Free chapter · Read without an account
7
kUDA ESTATE, BAUCHI BAUCHI
Tun bayan sallar la'asar a part ɗin Ummah ake shirye-shiryen tarbar mutanen Bloordale village, girki iri-iri aka yi kasancewar Flight ɗin 1pm zai biyo wanda a Nigeria kuma zai yi daidai da ƙarfe 6pm na yamma, sosai aka gama komai akan lokaci sannan Ummah ta sa aka gyarawa AK room ɗinsa aka saka turare. A daidai lokacin da jirginsu yayi landing aka gama clearing komai suka ɗungumo gaba ɗayansu, Asim, JK and AK, dialling number Sulaiman yayi, a friend of him wanda yazo aiki Jos kuma da yiyuwar zai tafi a ranar, hakan yasa ya biyo su tafi tare. Ana wasa ana dariya suka nufi motar ban da AK da tunaninsa ya tafi wani wuri na daban, bayan sun shiga Mota Sulaiman ya ja motar, a hanya suka tsaya suka yi sallar Magrib tukun suka wuce, ana kiran Isha suka isa Bauchi, kai tsaye estate ɗinsu suka wuce.
Kasancewar babu wanda ya san da dawowarsu in ka cire Ummah, Ummie Abbie, Uncle N, Abba da kuma Mammah. Part ɗin Abbie kai tsaye suka nufa, tun lokacin da motarsu ta gama parking ma'aikatan sashen suka nufo motar don sun san waye Sulaiman ga AK ɗin. Suna fitowa ma'aikatan suka biyo su da kayayyakinsu ciki. Ummah wacce ke zaune a parlour ta ci kwalliya tana zaman jiransu miƙewa tayi kai tsaye ta nufe su fuskarta sake.
Mutanen Bloordale village sai yanzu kuka iso?"
Cikin sakin fuska JK yace "Wallahi Ummah."
Ba tare da mayar masa da amsa ba ta mayar da kaklonta ga AK wanda ya saki fuskarsa kaɗan.
"It seems like you're exhausted, ku samu ku watsa ruwa sai ku ci abinci. Asim mutanen Bloordale." Ta ƙarasa tare da riƙo hannun Asim ɗin. "Ba magana ne? Ko dai Jalaal ya hana ka magana ne?"
Dariya Asim yayi yace "A'a, ina wuni Ummah"
"Lafiya ƙalau, yau dai sai wurin Mom ko?"
Asim yayi dariya yace "in dai ba ta zo ta ɗauke Ni ba ba zan je ba. Zan zauna tare da Ya Jahaan."
Ummah tayi dariya tace "To ka samu ka watsa ruwa kaima, he's your own room here" ta nuna masa da yatsa
"Thank you." Daga nan ya nufi ɗakin da gudu.
Shigowar ƴanmata da kuma yaran gidan daga sassa daban-daban yasa Ummah ƙarasawa wurinsu tana musu sannu da shigowa. Wurin suka samu suka zauna tare da gaida Ummah, amsarsa tayi cikin fara'a tana faɗin "Sun iso yanzu, wanka suka shiga."
Tana kai aya ta zauna itama kusa da ƴanmatan tare da nazartarsu ɗaya bayan ɗaya tana son gano ƙudirirrikan kowannensu.
Tsawon wasu mintuna JK da kuma Asim suka fara fitowa, cike da girmamawa ƴanmatan suka gaishe da JK ɗin shi kuma Asim ya gaida su.
Suna gaisawar AK ya fito, ji yayi kamar ya koma ganin yadda Safnah, Manal da kuma Nimra ke bin sa da kallo without minding that Ummah na zaune a parlourn. Siririn tsaki ya ja ciki-ciki sannan ya ƙaraso, fara gaishe shi suka yi ɗaya bayan ɗaya kowa da irin nasa salon na jan hankali, a daƙile ya amsa musu kai tsaye ya wuce dining, murmushi Ummah ta saki don zuwa yanzu ta gama fahimtar kowaccensu ta kuma ta matuƙar jin daɗin yadda AK ɗin bai sake musu fuska ba, itama miƙewa tayi tana faɗin "Ku tashi ku ci abinci ƴanmata." Ba musu suka miƙe kowacce tayi Tata hanyar zuwa dining, Nimrah, Safnah da Manal da kowacce ta ji dadin yadda AK bai ba wa ƴar'uwarta amsa cikin kulawa ba, that means duk cikinsu babu wanda yake da muhalli cikin ransa. Hakan yasa suka bi Ummah kowacce na saƙa ta yadda za ta mallaki AK ɗin ya zamo nata bisa huɗubar iyayensu.
A ɓangaren AK gaba-daya ba a sake yake da su ba, hakan yasa bai wani ci da yawa ba ya miƙe, Ummah ce ta dube shi tace "Ya dai Son?"
Shafa cikinsa yayi yace "I'm satisfied."
Cike da kulawa tace "Har yanzu ɗabi'arka tana nan Jalaal, Allah ya shirya ka"
Cikin ransa ya amsa da "Amin" sannan ya fice, garden ya nufa kai tsaye, ɗaya bayan ɗaya ƴanmatan suka yi wa Ummah sallama suka wuce wanda hakan ya matuƙar ba wa Ummah dariya sai ta bi su da kallo.
A can garden Jahaan ya tarar da Jalaal suka wuce sauran parts ɗin gidan suka yi gaisuwa, sun samu tarba wurin Mammahn Jahaan da kuma Aunty Salaha abokiyar zaman Mammah wato Maman Manal. Bayan gaisuwa shi kam Papa cewa yayi su haɗu da safe don a gajiye shi ma yake. Daga nan suka nufi part ɗin uncle N, shi kam ba su tarar da shi ba, Aunty Dr. Ta tarbe su sosai haka suka yi ƴar raharsu kamar dai yadda suke yi da mijinta. Part ɗin Daddy ma ba laifi Nenne mahaifiyar Nimra ta tarbe su akasin Mamah uwargidan Daddy wacce bayan gaisuwa babu wata magana ma da ta ƙara haɗa su, ko da suka tambaye ta Daddy ce musu tayi ba ya gari. Ba tare da saka hakan a ransu ba suka yi sallama, Jahaan ya wuce sashensu, shima Jalaal ya wuce wurin Ummie yana fatan Allah ya sa ya samu sauyi a wurinta.
Da sallama a bakinsa ya shiga parlourn nata wanda ke fitar da wani sassanyan ƙamshi, idanuwansa ya lumshe saboda yadda ƙamshin ke ratsa ko'ina na jikinsa, jin babu wanda ya amsa yasa ya tabbatar da cewa Ummien na ciki. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da nufar bedroom ɗin nata, knocking ya fara yi kafin ya murɗa handle ɗin a hankali bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa Ummie tayi ba tare da ta juyo ba, bai yi mamaki ba don tsawon rayuwarsa ba zai ce yau Ummien ta saka idonta a nasa ba in za ta masa magana, hasali ma ba ta yin doguwar magana da shi. Ƙarasawa yayi kusa da sallayar da Ummien ke zaune a kai ya ɗan tsugunna yana mamakin irin kwarjinin da kullum mahaifiyarsa ke ƙarawa gare sa. Cikin sanyin murya yace "Sannu da gida Ummie, mun same ku lafiya."
A taƙaice tace "Lafiya ƙalau, kun iso lafiya?"
Yace "lafiya ƙalau"
Ummie tace "To ma sha Allah, ya aikin?"
"Alhamdulillah Ummie"
Tace "haka ake so, a dai kula a kuma yi aiki da adalci."
"In sha Allah " daga haka ya ja bakinsa yayi shiru yana fatan a yau ta kawo masa wani zancen har ya samu damar yin doguwar zance da ita, sai dai jiya iyau, itama shirun ta masa. Ya jima a zaune sai da ya gaji ya miƙe tsaye yana faɗin "To Ummie, idan Abbie ya shigo ki sanar masa mun dawo lafiya, Allah ya tashe mu lafiya."
Da "Amin" ta amsa masa, cikin sanyin jiki da ruhi ya fito daga ɗakin.
Fitowarsa ya ga wulgawar mutum, amma sai ya basar kasancewar babu wani mahaluki a gidan bayan shi, Ummie da kuma Ummah, sau tari yakan ga irin waɗannan
Sashen Ummah ya nufa kai tsaye, kamar yadda yayi tsammani kuwa Ummahn tana zaune a parlourn kuma ya tabbatar da cewa shi take jira, tun yana yaro ƙanƙani yake matuƙar so da ƙaunar Ummah, halacci da kuma kararta gare shi ba ta da iyaka, abun da ya rasa a wurin mahaifiyarsa shi ya samu wurinta, tana nuna kulawarta gare shi, ta ɗauki damuwarsa a matsayin tata, ta kuma sadaukar masa da abubuwa da dama saboda farin cikinsa. Anya akwai irin waɗannan matan a duniya? Akwai matan uba irin Ummah kuwa? Da a ce matan uba za su riƙi ƴaƴan abokan zamansu irin yadda ta riƙe shi, to babu shakka da babu wani mahaluki da zai yi kukan maraicin uwa a duniya wai don tasa ta gusa a gefensa.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da daidaita kansa ya shiga ciki yana sallama. Ummah ta amsa tana faɗin "Na ɗauka ba za ka jima ba son, ina ta jiranka. Asim har ya yi bacci Abunsa."
Cike da kulawa yace "Ayya Ummahta, mun ɗan zagaya gidan ne."
Wani abu ne ya tsaya mata a maƙoshi, da ƙyar ta haɗiye tare da ƙirƙirar murmushi tace "Ai ka kyauta, Allah ya saka da Alkhairi."
"Amiin Ummahta."
Kuncinsa ta ɗan ja tace "Yau dai na san ka gaji, duk irin kewarka da nake dole na bari ka huta sai mu samu lokaci, yanzu na san kana buƙatar hutawa, da safe sai mu yi hirar."
"To Ummahta, zan shiga ciki" ya ƙarasa kusa da ita ya riƙo hannunta yayi kissing sannan yace "Ubangiji ya tashe mu lafiya."
"Amiin my son, bari na biyo ka da wani abun don na ga ba ka sake ka ci abinci ba, je ka ina zuwa " babu musu Jalaal ya wuce nasa ɗakinsa, yana toilet ya jiyo Muryar Ummah jikin ƙofar tana faɗin "Make sure You eat son, sai da safe." Daga haka ta fice daga ɗakin tare da rufe entrance door ta wuce nata ɗakin.
Samun kanta tayi da kiran wayar Yaya Zinatu. Cikin Sa'a kuwa wayar ta shiga, bayan ringing ɗin da ta fara Yaya Zinatu ta ɗaga. Ajiyar zuciya Ummah ta sauƙe suka gaisa. Yaya Zinatu tace "A'a, Asiya lafiya dai in ce don ban yi tsammanin kiranki ba."
Ummah ta marairaice fuska tace "Haba Yaya Zinatu, kin san dai ke nake tunkara da duk wata damuwata, ko so kike na tunkari Yaya Babba da zancen ta haɗa da Ni da ke ta zazzage mu?"
"A'a, yanzu dai faɗa min me ya faru."
Ummah ta sauƙe numfashi tace "Ai ba abun da bai faru ba Yaya Zinatu, ya kamata mu yi abun da ya dace kawai, yau Jalaal ya dawo, tun safe nake kiran layinki zan ce miki Karimah ta haɗo kayanta ta zo amma shiru Layinki ba ya tafiya."
Yaya Zinatu tace "Ayya, kin san wayar tawa ce ta samu matsala sai ɗazu na samu Alqasim ya gyaro ta."
"Kai Yaya, wai ke wayar ma ba za ki sayi ta arziƙi ba?, Shi ke nan dai, zan tura Miki kuɗi ki sayi wata, don a kwanakin nan zan yi ta nemanki."
Yaya Zinatu tace "Tooo, to na gode ƙanwata, yanzu dai faɗa min me yake faruwa na ji hankalinki a tashe."
Ummah ta furzar da wata zazzafar iska sannan tace "Ai ina faɗa miki Yaya, muna nan muna shiri ashe dangin uban yaron nan ma nasu shirin suke yi?"
"Kamar yaya kenan Asiya?" Yaya Zinatu ta tambaya cikin son sanin me yake faruwa.
"Hmm" Ummah ta faɗa "Ina faɗa miki ai yaron ya dawo ɗazu, babu tsammani kawai sai ga ƴanmatan gidan ɗaya bayan ɗaya kamar haɗin baki, wallahi duk ina lura da su akwai abu a zukatansu. Wallahi yaron yan tashi suka suka fice simi-simi suka bar ɗakin, shi yasa kawai nake so Karimah ta dawo gaba ɗaya zuwa hutun nasa ya ƙare, Ni kuma zan tunkare shi da maganar na san ta ɓangarensa ba za a samu matsala ba, kin ga idan haka ta faru duk na wurin dangin uban za a watsar da su, daga nan uban zai bayar da goyon bayan yin auren. Daga nan kuma sai mu yi abun da ya kamata."
"Gaskiya Gara da kika sanar da Ni da wuri, gobe-gobe Karimah za ta taho, Ni kuka zan je wurin Malam na masa bayanin komai in da taimakon da zai bayar to, kin san aikinsa kamar yankan wuƙa haka yake."
"To shi ke nan, zan haɗa Miki da kuɗin wayar da na malam ɗin na tura Miki. Ki yi abun da ya kamata kawai. Fatana dai burinmu ya cika, ba wai mu sarawa doki ciyawa ba."
Cikin ƙarfafa guiwa Yaya Zinatu tace "Haba dai Asiya, ki ma bar batun sarawa doki ciyawa, bautar da kika yi ta shekaru ba za ta tafi a banza ba, na san ki kuma na yadda da ke, za ki yi nasara, burinki zai cika babu wani mahaluki da zai hana hakan, idan kuwa wani ya kutso doke mu yi maganinsa. Wannan shi ne."
Ummah tace "Yauwa Yaya Zinatu na gode sosai, Allah ya bar ƙauna."
Daga haka suka yanke kiran. Umma ta sauƙe ajiyar zuciya a nata ɓangaren tana fatan burinta ya cika, tana da kyakkyawan tabbacin cewa da zarar Jalaal ya auri Karimah, burinta ya gama cika, a wannan lokacin ta tabbatar babu wani mahaluki da zai iya ƙwace shi daga gare ta, daga nan za ta fara aiwatar da Plans ɗin ta over him and his father, da zarar ta gama mallakar komai kuma, za ta yanke duk wata alaƙa da ke tsakaninsu bayan tabbatar da cewa su ɗin ba za su ƙara moruwa ba, wanan shi ne sakamakon da za ta yi wa ɗiyar ƴar aikinta da ta aurawa mijinta don ta haifa mata yaro ko yarinya daga nan kuma ta kashe ta, sai dai gashi yanzu ita ba ta tsira da komai ba sai yaron gaba-daya ta kwace mata mijin nata a hannunta ta kuma kwace duk wani so da kulawa da take samu a ce a wurinsa.
Zaria, Kaduna state.
Suna kashe kiran Yaya Zinatu ta sakin wani makirin murmushi tana ƙwalawa ƴarta kira. "Karimah, Karimah"
"Yes Mommy, ina zuwa."
Daga wurin da take tace "Yi maza ki zo, abun nema ya samu." Jin abun da Mommy tace yasa ta yi saurin zaro wayarta ta fito daga ɗakinta zuwa parlourn tana faɗin "Mommy me aka samu?"
Mommy ta nuna mata gefenta tace "Samu wuri dai ki zauna tukun" zama Karimah tayi tare da mayar da hankalinta kan mahaifiyar tata.
"Mommy ina jinki?"
Nutsuwa Mommy tayi tace "Kina ji na ko?" Karimah ta gyaɗa kai
"Yanzu na samu kira daga Asiya, kuma kiran saboda ke ne, don haka tun kafin na faɗa miki saina kafa Miki sharruɗa"
Shagwabe fuska Karimah tayi tace "Kai Mommy, nikam in za ki faɗa min kawai ki faɗa ba wai kina ja min rai ba."
"Ke matsalata da ke kenan, anya za ki min abun da ya kamata ma kuwa?"
"Zan yi mana" Karimah ta ba ta amsa tana Turo baki.
"Yauwa, ko nutsu ki saurare Ni Karimah, wannan dama ce da ta zo mana bagatatan duk da mun daɗe muna jiranta, wallahi kika kuskura wannan dama ta suɓuce mana sai na ba ki mamaki. Kina ji na?"
Ta gyaɗa kai tare da mayar da hankalinta ga Mommy ganin she's damn serious.
"Lokaci ya yi da za mu yi amfani da damar mu mu cika namu muradan, na farko, gobe za ki wuce Bauchi gidan Asiya akan batun yaron mijin nan nata Jalaal, kin san yaron an ce a ƙiyasi ya fi kowa kuɗi a gidan in ka cire mahaifinsa wanda shima kuɗin mahaifin nasa kinga kamar nasa ne tun da shi ɗaya ya haifa."
Mommy ta saurara sannan ta ci gaba "To, ita Asiya so take ki aure shi dama ai kin sani, amma fa ba don Allah take so ya aure ki ba sai don nata burin ya cika wanda ba zan faɗa Miki ba a yanzu sai zuwa lokacin da kika fahimta da kanki. Ki tuna kema kina da naki burin haka nima mahaifiyarki, za mu yi amfani da damar nan ne mu taimaka mata ya aure ki kamar yadda take so sai dai muma a namu ɓangaren ta taimake mu ne, idan har auren nan ya tabbata mu kuma daga nan za mu fara buga namu wasan kin gane?"
Wani irin murmushi Karimah tayi tana lashe baki "Kai Mommy wallahi kanki yana ja da yawa, Ni dai damuwata na aure shi kawai, kyakkyawa ne, da kika yi batun kuɗin nan sai naji kamar in na aure shi ma na raba shi da kowa nasa don na mora da yawa, amma Mommy ya zan yi da Nasir?"
"Nasir ɗin banza! Ke fa Karimah matsalata da ke sai ana zancen hankali ki fara mana shirme."
"Yi haƙuri Mommy kin san Nas yana kashe min kuɗi kuma shima aurensa zan yi don kuwa samun Namiji irin Nas a shimfiɗa..."
Ɗaka mata duka Mommy tayi tare da buge bakinta cike da takaici tace "Sakarya kawai, wallahi ki ma rabu da Nasir ɗin nan don ubanki, ina ƙoƙarin rufa Miki asiri kina ƙoƙarin tona min ko? To wallahi Karimah in kika rasa yaron nan Jalaal kin baɗe a ƙasa, yaro ga kyau ga kuɗi? To wallahi ki nutsu, yanzun nan ina sallamarki ko haɗa kayanki. Sannan in kin je za mu ke waya amma ban yadda Asiya ta san cewa muna magana ba, ko ta tambaye ki kice mata ba ma waya don ina so komai ya tafi yadda ya kamata. Kin gane?"
Karimah ta gyaɗa kai tana faɗin "Ba ki da matsala Inna Uwata, ai ki ma rubuta cewa Jalaal ko? Yauwah ki rubuta cewa mun yi aure, duk yadda zan yi na jawo hankalinsa gare Ni zan yi, ke kin san Ni ba wasa ba ce amma ina so ki ƙara ƙaimi wurin malaman nan naki da suna maka aiki yake ci. A yi auren kawai da wuri, ke kuma ki yi naki aikin ko?"
Murmusawa Mommy tayi tace "Yauwah Baby, ki je ki haɗa kayan, kafin ki tafi goben kya biya ki siyo min waya don Asiya ta Turo min kuɗi, duk yadda aka yi akwai abun da take ɓoye min tun da har ts Turo min uban kuɗin nan duk son zuciya irin na Asiya, amma dai zan tabbatar da cewa ta banbance tsakanin aya da tsakuwa, dole!"
Miƙewa Karimah tayi tana yauƙi kana ta nufi ɗakinta da sauri ta fara haɗa kayanta.
To my lovely fans, za mu shiga labarin kai tsaye, AK ya ce zai nemi mai son sa ne saboda Allah, ga su Karimah an bayyana bayan sun Nimrah, Safnah da Manal, sai dai ba mu san wace mai rabon ce za ta kwashe shi ba wannan a taƙaice shi ake kira da allura cikin ruwan...mai rabo kaɗai ka ɗauka. Hajiya Ummah ko me take nufi oho, me kuma Mommy take nufi da saka Ummah banbancewa tsakanin aya da tsakuwa?? Ku dai ku ci gaba da kasancewa da alƙalamina.