Free chapter · Read without an account
PAGE🔟⏩1️⃣2️⃣
by PRETTY SK NOVERLIST · ✦ 𝘿𝘼𝙍𝙀 Ɗ𝘼𝙔𝘼 ✦* _ 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒌𝒂𝒏𝒚𝒊 𝒃𝒂𝒕𝒖𝒓𝒆._ Soyayya 💔💔😍
PAGE🔟.⏩1️⃣2️⃣.
_________Yau sai nishaɗi take yi saboda zuwan su Ummi, ko wajen aiki ta ƙi zuwa saboda su, tare da Ammeey suka fara aiki girki, har zuwa lokacin da ta kintata ya kamata ta je ɗauko su, jallabiya ta zura ɓaki, ta yi rolling Vail sannan ta ɗau carkey, sneakers black ta zuwa tana fita compound. Motarta ƙirar Ferari ta shiga, already getman ya buɗe gidan sai ta yi waje, tana driving tana bin wayar larabcin da ke tashi a gidan radio, waƙan yabon Annabi ne, *Annabi* wanda take mutuwar so, tana son annabi fiye da komai da kowa, (```Allah ya ƙara ma Annabi daraja, Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ❤️🙏```). Tana jin tana bin waƙar da rausaya kai. Waƙan na ƙare wa aka sanya wani.
“Ana shuftik, itî simánà, yab-li-bi tik-tik, uhmmm......” har zuwa baitin ƙarshen, yau ta fara jin waƙan dan haka ta natsu ta gama saurara, yana ƙare wa tace.
“Hmmmm Soyayya ko hauka, amma fa mawaƙin nan ya cika maƙaryaci, ma'ana, yana ganinta zuciyarsa ta buga, then yana jin bugun zuciyar nasa yana tafiya kamar saurin agogo, kuma duk soyayya ce.” tsaki ta ja, tana danna ma motar gabanta horn da ƙarfi, motar ta tare hanya, dama waƙar yanzu ya sauya mata mood a ɗan fusace ta fito daga motan, taya za'a yi ya yi parking a tsakiyar titi, shi be shiga gidan dake gabansa ba, kuma ya tare hanya, Allah yaso ita kaɗai ce ma, da yanzu Go-slow ya haɗu.
Da mugun mamaki take kallonsa, ashe ya buɗe ƙofarma ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana waya cike da shaukin.
“Uhmmmm zuma ni banso, ni dai a'a." Baki ta buɗe galala ganin ƙaton namiji na shaƙwaɓa.
“Malam ka tare hanya." Ta faɗa cikin ɗaga murya, sai a lokacin ya lura da ita, da sauri ya fito daga mota.
“Ukthi ana asif." Tsaki taja tana komawa motarta, gyara motar ya yi yana shirin ya nufota dan bata haƙuri, Sai ta figa motan ta mugun gudu, har ta gogesa da sauri ya kauce yana zaro idanuwa waje............
_______Sun sha hanya, bayan sun sauka suka fito bakin Station ɗin da kayansu.
“Akwai rana sosai, Allah yasa Aunty Noor ta iso yanzu.” Faɗin Ruhaima. Kafin Ummi ta yi magana motar Noor ta faka a gabansu, tana fitowa suka runguma juna dan wannan aladarsu ce.
“Kun iso lafiya?."
“Alhamdullah Noor." Da haka Noor ta saka aka sanya musu kayansu a boat, sannan ta shiga motar suka ɗau hanya.
“Aunty Noor na yi missing na ki amma runguma ɗaya kawai kika min.” sai da ta furzar da iska daga bakinta tukun tace.
“Daughter I'm sorry, rai ne ya ɓaci."
“Noor."
“Na'am Aunty Fatima.”
“Ki yi tuƙi a natse, karki yi karo da abu.” sai ta yi murmushi tana rage gudu.
“Sorry Auntyna." Da haka ta ɗan sauka da fushin da take yi.
Suna isa gida, suka shiga me gadi ya shigar musu da kayansu. Ammeey ta tarbesu cike da farin ciki, zama su ka yi a falon, suna kuma gaisawa.
“Mijina ka zama ɗan lukuti sosai.” cewa Ammeey sai Abdulrahman ya yi dariya, yanada ƙiba sosai, dan lukuti ne shi.
“Babanki ne dai kaman ana miya da ruwan jikinsa, kullum tsotsewa wake yi.”
“Noor ai dole, be son cin abinci sai lemon tea, haka yake ai dole kullum ya dinga tsotsewa sai uban haske.”
“Nifa karku zaganmin Baba, Babana zo nan." Da haka Abdulraheem ya isa wajenta.
“Kuga yaro sak ubansa, ƙyaƙƙyawa, ai duk tsiya kuke sai Babana ya fi ku tsayi, dan kuwa dogon namiji ne wannan." Dariya suka sanya dukkansu.
“Ammeeey, wallahi ba zai fini tsayi ba, ai na girmesa.”
“Yauwa Ruhaima faɗa mata dai.”
“Noor ki dai yi addu'a ko irin wannan ne Allah ya baki.” murmushi ta kuma yi suna sauya hira zuwa wani. Haka wunin ranar suka sha hira, har zuwa lokacin da Abbeey ya dawo aka dasa da shi.
Su Ruhaima tuni sun yi barcin su, Abbeey ma ya shiga ciki, daga Fatima, Ammeey da Noor suka rage.
“Kwana biyar za ku yi fa Auntyn."
“Uku dai, dan kaya kala uku-uku muka ɗauko dukkan mu.” sai Noor ta yi dariya.
“Tab, ai har na faɗa ma Akee(Abba) dan kuwa Uwar ɗakina kala biyar ta ɗauko." Murmushi suka yi.
“Ai nasan halin Ruhaima, Allah ya shirye ta."
“Ameen, ai da gaskiyarta, kun daɗe ba ku zo ba ai, ta min dai-dai.” sun san ai Ammeey bayan Ruhaima za ta bi saboda takwararta ce, a lokacin da aka haife ta sun so su ɓoye mata suna amma Ammeey ta hana, tun basa iya faɗa har sunzo suna faɗa....
_______Yau tun bayan kai su Ruhaima daya dawo yake hutawa, yau dai ya samu hutu, dan kuwa Alhaji shi kaɗai ya fita, dan haka ya sanya handglobe ya gyara flawers ɗin gidan, ya cire masa ƙyau, sannan ya basu ruwa, da yake kullum yake yi kafin su fita da Alhaji, duk da ya yi da safe sai ya kuma gyarasu har da sanya ma wasu taki. Bayan ya gama ya taya Yâ Rasheed hira, daga baya suka ɗauko qur'ani suka hau bita yana maraja'a yana koya ma Rasheed Karatu. Alhaji sai misalin 10:45pm ya dawo, shi ya buɗe mai get, yana kullewa ya nufi Alhajin dan tayasa shiga da kayan hannusa.
“Marhab, Alhaji ya hanya?.”
“Alhamdillah, ai yau nace bara na barka ka huta, ai kana ƙoƙarin sosai."
“Na gode Alhaji.” ya kulle motan yana cewa.
“Ka kwanta da wuri gobe zamu fita da safe.”
“Insha Allah.” da haka Alhaji ya yi ciki shi kuma ya koma ya zauna yana mai ci gaba da maraja'ar sa, dan ya yi barci da rana shi yasa ya ce ma Rasheed ya shiga ya kwanta zuwa rabin dare sai ya amshe sa.
Alhaji yana shiga ya watsa ruwa, ya kwanta dan ya ci abinci a hanya, sai ya ji gidan babu daɗi, ko yayane idan ya gansu yana jin daɗi, sunyi waya da su dan haka be kira ba ya yi ƙwanciyarsa cike da kewansu dukkansu.......✍️
END.
> FREE PAGE'S Ya kusa ƙare wa, ba lalle mukai point din da nake so amma a haka zan datse muku, ba yawa 500 ne kawai, ga duk mai buƙata sai ya shirya. Hmmmm ko wasan ban fara ba wallahi.
_FOLLOW MM Y WHATSAPP GROUP 👇🏾_
***
_FOLLOW MY CHANNEL 👇🏾_
***
✦ 𝘿𝘼𝙍𝙀 Ɗ𝘼𝙔𝘼 ✦*
_ 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒌𝒂𝒏𝒚𝒊 𝒃𝒂𝒕𝒖𝒓𝒆._
Story and writing✍️
```PRETTY SK```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
```PAID BOOK ₦500 ONLY```