Free chapter · Read without an account

23

by Fareeda Abdallah · BA NI DA IKO...

23)

"Ina yini Ramatu."

Hajiya ta gaishe ta, bayan ta ga tunda Ramatun ta zauna ta tsuke fuska ta ƙi cewa komai.

Ƙasa-ƙasa ta kalli Hajiyar ta watsar, kamar baza ta amsa ba. Sai kuma ta ce

"Hajiya barka da dare."

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu. Malam dai sai bin su yake da idanu, a zuciyarsa yake jinjina halin ko wacce daga cikin matan nasa biyu. Da gaske ba banza ba mazaje da yawa idan suka ƙara aure suke juya ma matansu na farko baya, saboda da yawan uwaren gida munanan halayensu yana bayyana ne idan miji ya ƙara aure.

Dubi dai Ramatu, bazai ce kafin ya auro Binta ba sa samun matsala ba, amma tabbas zaman lafiya da fahimtar juna ke tsakaninsu kaso tamanin bisa ɗari. Tunda ya auro Binta kuwa sai ta aro baƙin halaye ta ƙara akan na ta, ko kuwa dama tun farko tana da waɗannan halayen dalili ne bai bayyana su ba? Allah masani. A da can baya da take matarshi ita kaɗai bai san Ramatu da zargi ba, bai san ta da laɓe ba, bai santa da rufe ido ta ƙi karɓan gaskiya ba bayan kuma ga gaskiyar tana gani ƙarara. Bai san Ramatu da rashin haƙuri ba, bai san ta da ɗora ma zuciyarta tsanar mutum haka kawai ba tare da ya yi mata komai ba. A baya kafin auro Binta idan aka ce shi da Ramatu za su tsaya kafaɗa da kafaɗa yana faɗe tana mayar mishi da martani kamar za su ba hammata iska zai iya rantsewa da girman Allah hakan bazai faru ba. Da sauran munanan halaye da yawa waɗanda a da can baya bai san Ramatu da su ba... Kamar dai an canja mishi mata... Kamar an canja Ramatu... Gaba ɗaya kishi ya rufe ma Ramatu ido ta kasa fuskantar gaskiya bayan ga ta nan ƙarara kowa yana gani...

"Kishi hauka ne?"

Zancen zuciyarsa ya fito fili. Idanunsa akan Ramatu.

"Uhmmm! Taya ni tambaya dai Balarabe."

Hajiya ta amshe zancen nashi. Itama idanunta akan Ramatu da take kallonsu idanunta a tsaitsaye babu ko ɗan risinawa.

"Allah ya sani ni kaina ina mamakin sauyawar halayen Ramatu a mafiyawancin lokuta. Kamar dai ba Ramatu matar nan mai haƙuri da masifar Balarabe a can baya ba. Kamar dai ba Ramatu mace mai ladabi da biyayya da gudun ɓacin ran Balarabe a baya ba. Me ya faru Ramatu? Don Allah me ya kawo wannan mummunar sauyin?"

Duk da jikinta ya ɗanyi sanyi da maganganun Hajiya. Ko a fuskarta bata bari sanyin jikinta ya bayyana ba. Ta watsa musu kallon uku saura kwata ta watsar da su, ta tsuke bakinta tsaf! ta ƙi cewa komai.

"Ramatu baki ce komai ba. Don Allah ki ce wani abu mana, yau dai idan zai yiwu ina so mu tattauna don gano bakin zaren, mu samo maslahar da muka daɗe muna fatan samu a zamantakewar aurenku."

Hajiya ta sake faɗin haka muryarta a tausashe.

"Uhmmm!"

Ramatu ta faɗi, sai kuma ta muskuta ta gyatta zama.

"Hajiya kenan! Ai ki bar ma wannan maganar. In dai zancen maslaha kike yi tsakanina da wancan"

Ta nuna Binta da yatsarta manuniya tana taɓe baki, sai kuma ta girgiza kai.

"Baza a taɓa samun maslaha tsakanina da ita a cikin gidannan ba."

Ta sake faɗa a karo na uku.

"Zancen yanayin zamantakewarmu na baya da kike yi kuma ni ɗin ce dai ba wata ba. Yanayin kiɗar ne ya canja, kin ga kuwa dole rawar ma ta canja."

Tana gama faɗin haka ta sake tsuke fuska tamau!

Kafin Hajiya ta amsa mata Malam yayi saurin katse maganar ya sako wacce ta tara su.

"Ina Aliya da Hadiza?"

"Suna ɗaki."

Ta amsa tana kumbura baki.

"Na baro su sunyi barci, tunda ba lafiya ce da su ba."

Ta ƙara bayani don ma kar ya ce dole ta kirawo su.

Kamar ya fahimce ta, sai ya miƙe tsaye ya ce

"Ina zuwa."

Ficewa yayi daga ɗakin da sauri.

Bayan mintuna uku sai ga sallamar Hadiza da Aliya a ƙofar ɗakin Hajiyar. Ƙirjin Ramatu ya buga daram! Nan take ɓacin ranta ya ƙara ninkuwa, ta cika tayi taf! Ƙiris take jira a taɓa ta tayi bindiga.

Ko da aka amsa sallamar su Hadiza suka shiga ɗakin, Malam na biye da su a baya. Hannunsa riƙe da wata zabgegiyar dorina mai baki biyu.

Jikin yaran sai rawa yake yi, har sun zauna kusa da ƙafafun Innarsu ya daka musu tsawa ya ce su koma tsakiyar ɗakin su zauna.

Ko bayan sun zauna a inda ya umarcesu sai zazzare ido suke yi suna kallon Mahaifinsu, tsoro ƙarara a fuskokinsu. Tsakanin jiya da abin ya faru zuwa yau har sunyi zuru-zuru kamar waɗanda sukayi amai da gudawa. Sai idanunsu da suka yi luhu-luhu saboda yawan kuka, har yanzu basu saɓe ba.

"Aliya, Hadiza, tambaya ɗaya zanyi muku bazanyi na biyu ba. A gaban Hajiya, mahaifiyarku da Binta ina so ku faɗi gaskiyar abinda ya faru a makarantarku. Domin na faɗa ma Innarku ta ce sharri ake yi muku, don haka ina so ta ji gaskiyar magana daga bakinku."

Haɗa idanu suka yi, sai kuma suka sauke idanunsu ƙasa, jikinsu a sanyaye. Tun jiya da suka fara dawowa hayyacinsu Innarsu take ta jaddada musu lallai ko me za a yi musu nan gaba kar su kuskura su sake amsa laifin da ake tuhumarsu da shi. Ko da ma ace sun aikata, balle kuma ta san ma abinda suka aikata bai kai wanda ake tuhumarsu da shi ba. Daga jiya har zuwa yau kalaman da take ta jaddada musu kenan, tana ƙara jan kunnensu da yi musu gargaɗi.

Da farko sun amince da maganarta. Amma a yanzu da suka ga wannan doguwar dorina a hannun mahaifinsu, sai tunaninsu ya rabu biyu. Allah ya gani jiya sun daku ba kaɗan ba, har yanzu basu gama warwarewa ba, tsakani da Allah a yanzu baza su so duk wani abu da zai sa a sake taɓa lafiyar jikinsu ba.

Aliya ita ce ta fara buɗe baki kanta a ƙasa take faɗin irin abubuwan da suka aikata, daga bisani Hadiza ta karɓe ta. Suka ƙarasa bayar da labarin cikin kuka, da nuna nadama da da na sani a fili, a ƙarshe suka rufe maganganunsu da neman gafarar Mahaifinsu da Binta, tare da alƙawarin in Allah ya yarda baza su sake cutar da Humaira cikin sani ko rashin sani ba.

Jikin Hajiya ya yi sanyi ƙalau. Ashe ita bata ma ji komai ba daga bakin Malam, sai a yanzu da yaran suka faɗi ire-iren abubuwan da suka aikata da bakinsu ta gane girman al'amarin ya wuce yadda take tsammani.

Ita kanta Binta hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, tun kafin su gama bada labarin ta cusa fuskarta cikin hijabi tana sharɓan kuka. Zuciyarta cike da tausayin Humaira, wato tsarewa ta Allah ce kawai yasa yarinyar ta kawo yanzu basu sabauta ta ba.

Ita kanta Ramatu jikinta ya yi sanyi, bakinta ya mutu murus! Amma da yake ta ƙware a iya ɓoye gaskiyar yanayi ko kaɗan bata bari da na sani ya bayyana a fuskarta ba. Sai ma ta dinga jan wasu ƙananun tsaki tana muskuce-muskuce kamar mai jin fitsari.

"Ramatu yanzu kin yarda? Da kika ji da kunnenki daga bakin ƴaƴan da kike sha ma alwashi?"

Malam ya tambayeta da ɓacin rai a fuskarsa.

Ta ƙi tankawa, sai ma ta kawar da kai gefe ɗaya kamar ba da ita yake yi ba.

Ya aika mata wani mugun kallo, sannan ya dawo da kallonsa kan yaran yana ƙara gyara riƙon bulalar da ke hannunsa.

"A niyyata da farko, bulala hamsin-hamsin zanyi ma ko wacce daga cikinku. Amma albarkacin faɗin gaskiya da kuka yi zanyi muku bulala talatin-talatin, a gadon bayanku. Don haka ku kwanta a nan..."

Hannun da Binta ta ɗaga sama alamun tana so tayi magana ne ya katse shi, su kuwa yaran har sun fara rusa kuka, sai da Malam ya daka musu tsawa sannan suka sassauta muryoyinsu.

"Ya aka yi Binta?"

Malam ya tambayeta.

Gefen fuskarta ta fito da shi ta kalli Malam, ita ma idanunta sun kumbura, kuma sun yi ja saboda kuka da damuwa. Da muryarta da ya ɗashe ta fara magana a hankali

"Don girman Allah, ina roƙa ma yarannan alfarma a gurinku. Hajiya, Malam, a tunanina kaso saba'in cikin ɗari na laifinnan Humaira aka yi ma, to a matsayina na mahaifiyar Humaira zan ari bakinta in ci mata albasa..."

Ta maida numfashi, sannan ta cigaba da magana

"Na yafe musu laifin da suka aikata ma ƴata Humaira. Ina roƙon Allah ya yafe musu. Sannan don Allah Malam in dai zan baka shawara ka ji a ganina bayan dukan da aka yi ma yarannan a makaranta ayi haƙuri, a yafe musu kar a sake dukansu a gida.

Ina daga cikin iyayen da suke ganin duka ba shi ne abu mafi sauri wajen ladabtar da yaro ba. A matsayinku na iyayensu da suke jin maganarku fiye da kowa, da ke Hajiya matsayinki na kakarsu ku ja su a jiki, kuyi musu nasiha, ku nunar musu illar abinda suka aikata ga ƴar'uwarsu.

Hajiya ke ma kiyi haƙuri, don Allah ki saka baki, ayi ma yarannan haƙuri, a yafe musu. A madadin mayar da maganar rayuka suna ƙara ɓaci godiya ga Allah ya kamata muyi da ya taƙaita al'amarin, ya tsare Humaira daga sharrinsu. Su kuma mu cigaba da yi musu addu'ar Allah ya shirye su."

Wannan doguwar magana da Binta tayi mai cike da nutsuwa, tausasa harshe, iya kalami, shi ya hana Malam ɗaukar matakin da yayi niyya akan su Aliya. Hajiya ma jikinta yayi sanyi sosai, a fili ta ƙara jinjina kaifin basira da hangen nesa irinna Binta. Haka tai ta saka mata albarka har ta fice daga ɗakin, bayan ta basu izurin barin Humaira da ke zazzaɓi a ɗaki ita kaɗai, duk da dai barci take yi.

Ɗakin Hajiya ya rage daga Ramatu da ƴaƴanta, sai Malam da Hajiya. Shiru ya ratsa tsakaninsu na mintuna biyu. Malam ne ya fara kore shirun da cewa

"Hajiya kin ga banbanci ɗaya da ke tsakanin Ramatu da Binta ko?"

"Uhmmm! Na gani Balarabe."

Hajiya ta amsa da sanyin murya. Idanunta akan Ramatu tana kallonta da tausayi, don tsakani da Allah sai ta ji ta fara tausayin Ramatun, saboda ta ɓangarori da dama Binta ta kere mata, musamman ta ɓangaren iya mu'amala.

"To Hajiya waɗannan banbance-banbancen da ke tsakaninsu su ne abubuwan da a shekarun baya nake yawan ɓata lokaci ina nusar da Ramatu akan ta gyara, ta gyara, amma kullum idan na nufi gabas ita sai ta nufi yamma. Ga gaskiya ƙarara sai ta rufe ido ta juya min zance, kullum maganarta shi ne Binta ta mallake ni, ta gama da ni, ta wanke ta bani na sha. To Hajiya da irin waɗannan halayen na Binta ta ya baza ta mallakeni babu boka babu Malam ba?"

"Uhmmm! Allah ya kyauta."

Hajiya ta faɗa da damuwa a fuskarta.

Sai da safe Malam yayi mata ya fice daga ɗakin.

Yana fita Ramatu ta ja tsaki, ta bi bayansa da harara kamar idanuwanta za su faɗo. Har ta miƙe za ta fita Hajiya ta dakatar da ita.

Nasiha mai tsawo Hajiya ta ɗauki lokaci tana yi mata, ta buga mata misalai kala-kala na matakan da ake bi aci ribar zaman aure babu boka babu Malam. Haka tayi ta zaƙulo kura-kuran Ramatun tana buga mata misali da su, da cewa da ba haka tayi ba, da abu kaza tayi da ta fi cin riba. Sai da ta tabbatar nasihunta sun ratsa Ramatu, har ta fara matsar ƙwallah.

Sannan ta mayar da akalar nasiha da faɗan zuwa kan Aliya da Hadiza. Suma sai da tayi musu tas! Jikinsu yai sanyi ƙalau, sannan ta sallamesu.

Gaba ɗayansu ukun godiya suka yi mata, sannan suka fice daga ɗakin.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol