Free chapter 路 Read without an account
08
RA'AYI NE KO BURI..?
Wattpad:Janafnanfy13
Mallakar:Janafty馃挅
8
"Hankula Tashe suka baro porthercourt zuwa kano Cikin Tashin Hankali da damuwa Fatima tayi kukan maraicin Rashin Uba akaro na Biyu,Domin Tabbas Alhaji Jada tamkar Uba shakiki yake awajenta.....
Goggo Asiya tayi kuka Sosai na Rashin Alhaji jada,A dawakin Tofa aka karbi Gaisuwarsa sai da akayi bakwai kana suka koma kano Hatta Bintalo tana tare Dasu sai da akayi bakwai kana ta koma Amina ma tazo ita da mijinta saunyi gaisuwa sun koma,Ganin Halin da goggo Asiya take ciki ne na Damuwa yasa Fatima ta ki yarda tabi Sa"ed su koma yakuma ce zai koma da mutaddif saboda makaranta Ta hana tace ya barmata yaronta In ya tafi Dashi wazai kula dashi GoggoAsiya ne tace ya kyaleta bayan an kwana Biyu yazo ya Dauketa su koma tare Shiyasa ya tafi ya barta.
Wannan Dalilin Shine Mafarin Barin Fatima porthercourt Komawa da batayi ba kenan har Abada,Da Sa"ed ya sake Dawowa sai Fatima ta nuna zata cigaba da zama anan tare da goggo Asiya in ya samu hutu ya Dinga zuwa ganinsu shima bai musa ba Saboda Tun bayan Rasuwar Alhaji jada Hawan jini ya Rafke Goggo yau lafiya gobe babu Kullun Suna kan Hanyar zuwa Asibiti ana Dubata sai ya barta anan kano sai dai ya kan zo Lokaci bayan lokaci ya Dubasu.
Sai aka saka Mutaddif awata makaranta mai suna Frine collage kano yacigaba Da karatunsa Daga Jss1 direba Alhaji Sa"ed ya samu wanda ke kaisa yana zuwa ya Daukosa Rayuwar Fatima da D'anta agarin kano Rayuwa ce mai cike da Sadaukarwa,Soyayyah kulawa da kauna mai tsanani Abdulmutaddif yaro ne mai hazaka da Kokari Fatima ta kasance malamarsa wajen koyamai Abunda ya Shafi Addini Shiyasa Islamiyarsa da Haddarsa Dayake zuwa suke Mamakin Kokarin yaron basu sam Wata malama garesa na musamman ba agida,In ya Dawo makaranta kafin Lesson Teacher dinsa yazo haka Fatima zata zauna da Littafinta Abdulmutaddif na koyamata ABCD goggo Asiya tayi ta musu Dariya mai cike da kauna ganin yadda Fatima take Dagewa wajen koyan Abunda Mutaddif din yake Koyamata Tun Haihuwanshi,bata iya Kiran sunansa Saboda Sunan Baffa ne sai take cemai Baffijo ko Abba Toh Abba ne yafi Binshi kowa dashi yake kiransa,ammh ita Baffijon yafi kama Bakinta.
Mafarin komai ya Fara ne Tun Abdulmutaddif na karaminsa zan iya cewa Da Burin waka yazo Duniya Tun yana dan karaminsa Daya fara girma Waka take cikin Abubuwan Dayake bala"in so na Daya Fatima bata barinsa kallace kallacen banza,balle Sauraran Wasu wakokin in Ta barshi yayi kallo Sai dai in Cartoon ne, Sakamakon shi bamai yawan mgana bane balle Hayaniya sai ya Zauna yayi Shuru cikin Zuciyarsa kawai yana Rera waka Bai taba kwatantan Rubutawa ba ammh acikin kwakwalwarsa ya Dade da Rera wakoki Dadama Abu Daya ke kashemai gwiwa Ummansa Fatima wacce Watarana Suna cikin Karatu sai take cemai Baffijona me kake so ka zama nan gaba..? Shuru yayi yana kallonta lokaci Daya kuma yace mata mawaki yana so ya zama mawaki ba Domin komai ba Sai Domin Cika Burinsa,Fatima ta Dade tana kallonsa cike da Takaichi da mamaki Tana maimata kalmar mawaki kai ya gyadamata cikin Shaukin Abun Mirmishi ta saki tana ganin kamar yarinta ne sai ta kama Hannuwanshi tana Fadin"A"a bazaka Taba zama mawaki ba Baffijona kasan menene Abun da mahaifiyarka take Burin ka zama..?ya kalleta yana jiran amsarta tashafa kanshi tana Fadin"Babban Burina Shine ka zama Matukin Jirgin sama kana son ka zama..?...
Wannan Mganar shike kashemai Gwiwa baya da Tunanin komai sai na yaga ya cika Burinsa,bayan itama ya taba gayama Abbansa wato Alhaji Sa"ed wanda yayi Dariya ya Shafa kanshi yana Fadin"Baban Fatima karka damu komai kake son zama aduniyar nan ni mahaifinka zan Shige maka gaba har ka samu cikar Burinka.."Da wannan ya gane A Ra"ayin An samu Rashin Fahimta tsakanin Duka iyayen nashi,bai kara maida kai ga Abun ba,duk da Hakan na cikin Ranshi sai shigarsa Frine collage lokacin suna Jss2 a ajinsu akwai wani yaro Nura Magaji wanda dashi kadai ne Mutaddif ke mgana itama sai ta kama Dole,Shine watarana bayan an tashi break yazo ya samu Mutaddif na Zaune shi kadai a kujeran zamansa kamar yadda ya saba,ya Zauna yana Tambayanshi meke sakashi ya zauna ya lumshe ido yayi Shuru wani lokacin kuma sai aga yana sakin Mirmishi,jin haka yasa sai yaji yana Bukatar sanar dawani Burinsa sai ya kalli Nura kawai sai ya Fara Rairamai wakarsa ta farko mai taken Mommah my Happiness.. sake baki Nura yayi yana Sauraransa cike da Shauki da mamaki idanuwansa suna lumshe ne yana Raira wakar cike da muradi da Buri bai gama ba, yaji ajinsu ya Dauki tafi da ihu Ashe Tuni Sauran yan ajinsu sun Dawo sun iskeshi yana Rera wakar suka Zagayeshi suna kallonshi cike da Shawa"awa haka suke mai ihu suna Fadin A.S. MAINASARA..,.
Abun ya sakashi Nishadi Sosai Tunda Ga Ranar kullum aka tashi Break sai sun matsamai ya Rera musu waka muryansa gabadaya Tafiya take dasu wasu acikinsu Har suka Fara zuwa da Abun nadan Sauti suna Nadan Muryan Mutaddif,wanda Sanadiyar haka yayan Nura magaji Bashir magaji ya Taba jin wakar Abun ya Burgeshi ya kira Nura yana Tambayanshi waye,nan yake sanar dashi labarin Mutaddif dan baiwa nan da nan ko yace yana son ganinshi toh acikin wannan Halin ne Allah ya Dauki Ran Goggo Asiya Sai Mutaddif ya kwana 2 bai zo makaranta ba,awajen Hukumar makaranta suke jin labarin Rasuwar kakarsa Yayan Nura ya Tasashi ya kaisa har gidansu mutaddif suka ma Alhaji Sa'ed gaisuwa kana yasamu kebewa da Mutaddif inda yake Tambayanshi yana son ya zama mawaki..? Yana bukatar Duniya ta shaida Basiransa..?
Sai mutaddif yayi Shuru kawai yarasa mafita azahirin Batu waka Burinsa ne ammh kuma bazai iya gudanar da komai ba sai da izinin mahaifinsa,uwa uba kuma mahaifiyarsa,ganin haka yasa shi Bashir din ya Dinga Forcing dinsa kan hakika yana da Tarin basira in zai yarda zai gabatar ma wani abokinsa mawaki Wato Sadiq musa waye,shima wani Babban mawaki ne da Duk fadin kano ake ji dashi mawakin Turanci dana Hausa,batare da Tunanin komai ba sai mutaddif ya amince suka Rabu kan zai gabatar mai da wakar yarda sukayi zai nemasa Batare da kowa ya sani ba kuma shima bai gayama kowa ba yaso dai yagama Abbansa sai kuma ana bakwai ya koma bakin aiki shiyasa sai bai samu damar gayamai ba.
Bashir ya Dauki lokaci kafin su samu zama da Sadiq ya gabatar mai da Wakar Mutaddif wanda Nura ya nada cikin Na"uran nadan Sauti, Da Farko Sadiq ya zata Shirme ne sai da yaji kuma ya Saurara sai Abun ya kara bashi mamaki yana kara tambayan Wai kuma Dan Jss2 ne ya iya sarrafa wannan wakar lalle ko waye dan baiwa ne nan take yace yana bukatar haduwa da Mutaddif Domin matukar aka Dauki wakar aka kaita Studio bakaramin hawa zatayi ba Bashir yaji Dadin haka Yakoma gida ya kira Nura ya sanar dashi shima yayi Farinciki Washegari suna zuwa makaranta Nura ya sanar da Mutaddif wanda yaji Dadi sosai na ganin zai cika Burinsa batare da shawara da kowa ba daga makaranta ya Sulale yabi Nura gidansu yaje ya hadu da Bashir suka rankaya zuwa Studio din Sadiq aranar sai ga Mutaddif yana Raira waka acikin Jama"a Waje ya Dauki ihu da Sowa kowa na mamakin yaro kamar wannan ya iya Raira wannan wakar,kuma uwa uba baitaba Rubuta waka ba gashi acikin Harshen Turanci Gabadaya Studion din Sadiq ranar ta Rude da Fasahar Mainasara Lokaci daya waje ya Dauki Sunansa Shikanshi Sadiq haka bakinsa yaki Rufuwa ya Rumgume mutaddif Nura kuwa baki yaki Rufuwa saboda Murna Shiko Mutaddif Zuwansu yana cikin Tsoro,saboda ya gudu kafin Direban gidansu yazo,yasan kuma in ya koma batare dashi ba Hankalin Umma zai tashi ammh lokacin Daya ganshi tsaye yana Rera waka duk sai wannan ya bar ransa ko bakomai waka cikar Burinsa ne.
Ranar sai yammah ya koma Gida ya Rasa Islamiya koda yakoma umma tasha kuka ta gaji,Saboda Rashin sanin inda yaje taje makarantarsu yafi sau goma Hukumar makaranta tace bata ganshi ba labarin har wajen Alhaji Sa"ed,hankalinshi shima ya tashi koda ya Dawo saboda bacin rai sai da umma ta kasheshi da mari,sanda yake sanar da ita Daga gidansu Nura yake,Ranar yasha fada sosai Tsausayin Ummansa ya kamashi Domin ta wahala dashi Tun wajen Haihuwarsa harzuwa yau Abbansa an hadasu awaya yayi masa Fada cewa karya kara tafiya wani waje batare da sanin Mahaifiyarsa ba,yayi ta bashi hakuri ammh sai ya samu kanshi da kin gayamusu gaskiyan lamari.
Tafi tafi na Rayuwa Mutaddif na Cigaba da zuwa Studion din Sadiq a boye da taimakon Direbansa wanda ke kaisa Boko da Islamiya,shi zai kaisa ya kuma Jirasa ya gama Abunda yake ya Fito su koma gida in Umma tayi mgana sai yace suna tsayawa a lesson ne ahaka har ya shiga matakin Jss3 yana da Shekara 15 aduniya Zuwa wannan lokacin Tuni wakokinsa Guda uku na Turanci Sadiq ya saka antacesu sun Fita zuwa ga mutane ammh Yana Boye sunansa da Mainasara Saboda ya gaya musu shi bai Fara Waka domin neman suna bane A"a yanayi ne domin Burinsa kawai.
Ya zana Jarabawar Jsce Wata Baraka ta Fara Bullah Tsakanin Umma da Abba Lokacin da ya Bijiro da mganar Auren Hajiya latifa wacce ta kasance Haifaffiyar garin kano ne ammh Babanta bayarbe ne Daga garin Imo,yazo kano kasuwanci shine har ya auri mahaifiyarsu Bahaushiya Hajiya Hadiza,ta haifi Hajiya latifa da yar"uwanta Sharifa,Sun taso cikin gata da ilimin Boko dana Arabi da kuma neman na kai ammh sunfi bama na Bokon karfi Saboda bayarbe ya yarda da neman Ilimin Boko Sosai kodon Dogara Dakai Hajiya latifa Sai da ta kai matakin masters Tana da Shekara 29 aduniya ta girmema Fatima Sosai Sun hadu da Alhaji Sa"ed ne a Airport din mallam Aminu lokacin Daya Dawo Daga porthercaout,ita kuma Ta Dawo Daga Jahar ekiti taje Domin Hada project dinta Haduwar Farko Alhaji Sa"ed yasan yagama samun irin macen Dayake so kuma yake Muradi,Domin har suka Rabu basu iya kalmar Hausa ba sai Turanci kawai har sukayi musayan Nombar waya bai koma bakin aiki ba sai da ya gabatar da kansa wajen mahaifinta mai suna Alhaji Abdul"aziz Sanin Darajar mahaifinsa yasa ba bata lokaci yace ya turo magabatansa,Domin yagama yabawa da Rikon Auran Hausawa Da kuma Dattakonsu Tunda itace Uwar ya"yansa.
Da kanshi yaje Dawakin Tofa ya sanar Dasu,kan mganar ya kuma basu kudin duk Abunda zasu bukata kafin ya Dawo Fatima ta kwashi mutaddif sun Tafi Rugar Hardo wajen Bintalo tana mata kuka Saboda bakincikin Abunda Sa"ed ya gayamata Datace mai ta Rageshi dashi da zai kara mata kishiya?,ya kalleta cikin bacin rai yace Saboda yana bukatar wayayyiyar mace mai ilimin Zamani wacce zai shiga da ita ko"ina bai ji kunya ba,Taya zai ta zama da ita karta manta matsayinshi,bata ganin ya in Zauna da ita ahaka kamar bata kwareshi ba..?,Tunda ita taki yarda tayi karatu Ko hanyar boko bata Taba Zuwa ba,Kuma sai ta tambayeshi miye Dalilinsa na kara aure? Tunda Yagayamata wadanan Mganganun Fatima ke kuka mai Cinrai wani bakinciki da takaichi suka kusa kasheta,Mutuwar goggo Asiya ta dawo mata Sabuwa Ta Rumgume Mutaddif tana kuka Shi ma sai ya Sa kukan yana yi yana Share mata Hawaye wannan Dalilin shi ya sanya Tayi yaji zuwa Rugar hardo kuma taje ta iske Bintalo na kwance bata da lafiya wani Ciwo ya Fito mata awuya mai kama da ciwon daji ita ta hana ma akira su Fatin asanar dasu ganin Halin da mahaifiyarta ke ciki sai ta bar mganar yaji ta kira Alhaji Sa"ed da Amina ta sanar dasu hankali Tashe ya nufo Rugar Hardo daga Dawakin Tofa Halin Daya iske Bintalo Abun baimin Dadi ba yayi kokarin ta yarda su kaita Asibiti ammh taki Ta kallesu tana Mirmishi tana Fadin"Sa"edu meke Faruwa ne Fatima tazo min cikin wani Hali Kallon Fuskarta kadai nayi na gane tana cikin damuwa..?.
Kansa ya Sunkuyar kafin ya kora mata jawabin komai,cikin karfin Hali da ciwo Bintalo tace"Assha Bintalo na kina babba Ammh baki san ya kamata ba ina laifin Sa"edu don yace zai kara Aure..? Bai miki hallaci ba kiga ba inda kika rayu ba wayewa ba Ilimin zamani kun Rayu cikin Wannan Rugar ko gefen gari baku taba Fita ba,ammh Aka Aurasa masa ke ya karba ya rikeki kuma ya zauna dake,Haba Fatima kima Sa"edu Adalci shima ya Auri Daidai da Ra"ayinsa da kuma Burinsa kada ki zama Sila wajen Ruguzama mijinki Burinsa Don Allah ki kwantar da Hankalinki kiba mijinki goyon baya...Na tabbata Sa"edu ko bayan bani bazai taba Tozartaki ba....Ki rikeshi Hannun bibbiyu in kika sabamai Ban yafe miki ba Bintalo ga yar"uwanki nan Amina ki Rike mata Zumunci Saboda bayan ke bata da kowa..Allah yayi muku albarka daku da Zuru"arku gabadaya.."
Tafada tana Shafa kan Mutaddif lokaci Daya hawaye na wanke mata Fuska Alhaji Sa"ed jikinsa ya mutu sosai Fatima kuwa sai kuka take adaren suka Daukota zuwa Asibitin Aminu na kano Washegari ko gwaje gwajen ba"a gama mata ba tace ga garinku nan,Koda Amina ta iso ita da mijinta da ya"yanta dayake tana Haihuwan kusacda kusa tsakanin Sulaiman da Mutaddif Shekara Shida ne,sosai dai suka tarar da gawa,sunyi kuka Sosai kamar Ransu zai fita achan Rugar Hardo akayi zaman makoki Daga Aminar har Fatima basu koma ba Sai da sukayi Sati biyu Agidansu Mutaddif kuwa ya koma gida Shida Alhaji Sa"ed da bai koma ba saboda mganar Auransa da Latifa ga kuma Rasuwa Shiyasa ko Aminar bata wani saba da mutaddif ba,Saboda koda sunzo kano baya nan yana makaranta Kuma Ringim di sau Daya Fatima tataba zuwa Dashi.
Tun alokacin aka Raba musu gado,sai Fatima ta hada duka Dabobinta ta Damkama Mijin Amina Suka hada danata suka tafi Dasu Ringim Tunda Shima yana da garken Dabbobin achan garin ita kuma ta Dawo gidanta Tundaga Lokacin Fatima ta chanza ta Daina yawan Dariya da Sakin Fuska Shikanshi Alhaji Sa"ed baya gane kanta Harkan gabanta kadai take da ita da Danta Mutaddif wanda Ta Dake ya Fara koyamata Hada kalmomin Hausa,har aka sa lokacin biki wata uku masu zuwa Da yake gayamata Allah sanya alheri kadai tayimai,yazo ya fara gyaran gida aka Fitarma da Latifa Shashenta,ko Wasu Shiryen Shiyen Bikin yan Dawakin Tofa sukayi,kayan aure kuma bata sani ba kila ita latifan ta Siya ma kanta ita dai kudi ya bata ta aika ma Amina aka Siya Wasu Dabobbin.
Acikin Hatsaniyar Bikin ne Fatima ta gane tana da shigar ciki Lokacin Tuni Mutaddif ya koma Frine Collage ya Dora karatunsa Daga SS1,kuma yana cigaba da wakarsa aboye bata tare da iyayensa sun sani ba Haka akayi bikin Alhaji Sa"ed da amaryansa latifa kuma aka kawota gidan,wanda tare da yar"uwanta Sharifa aka yi musu aure,ita ta auri wani bayarbe ne Dan"uwan mahaifinta,ita Abuja aka kaita inda yake aiki.
Fatima wata irin macece mai kishi Sosai,Tunda Latifa ta Shigo gidan bata samu kyakyawan kallo Daga Fatima ba Hatta Mutaddif tahanashi Raban Shashen Latifa tayi ita kuma gata mai Sanyin Hali kullum da Safe zata Shigo ta gaida Fatima ammh Sai ta ga dama take amsawa Mutaddif kuwa ko agabanta ne tace Son yanzu zata zaremai ido zai tashi ya koma Daki Abun yana damun Latifa tama Alhaji Sa"ed mgana Shine ya ma Fatimar Fada ammh kuma bata Daina ba yarasa yadda zaiyi da ita,kamar Zuciyar Fatima ba sanin Allah tafara Fito da wasu Dabi"u marasa kyau Tafiyarsa na Farko Daya bar latifa bata ji da Dadi ba Domin Watarana Data Kira Mutaddif zuwa Shashenta suna Hira haka kurum yaron ya Shiga Ranta haka Fatima tazo ta Finciki hannun danta ta kuma ja ma Latifa kunni ta kiyayan mata Da Tunda ba ita ta haifan mata shi ba Abun yafara Damun latiifa tayi dai Shuru bata gayama kowa ba,watan Latifa biyar da Aure ta samu cikin Ziyada Zuwa lokacin kuma cikin Fatima yakai Wata takwas,kuma har zuwa lokacin bata chanza zani ba,Zamansu na Doya da manja bamai Shiga Harkan kowa Tunda latifan ta gane Fatima bata kaunar ta rabeta ammh duk da Haka Mutaddif na Shiga bangarenta su zauna tayi ta tambayanshi Burinshi cikin Hirarsu ne ya Shaida mata Burinsa na son zama mawaki har ma ya gayamata ya fara waka Abunda ko mahaifinsa bai sani ba Latifa tayi murna Saboda tana Bala"in son yara masu Fasaha,ta dinga murna ta kuma mai alkawarin zata Taimakamai wajen cikar Burinsa bata jira komai ba ta kira Alhaji Sa"ed ta gayamai wanda yaji mganar Daga sama bai gasgasta ba Sai da ya Dawo Weekend Mutaddif ya Daukesu Shida Latifa har zuwa Studion Din Sadiq,yayi musu bayanin komai a ka kuma sa musu Duka wakokinsa,basu kara yarda da cewa Mutaddif ne Allah yabama Wannan baiwar ba sai da ya Shiga ya Rera suka ji suka gani Alhaji Sa"ed sai da yayi kwallar Tsausayin Dansa na ganin cewa da gaske yake Burinsa da muradin na zama mawaki tana cikin Ransa Latifa kuwa gaban kowa ta Rumgumeshi ta na Murna Sosai Haka suka Dawo Gida cike da Farinciki Latifa na bama Alhaji Sa"ed shawaran ya Budema Mutaddif Studion Don Allah kar ya bari ya Dakushemai Burinsa Har ga Ransa bashi da matsala Babban Damuwansa Fatima ne Saboda sanin Halinta kan Abunda ya Shafi Danta.
Ganin Halin Data ke ciki na Tsohon ciki yasa ba wanda ya Tuntubeta da mganar,kawai Yabi Shawaran Latifa ya Samu Sadiq sukayi mgana kan cikama Mutaddif Burinsa na zama mawaki Sadiq yaji Dadin yadda Mahaifin Mainasara zai bashi dama nan da nan ya shige gaba wajen samama Mutaddif katon Studio da kayan aiki harda ma"aikata Saboda baiwarsa Dama Tuni wakokinsa sun gama isa wayar mutane,karbuwa kuwa ta karbu Sosai Sadiq yasha amsa wayoyin jama"a kan suna so su tambayeshi waye mai Nasara sai da yayi Dariya Saboda Sun riga sunyi alkawari da mai Mainasaara bazai taba yarda wani yasan shine mawaki mai nasara saboda shi bai yi waka Domin Suna ba sai domin Raayi da Kuma Cikar Burinsa.
Ranar da Mutaddif yagama Zana Jarabawar Neco dinsa Dayake a SS2 ya Rubuta Jarabawar tashi a kuma Ranar Latifa da Alhaji Sa"ed suka kaisa Sabon Studio dinsa Saboda murna sai da yayi hawaye lokaci daya ya kalli Abbansa yace Umma fa,shuru kawai yayi mai yana wani Nazari kafin yace su koma gida suna komawa Dukkansu suka Shiga Shashen Fatima suka isketa zaune tana Bitan rubutun da Mutaddif ya Rubuta mata na Kalmomin Hausa Tana ganinsu gabanta ya Fadi mutaddif ya isa gareta ya Riko hannunta lokaci Daya yake Fadin Umma yau na gama makaranta matakin Secondry kuma ayau Abbana ya gabatar min da cikar Burina kiyi hakuri ban gaya miki ba Umma Mommy latifa da Abba sun Taimaka min na cika burina na zama mawaki yanzu haka Daga Babban Studion din da ya budemin muke..Kizo muje kema ki gani Umma kisa albarka.."
Galala Fatima ta tsaya tana kallon Mutaddif Da Latifa da Alhaji Sa"ed cike da wani bakinciki D'an nata kwara Daya tak aduniya Latifa ta gurbatama Tarbiya,kuma Sa"ed ya biye mata Dan nata dataci buri akansa Shine aka ma maida mata Mawaki Dan nanaye bayan ta gama kwace mata miji yau kuma Dan nata zata rabata dashi bata tsaya wani Tunani ba ta Daga Hannu ta Tsinke Mutaddif Da tawagen maruka lokaci Daya hawaye na wanke mata Fuska tace fita ka bani waje Tunda ka nuna ni ba Mahaifiyarka bace latifa ce uwarka Tunda har zata iya zaba maka Abunda ya dace dakai bansani ba.Kun cuceni Latifa da Sa"ed kun cutar da Da'na wajen Maidashi abunda ba Burina ba...Bazan taba yafe muku ba..Tafada lokaci daya tana Fashewa da kuka kafin ta sulale rike da ciki.
Naguda ce tatashi gadangadan Lokaci daya suka kwasheta zuwa Wani Private Hospital,bata Dauki Lokaci mai Tsawo ba ta Haifi yarta mace Wacce taci sunan Aliimah Har kuma aka sallamota Daga Asibiti bata bari mutaddif yazo inda take kuma bata ma Latifa mgana balle shi kanshi Alhaji Sa"ed din,sai dai ta kule adaki tayi ta kuka Hakama Mutaddif ya roketa tayi hakuri taki hakura yace ya hakura da Burinsa na zama mawaki nan ma tace ya fita ya bata waje ta barma latifa shi ganin Abun na Fatima na kara yawa ne yasa da Alhaji Sa"ed zai koma ya tafi da Latifa da Mutaddif wanda ya nuna bazai Bisu ba Alhaji Sa"ed yace maza ya Shirya su tafi kamar yadda tace tabarma latifa toh wajenta zai koma Lokacin da Fatima taji labari kamar ta mutu tana ji tana gani Alhaji Sa"ed ya Dauke Latifa da mutaddif ya barta ita kadai Daga ita sai Aliima,ranar kwana tayi kukan bakinciki Tundaga lokacin ta saka aranta mutaddif baya jin Tsausayinta tunda zai iya barinta yabi bayan mahaifin ya kuma bi latifa,Toh Tabbas zata goge kanta a matsayin mahaifiyarsa na Har Abada.