Free chapter · Read without an account

Chapter 5&6

by Fatima Isa Manu · DANGIN MUTUWA

*DANGIN MUTUWA 🔥*

A story of full hatred, vengeance of the spirit, betray, unconditional love and heart touching.



*STORY & WRITTEN BY ✍️ FATIMA ISA MANU 🥀🌻*



*( DR TEEMAH ✍️ )*



*( SAHIBAR JAJIRTATTU 💃🌼 )*




___________________________________

_Masu neman littafin *DANGIN MUTUWA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following din channel ɗi na dan samu_👇***

___________________________________

               

****

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A) 

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

____________________________________

              

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*

      *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*

          *(We stand together)*

                    🤝🤝🤝


___________________________________





*PAGE 5 & 6*





*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*





AMJAD ne ya ce.” Inspector wannan maganar ya da ɗe da mutuwa fa.”


Dariya Inspector ya yi mai sauti yana cewa.” A gurin ku ne ya daɗe da mutuwa? Kuma ai kai ma kamar ka taɓa raped din yarinya a hotel din Kaduna."


A razane duk ƴan parlon suke kallon AMJAD wanda tuni ya sunkuyar da kai.


KAWU BELLO ne ya ce. “ Babana wani magana na ke ji ne?.”


Runtse idanunsa AMJAD ya yi, yana jin zuciyarsa na zafi.


Dariya Inspector LAWAN ya yi, kana ya kama baki yana cewa. “ Oh sorry Sir ashe baka faɗawa kowa ba, ka sanni da saurin surutu.” 


Takowa KAWU BELLO ya yi gurin AMJAD, kana ya dafa shi yana cewa. “ Babana me ya ke faruwa ne?.”


Buɗe jajayen idanunsa ya yi yana watsawa Inspector LAWAN.


Murmushi Inspector ya sakar masa yana ɗaga masa gira.


Haɗiye yawu mai ɗaci AMJAD ya yi, kana ya juya ya fice a parlon.


Juyawa AYMA ta yi zata fita, Inspector LAWAN ya ce. 


“ Barrister muna da shari’a fa.” 


Runtse ido ta yi tana jin kamar ta buge shi ya mutu, amma sai ta ɗaure ta ɗaura murmushi akan fuskarta, kana ta juyo tana cewa.


“ Kar ka damu nasara kullum namu ne, ka zuba ido kawai ka ga yanda wasan zata kaya. “


“ Bayan an dakatar da Barrister din, ta ya zata yi nasara?.”


Gyara tsayuwa ta yi tana cewa. “ Dakatarwa ba shi ne kora ba, kai har yanzu sabon shiga ne a aikin, just experiencing your work and move, abar masu basira irin GANDARA families su yi aiki Okay.” Ta ida maganar tana murmushi.


Haɗiye miyau ya yi yana kau da kai gefe, ABBA da ya rikice ne ya buɗe baki zai yi magana ya ji AYMA na cewa.


“ Kar tunani ya sa ka yi kuskure a aiki, kasan GANDARA’S family ba sa yafiya idan anyi kisar da bai musu ba.”


A fusace Inspctor LAWAN ya ce. “ AYMA it is enough.”


“ LAWAN ka sai ta harshenka a gaban Barrister ka ke fa.” Ta ida faɗar hakan tana nunasa da yatsa.


Dif ya yi shuru yana kallon ta, dama ba shiri suke ba tunda case ya taɓa haɗa su.


Gaba daya kowa shuru ya yi, REYYAN ne ɗan AMJAD wanda shekaransa uku a duniya ya soma magana da batacciyar hausan sa.



“ Ammiey yunwa a ke ji.”


Dama da haka yake kiran AYMA, murmushi ta masa tana buɗe masa hannu yazo da gudu yana dariya.


Ɗaukansa ta yi za ta fita a parlon Inspector LAWAN ya ce." Har ɗan shegen ya girma?.”


Wani banzan kallo ta watsa masa, har ta buɗe baki zata mayar masa da murtani REYYAN ya fara kuka, hakan ya sa ta masa kallon warning kawai ta fice a parlon.


MARWAN ne da YAZEED suka haɗa ido, murmushi suka sakarwa junan su kafin suka kalle IYA da KAWU YA’U.


Wucewa akayi da IYA da KAWU YA’U, su kuma suka fita aka rufe bangaren, dan tun ɗazu aka tafi da gawar.








Yana shiga bangaren sa ya rufe ƙofar da key, akan three siter ya ƙwanta yana tuna abubbuwa da dama.


Lokaci daya ya ji hawaye na zarya akan kuncinsa, kewar mahaifiyarsa duk ya dame shi.


Runtse idanunsa ya yi yana magana kamar wawa.


“ AMMIEY na yi kewarki, ko sau daya ki dawo naga murmushin ki dan Allah, rayuwa zafi take min idan ba ke, mahaifiya mai ɗaukewa ɗanta damuwa, yau na waye gari babu ke babu alamarki, AMMIEY akan me ya sa bazan dau fansa ba? An dakatar da ni akan laifin da bansan na yi ba, sun kashe min matata, sun kashe min ke, me amfanin rayuwata Ammiey?.” Ya ƙarashe maganar yana sakin sabon kuka.


“ Kai kuwa rayuwarka take da amfani AMJAD, bama kai kaɗai ba har da sauran jama’a da yaronka.”


Shuru ya yi yana jin maganar, cigaba da maganar aka yi.


“ Ka ringa addu’a a ko da yaushe idan ka tsinci kan ka cikin halin rayuwa, tabbas komai mukaddari ne, haka kuma komai a rubuce ya ke, Allah baya barin wani dan wani, kuma In Sha Allah Allah zai zama gatanka a ko da yaushe, fatan nasara ga kwarzon namiji.”


Juyowa ya yi da sauri yana duba gurin da ya ji maganar, tabbas wannan muryan Ammieyn sa ne, murmushi ya yi yana mai jin dadin duk lokacin da ya shiga duhu tana fitar da shi.


Knocked akayi, ko bada izini bai yi ba aka shigo, ya san wacce zata tai hakan shi ya sa ko juyowa bai yi ba tun da ya san tana da key.


Hannunta ɗauke da REYYAN suka shigo.


Sauke shi ta yi ya nufa gurin AMJAD da gudu yana cewa. 


“ Abbiey wanka sleep.”


Dariya ya yi yana cewa. “ To wanne zamu fara yi?.”


“ Abbiey wanka jinina wayi aka yi.” Ya yi maganar yana wani shinshina jikinsa din.


Dariya abun ya basu sai kawai suka fara yi, AMJAD ne ya ce.


“ Babban mutum jikinka fa baya wari kamshin turaren Ammiey ka ya ke.”


Ya faɗi hakan yana kallon AYMA, tsuke fuska ta yi tana cewa.


“ REYYAN zo na maka wankan.”


Ɓata fuska ya yi yana kau da kai alamun bazai zo ba, ware ido ta yi tana cewa.


“ REYYAN ni ne fa.”


“ A jon ba.”


“ Okay ka kyauta.”


“ Sorry AMMIEY.”


Hararan shi ta yi tana nufan hanyar kitchen.


Kallon AMJAD REYYAN ya yi yana k’ok’arin yin kuka, haɗa rai ya yi yana cewa.


“ Je ka bata hakuri.” 


Sauƙa ya yi a jikinsa ya nufa hanyar kitchen da gudu.


A bakin ƙofar kitchen din ya tsaya yana lekenta.


Tana tsaye a gaban gas tana dafa indomie.


A ɗan tsorace ya ce. “ AMMIEY sorry.”


“ Sorry for your self REYYAN.”


Kuka ya sa mata yana zuwa ta baya ya rungume ƙafafunta, murmushi ta dan yi tana cigaba da aikinta.


Jin taki kulasa ne ya sa ya zauna a ƙasa, da sauri ta ɗauke shi tana cewa.


“ REYYAN ka ringa barin ABBIEY dinka yana samun rest mana.”


Ɗaga mata kai ya yi, murmushi ta masa tana cigaba da cewa.


“ Yawwa My boy, bari na gama maka indomie din sai ayi wanka ko?.”


“ AMMIEY har da ABBIEY a food din?.”


“ Shi ai baya cin indomie.”


“ AMMIEY a zuba mai ja ci.”


Shuru ta ɗan yi kafin ta gyaɗa kai, da haka ta gama indomie, tana yi suna hira har ta gama ta sauke.


Plate ta ɗauko ta ɗauraye, kana ta zuzzuba musu, ɗaukan REYYAN ta yi kana ta ɗauka plate din shi suka fita.


A gurin da suka bar shi a nan ya ke, amma yanzu ya ƙwanta ne ba kamar ɗazu daya tsaya ba.


Kallo daya ta masa tana ɗauke kai, kana ta ajiye REYYAN akan carpet tana bashi abincin.


Turo baki gaba ya yi alamu baya son ta bashi abincin, murmushi kawai ta yi tana tashi ta wuce kitchen.


Haɗa masa nasa ta yi akan tray tana ɗaukan ruwa, kana ta fito parlon.


Ajiye masa ta yi a gaban shi tana cewa. “ Ka tashi ka ɗan ci abincin.”


“ Ai kinsan bana cin indomie ko.” Ya faɗa a gadarance.


“ Dama ba ma kai na dafawa ba, ɗanka ne ya ce a zuba maka.”


Kallon ta ya ɗan yi yana jan tsaki.


Ɓata kulasa ba ta je gurin REYYAN da tuni ya gama cinye indomie, ɗaukan shi ta yi tana cewa.


“ Son ka bata jikinka fa.”


“ AMMIEY food ne dadi shosai.”


Dariya ta masa tana cewa. “ Mu je na maka wanka a ɗakina.” 


Da haka suka fita suna hira.



Kallon abincin ya yi yana ɓata fuska, kamar baya so haka ya tashi ya fara ci, yana ci yana ɓata fuska, dake ba wani iya ci ya yi ba hakan ya sa ya ci kaɗan ya tashi.









@@@@@@@@@@@









Guraren ƙarfe sha biyu na dare suka haɗu a ƙofar sirrin su, dukan su baƙin kaya ne a jikin su.


Duba agogon wayan hannunsa AMJAD ya yi yana kallon su, kafin ya ce.


“ Har yanzu fa AYMA bata iso ba.”


RUMAISA ce ta ce. “ Ni har na fara tsoron kar ita ma sun kashe ta.”


“ Ban tunanin haka RUMAISA, sai dai ko wani abun daban.” A cewar MARWAN.


“ Ai koma mai take yi yanzu kam ya ci ace ta iso, tun ƙarfe sha biyu fa muna nan, kuma kunsan idan har yau bamu shiga nan gurin ba duk abunda muka yi ta wargaje.” AMJAD ya faɗa.


“ To wai ina AYMA ne?…







COMMENTS AND SHARING PLS🤝🙏







*SIGN BY DR TEEMAH✍🏼*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol