."

"Hida tace "aure kuma Marwa garin yaya hakan ta faru sannu kiyi hak'uri, amma fad'a ko duka bashi zai saka ki kwace Mijinki ba kawai ki d'auke shawarar dana saba baki su Rashida na d'ora ki a ta banza." Datse kiran Marwa tayi tana dannawa Rashida kira tana d'auka Marwa tace "Rashida kizo gidana yanzu ina jiranki."

Rashida tace "Lafiya kuwa meke faruwa ne.?" Marwa tace"Alhaji ne ya kawo Amaryarsa a gidan nan yau ta tare wallahi ubanta zamuci." Rashida tace"Okey gani nan zuwa bara na kira, Ummei muzo tare." Ta kashe wayar, Ayma kuwa kiran Anam tayi ta sanar da ita inda take, tace ta had'o kayanta tazo,

ba'ayi minti ashrin ba saiga Anam tazo gidan suka baje parlou suna hira Ayma ta zuba musu abinci suna ci ana hira, saiga Ummie da Rashida, sun shigo kamar an jefosu, Anam tace "Jakunan ina ne ku zaku fad'uwa mutane ko sallma babu.?" Ayma tace "Rabudasu Anam jakunan k'awayen Ballagazar Matar gidan ne." 

Ummei tace "kan Uba wallahi kune jakuna y'an iska na ranste da Allah yau sai kun bar gidan nan." Ayma tayi banza dasu suka cigaba abinda sukeyi Rashida tace "Muje Ummei rabuda shegu zamu dawo ta kansu ne ." Zaune suka tarar da Marwa kan bed tana jiransu sukaci uwar d'amara suka fito zasu dake su Ayma,

basu tarar dasu parlou ba Marwa tace"Kaga y'an iska sunji tsoro sun gudu." Ummei tace "Sunyi tsammanin zamuyi musu da sauk'i ne ashe k'ananan y'an iska ne." Suka saka dariya saiga Ayma da Anam sun fito d'auke da muciya, sun wane rik'e k'ugu kamar wa y'an da zasuje wasan buga kwallo Ayma tace"To gamu sai a kaimu kabarin mu yanzu."

Marwa tace "Idan akwai abinda yafi kabari chan zan aika ku karuwan banza." Anam tace "Besty nifa na fara gajiya mu afka musu kawai." Ummei tace "Muje zuwa." Ai kuwa suka afkawa juna suka kacame da rigima, sai cin uban juna sukeyi, gaba d'aya sun rikita parlon sunyi muguwar b'arna sun fasa Tv da sauran abubuwan K'awata parloun, Ayma kuwa ta samu sa'ar Marwa sai jibgar banza takeyi tana ihun neman agaji, 

da kyar Anam ta janye Ayma kan Marwa, ta fasa mata baki da hanci, su Ummie kuwa da Rashida kuwa sunci shegen duka sai jan jiki sukeyi, Alhaji Abubakar ne ya shigo parlon yana k'are mai kallo gaba d'aya sun tarwatsa duk Wani abin amfani a parloun dama yasan za'a rina Marwa da K'awayenta ba hankali ne dasu ba, Wurin Ayma ya nufa yana fad'in,

Babyana meya sameki ne haka ina fatar basu jimiki ciyo ba.?" Cikin shagwab'a Ayma tace "A'a My honey hannuna ne kawai keciyo saboda dukan waccen kazar gidan marar amfani." Kallon Inda Marwa take yayi tare da kawar da kansa yace"sorry Baby ai be kamata ki saka lallausan hannunki a jikin waccen dake fama da fata kamar jikin bishiya." 

Marwa tace "Lallai Alhaji ka bani mamaki yanzu ni zakayiwa wannan cin zarafi a gaban karuwar....Wata tsawa ya daka mata, yace "Ke Marwa karki k'ara kira min Mata da karuwa saboda tafi karfinki, idan ba haka ba wallahi yau zaki bar gidan nan ki koma gidanku." shiru Marwa tayi saboda hankalinta ya tashe maida hankali ya yi kan Ayma yace "Baby muje nayi miki wanka nasan ke gaji."

Ayma tace "Bazan iya tashi ba ka d'auke ni mu tafi." Yace Bakida matsala My love." D'aukarta ya yi suka haura sama Anam ta saka dariya hadda fito, tace "To umma ta gaida Aysha." Ta haura sama zuwa d'akin Ayma Marwa kuwa Wani kukan bak'in ciki ne ya kamata, Rashida tace "Sorry Marwa ki shirya zuwa gobe muje wurin Boka kawai a kore shegiya."

Ummie tace "Sosai kuwa kega Yanzu hankalin Alhaji gaba d'aya baya kanki dole sai an had'a da neman taimako wurin boka." Marwa tace "In dai Mijina zai dawo tafin hannuna to zanje." Rashida tace wuyarta kawai rashin zuwa yanzu ki d'auko muna kud'in napep zamuje gida." Marwa ta haura sama ta d'auko musu kud'i suka wuce a hanya Ummei ke cewa Rashida,

"K'awata gurin wane Boka zamu kai Sakarar.?" Rashida tace "Idan gobe tayi zaki gani ai damu take zancen ba dai aure ta barmu zaune gidan iayeyen mu ta kasa had'a mu da Abokan Alhaji Abubakar ba hamm." Ummie tace "Ashe bani kad'ai abin ke damu ba ni wallahi Alhaji Abubakar nike son ya aure ni Marwa ta gane bata da wayo." Rashida tace "Ashe burina kad'an ne naki yafi nawa, Lallai Akwai aiki dole sai an fitar da Amaryarsa daga nan mu dawo kan Marwa."


Writer Bey Pinky Darling Mrs Jay ✍🏼
More comment More typing please share like

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.