Free chapter 路 Read without an account

PAGE 46

by Aminatu Ibrahim 路 GANIN IDO

GANIN IDO 馃馃

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHIM

OUM-AMEER

*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671

FREE-BOOK

PAGE 46

Tun da muka dawo tsawon sati biyu kenan amma na rasa gane miye abin da yake damun mijina. Ko ka蓷an bai canja min daga irin yan da yake kulawa dani da kuma nuna min soyayya ba, hasalima 茩aunarsa da kulawarsa a gareni 茩aruwa suka yi wanda nike jin yanzu a duniya kamar nafi kowace irin mace sa'a. Duk yan da zai jima a wurin aiki 茩arfe shidda na yamma a gida take masa komai yawan ayyukan da yake da su kuwa. Idan kuma ya dawo, zamu kasance a tare wanda sallah ka蓷ai ke rabamu, sannan idan 茩arfe takwas ta yi na dare, to zai ta蓳a aiki na hour 蓷aya kacal sannan ya ajiye sai kuma gobe.

Sai dai kuma, Komai da yake yi sam babu walwala a ciki tunda muka dawo, idan na tambayesa abin da yake damunsa sai dai ya yi murmushi ya kalallameni yace min ba komai har sai na yarda a raina da cewa ba komai 蓷in.

Yau ma koda na farka har ya gama shirin fita. A gaggauce na diro daga kan gadon cikin nuna rashin jinda蓷i na ce.

"Eyyah! Please I'm sorry...bacci ne ya kwasheni sosai har ban san cewa ka gama shiryawa ba.."

Da sauri ya ri茩o tsintsiyar hannuna a hankali ya tura ni cikin jikin sa ya rungumeni na 蓷an lokaci sannan ya sumbaci gefen Wuyana wanda na tabbar hakan yana matu茩ar yi masa da蓷i sannan ya janye yana mai kallon cikin 茩wayar idanuna ya yi mini murmushin nan nasa mai sanyi ya ce.

"Tun da yanzu Bibina ta rage yin raki ai ni kam komai ya yi daidai. Kwalliya ta biya ku蓷in sabulu..."

Cikin 茩irjinsa na mayar da fuskata domin ni dai ba zan iya kallon sa da wannan abin kunyar da yake fa蓷a ba. Mutum duk yan da ake nema a faranta masa kuma sai ya nemi yanda zai mayar da shi abin tsokana.

"Madam Amima ta riga ta gabatar min da breakfast na ci kada ki damu...蓷auko Hijab 蓷in ki ki rakani mota."

Juyawa na yi na 蓷auko na sanya muka fito hannu na a cikin nasa har wurin jerin gwanon motocinsa. Su Sharath na ganina suka shiga gaishe ni kamar yanda suka saba inda sun yi tozali dani.

Bayan ya shiga nima sai na shiga tare da zaunawa na ri茩o hannunsa ina murmusawa ba tare da nace komai ba.

"Tare zamu tafi office 蓷in ne?"

Girgiza kaina na yi alamar a a, sannan ya sake cewa.

"To ko na fasa fitar ne?"

Nan ma girgixa kaina na sake yi tare da 蓷agowa na kallesa ina mai karyar da muryata ba tare da na saki hannun nasa ba, na ce.

"Abincin da madam Amima ta ajiye ko ka蓷an baka ta蓳a ba, na fahimci hakan ne daga yanda aka saba jera kayan komai ba'a ta蓳a ba a ciki. A '拼an kwanakin nan kwana kake a zaune,inma kana sallah ko kuma kana kwance idanuwanka a bu蓷e,hakan yasa baka samun ishashshen bacci wanda hatta idanuwanka idan na kalla ina gane hakan, kuma sam hakan baya min da蓷i. Yana sakani a damuwa nima. Dan Allah idan har ni ce nake maka wani abun wanda baya maka da蓷i dan Allah ka gayamin, idan ma wani ne can a waje, ko kuma a wurin aikin ka ka sanar dani. Idan na bayar da shawara ne sai na baka, idan kuma ba hurumina ba ne sai na taya ka da addu'a, duk da cewa kana cikin addu'a ta....."

Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya bu蓷e su a kaina yana mai jin yanda zuciyarsa ke masa wani irin sanyi tamkar ana zuba masa ruwan 茩an茩ara akan yanda kalamai na ke shiga kunnuwansa suna yin tasiri...yarinya 茩arama, amma idan ta yi magana tamkar wata babbar mace. Hankali da baiwar magana ba lallai dole sai mai tsagwaron shekaru ba. Idan Allah ya datar da kai mata ta gari ka huta da duk wata damuwar duniya, domin daga lokacin da ka samu mata ta gari to tabbas kaso saba'in na daga cikin matsalolin rayuwarka za su yi 茩aura su canza she茩a yayin da sukuninka zai 茩ara ya蓷uwa. Yarinya 茩arama cikin 茩an茩anin lokaci ta iya fahimtarsa fiye da kowa...akan me Jadda za ta uzzura akan wani dalilinsu wanda ba komai a ciki sai son zuciya? Miye ta yi masa da zafi haka alhali ko shekara ba su rufa ba ace wai ya 茩ara mata? Ya fa san kishin mata duk da cewa bai ta蓳a yin ko 蓷aya ba. Gidan abokin sa Jalal kullum a cikin tashin hankali suke da rashin jituwa tun daga lokacin da ya yi aure na biyu. Haka ma abokin sa Engineer Abdul-qadeer matan sa hu蓷u amma gaba蓷ayan su 蓷aya ce kawai ta 茩warai mai son a zauna lafiya, sauran kullum cikin tashin hankali suke duk da cewa ba'a gida 蓷aya suke ba ma, amma kullum cikin 茩orafi da nuna cewa yafi bai wa waccan kulawa fiye da waccan. Sannan nan kusa ma ga Labibarsa...ba don Allah ya yi ta mai sanyin hali da ha茩uri ba da matar Mijinta ta hana mata zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya tuna ranar da Raudahr sa ta mutu...matar nan har yanzu ya kasa manta yanda ta dinga farin ciki tana ta annushuwa kamar wacce aka cewa 茩aruwar haihuwa aka samu...Gidan Ubaid ne kawai zai ce a gidan ana zaman lafiya a tsakanin matan sa wanda komai na su iri 蓷aya tamkar ba kishiyoyi ba. To tunda har bai san abin da gobe za ta yi ba, ba lallai ya samu haka a gidan nasa ba...Duk wannan tunanin da yake ta yi amsa 蓷aya yake samu, cewa idan yace zai cika musu muradinsu to tabbas Bibinsa ba za ta kasance a farin ciki ba. Ita ce fa wacce ta sadaukar da kanta da rayuwarta don kawai taga cewa ta cecesa ba tare da ma ta ta蓳a ganin sa ba. Duk da irin tazarar shekarun da ke tsakanin su, da ta gansa hakan bai sare mata gwiwa ba, a haka take son sa wanda a da kokonta yake yanzu kuma daga irin mu'amalar su ya gasgata irin 茩aunar da take masa...

Kai na na mayar a hankali na kwantar akan 茩irjinsa ganin ya yi shiru yana kallona,murya a 茩asa sosai na ce.

"Kada mu ce zamu ri茩a matsawa kanmu da zukatanmu akan matsalolin duniya da rayuwa domin Allah ma bai 蓷ora mana ba. Idan kana damuwa hakan yana ta蓳ani Mijina...ba zan matsa maka ba idan har ba ka so ka sanar dani amma dan Allah ka sassauta."

Hannayensa na ji a jikina ya saka ya kewaye ni a hankali ya 蓷ora fuskar sa akan gefen wuyana. Mun jima a haka tsawon lokaci sannan daga 茩arshe ya 蓷agoni yana kallon fuskata ya ce.

" Thank you Bibi...Allah ya yi miki albarka. Allah ya 茩ara mana zaman lafiya da kwanciyar ya bani ikon faranta miki a koda yaushe...In Sha Allahu na yi miki al茩awarin ba zan 茩ara damuwa da komai ba."

Murmushi na masa ina mai jinjina kai na nace.

"Amin Yah Allah. Allah ya tsare ka, ya kai min lafiya ya dawo da kai lafiya..."

"Amin. Suhaib ya sanar mini jiya cewa zai zo. To na ce ya bari sai na sanar miki tukunna..."

A mamakance na ce.

"What? Sai ka sanar mini fa ka ce?"

"Yeah! Ai kece mai gida. Yanda kika ce haka za'a yi."

Ina wani irin murmushi na jinjina masa kaina na ce.

"To na amince ya zo dan Allah...kada fa kasa Hairi ta yi fushi dani..."

Dariya ya yi ya ce.

"Ba za ta yi ba ai. Domin ta san cewa you won't hurt her.."

"Allah ya tsare, bare na je kada na saka ka kayi latti."

Daga haka na sauka da kaina na rufe masa motar sannan drivernsa ya shiga suka wuce.

Har na shige ciki ban daina murmushi ba, hakan yasa ni ban ma lura da fitowar Hairiyyar ba sai da naji tana dariya a bayana. Waigowa na yi ina 茩ara fa蓷a蓷a murmushina na ce.

"Miye kike a nan 蓷in??"

Tana dariya ta ce.

"Soyayya da蓷i ko Aunty Beenafah? Kuna son juna sosai...Daddy yana matu茩ar 茩aunar ki."

Bansan lokacin da wani irin kyakkyawan murmushi ya su蓳uce min ba sannan na jinjina mata kaina na ce.

"Ni ma haka Hairi...ina matu茩ar 茩aunarsa a raina..."

Tana wani irin blushing ta jinjina Kanta ta ce.

"Ina jin wani abu makamancin haka a kan Suhaib Aunty Beenafah...sati biyu kacal! Amma soyayya nema take ta zautar da ni..."

Dariya na fashe da ita cikin sigar zolaya na ce.

"Ga Soyayya ga exams jibi. Wanne za'a fasa daga ciki? Idan kika za蓳i exams Suhaib zai ji wani iri, idan kuma kika za蓳i Suhaib kika bari soyyaya ta saka kika fa蓷i exams Daddy zai ci 茩aniyar mutum..."

Dariya ta fashe da ita tana wani girgiza kai ta ce.

"Amma dai gaskiya Aunty Beenafah kin min 蓷aya...shi ne za ki bini da bad thought..maimakon ki 茩arfafa ni? Soyayyar nan fa yanzu na fara ta..."

"Da gaske?"

Na tambaye ta ina mai bin ta da wani irin kallon mamaki domin sai nake jin kamar ma ban yarda da ba ace wai bata ta蓳a yin soyayya ba.

"Wallahy Saurayina guda 蓷aya ne Khaleel, kuma kullum muyi fa蓷a mu shirya muyi fa蓷a mu shirya haka muke. Duk da cewa muna da buri watarana muga munyi aure...to Amma shigowar Suhaib a cikin rayuwata, yanayin daban ne Aunty Beenafah, ina jin wasu abubuwa a raina wanda ban ta蓳a ji akan Khaleel ba..."

Jinjina kaina na yi ina murmusawa na ce.

" Hakan shi ne mafi alheri a gare ki In Sha Allah. Allah dai ya nuna mana lokaci lafiya. Shin nan da shekara biyu aka ce ko?"

Bata san lokacin da ta maka min wata uwar harara ba tace.

" Wai ma! Kafin azumin nan fa, shekaranjiya na ji Daddy yana magana da Baba Ustaz yana shaida masa..."

Waro ido na yi ina dariya na ce.

"Kambu! Yau Hairi ni za ki harara akan Suhaib? Ya yi kyau! Bari na kira Daddy na fa蓷a masa.."

Da gudu ta fa蓷o jikina tana mai rirri茩eni cike da magiya tana dariya ta ce.

" Na shiga uku! Wai daman hararen ki na yi Mummy? Please forgive me...ba zan sake ba. Ba laifina ba ne laifin soyayyar IG SUHAIB ce....ki yi hak'uri dan Allah...Yo idan kika fa蓷a wa Daddy ai na san daga yau sai dai na nemi wani gidan uban ba wannan ba..."

Dariya muka sake fashewa da Ita sannan na ce.

" To na ji. Sake ni naje na yi wanka. Kin ci abinci? "

Girgixa kanta ta yi tana mai janye jikinta daga nawa ta ce.

" Nima tashina kenan, wanka kawai na yi."

"Ok...bari na yi wanka na fito."

"To miye abin da za'a yi wa Suhaib 蓷in?"

Waigowa na yi na ce.

"Na me kenan?"

"abinci haka...yanda za'a tarbeshi"

Girgiza kaina na yi ina dariya na ce.

"Bari na yi wanka na fito, sai mu shiga kitchen 蓷in mu gani."

"OK!"

*******

Gefen su Aunty Labiba kuwa, koda suka koma gida har Ziza tana gidan, ta dawo kamar yanda Emraan ya sanar mata cewa ta shirya ta dawo gida kafin ya iso.

Sun yi matu茩ar ka蓷uwa da suka ji Ziza na jajanta musu abin da ya faru. Wato Hajiya bata ji duk abin da ake fa蓷a mata ba? Idan ba shi ba miye na zuwa ta fa蓷awa Ziza wannan abun dan Allah?

Duk yanda suka nuna mata rashin jin da蓷insu ita ko ka蓷an hakan bai dame ta ba, domin a yanzu ta yarda cewa fa蓷in gaskiya da kuma tsayawa akan gaskiya yafi komai da蓷i da sa mutum ya kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Ziza ma ai yanzu ita 蓷in cikin dangi take, ya kamata duk abin da ake ciki a ri茩a sanar mata domin 蓳oye-蓳oye ba shi da wani amfani.

Bayan Nadeeyah ta koma Kaduna da kwana Biyu Labiba ta zo gidan sanadiyyar kiranta da Emraan ya yi.

Tana shigowa ta tarar da su zaune, Hajiya, Ziza da kuma Emraan 蓷in.

Zaunawa ta yi ta gaishe da Hajiya sannan suka gaisa da Ziza ta kalli Emraan ta ce.

"Ina fata lafiya?"

Jinjina kansa ya yi yana mai yin 蓷an guntun murmushi ya ce.

"Lafiya 茩alau. Kawai ina so muyi wata Magana ce mai muhimmanci....and..i call the presence of you ne don ku zama shaida akan maganganuna....Tun jiya da na shaidawa Ziza zancen aurena ta hana min sukuni take ta tashin hankali. To abin da nake so ku ji ku kuma shaida...wallahy tallahy ba ta isa ta hanani yin abin da raina yake so ba. Zan 茩ara maimaitawa a gaban ku. Zan yi aure ba don na gaji da ita ba, zan yi aure ba don tana min wani laifin ba, ina son ta. Amma kuma ba shi zai hanani 茩ara aure ba. Ku ja mata kunne ta kiyaye, bani da niyyar cutarwa a gareta, Idan ta bani ha蓷in kai lafiya 茩alau za mu zauna kamar yanda Suwara ta bani kalaman ta..."

Wani irin kuka ne mai 茩arfi ya 茩wace mata jin sunan Suwara da ya ambata wanda tun a daren jiya wannan sunan ya tsaya mata a 茩ahon zuciya. Bata san lokacin da ta shiga Girgixa kanta ba tana fa蓷in.

" Wallahy Hajiya Emraan baya sona. Ina murna cewa tun da ya rasa Beenafah shi kenan ya ha茩ura, yanzu kawai rana tsaka kuma ya dawo min da wani zance na auren wata banza er Sudan..."

"Ziza ki daina kiran er uwata da banza! Tun Jiya na yi warning na ki akan ki kiyaye kalaman ki a Kanta domin Ita 蓷in er uwa ta ce...Ziza idan fa kin so zaman lafiya zamu zauna mu ma fi ruwa zaman lafiya. Idan kuma tashin hankali kike nema to sai dai ki tafi can gidanku ki 茦arata. Sannan kada ki manta...wan can lokacin da kika tafi gida, kin dawo gidan nan ne bayan Yaya Mohaa ya dawo dake...to kuma a yanzu ki fahimta...ita wannan 蓷in 茩anwarsa ce. Ba lallai ya tafi don dawowa da ke ba. Idan kika sake tafiya da sunan ya ji, ki 蓷auka cewa mun rabu kenan na har abada, domin ni ba zan 蓷auki wannan ba..."

Kallon shi Aunty Labiba ta yi cikin tsantsar mamaki ta ce.

" Haba Emraan! Miyasa za ka nemi tsaurara kalaman ka haka? Ita 蓷in fa macece, kuma kishi gaskiya ne...ko ma miye ai dai kana 蓷aga mata 茩afa ko don yanayin ta tunda kasan ciki ne da ita...wai miyasa ku maza baku da adalci ne wani lokacin..."

Cikin jin wani irin 蓳acin rai ya shiga jinjina kansa yana fa蓷in.

" Shin yanzu Labiba kina goyon bayanta ne ni kuma kina 蓷ora min laifi ko ya ya?"

" Eh! Idan ma hakan ka 蓷auka Hakane! Idan har ka kira mu ne a matsayin na gaba da ku domin neman maslaha ai ba cancanta ka ri茩a magama irin haka ba. Kishiya fa za ka mata, to sai ka dake ta ka hana ta kuka...ka bari abi komai a sannu mana.."

Mi茩ewa ya yi yana wani irin huci tamkar wani kumurcin maciji akan 蓳acin rai ya fice ya bar musu parlourn.

Itama Ziza yun茩urawa ta yi a hankali ta tashi ta wuce 蓷akinta ta bar su nan su biyu tana ta kuka. Abu ne ya game mata goma da ashirin, gidan Iyayenta sun ha蓷e mata kai nan ma sun ha蓷e mata kai babu mai ganin laifin shi sai na ta ake gani saboda tsabar son zuciya.

Kallonta ta mayar gun Hajiya tana fa蓷in.

" Hajiya wai kin yi shiru ba ki ce komai ba?"

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta ce.

" To Labiba mi zance? Emraan ya 茩i ya saurareni, sannan itama Ziza ta茩i ta kwantar da hankalinta. Shin duk abin da zaman lafiya bai bayar ba dan Allah tashin hankali na bayar da shi? Tun a wancan lokacin da ya ke neman Beenafah nake ta tausar mata zuciya bata saurare ni ba. Idan tace ba za ta iya ha蓷a miji da Beenafah fa to ita wannan 蓷in miye aibinta? Sam bana son wani abin da zai kawo musu 蓳araka a tsakanin auren su, to amma dukkan su babu wanda za ki fa蓷a masa ya ji."

" A a kam! Bari na je na yi mata magana.."

Tana gama fa蓷ar haka ta tashi ta bita har sashenda take inda ta cimma ta zaune a 茩asa ta mi茩e 茩afafunta sannan ta 蓷ora kanta akan gefen kujera tana kuka.

Zaunawa ta yi gefen ta a hankali ta kira sunanta.

茒agowa ta yi ta kalle ta kawai ba tare da ta amsa ba.

"Ki na ji ko Ziza...ita fa rayuwar nan cike take da 茩alubale akoda yaushe...茩arfin imaninmu da ha茩urin mu shi ne zai 蓷oramu akan ta har mukai ga yin galaba a kanta Watarana. Kin auri Emraan akan kina sonsa kamar yanda shima ya aure ki akan yana son ki...kuma har yau har gobe,har abada nasan a wannan tafarkin kuke so ku kasance har zuwa numfashinku na 茩arshe. Tun da kuke da shi ba ku ta蓳a samun wata matsala ba, domin kuna son juna kuma kuna bin hanyoyi domin kiyayewa. To ina so kisan cewa aure a wurin namiji zuwa yake, lokaci ne kuma idan har hakan ya kasance to ki yarda cewa yana daga cikin zanen 茩addarar sa......Wani, da mata 蓷aya yake rayuwa har ya mutu, wani da mata biyu, wani uku wani kuma hu蓷u. Duk cikin su babu wanda Allah yace ya sa蓳a ko ya kauce hanya. Tun da har kika ga cewa mijin ki ya za蓳i cewa ya auri Wata bayan ke, to ki zama mai ha茩uri ki amshi wannan 茩addarar. Koda ace ran ki baya so ki yi ha茩uri ki bai wa zuciyar ki magana. Ki daina 蓷aga masa hankali kina 蓷agawa kan ki. Idan fa suna cikin giyar neman auren nan wallahy ko mutuwa za ki yi ko ka蓷an ba zai ji cewa zai iya fasawa ba. Ke a lokacin da kike hauka shi a lokacin ji yake tamkar kina 茩ara tura sa ne cewa yaje ya yi. Bari na fa蓷a miki wani sirrin da baki san da shi ba Ziza. Idan Kika nuna kin yi farin ciki kuma kin amsa hannu biyu, wallahy tallahy kunyar ki zai ri茩a ji kuma za ki 茩ara miki girma da daraja a idonsa, duk abin da zai yi sai ki ga sai ya nemi shawarar ki, duk abinda kika ce shi za'a yi. Amma idan kika nuna hauka da rashin ha茩uri, to shi kuma a lokacin zai dinga fito miki da hanyoyin na rashin mutunci domin kawai ya ga kin 茦untata...dan Allah Ziza ba don ni ba, don Allah Ziza ba don Emraan yana 茩anina ba. Ki yi hak'uri ki kwantar da hankalinki ki bari ku zauna lafiya. Kin ce bakya son kisantaka da Beenafah, yanzu ma kince bakya so da wannan, tun yana neman abin 茩warai har sai kin sa ya kai watarana ga nemo miki abin da zai fi 茩arfin ki."

Jinjina kanta ta yi tare da share Hawayenta ta ce.

" Na gode sosai Aunty Labiba. In Sha Allahu zan gwada amfani da wannan shawarar in gani ko zan iya.."

Cike da murmushin nasara ta jinjina Kanta ta ce.

" Na gode sosai da kika fahimce ni. Allah ya baku ha茩uri ya baku zaman lafiya...Ziza! Ba wai ina fa蓷a miki haka ne don GANIN IDON ki ba, har cikin zuciyata nake fa蓷a miki wa蓷an nan kalaman, domin kamar yanda kike kallona a matsayin dangin mijinki, nima 蓷in dangin mijin wasu ce, idan har har na cutar da ke, to nima zan iya ha蓷uwa da kalar nawa 茩alubalen wurin nawa dangin mijin."

Daga haka ta mi茩e ta fice daga 蓷akin ta koma tana ta kiran Emraan a waya amma bata samun sa. Hakan yasa dole ta hak'ura ta fita kitchen wurin su Munira.

Suna ganin ta suka ta so suka gaishe da ita sannan ta ce.

" Kun kaiwa Ziza abinci yau kuwa?"

Girgiza kai Haulatu ta yi tace.

"A'a. Bamu kai mata 蓷aki ba, mun dai jera a table..."

"To ku ha蓷a mata please ku kai mata a 蓷aki. Kuma ku ri茩a lalla蓳awa da ita musamman kunga yanayinta a yanzu dole sai ha茩uri."

"In Sha Allahu Aunty."

Murmushi ta yi tana kallon Munira ta ce.

"Munira har yau baki ta蓳a tambayata 茩awar ki ba."

Ai kuwa, tamkar ta sosa mata wurin da yake mata 茩ai茩ayi, bakinta har yana rawa wurin furta.

"Wallahy Aunty Labiba Beenafah tana ranmu, mun kasa mantawa da ita, kuma bamu san a ina take ba. Ranar ma da muka matsawa Oga Sule shine ya 蓷aukemu ya kaimu gidan su amma sai aka ce mana sun tashi daga nan."

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Tabbas sun tashi. Amma ta yi aure ta auri Daddy, tana zaune a Dubai yanzu haka a tare da shi...."

Tamkar idanuwansu za su zazzago su fa蓷o 茩asa, haka suka ri茩a kallonta da wani irin ma蓷aukakin mamakin da ya hana musu ma yin magana.

"In Sha Allahu watarana za su zo, za ku ganta."

Cikin nuna farin ciki Munira tace.

"Allah ya 茩addara ya nuna mana wannan lokacin...hmm! Allah mai iko da Buwaya! Yanzu Beenafah ita ce ashe ta auri Daddy? Allah ya sanya alheri da albarka ya bada zaman lafiya."

"Amin."

Juyawa ta yi ta koma ciki yayin da suka shiga yin aikin da ta basu suna yi suna firar Beenafah cike da farin cikin irin mijin da ta samu. Tambayar kan su suka shiga yi cewa ko ya akayi hakan ta kasance?

*******

Gefen su Daddy kuwa. A hankali ya shiga warwarewa lafiya na samuwa har ya murmure baki 蓷aya.

Sai dai kuma, abubuwa sun juye musu fiye da tunaninsu, komai ya lalace musu wanda hatta abincin da za su ci, Salman ne da Ahlan ke 蓷auke da nauyin abincin su da ma wasu sauran bu茩atocin rayuwa.

Humaida ma sun samu wata private school wacce ba mai tsada sosai ba suka mayar da ita wanda babu watarana da za ta zo ba tare da ta yi kuka ba.

Aunty Aysha tana nan a tare dasu bata koma ba, amma Ita Hassana daman ba su jima da dawowa Gusau 蓷in ba ta koma garin Mijinta, amma kullum tana biye da su da labarin duk wani motsin su.

Husaina kuma tana nan tare da Fahil wanda jira suke Daddy ya 茩ara warwarewa ya turo magabatansa.

Rayuwar su yanzu gaba蓷aya ta yi sanyi sosai kamar ba su ba. Musamman Daddy da ya koma wani abin tausayi kullum yana ri茩e da carbi a hannun sa yana tasbihi, daga zaran ka kalleshi sau 蓷aya sai ya baka tausayi. Aysha da Husaina sune ke ta hidima da su. Yau ma Aysha na zaune  a bakin rijiya tana wanke musu kayan su suna firar Fahil da Husaina sai ga Mummy ta fito daga 蓷aki ta kalli Aysha ta ce.

"Aysha!"

茒agowa ta yi ta Kalleta ta ce.

"Na'am Mummy."

茒an matsowa ta yi dab da Ita suna kallon juna ta ce.

"Aysha ya kamata ki zo ki shirya ki koma gidan mijinki haka nan. Kada mu zo muyi abu har na wuce hankali. Alhamdulillah! Alhaji dai ya samu sau茩i kuma abubuwa sun natsa mana. Kinga kin baro shi da Baffa tsawon lokacin nan, ya kamata ki koma gida hakanan..."

Jinjina kanta ta yi ta ce.

" Daman munyi maganar da Ahlan shekaranjiya, ya ce min yaushe zan dawo tunda Daddy ya samu sau茩i. Shi ne nace ya saka lokaci, ya ce min to in shirya 茩arshen satin nan sai na koma."

"To ba laifi. Allah ya nuna mana lokacin lafiya."

Daddy wanda tun da ya fita sallar asuba bai dawo ba sai yanxu sha 蓷aya na safe. Karo ya ci da Babansu Ya Jafaru wanda har wayau ya kasa sakewa da shi. Shi ne farkon wanda ya fara mi茩a masa hannu domin su gaisa.

Bayan sun gaisa ne Baba Habibun ya kalle shi ya ce.

"Ya jikin?"

"Jiki Alhamdulillah malam Habibu mun godewa Allah.."

"To, Allah ya 茩ara afuwa.."

"Amin, Na gode."

Har ya juya da nufin tafiya ya ji muryar Daddyn a hankali yana fa蓷in.

"Malam Habibu..."

Waigowa Baba ya yi ya ce.

"Na'am"

"Amm...Dan Allah na ce har yanzu ba ka ji labarin inda Hajiya Mulaifa take ba? Dan Allah idan ka sani ka taimakeni ka fa蓷a mini, akwai abubuwa masu muhimmanci da nake so in sanar da ita dan Allah.."

A kaikaice Baba Habibu yake kallonsa har ya dasa aya. Girgiza kansa ya yi kai tsaye ya ce.

" Gaskiya dai bani da labarin ta kamar yanda na saba fa蓷a maka...Allah ya bayyanar maka da ita, shi ne addu'a ta a gareka.."

Cike da karyewar zuciya ya ce.

" To amin Ya Allah Malam Habibu, na gode sosai."

Hanya Baba Habibun ya kama wanda yana tafiya yana gunguni a ransa, Sam dawowar wannan mutumin wannan unguwar bai yi masa da蓷i ba, domin wallahy baya ma son ganin sa. Shiyasa ya hana Maman Fakiha hul蓷a da su, kuma ya garga蓷eta akan ri茩e sirrin inda Ammie take domin ita da kanta ta neme su alfarma da cewa ko a mafarki kada su ta蓳a fa蓷awa su Daddy cewa ga inda take kamar yanda suka yi al茩awari da Aysha.

Yana batun bu蓷e 茩ofar gidansa ya ji ana yi masa magana ta bayan sa.

Koda ya waigo sai ya ga ashe wasu mutane ne guda biyu.

Bayan ya basu hannu sun gaisa ne 蓷aya daga cikin su ya mi茩a masa takarda.

Da sauri Daddy ya 蓷aga masa hannu ya ce.

"Dan Allah na ro茩eku da ku fa蓷amin miye abin da wannan takarda ta 茩unsa kai tsaye kada ku tsaya wahalar da ni."

Ajiyar zuciya mai shirin mi茩a masa takardar ya sauke sannan ya ce.

"To a gaskiya...wannan 蓷in takardar sammaci ce daga kotu da aka shigar da kai 茩ara domin tuhumarka akan dukiyar Hajiya Mulaifa da ta '拼a'拼anta da kuma tauye musu ha茩茩i na tsawon shekaru..."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Abin da ya iya furta wa kenan yana mai girgiza kansa cike da damuwa.

Hannu ya mi茩a ya kar蓳a yana mai yi musu godiya sannan ya juya ya shiga gidan.

Ganin irin yanayin da yake ciki lokaci 蓷aya ya 蓷aga musu hankali musamman Mummy. Sai fa蓷in take.

" Alhaji Lafiya kuwa?"

Girgiza kansa ya shiga yi hankali tashe ya ce.

"Ba lafiya kam! Wallahy ba lafiya Zaliha. Takardar sammaci ce daga kotu, Mulaifa ta shigar dani 茩ara, za ta yi shari'a da ni...kuma a wannan karon Zaliha...daga ni har ke, tabbas kashinmu ya bushe"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Mummyn ta fa蓷a tana mai 蓷ora hannun ta a kai ta fashe da wani irin kuka.

Da sauri Aysha ta kar蓳i takardar ta shiga karantawa tamkar idanuwanta za su zazzago. Sai da ta karantar takardar yakai sau goma sannan ta mi茩e da gudu ta fa蓷a 蓷aki ta 蓷auko wayarta jiki na rawa ta kira numbern Ammie. Tana 蓷agawa ba ta jira komai ba ta fara mata wata irin magiya tana kuka tana fa蓷in.

"Dan Allah Ammie...don girman Allah, don 茩aunar ki ga fiyayyen halitta ki yi ha茩uri Ammie ba don halin su ba ki yafe musu? Na sani, ni ban isa ba....ban cancanta na tsaya a gabanki domin nema musu gafara ba...saboda Allah da za ki yi...Ha茩i茩a sun aikata miki kuskure mafi girman Kuskure kuma sun cutar da ke da '拼a' 拼anki....ki taimaka ko don mu ki yafe musu ki janye 茩arar nan...ko a yanzu Ammie sun jiya a jikin su kuma sun san ke ce da Riba.."

Daga can 蓳angaren Ammie, cikin wani irin mamaki ta ce.

" Wai ni kam Aysha wannan magiyar kam duk ta miye? Ban fahimci abin da kike magana a kai ba..."

Cikin wasu irin hawayen ba茩in ciki ta ce.

"Ammie 茩arar da kika shigar akan Daddy nake magana.."

"茦ara kuma Aysha??"

Gya蓷a kanta ta yi tamkar tana a gabanta ta ce.

"Eh Ammie! Dan Allah Ammie ki yi ha茩uri ki yafe musu...Ga ni na dur茩usa akan gwiwoyina dan Allah Ki yafe musu..."

Cikin zallar mamaki ta ce.

"Aysha ni fa ban shigar da Alhaji Mudassir kowace irin 茩ara ba. Ban san mi kike magana akai ba..."

Cikin rashin yarda da maganarta ta sake girgiza kanta ta ce.

"A a Ammie! kin shigar da 茩ara, domin ga takardar sammaci nan zuwa kotu an kawo wa Daddy...dan Allah Ammie..."

"Aysha!"

Tana share hawayenta a sanyaye ta amsa ta ce.

"Na'am Ammie.."

"Ni ban shigar da kowa 茩ara a kotu ba. Duk abin da ba zan iyayinsa a GANIN IDON ki ba, har abada ba zan je bayan ki na aikata shi ba. Saboda haka, magana 蓷aya ce kuma ita ce ta gaskiya, ban shigar da iyayen ki kowace 茩ara ba."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Abin da ta maimaita kenan har sau biyu sannan daga 茩arshe ta yanke kiran ta lalubo numbern Beenafah ta kira. Bayan sun gaisa ne Daga can 蓳angaren Beenafah ta ce.

"Aunty Aysha Lafiya kuwa? Na ji muryarki ta yi wani iri.."

"Beenafah ba lafiya ba..."

Nan ta yi min bayani kamar yanda ta yiwa Ammie sannan daga 茩arshe ta ce.

"Beenafah dan Allah ki dubi Allah ki yafe musu.."

Girgiza kaina nayi cikin rashin sanin abin da take magana a kai na ce.

"Wallahy Aunty ban san komai a wannan maganar ba. Ba ni bace..."

"Ko mijin ki ne Beenafah??"

Shiru na yi na 蓷an lokaci sannan daga 茩arshe na girgiza kaina na ce.

"Kai...gaskiya a'a. Dayaa ba shi da lokacin wannan. Ba shi ba ne gaskiya."

Kashe kiran ta yi ta sake kiran Ammie wai don ta ji ko Dr. Basheer ne ya shigar da 茩arar amma kuma nan ma ba shi ba ne. Wasa-wasa sun nemi kowa da suka san yana da mu'amala da su amma kuma kowa ya ce ba shi ba ne. Kallonta Daddy ya yi a rauna ne ya ce.

"Aysha ashe daman kina magana da Mulaifa tsawon lokacin nan kika ce min baki san a ina take ba??"

Tana wani irin kuka ta shiga 蓷aga murya tana fa蓷in.

"Eh Daddy! To amma akan me zan sanar maka inda suke bayan ka riga ka gama da rayuwarsu? Ita 蓷in da ace irin zuciyarku ke gareta da ko kallon inda nake tana yi? Allah ne wanda ya ha蓷ani da su ba zato ba tsammani. Kuma sai da muka yi shara蓷i da ita akan bata son kusan inda take kuma na amince....to akanmi zan sanar muku inda take. Babu irin nasihar da ban muku ba, babu irin fa蓷a muku gaskiyar da ban yi ba. Amma haka kuka zo ku ka share maganata ku ka yi ta yin abin da ranku yake so kuka manta da cewa akwai Allah wanda baya bacci baya angaje....inda nake iya neman alfarma na ro茩o, sunce ba hannun su a ciki, saboda haka sai ku shirya zaman gidan yari tun da haka kuka za蓳arwa kanku.."

Daga haka ta shige 蓷aki ta fa蓷a kan katifa ta fashe da wani irin kuka na takaici da ba茩in ciki.

Suna nan inda ta barsu su Mummy ana ta kukan nadama Sai ga Hafiz ya iso. Daman da 茩yar Uncle Isma'ila ya amince akan ya ri茩a zuwa shagon sa yana masa tsaro duk wata yana biyansa.

"Daddy!"

Ya ambata cike da karyewar zuciya.

"Daddy Allah ya yi mana maganin wannan masifar da muka siyo da ku蓷inmu...wallahy munci amana Daddy..mun cutar da Ammie, da Daddy Bello.."

Ganin kawai suka yi a hankali ya sulale daga inda yake tsaye ya zube 茩asa numfashinsa ya lokaci 蓷aya yanke. Da gudu suka yo kansa suna fa蓷in.

" Daddy...Daddy.."

Aysha bata batasan lokacin da ta fito da gudu ba, hankali a matu茩ar tashe tana fa蓷in.

" Miye abun da ya samu Daddyn kuma?"

Da gudu Hafiz ya bar gidan ya fita neman mai Napep 蓷inda za su 蓷auke shi zuwa asibiti.

Suna nan ba jimawa sai gashi ya dawo suka tattala shi da 茩yar suka nufi asibiti da shi cike da tashin hankali.

*******

Gefen Ya Mohaa kuwa, sosai abin da yake ganin kamar ba komai ba yake neman yafi 茩arfin tunanin sa. Da ba don kada ya zamto mai butulci a wurin Allah ba, shi kam da yace ya yi dana sanin gano dangin mahaifiyar sa da ya yi a wannan karon. Domin bai haddasa masa komai ba sai rashin kwanciyar hankali da dagulewar lissafi.

Ubaid da ya shigo Office 蓷in nasa a yanzu ne ya 蓷an daki table 蓷inda ke gaban sa ko Allah zai sa ya farka daga duniyar tunanin da ya abka.

Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya bu蓷e su sannan ya kalle sa murya a 茩asa sosai ya ce.

"I don't know what to do right now..."

"Akwai abin da za ka yi mana..."

Ubaid 蓷in ya fa蓷a yana mai samun wuri kan kujerar da ke facing 蓷insa ya zauna ya ce.

"Use your brain as you always do...za ka samu mafita."

Girgiza kai ya yi cike da karaya ya ce.

"Ban da mafita Ubaid...na auna yafi sau dubu amma na kasa samun mafita, domin ba zan ta蓳a iya yin wani aure ba a yanzu...idan na Kalleta tausayi take bani....rayuwarta da dukkan wani fatanta yana a kaina ne..ko shekara 蓷aya bamu yi spending a tare ba. Ta ya ya zan je mata da zancen wani aure? Daga ni har su Jaddan ta kallemu ya ya? Ma su son kan su da manta alheri??"

Girgiza kansa ya yi yana mai 茩ure kallon Mohaa 蓷in ya ce.

" Ko 蓷aya! Ai ita 蓷in yarinya ce kamar yanda ka ce tun farko. Tana sonka sosai, bana tunanin idan har kaje mata da magana musamman akan umarnin Jadda za ta 蓷aga hankalinta..."

Da sauri ya girgiza kansa ya ce.

"Ubaid! Ita 蓷in fa ba tsana ba ce. Mutum ce kamar kowa wacce ke da zuciya a 茩irjinta. Duniya ta daga ni sai Beenafah nake son kasancewa a Cikinta. Ka manta da cewa za ta damu ko ba za ta damu ba, I want only her in my life..."

"Su kuma iyayenka da abin da zaka saka musu kenan bayan shekarun da kuka kwashe baka tare da su? Kasan irin yanda suka cutu tsawon shekaru akan rashin ka? Yanzu da ka same su ashe basu cancanci ace ka yi duk abinda suka ce ba muddin dai zai saka su farin ciki?....Engineer! A Rayuwar nan ko? 蓷an Adam matu茩ar dai ya yarda da 茩addara to dole ya shirya amsarta a duk yanda ta zo masa....ba dole sai fa ka samu abinda kake so 100% ba, Ka yi duba daga inda ka faro...kada ka tsaurara abubuwa. Idan har kana son duniyar ka ta yalwata da farin ciki da kwanciyar hankali, to ka amince da auren Noura,tunda har sun nace ka yi ha茩uri ka bai wa zuciyar ka magana. Ka duba ka gani tun da ka dawo tsohuwar nan ta 茩i amincewa ta amsar wayarka. Ba don bata sonka take maka haka ba, ta yi ne saboda 茩arfafa zumunci. Kuma shin ka lura da wani abu kuwa? Ganin 茩anin ka zai auri Suwara, 茦anwar ka za ta auri Suhaib ne ta ji cewa hakan ya burgeta idan Kaima za ka 蓷auka daga cikin dangin abin sai yafi da蓷i sosai da kuma armashi. Ka daure ka amsa tayinsu, hakan shi ne zai ba 茦wa茩walwarka hutu daga mugayen mafarkai dare da rana. Sannan matarka za ta daina damuwa akan damuwar ka, sannan za ka saka iyayenka a farin ciki.....ya kamata fa kayi tunani, domin da kunya sosai ace tun karon farko sun nemi alfarma ka kasa cika musu."

"Ubaid! I know, you are all telling me this Saboda kawai ka dace da matan ka basa fa蓷a da juna...but kada ka manta, don ka samu hakan ba lallai ace nima na samu ba...gidan Abdul-qadeer kullum cikin tashin hankali suke ba jituwa sam, Kaga dai duk da cewa ba'a gida 蓷aya suke ba. Kullum cikin tashin hankali yake da rashin nutsuwa..."

Murmushi Ubaid 蓷in ya yi tare da girgiza kansa ya ce.

" Ya kamata ka kyautatawa Allah za to Engineer. Lokacin da ka faro, tsawon shekaru ka shafe ko mata 蓷aya baka da ita, lokaci 茩an茩ani Allah ya azurtaka da samun Beenafah, wanda ba wayonka ko dabarar ka ba ne suka baka ita ba Ikon sa ne...ba ina fa蓷a maka haka bane don in turaka 茩arshen rame...ni kawai ina nema maka maslaha ne. Kai ne za ka tsara yanda kake so. Ba lallai sai ka ajiye su a gida 蓷aya ba, ba lallai sai ka ajiye su a unguwa 蓷aya ba, in fact! Ko cewa ka yi ba a 茦asa 蓷aya zaka ajiye su ba, no body will judge you. Kawai dai za ka sha azabar yawo, don jikinka ma sai ya fa蓷a maka ba. Idan har kana gudun matsala ka ajiye Noura a Nigeria ko a Sudan 蓷in. Kaga babu wacce za ta san a wanne hali er uwar ta take, sai idan kai ne kaso su ha蓷u...."

Da sauri ya wani runtse idanunsa yana girgiza kai ya ce.

" Ita ka蓷ai nake so Ubaid...ina tsoro kada Allah ya kamani da laifin rashin yin adalci... "

" To ai baka zauna da Noura 蓷in itama ka gani ba. In Sha Allahu za ka iya. Kai dai kawai ka ro茩i Allah mafi alheri. Idan har kaga an yi auren, to tabbas ita ce mafi alheri. Yanzu tun da har ta kafe akan sai ka je ka ganta, to ina baka shawara akan ka shirya ka je 蓷in, don ka ganta ai ba shi ne auren ba, ka dai tafi shi ne muradinta."

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana mai jinjina kansa ya ce.

" In Sha Allahu zan je. Amma ba don na amsa da zancen auren ba, zan je domin zumunci. Thank you so much for the advice."

Daga haka suka yi sallama da Engineer Ubaid 蓷in ya wuce. Yana fita bai ma jira 6pm 蓷in ta yi clocking ba ya tattara ya kama hanyar gida. Tabbas ya yarda da maganar Ubaid cewa ganin ta da zai je ya yi ai ba shi ne auren ba. Zai ma iya faruwa ita kanta tun da ba yarinya ba ce ta ji bai yi mata ba, kuma babu wanda zai tilasta mata. Allah ma yasa hakan ta kasance. Da sai ya fi kowa farin ciki.

Bayan ya dawo sosai ya saki jikinsa wanda ni abun har mamaki ya 蓷an bani. Bayan mun gama shirin kwanciya bacci ya zaunar dani akan 茩afarsa yana murmushi ya ce.

" Zan je ziyarar dangin su Jadda, but I will spend only two days I promise..."

Langa蓳ar da kai na yi cike da shagwa蓳ewa na ce.

"To zan je mana...dan Allah ka je dani ka ji.."

Wani irin bugawa 茩irjinsa yayi wanda cikin seconds yanayinsa ya nuna Kamar akwai wata damuwa. Hannuna ya kama cikin fargaba ya ce.

"Kina ji ko Bibina...daga zaran na dawo da kwana 蓷aya zamu wuce Kaduna a tare wurin yin wannan aikin da na fa蓷a miki.."

Cikin jin da蓷i na wani 茩an茩ame wuyansa na sumbaci gefen kumatunsa na ce.

"Thank youuuu!!"

Janyewa na yi ina kallonsa da murmushi na ce.

"To gaskiya na ha茩ura, domin na fi son zuwa Nigeria, ina kewar Ammiena da Bahrain sosai...ai za ka kai ni na gansu ko?"

Da sauri ya jinjina kansa ya ce.

"Sosai ma kuwa. Duk inda kike so na kaiki zan kaiki In Sha Allahu."

"To na gode...bari na fara 茩irgen days 蓷in. Amma kai ma fa a gidanmu za ka zauna har mu dawo tunda nima na zauna a gidanku da muka je Sudan...bari na kira su Aunty Labiba na sanar musu zuwana...har Jadda ma sai na fa蓷a mata"

Wayata na 蓷auko na dawo saman jikin sa na kwanta ina ta kiraye-kirayen mutanen da na ce.

Murmushi kawai yake tare da tsuramin idanu yana ta kallona. Duk abin da nake a duniya burgesa yake kamar yanda yake fa蓷amin koda yaushe.

Tun ina wayar yake ta shinshinar 茩amshina yana shafa fatar jikina, wanda na san tunda har gobe zai tafi, to babu abin da zai hana masa shanye da蓷ina a wannan daren. Haka na biyesa har muka kambala sannan muka yi wanka muka kwanta.

******

Washe gari da wuri ya shirya na rakashi mota sannan na dawo gida cike da jin kewar sa.

Bacci na koma nasha son raina sannan na ta shi na yi sallar Azahar na 蓷auko wayata na zauna na fara sana'a. Wato kiran waya wacce idan baya nan aikin da nake yi kenan sai kuma charting. Hairi na fara kira muka gaisa na yi mata ya exams sannan na kira Jadda muka sha fira har da su Taimiyya. Daga nan na kira Ammie wanda a nan ne muka 茩ara tattauna maganar Daddy domin gano waye wanda ya shirgar da shi 茩ara amma bamu gane ba. Gashi ta ce min yanzu haka yana gadon asibiti ciwon shanyewar 蓳arin jiki ya kama shi. Nan na yi mata al茩awarin cewa zan kira Aunty Aysha in mata ya mai jiki kamar yanda ta umurce ni. Sannan daga nan na kira Aunty Labiba. Bayan na gama naje na ci abinci na dawo na zauna na yi ta shiriritar kallo da charting.

Misalin 茩arfe shida na yamma, ina zaune a garden muna chart da Aunty Nadeeyah kiran wayar shi ya shigo. Cike da jin da蓷in ganin kiran nasa na yi saurin 蓷agawa, daman tun da ya fita yau bamu yi magana ba.

Ina 蓷agawa na ce.

"Na yi kewar ka tun ba'a kwana ba...da fatan ka sauka lafiya?"

"Uhm! Ni ma haka Bibina...kina ji?"

Gya蓷a kaina na yi tamkar ina a gabansa na ce.

"Uhm! I'm all ears sweetie.."

"Did your Mum get twin sis?? Ina nufin ita 蓷in '拼an biyu ne??"

         鉁嶏笍  OUM-AMEER  鉁嶏笍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.