Free chapter 路 Read without an account
05
RA'AYI NE KO BURI..?*
NA
JANAFTY馃挒
Wattpad:Jamilaumar351
5
"'Nikaina basan wani lokaci bane..? ko kuma watarana ne naji Na kamu da soyayyar wanda bantaba gani ba,Ta sanadin Wakarsa wacce tafara daga Shakuwa da farko ina Tunanin Harda yarinta ke damuna sai da na kara girma Abun na karuwa na Fahimci na fada cikin Wani hali mai wuyar Fassarawa.
Tun Abun yana iya boyuwa har yafara baya boyuwa Hatta da ya sulaiman yasan yadda nake bama wakokin Mainasara muhimmanci acikin Rayuwata,ya Gaddafi kuwa shike Turomin sabbin wakokinsa in yazo hutu ya Turamin bantaba ganin hotonsa ba kamar yadda ya gaddafi ya gayamin babu wanda zai iya bada labarin ya kammanin Mainasara yake bai taba Fitar da Vidio Albulm ba,Kuma waka baya kidayan Lokaci Duk lokacin da Shaukin Abun ya tasomai yana Daga chan lagos zai rerata sai dai ya turoma ma"aikatansa na Studio dinsa Dake kano,Ayadda ya Gaddafi ya gayamin yace wani abokinsa ya gayamai an taba hira dashi a gidan Tibin NTA dake Abuja a inda yake sanar ma mutane waka bai Dauketa a matsayin Sana"a ba sai dai yana Daraja waka saboda Hobby dinshi ne,Kuma ta kasance Wani buri Dake cikin Rayuwarsa Tun yana karami nan yake sanar da mutane shi matukin Jirgin sama ne Ma"ana pilot.
Wannan labarin ya Dada Tsumdumani cikin So da kaunar Mainasara,Na kara tabbatarma kaina cewa Gwanina Mainasara na Dabam ne,Ya bambamta da Sauran mawakan da mukejin Wakarsu,Shi mainasara baya wakar Aure baya na Siyasa,baya na Fadanci baya na Sarauta yana Waka ne don karon kanshi,bai taba Shiga wata kungiyar mawaka ba saboda baya Daukan kansa amatsayin mawakin jama"a yafi Daukan kansa amatsayin mawakin kansa Wanda yakeyi domin Ra"ayin kansa.
Innata bata nuna damuwarta kan Halin Danike ciki tana gani da Zarar nayi aure zan daina wannan Shirmen uwa uba kuma ganin ban fasa karatu ba,Tunda Saukan Qur"aninmu Nida Aliya awajen Baba mukayi sai muka koma wata Makarantar Haddar Da"ake gudanar a garin Ringim awata makaranta wanda ta boko ce ake amfani da ita ana Hadda aciki, Babu wani Tazara da gidanmu matasan anguwanmu masu ilimi wanda Babanmu ya koyar dasu suke Daukanmu muna bada karatu suna karamana in mun koma gida Da Daddare mu zauna karatun Sauran Littafai Wannam Dalilin Yasanya ko karata Hajjo takai ma Baba bai maida kai domin kaf gidanmu bayan su ya Gaddafi bamai kokarina Da maida Hankali,Nasani cewa Baba na matukar alfahari Dani wanda ke kara batama Larai rai,Domin tana ganin Duka gidan innata ta gama kwacewa ita keda manya ya"ya maza kuma Gabadaya Daga Babanmu har zuwa gidan Baba Hayatu kowa na Daraja innata,Sabanin maijidda dako Saukan batayi ba balle takai ga Hadda karatun Dare da Baba ke mana da anfara zata Fara hammar barci Baba yayi Fadan Haryagaji ya kyaleta ko kanwata mujadala tafita himma da kokari ni kuma akwaini da nacin karatu Daga na bokon har na arabi bana Wasa Sau tari in ya sulaiman ya Dawo nike matsamai ya dinga koyamana Darasin Turanci da Lissafi nida Aliya wanda shike taimakonmu,Shiyasa ko Makaranta harshen mu ya Fita Dabam hakama nake ma ya Gaddafi Na makalemai sai na Koyi wani abu,Tun yana korana har ya hakura laptop dinsa Daya siya da karambani da naci sai da na koya shiyasa wani lokacin Innata ke alfahari dani saboda ina da nacin Abu da sakama rai Abu in na kafama Abu kahon zuga sai na iyashi nake samun Sukuni Dani da Aliya halinmu Daya wani Lokacin ma na fita Naciya kan wani Abun.
Muna kammallah jss3 dinmu a Sabon gari Goverment Junior Secondary School Ringim muka Fada Goverment Unity School Ringim muka Fara SS1,mu uku wannan karon ma Nida maijidda,aka hadamu aji Daya aka sake Rabamu da Aliya Ammh duk da Haka bamu maida kanmu cikin masu wasa ba Tunda mun fahimci ko mu mata in bamu da ilimi bamu da wani Daraja ni acikin Raina har jami"a sai nayi irinta ya Gaddafi da ya sulaiman da suka zama zara cikin wata in suna turanci Abun sai ya baka mamaki.
Hajiya Amina mahaifiyar ya sulaiman macece mai kunya sosai ga kawaici irinta Fulanin Daji Duk da suna da kyakyawan Fahimta da innata,Tunlokacin da aka mana alkawarin Aure Daya Sulaiman take jin kunya na kuma Aliya yar dakinta ne Tunda ga yaye tabar Dakin mairo,ni kuma muna tare da Aliya koda yaushe agidanmu ko gidan Baba Hayatu,Muna dakin Hajiya Amina wacce kowa ke kiranta Hajiya,Tana nuna tana jin kunyata nikuwa ko ajikina Sau dayawa ma munsha kwana adakinta bana damuwa Tunda Haka take,saboda jinin Fulani ammh Har cikin Zuciyarta take alfahari dani tana kuma jin Dadin Sulaiman yagama dacen samun mata irina,Tunda kamar kawaye suke da innata Mairo kuma itama suna da kyakyawan alaqa anriga an zama Daya larai ce take ganin kamar sun wareta sai da takaima Hajjo munafunci ta tarasu ta musu tas wai suna nuna ma larai wariyar launin Fata.
Hajiya Amina Tana da yaya wacce suka Fito Ciki Daya,su Biyu kadai iyayensu suka Haifa suka kuma mutu suka bari mai suna Hajiya Fatima tana aure acikin garin kano,wani babban ma"aikacin hukumar Costome ne ya"yanta biyu mata Tana zuwa Lokaci bayan lokaci ita da yaran nata matar Ta Burgeni Nidai saboda yadda takema Addinin musulunci hidima gata da ilimin Addini sosai Duk da batayi boko ba ammh mace ce wacce tasan kanta Ya"yanta suna da Kyakyawan Tarbiya komai nasu cikin Tsari basu wuce sa"aninmu,ba Aliimanh ce babba sai Asiya tsakaninsu ba wani nisa,yadda suke tafiyar da rayuwarsu zaka Fahimci suna bala"in girmama mahaifiyarsu yaran in ka gansu bazaka kirasu wayayyyi ba ammh kuma kana ganinsu zaka fahimci suna da ilimi da wayewar Birni,Gadonsu da' aka raba na Shanaye da Awakai Ita Hajiya Amina mijinta da damkamawa Yahada danashi suna cigaba da kiwatawa sai tabama Hajiya fatin Shawaran yakamata itama ta kawo nata nan ta Hada da nata sun kiwata tare Batayi gaddama ba ta kwaso komai ta Damkama Baba hayatu ya hada dana Matarshi suna kula dasu lokaci bayan lokaci tana aiko da kudin da za"a siya musu abinci,kafin kace kwabo sun tara Garke Guda ciki suke hidimar komai har makkan da sukeje acikine Duk da Ita Hajiya Fatimar Mijinta ya kaita Tun bayan Haihuwanta na Fari.
Takan zo lokaci bayan Lokaci Duba yar"uwanta itama Hajiya takan lekata Tunda cikin kano ne,Hajiya ke sanar damu mijinta yana garin lagos bayan sati biyu yake zuwa kano yana da mata da ya"ya achan,in tazo haka zata zo da Tsaraba arabama makota da yan"uwa Kwana daya take ta juya muda Aliya muyi ta santin su Asiya saboda yan gayu ne sosai Tare muke inda suka zo suyita bamu labarin makarantarsu,suna Tambayanmu yaushe zamu zo kano Muna son zuwa ammh matsalan Baba bazai barmu ba saboda karatunmu bama zuwa ko"ina Daga makaranta sai gida Sai ko in munje gidan su ya Hasiya,ko gidan ya zainaaba shima bama wani Dadewa muke Dawowa Saboda gudun Fadan Baba dakoda yaushe yake kofar gida zaune yana ganin Shiga da Fitan kowa.
Su ya sulaiman suna shekararsu ta karshene mu kuma muna SS2,an tsaida mganar bikinmu Nida ya sulaiman bayan mun gama candy,Daga Aliya har maijidda sunsan,Cewa su kansu bazasu wuce wannan lokacin ba,mune ma muka fita zakka aka barmu har zamu kamallah Babban Sakandiri,ba ruwansu da basu samu ba Lokaci nayi kawai sai dai suji zence ya tashi inata musu tsiyan cewa gwara ni nasan inda na dosa,sufa waya sani ma ko cikin masu Daukan karatu awajen Baba ne Aliya ne in taji haka sai ta sakarmin Dundu ita kuwa maijidda Daure Fuska take cikin Ranta tana tunanin da gayyah nake musu dariya.
Hajjo kuwa darunta sai Abunda yayi gaba bama ga maciji,balle shan Inuwa Daya koda yaushe cikin Hantara take ni kuwa bana mata Shuru,haka zata fito tsakar gida tana Fadanta na fama namata banza kan wakar danike sakawa tasha kai karata wajen ya Nasiru sai dai yamin fada banaji Sai kuma ta koma gayama ya sulaiman yazo Hutu wai shi ya koyamin jin wakokin banza,ni na gayamata karta ga laifinsa dako ta fahinci ya gaddafi ke Sakamin wakokin ranar har dakinsa tabishi tamai tas daya gaji ne ya jawo hannunta waje ya maida kofarsa ya Rufe kusan nidashi mune Daidai da ita,tana gaya mana muke maidamata shiyasa take Fadin koda yaushe innarmu ce ta Daure mana gindi muke iskanci in kaji Hajjo na yabon wani to ya Nasiru ne Tunda shima kamar su Babanmu yake tana Fadanta suna bata hakuri,harta Rabi bata kyale ba Abu kadan zatayi sai ta iskota har sasanta ta Zageta tsakani ga Allah hajjo ciwon kai ne da damuwa acikin Gidanmu awajena Maijidda kuwa yar Dakinta ne,Watarana ma nan take kwana ni kuwa bana ko kallon Dakin balle nace zan Shiga Tunda ko na Shiga Koroni take.
Sau tari in ya sulaiman yazo wajena Zence wanda muke yi adakin ya gaddafi labarina kaf na gwanina mai nasara ne,Bayan zencen karatu,ya sulaiman nasona sosai baya kaunar bacin raina duk wani Abun gayu na mata kayan kwalliya shike Siyanmu watarana ya hadamu nida Aliya,Abunda ke kara kuntatama larai rai kenan ganin akomai nafi maijidda,Aduniya komai nake so zai min gashi bayason bacin rai na,ko Zencen bai mai Dadi haka zai ta Saurara bashi da Hayaniya wani lokaci sai dai ya murmusa yana Fadin"Humairata wai tsakanin ni da Mainasara mawaki wakika fi so..?
Na kalleshi cikin mamaki kafin nace'Bangane wannan mganar ba...?Nafada ina kokarin boye Razana ta tsakani ga Allah ina jin Mainasara fiye da yadda nake jin ya sulaiman ina kokarin boyewa ne sanin cewa ko zan mutu kila bazan taba ganin mainasara ba sai da na Mutu ina sonsa da kaunar wakokinsa ganin Raina yabaci sai ya bar mganar ya shiga bani hakuri mganar ta wuce ammh shi kanshi yasan cewa Zuciyata ta kamu da soyayyar Mainasara Koda ina sane koda kuma bansani ba.
Nikuwa ina ta Tunanin Ko zan iya Furtama mutane cewa MAWAKI ZAN AURA.. To ko na fada ai ba amfani domin Mainasara dai yafi karfina kilama sai dai na tsira da jin wakokinsa,bazan taba ganinsa ba balle kuma har ya iya Furta yana sona ina yar kauye dani Shikuma Mai ilimi celebirty wanda Duniya tasanshi gabadaya ammh duk da haka ban taba Cire Zuciyata ga Shaukinsa ba ina son Mainasara ina bala"in kaunar muryansa mai cike da Zati da Haiba wacce ke narkarmin da Zuciya.
Aliya ce kadai nataba gayama gaskiya Abunda ke Damuna,Tamin Fada sosai kan n cire wannan Tunanin acikin Raina gwara na tsaya ga zahiri nadaina Tunanin wanda ba zahiri ba in nace mawaki zan aura ina na ganshi..? Na taba ganin wanda ya taba ganinsa ne ko yasan labarin shi..? Nace mata babu tace toh na cire wannan Araina kada nasaka zuciyata aciki Abunda bazan samu ba naji shawaranta nakuma yi kokarin Cire komai acikin Raina ammh kuma Abun yaci Tura sai na barma zuciyata kawai Domin na tabbata duk wanda zan gayamawa irin Shawaran da Aliya ta bani zai bani maijidda kuwa in taji ina jin waka ta Dinga yadamin mgana cewa iska na wahalar dani ko yar aikin gidan Mainasara bazai Daukeni ba,ina jinta sai dai na mata banza Hajjo ke biyemata suyi ta gasamin mgana wai kilama Duk Ranar dayaji labarin ina jin wakokinsa sai ya daina waka ire iren haka dai bana tatasu nidai Abunda na sani ina son mainasara koda da Soyayyarsa Da Jin wakokinsa kadai zan tsira naji Dadi ammh zanfi jin Dadi koda ace sau daya Mainasara yasann dani cikin jerin masoyansa.
******
KANO
State Road...
Wani Gida ne Flat Hause Madaidaici ne,wanda ya tsaru wajen mazanin gidan da kuma magini bai da wani girma na azo agani,duka duka haraban gidan bai wuce zaman motoci guda uku ba,Daga cikin Gidan ma Babban Falo ne Guda Daya sai,5 bedroom da Kichen guda Daya,Daya na Umma ne Daya kuma na su Alima ne Daya kuma Dakin ya Abba ne wanda in yazo yake Sauka,sai Daya kuma na Abbansu wanda bai cika sauka aciki ba yafi sauka cikin Bedroom din Umma sai da in Mommy latifa tazo Daga lagos take Sauka anan Daya kuma na baki ne.
Komai na gidan cikin Tsari ne Daga baya akwai wani Fili mai Dauke da wajen pampo da Tankin Ruwa,nan wani Lokacin suke wanke wanke da Shanyan kaya,ko kuma in suna jin Shan iska su bude su fita,su saka tabarma su zauna Tunda anan Lesson Teacher dinsu ke musu karatu Tunda Wajen yana da mashigaguda biyu ne Data cikin gida da kuma na Wajen Haraban gidan
Dukkansu suna cikin kichen da misalin karfe 11am na Safiyar Ranar Asabar Umma da ya"yanta Aliimah da Asiya suna Hada Abinci Sakamakon yau Daddy dinsu yana Tafe,Hajiya fatima tana da kyakyawan tsari acikin gidanta Ko yar aiki bata dashi tun su Asiya basu kawo girma ba itake komai acikin gidanta suna Fara girma ta koya musu komai kama Daga gyaran gida da girke girke wanda ba kalan Da basu iya ba har Catering School ta sanyasu sukayi na wata Shidda har Certificate sai da aka basu bata wasa da Abu mai muhimmanci acikin Rayuwarsu kamar yadda mahaifinsu yabasu ilimi Addini itama ta Dage musu kullum Bayan sallar Asuba suna karatu bayan Hadda Safe Data sanyasu asabar da Lahadi wanda in suka Tafi sai yammah hade da islamiyace Ranakun Dabana makaranta ba sai La"asar suke Tafiya islamiya bayan sun taso Daga makaranta.
Kai tsaye bazaka kirata mai tsanani ga Ya"yanta ba ammh tana da Kishin kai da Tattsauran Ra"ayi shiyasa in ta saka musu Doka bamai iya tsallakewa suna matukar sonta da kaunarta saboda tana killacesu bata barinsu zuwa ko"ina in Sun Fita to makaranta ne ba inda take zuwa dasu Daga Ringim gidan Inna Amina sai ko Rigar Hardo Wato Tsatson kakaninsu ta bangaren Uwa ko lagos Sau Daya tataba bari suka Tafi Shima Alhaji Sa"aed ne ya mata jan ido suka hau sama Suka fado kafin tabari suka tafi Shima basu Dade ba Sati Daya sukayi ta dinga waya kan maza su dawo bata kaunar Abunda zai Dinga Hada Duk Abunda ya Dangaceta da Hajiya latifa Shiyasa ko da yan"uwansu na chan basu da wani jituwa Tunda Daddynsu ya sanar dasu tsakanin Aliimah da Ziyada watanni ne,Haka kuma Asiya na gaban Zuhra dukkansu Shekaru bazasu gaza 16 ba yara a ne ba wasu manya ba ammh Umma bata taba Zaunar dasu tana basu irin wadanan lbaran ba ko alama bata kaunar Haduwarta waje Daya Hajiya Latifa.
Tuwon shinkafa sukeyi Aliimah ce ke Kulle tuwo aleda ita kuma Asiya na Kokarin saka Dandanon jully cikin zobon Data hada Umma kuma tana wajen miya tana Juyawa wacce taji Kashin rago Da manshanu sai tashin kamshi,Alhaji Sa"ed ne keson Tuwo sosai kuma indai zai zo sai ya roki fatimar Data Dafamai Tuwo,Tun jiya daya gayamata yau yana tafe gari na wayewa ta aiki Hamisu Direbansu kasuwa yamata Cefene saboda zuwan Abban nasu suka marairaicema Ummmar kan ta barsu na yau kadai Dakyar ta yarda ta kyalesu da Sharadin anjuma zasu islamiya cikin Zumudi suka amince.
Labari Asiya ke bama Umma na Competition din da sukayi a makarantarsu da yan SS3 tunda suna SS1 ne,suka cinye yan SS3 Umma na Sauraransu cike da kauna mai tsanani Wayar Dake Falo ta Dauki Tsuwa.
Aliimah ce tace"Umma kamar Ringing din wayarki nake ji fa..? Tsayawa sukayi kafin Asiya tace"itace Umma bari na miko miki.."Dakatar da ita tayi da Fadin"A"a barshi ku cigaba da aikinku Bari naje naga wake kiran.."Da toh suka karba kafin ta Fice da Hanzari wayar tana kan Daya cikin kujerun da sukama Falon kwanya cikin Sauri ta saka Hannu ta Dauka Sunan Alhajina ya fito ta saman wayar cikin Mirmishi ta Dauka Tana Fadin"Alhajina ka kariso ne..?
Alhaji Sa"ed ya amsa cikin Fara"a yana Fadin"Eh Fatitina Muna Filin Jirgin mallam Aminu ki aiko mana da Hamisu direba ya taho damu.."cikin mamaki tace"Ya taho daku.? Kai da waye..?
Cikin Ajiyar rai yace"Nida ya"yanki ne Ziyada da Zuhra da Sharifa sun matsa suna son zuwa wajen yan"uwansu suyi Hutu..."Tuni Annurin Fuskar Umma ya bace Tayi Shuru tana jaddadama Ranta latifa bazata taba barim Rayuwarta ya zauna cikin Jin Dadi ba yanzu mijin ma Sai taga dama yake zuwa ganinta kuma abarshi yazo shi kadai ya gana da ita da yaranta don mugun munafurcin yarbawa sai ta hadosa da yaranta,Bakinciki ya cikamata zuciya kamar tayi kwallah.
Jin shuru yasa ya shiga fadin"Fatima kina jina...? Cikin karfin Hali tace"Yanzu zai taho..."Tana kokarin yanke kiran yayi saurin cewa"Ki saka su Aliimah su gyara musu Dakin baki tunda harda Sharifa sai su sauka anan..."Kamar ta kurma ihu Ammh sai ta cije jin Shurun ta yasa yace"Don Allah Fatima...kinji..."Yafada cikin marairacewa kamar wani karamin yaro.
Ajiyar zuciya ta saki kafin tace"Shikenan..Sai kun kariso.."Bata jira cewarsa ba ta yanke kiran Lokaci Daya tana sakin Siririn tsaki,wayar ta maida kan kujera kafin ta saki wani mirmishi mai kama dana Haushi ta koma kitchen din Suna hirarsu kasa kasa ta shigo basu lura da ita sai dai suka ji tana Fadin"Asiya in kin gama hada zobon ki saka cikin Fridge yayi sanyi kizo ki gyara dakin baki.."Da mamaki suka bita da kallo Lokaci Daya suka hango damuwa cikin idanuwanta kafin su samu zarafin mgana ta rigasu da cewa"Babanku ne zai zo dasu Ziyada wai zasu mana hutunsu anan..".
Tafada tana kallon Fuskokinsu Jin Haka yasa suka washe baki suna Fadin"Da gaske Ummah..?"Wani kallo ta watsa musu sai kowacce ta kunshe murnanta Fita tayi tana Fadin"Aliimah ki gama kulle Tuwon nan da Sauri ki jera komai bisa Dinning zan shiga wanka ke kuma Asiya kafin ki fara aikin Dana sakaki Fita haraba ki sanar ma Hamisu ya Tafi Filin Jirgi ya taho dasu Alhaji.."Daga haka ta fice da Sauri Zuwa dakinta Lokaci Daya Tana cije Abunda ke ranta.
Tana fita suka Rumgume juna,Suna murna kafin su tafa suna Dariya,Fita Asiya tayi da Sauri bayan ta koma daki ta Dauko Hijabi saboda umma ta hanasu fita ba mayafi,ta gayamai sakon Umma kafin ta koma cikin Dakin Dakin bakin ta shiga Tana gyarawa Duk da baida wani Datti Don bayan kowani lokaci suna gyarashi.
Alima tagama Kulla Tuwon ta Fito da manyan Food flaks ta Jera komai aciki ta Zuba miyan ta Rika Dauka tana Kaiwa saman Dinning,Bayan tagama ta Rika kai Filets da cokula da Ruwa sai zobon Data zuba cikin Wani katon Jug shima ta kai tana gyara kitchen din ne ta karajin wayar Ummah na kara ta Fito da Sauri tana Fadin"Umma wayarki...".
Tafada tana isa kusa da wayar Ta Daukota BAFFIJO da manyan baki,Tagani Mirmishi ta saki cikin Shauki ta Daga kiran tana Fadin"Ina kwana ya Abba..."
Tafada tana leken Bedroom din Umma karta fito da gudu ta Rumtuma dakin bakin da Asiya ke gyarawa tana fadin"Asiya ga ya Abba ya kira Umma na Dauka naga kamar ta shiga wanka.."
Tafada tana kara kanga wayar akunne Lokaci Daya da Asiya ta matsowa tana Washe baki kamar Gonar Auduga.