Free chapter · Read without an account
Chapter 59&60
59 - 60 *DANGIN MUTUWA🔥*
_( The family of death ☠️)_
_A story of full hatred, vengeance of the spirit, betray, unconditional love and heart touching._
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
💪 _JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION_💪 ✍️ *(J.W.A)*
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
_BONUS PAGE_
59 - 60
“ Ko muƙullin ko azurfa, dole sai daya daga cikin su ne zai iya tonawa, kuma wanda ya zamana yana da zanen taswiran nan.”
“ Muƙullin zamu kashe farko, kafin mu nemo azurfan.”
“ Amma ta ya?.”
Tun da Amjad ya bar garin Aliyah ta daina zama a gida, yau kusan sati kenan bata gida, da zarar an tambaye ta sai ta fara masifa cewa ana saka mata ido, ko kuma ta kafe da cewa gidan iyayenta ta je.
Najeeb da Ilham sun dawo, sai dai jikin Ilham din sai addu’a kawai, amma da sauƙi sosai, sabida anyi aiki sosai tare da ƙwararrun likitoci.
Kullum sai anyi faɗa a gidan, tsakanin Kawu Ya’u da Marwan, Adeel sai Najeeb, shi ya dame su kan cewa suyi aure su kuma sun ce baza suyi ba, tun da kusan sau uku suna zuwa nema ana hana su, ƙarshe a ce musu su DANGIN MUTUWA ne.
Yau ma kamar kullum, Kawu Ya’u ne da Kawu Amadu suka fito da shirin fita, hango Aliyah suka yi ta shigo gidan duk a birkice, tana nufan bangaren ta, kiran ta Kawu Amadu ya yi.
“ Aliyah.”
Cike da izza da isa ta juyo tana cewa. “ Na’am.”
“ Daga ina ki ke?.”
“ Akwai igiyar auren ka ne a kaina da ka ke tambaya, ko kai sirikina ne? Ko ubana ne?.”
Da mamaki Kawu Ya’u ya ke cewa. “ Ke baki da hankali ne ko me.”
Kallon up an down ta masa tana tsaki, kana ta juya hagu da damanta, ganin ba kowa ne ya sa ta ce. “ Nafa san abun da ku ke aikatawa, idan zaku kwantar da hankalin ku to tun wuri ku kwantar, kar ku bawa kan ku wahala gurin neman Azurfa da Muƙullin, duk kuna tare da su a cikin gidan.”
Kallon junan su suka yi, kafin Kawu Amadu ya ce. “ Suna ina to? Sannan su waye ne su?.”
“ Biya zaku yi kafin na fad’a muku, ko kuma kumin aiki kafin na gaya.”
“ Ke mufa da ki ke gani ba sa’annin ki bane, kar ki raina wa kan ki hankali, mu za ki saka aiki?.” A cewar Kawu Amadu.
“ Kun fi ƙarfi ne?.“
Da sauri Kawu Ya’u ke cewa. “ Me aikin?.”
“ Kashe Ayma zaku yi.”
A razane suke kallon ta, cikin kiɗima Kawu Ya’u kan cewa. “ Ke kina da hankali kuwa? Ko kina shan wani abu ne? Yarinyar da tun tana ƙarama muka gagara taɓa ta, shi ne zamu iya kashe ta yanzu.”
“ Idan ba zaku yi dan ni ba, za kuyi dan kan ku ai.” Da haka ta juya ta nufi bangaren ta.
“ Ya’u da baka fad’a haka ba ai, kasan muna neman mu san waye ne mukulli da azurfa, kuma ta nuna ta sani amma ka bata mata rai.”
“ Bar ta, sai tana raye din ai kafin ta tona mana asiri, waya gaya mata mu sa’annin ta ne.”
“ Me ka ke nufi ne Ya’u?.”
“ Me kuwa nake nufi ban da mu kashe ta.” Dariya suka kwashe da shi, kafin suka shiga mota suka fita.
“ Ya Najeeb ina son ganin Anuty Ayma.”
“ Ki mata me?.”
“ Magana zan fad’a mata.”
“ Ki fad’a min sai na isar mata.”
“ Dan Allah.”
“ Kee!!! Kinsan nayi shuru ne ba tare dana tambaye ki taya akayi ki ka shiga bayan motana ba.”
“ Ya Najeeb kashe ni suka zo yi, shi ya sa na shiga.”
“ Su waye?.”
“ Hatsari ne na fad’a maka, ma Anuty Ayma kaɗai zan faɗawa.”
“ Hanifah kinsan Allah idan baki gaya min su waye suke kisan nan ba, babu inda zan barki ki tafi.”
Ja baya ta yi daga gare shi, a dan tsorace ta ce. “ Ba zan iya ba.”
Wanka mata mari ya yi, wanda ya yi silan ɗaukewar numfashin ta na wucen gadi, kuka ta fashe da shi tana cewa. “ Sai dai ka kashe ni, amma bazan fad’a ba.”
Tausasa murya ya yi yana lallabar ta. “ Hanifah kiyi hakuri ki faɗa min su waye ne, na miki alƙawari bazan faɗawa kowa ba.”
“ Akwai hatsari sosai idan na fad’a maka, dan baka da kariya a jikin ka, ita kuma tana da shi.”
“ Na kira miki ita ta vc za ki faɗa?.”
“ Eh.”
Wayansa ya ciro daga aljuhun rigarsa, ya fara kiran Ayma ta vc, kusan sau haɗu yana kira ba’a ɗauka, duban Hanifah ya yi yana cewa. “ Bata ɗauka ba.”
“ Ka kira Ya Amjad.”
“ Shi kuma ya yi me?.”
“ Zan faɗa masa ne, dan shi ma akwai kariya a jikinsa baza su iya masa komai ba, sai dai na Anuty Ayma ya fi ƙarfi.”
Babu musu ya kira Amjad vc, ana uku ya ɗauka yana cewa. “ Yes Najeeb ya hanya.”
“ Alhamdulillah mun iso lafiya, ya Ayma din?.”
“ Tana ciki.”
“ Kamar hospital naga ka ke, What’s wrong?.”
“ Uhm Ayma ce ta yi miscarriage.”
“ Subhanallah, a garin ya ya?.”
“ Waya san mata ne, kila garin kwaɗayin ta ne taci wani abu.”
“ Kai Allah ya tsare gaba.”
“ Ameen, ya jikin Ilham?.”
“ Da sauƙi.” Sai shuru ya biyo baya, kafin Amjad ya katse shurun da cewa. “ Me ya faru ne naga fuskan ka wani iri, hope komai lafiya, ba dai wani mutuwa aka kuma yi ba.”
“ Amjad Hanifah ce take son magana da Ayma.”
“ Hanifah kuma? Dama kasan gurin da take ne?.”
Bai bashi amsa ba, ya juyar da akalan vc din zuwa kan Hanifah, da mamaki Amjad ke cewa. “ Hanifah ina ki ka shiga?.”
Kuka ta fashe da shi tana cewa. “ Yaya ba lokaci suna daf da kashe ta.”
“ Waye din.”
“ Anuty Ayma.”
“ Ban gane ba.”
“ Yaya dan Allah ka kai mata wayan, idan tana bacci ka tashe ta.”
“ Am…” Saurin katsai shi ta yi ta hanyar cewa. “ Dan Allah kayi sauri.” Tashi ya yi ya nufa ɗakin da aka kwantar da Ayma, yana shiga ya hango ta zaune tana zubawa ƙofar ido, suna had’a ido ta yi saurin kau da kanta gefe.
“ Ya jikin.”
Bata kula shi ba ta yunkura zata kwanta, saurin dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa. “ Hanifah ke son magana da ke.”
Da sauri ta juyo tana cewa. “ Hanifah kuma? Dama tana raye?.”
“ Gashi sai ki tambaye ta.” Ya miƙa mata wayan yana zama kusa da ita.
Kuka Hanifah ta fashe da shi ta cikin wayan tana cewa. “ Anuty dan Allah kiyi hakuri.”
“ Hakurin me kenan? Ina ki ka je? Gurin wa ki ka zauna?.”
“ A gurin Ya Najeeb.” Ta fad’a tana goge hawayen fuskarta.
“ Shi din da baya gari.”
“ Anuty tun a daren ranar dana fita nake gurin shi.”
“ Me ya sa za ki fita daga gidan ba tare da an miki komai ba?.”
“ Anuty su suka biyo ni zasu kashe ni, shi ne suka saka ni a bayan mota, sai suka fita suka koma gurin Ilham, kafin su dawo nayi saurin shiga motan Ya Najeeb, tun daga ranar nake gurin shi.”
“ Su waye?.”
Sai da taga fuskokin su kafin ta buɗi baki tana cewa…..
*SIGN BY DR TEEMAH✍🏼*