Free chapter · Read without an account
Chapter 25
25...........
Ammi na zaune tare da cousins ɗinta guda biyu, kana ganin yanayin su kasan ransu a mugun ɓace yake Ammi tayi kasa da murya tace "Ni dai kuyi hakuri har ku koma Niger dan Allah kar wanda ya tanka ta, neman magana kawai take yi, shiyasa take Abunda zaisa a tanka ta" Binta ta zauna tana girgiza kafa tace "Wallahi Dada sirbajo sai dai matan nan bata sake shiga harkar mu ba wallahi sai na gwada mata ni dangin fulani ne bata taɓa mu a kwana lafiya" Ammi tayi shiru tana kallon ta tama rasa me zata ce musu su fahimce ta Mairamah tace "Ah toh, wallahi ba zamu kyale ta ba, cin uban Shegiya zamu yi, hassada ce fal a cikin ta, kuma inda akayi decorn ko kusa da sashin ta ba'a kai ba amma ta fito ko kunyan ido bata ji ba zato ta wargaza wajan" Ammi sai binsu da ido take yi dan taga ran su ya ɓaci ba sauraron ta zasu yi ba, Binta na kallon Mairamah tace "Ke tashi mu fita karta ga kamar tsoron ta muke ji shiyasa muka shigo ciki" Mairamah ta mike tace "ai kuwa tayi kaɗan dan uban ta" Ammi na musu magana ko kulata ba suyi ba suka fice daga parlorn abun su. Yana zaune akan sofa hankalin sa gaba ɗaya na kan wayan da ke hannun sa a gefen sa kuma wata Dattijiwa ce da ba zata haura 53 years ba sai wasu ƴan mata guda biyu wanda ɗayan takai 28 dayan kuma tana 25, Duk maganar da Ummi take yi be ɗago ba Nimrah tace "Wallahi gaskiyar Ummi ne, ya za'ayi biki ace lami? atleast ko dinner ace ba za'ayi ba?" wani kallo ya mata ta ja bakin ta tayi shiru, Ummi tace "yanzu event ɗin karɓar lefen ma kar ayi kenan?" ya kalli Ummi sannan yace "Toh me amfanin hakan Ummi? Kawai akai akwati shikenan sai anyi wani shirmen?" Nawaal ta taɓe baki ta mayar da kallon ta wajen kanwar ta Nimrah tace "Ke Nimrah dama Allah Allah nake na dawo kasar nan ki bani labari wacece wanda Ya MD zai aura? Yanzu ya gama zagaye zagayen kenan?" Nimrah ta gyara zama tace "Ya Nawaal kenan! Kema kinsa Ya MD da taste, Leena sunan ta, She's not just fine, she's flawless wollah, yarinyar ta haɗu ta ko ina ne Famous ce ita fah, bari ki ganta" ta karasa maganar tana duba wayan ta mikawa Nawaal tayi ta karba tana kallo Nimrah ta kuma tace "Shine wai Ya MD ba zai kara mata gold a ciki ba" sai sannan ya kalle ta yace "Toh ki bani kuɗin mana" Nimrah tayi dariya Nawaal tace "ikon Allah, Ni kuma ban taɓa ganin pic ɗinta ko da a IG ne" Ummi da ke jin su tace "Shi ko bikin lami yake so ayi, ko me za'ayi yace A'a daga daura aure sai daura aure ko buɗan kai ma yace A'a ana dauko masa ita gidan sa za'a kai ta" Nawaal ta sake baki tana kallon sa tace "Toh ai da na sani da banzo ba, meye amfanin zuwan nawa toh tunda ba abinda za'ayi?" Sai sannan Muhammad ya kalle su, system ɗin sa dake chagy ya ɗauka ya bar parlorn Ummi tace "Ikon Allah!" Nawaal ta bisa da kallo tace "Shi kuma yaushe ya koma haka?". Dawowan Leena kenan tana sanye da Nikab a fuskar ta saboda gyaran jiki da ake mata ta gaida gatekeeper ya buɗe mata gate ɗin ta shiga kallon compound ɗin ta tsaya yi da kallo daga haka ta wuce ciki da sallama ta shiga parlorn Ammi dake kallon ta tace "ki samu ki ci abinci, saboda ku gama dilken kafin su karaso" Leena tayi jim sai kuma ta gyada ma Ammi kai gaishe da kannan Ammi tayi sannan ta wuce ɗakin ta dan ajiye jakkan ta, gaba ɗaya ta rasa me yasa ta nemi sukuni ta rasa meke damun ta ji take kamar bata da lafiya ta ajiye jakkan ta ta jona wayan ta a chargy ta yaye Nikab ɗin fuskan ta sai ga Binta ta biyo ta da abinci tana kallon ta "gashi" Leena ta karba tace "thank you Aunt Binta" nan bakin gadon ta ta zauna Binta na kallon ta tace "Leena lafiya dai ko?" Ga mamakin ta kawai taga hawaye na sauka idon ta tace "SubhanAllah me aka Miki?" ta karasa maganar tana zama gefen Leena, Leena tace "I'm just Scared!" tana kaiwa nan ta fashe da kuka Anty Binta ta jawo ta jikin ta ta rasa me zata ce mata tace "Scared of what?" Leena tace "i don't know, kawai ina jin zuciya ta na tsinkewa time to time" Binta na patting bayan ta tace "Hakuri zakiyi Leena, kuma kiyi ta addu'a daman hakan ya kan faru ba zaki samu peace of mind ba har sai an kaiki" Leena tayi shiru tana jinta dan gaba ɗaya taga ba ta ma fahimci inda ta dosa ba ne, bayan ta gama cin abinci me dilke ta shigo, yi mata kawai ake amma ita gaba ɗaya she's just spaced out bata ma san meke faruwa ba wayan ta ne ya fara ringing matar dake mata dilke ta kalle ta ganin da gaske fah she's Spaced out, tayi murmushi cike da tausaya mata tace "Leena toh ki ɗauka mana" sai sannan Leena táyi realizing ashe kiran ta ake yi ganin Muhammad ke kira yasa ta daga kiran ta kai kunne da sallama ɗauke a bakin ta, bayan ta gashe shi sai kuma tace "Toh, in shaa Allah" a haka suka yi sallama ta ajiye wayan a gefen ta Matar tace "Leena da zaki gane ki daina wannan Daydream ɗin, zaki jima kanki ciwo a banza, yanzu ƴan matan wannan zamanin basu ɗaga ma kansu hankali balle ma auren soyayya zakiyi kuma yana da kudi toh damuwar me zaki shiga har haka?" Leena ta kalli mata sai kuma taji hawaye na taruwa a idon ta wato kowa baya jin abinda take ji? Ita kadai ke ji kenan, ta runtse idon ta sosai. Mummy dake tsaye kan Rayyan tana kallon sa cike da tausayin yadda ya koma a ƴan cikin kwanakin nan tayi kasa da murya tace "Son, Dan Allah ka tashi kaci wani abun mana haka zaka ta zama ba abinci a cikin ka?" ya gyaɗa mata kai kawai daukan bowl ɗin pepper soup tayi ta sa spoon a ciki ta ɗeba ta kai masa makin sa girgiza mata kai yayi ya karba yana kallon ta yace "Mummy zanci amma dan Allah ki tafi ina son na samu hutu ne" tana kallon sa tace "amma ka tabbata zaka ci?" ya gyada mata kai daga haka ta mike ta fita ɗakin su Nisreen ta wuce ta samu Niswa na kwance tana danna waya Nisreen Kuma na bacci, Niswa ganin ta shigo yasa ta ajiye wayan a gefe Mummy ta karasa har bakin gadon su ta zauna Niswa tace "Sannu Mummy" Mummy tace "Nikam Niswa har yanzu naji baki kara ce min komai game da mutumin can ba?" Niswa ta yamutsa fuska ta mike ta zauna tace "Dan Allah Mummy ni ki kyale ni da zancen wannan mutumin" Mummy ta mata wani kallo tace "ban gane ba?" Niswa tace "Toh wai har nawa nake da za'a fara takura ni da maganan aure ne? Ko fah makarantar ban gama ba" Mummy ta sake baki tana kallon ta tace "Har nawa kike zaki ce? Toh dan Uwar ki Leena ba kanwar bayan ki ba ce? Kuma dan asara ace dan minister ne zai aure ta" tayi shiru sai kuma tayi murmushi tace "ayi mugani" Niswa ta kalle ta tace "Mummy, Leena daban, Ni daban, beside yanzu ina fara sa wannan damuwan a rai na sai ya hanani exams sannan na sama kaina damuwa" Mummy ta sake baki tana kallon ta da mamaki tace "Eh lalle kam kwarai, toh ni yanzu maganan wannan mutumin nake Miki" Niswa ta yamutsa fuska tace "Ni fah dan Allah Mummy ki raba ni da zancen wannan mutumin, dan ni rashin mutunci ma nayi masa, saboda Leena zata yi aure shikenan sai akawo min wani gaja, gaskiya Ni ba taste ɗina bane, ita kawar taki idan har Mutumin arziki ne zata yarda ta kawo mini shine? Ai saidai ta haɗa shi da ƴar ta Layla naga" Mummy ta sake baki tana kallon Niswa ta mike tace "wallahi zaki sha mamaki na Niswa, ina ni kike wa tsiwa har haka? Toh ke idan banda rawan ido naga mutumin nan a NNPC yake aiki kuma gidan su suna da kudi na gani na fada" Niswa tace "Ni yanzu ba wannan ba, wallahi Mummy idan nace miki baki fahimtar abu sai ki ce min A'a, amma har yanzu kin kasa gane meke damun Ya Rayyan" Mummy na kallon ta tace "toh meke damun sa uwa ta? Niswa tace "ko ƙaffara ba zanyi ba Yaya saboda Leena ya kwanta rashin lafiya, kalli baya tashi rashin lafiya sai sanda kika masa baki akan ta da lokacin da aka kawo gaisuwan ta sai kuma yau da za'a kawo lefen ta, aure kuma jibi za'a daura, kin yarda?" Mummy tayi shiru tana tunani gaba ɗaya hankalin ta be taɓa kawowa nan ba Niswa ta taɓe baki tace "Ni wallahi har ya fara bani tausayi, ciwon so zafi gare sa, kuma wallahi suna son junan su, tun farko da kika raba sune amma da kila shi zata aura yanzu" Mummy ta daka mata wani tsawa har sai da Niswa ta tsorata Nisreen dake bacci ma ta farka a gigice Mummy ta mike tana kallon Niswa tace "kika sake dangan ta ta da ɗana zaki sha mamaki ba ina faɗa Miki wannan" daga haka ta wuce ta fita daga daki. Leena na kallon Anty Binta da Amty Mairamah dake kanta tace "wallahi anty yace baya son wani event ɗin da za'ayi, yace harda na karɓan Lefen ma baya son ayi" Anty Binta ta taɓe baki tace "na karɓan Lefen kuma yayi karya shi yaji wajan, Abunda ba agidan sa za'a yi ba, so wannan kam be isa ya hana ba" Mairamah tayi kasa da murya tace "Leena ba wai me hayaniya za'ayi ba kawai dan karrama ƴan-uwan sa ne kinji?" Leena ta gƴaɗa kai kawai Anty Binta ta mika mata roban hannun ta tace "cinye a gaba, na yau kam ba zaki samu asara ba" Leena ta karba tana bata fuska ta gutsura takai maki tana taunawa kamar magani. Mummy tayi tagumi a bakin gadon dakin ta tayi nisa cikin tunanin da take yi harga Allah yanzu hankalin ta ya fara tashi ita bata ga wani progress a abinda take yi ba zufa ne ya fara zarya mata da ta tuna ashe jibi daura auren, tana nan haka, kiɗan masu ganga ta fara ji, sun cika gidan da kiɗe kiɗen gargajiya hankalin ta taji ya ninku ana da ta jawo wayan ta tayi dialing numbern Fatima ji tayi akashe bata san sanda tayi wulli da wayan ba ta figi makullin motar ta ta yafa gyallen sannan ta kama hanyar fita, anan parlor taci karo da Daddy da Colleague ɗin Rayyan, yana kallon ta yace "ina zaki kuma?" kame kame ta fara daga karshe tace "En dama, dama zani gidan Fatima ne an kwantar da Layla a asibiti ne" Daddy ganin Abokin Rayyan da suka shigo tare yasa bece komai ba tana fita a parlorn ta sauke ajiyan zuciya, dakin Rayyan suka wuce samun Rayyan suka yi yana bacci Daddy yana kallon sa cike da tausayi dan yasan meke damunsa ko da be faɗa masa ba abokin nasa ya karasa ya cire masa drip din hannun sa yace "inaga Daddy wannan ya isa sai muga zuwa anjima ya jikin nasa tukun sai asan next move din" Daddy ya gƴaɗa masa kai ya kama hannun abokin Rayyan suka fita yace "tunda naga ya samu bacci toh bana so surutun mu ya ɗaga sa dan baya bacci da daddare" Daddy ya karasa maganan cike da damuwa dan be san ya zaiyi da wannan lamarin bane kuma kwata kwata yasan bayi da power addu'an sa shine Allah basa hakurin jurewa da kuma cin wannan jarabawar sannan Allah yaye masa, Colleague ɗin Rayyan yace "ina ga sai in shaa Allah da daddaren na shigo" Daddy ya masa godiya tare suka fita dan be san nema zeyi a gidan ba bayan baki na shigowa anjima. Fatima ta ɗaga kai tana kallon Mummy ta ta shigo mata ko sallaman kirki babu tace "Lafiya dai? Meya faru kuma?" Mummy ta zauna tana maida numfashi tace "kenan kika ganni kinsan ba lafiya bane, hankali na ne ya katse kwanciya gashi ƴan iskan kannan nata ba su da kunya nake gaya miki dan wallahi su suke zuga ita shegiyar uwar Leenan" Aminiyarta dake kallon ta kashe tvn tace "yanzu kuma meya faru? Ke da gidan ki ba zaki ci uwar su bane" Mummy tace "Uhm, ba zaki gane bane, Ni yanzu ki tashi ki shirya mu kara zuwa gun mutumin nan muji ya ake ciki" Aminiyar ta ta sake baki tana kallon ta tace "Wallahi ni rashin hakurin ki ya fara damu na kalli yadda kika wani susuce? Mutumin nan yace muyi hakuri zamu ga aiki da cikawa amma ke kinki sama kanki salama" Mummy tace "Idan kuma aikin beyi ba fah? Kinga fah jibi ne ɗaura auren" Aminiyarta tace "Okay, kina ganin ba zaiyi ba kenan ko?" Mummy ta girgiza kai cike da confusion Aminiyarta ta dafa ta tace "na miki alkawari zaki sha mamakin aikin sa kuwa, just calm down" fitowan Layla daga ɗakin ta yasa duk suka yi shiru ta karasa cikin parlorn tana kallon Mummy ta zauna kan hannun cushion tace "ina wuni, Mummy" Mummy na Murmushi karfin hali tace "Lafiya kalau, fita zaki yi kenan" tana taunan chewing gum tace "Sure" ta kalli uwarta tace "Toh sai na dawo" daga haka ta mike ta ɗaura sun glasses dinta a kanta, suka bita da kallo, wani kalan shiga tayi na fitted gown tasha kitso attached har baya gashi ta wani sako Labombom sannan gyallen ma ba ya fawa tayi ba, rataya shi tayi a gefen kafaɗa bayan fitan ta Fatima ta sauke ajiyan zuciya tace "wallahi Layla kyar take kallon mu, na kosa naga ta bar gidan nan" Mummy tace "Toh yanzun ina zata?" tace "Ohon ta kila wajan kawayen ta ne" Mummy ta jinjina kai ita damuwan ta yafi wannan Aminiyarta tace "yanzu an kawo lefen ne?" Girgiza kai kawai tayi Aminiyarta ta kuma cewa "ina son gaskiya yanzu Rayyan ya fara zuwa wajan Layla, in ma bayi da lokacin hira ne hakan ma ba damuwa ba ce, Ni yanzu gaskiya kiyi wa Daddyn su magana su zo neman auren Layla kuma gaskiya bana son bikin ya wuce wata ɗaya" Mummy tace "wannan fa duk me sauki ne, damuwa na wancan yarinyar ce, muddun komai ya rushe wannan ba me sauki bane ko da 2weeks kike so za'ayi hakan". Niswa ta buɗe dakin nasa ta shiga sannan ta rufe ta tsaya tana kallon sa daga bakin kofar, shi kuma jin an buɗe dakin an shigo kuma beji alamar Mummy bace ko Daddy yasa ya buɗe ido dan kallon wanene, ya buɗe ido yana kallon Niswa da ta kafe sa da ido tun daga bakin kofar alamar menene ya mata da hannu hawaye taji ya taru a idon ta, ba zata juri kallon yayan nata a wannan sabon yanayin ba ta karasa har jikin gadon sa ta durkusa tana kallon sa kamar yadda shima kallon nata yake yi, tace "Yaya nasan saboda Leena zata yi aure yasa kake kwance ko?" ta karasa maganar hawaye na gangaro mata kallon ta yake ba ko kiftawa.....
Assalamu Alaikum, everyone!
Da fatan anyi sallah lafiya? Allah Ubangijin ya maimaita mana, yasa muna cikin bayin sa da yayi wa Rahama, Amin ya hayyu ya qayyum.