Free chapter · Read without an account
Chapter 11
by Salis M Reza · TAZARA
TAZARA!
©By S-reza ✍️
FCWA
🪀Whasop chanal
***
Last free page (Ƙarshen na kyauta ya ƙare daga wannan)
Chapter 1️⃣1️⃣
Tun misalin ƙarfe bakwai gidan na marayu ya fara ɗauka harama, duk wani ɗan gidan wanda yasan yayi katin zaɓe to ya iso ko dai ya na kan hanya ko kuma shirin zuwa gidan. Wannan dalilin yasa yau gidan aka dafa abinci mai yawa domin ƙaruwar da aka yi. Ko ina ka leƙa al'umma ne kaman ana yin wani gagarumin bikin. Misalin ƙarfe takwas na safe kuwa kowa yazo, suma jagororin yin zaɓen sun iso har sun gyara ko ina an fara hawa kan layi. Manyan gidan ne a gaba haka aka dinga zaɓar jam'i ɗaya a cikin gidan yaro da babba mace da namiji. Sai da manyan suka gama aka sake nunawa kowa gurin da zai dangwala abun saboda samun matsala. Haka aka dinga yi har aka zo kan Anty Hinde wanda tun da tazo gidan sai wani girma ake bata, musamman ma matan da suke son ƙara yi mata godiya akan abun da tai musu. Tun a gida take ta shawara da zuciyarta akan wanda zata zaɓa, tabbas Alhaji Madu ya chan-chanci ta zaɓe shi ko dan taimakon da yake musu, amma kuma yaya za'ayi ta tsallake mahaifin Saif ta zaɓi wannan, idan tayi haka bata kyuta ba. Hakan yasa zuciyarta ta kasu gida biyu domin bata taɓa yin zaɓe ba sai wannan karan hakan yasa ta na dosar gurin gabanta na ƙara faduwa, sai take jin kamar ita kaɗai ce zata bada wannan mulkin, domin ji take duk wanda ta zaɓa shi zai ci. Ta na isa gurin taga Gali a bayanta, hakan ya tabbatar mata da cewar yazo ne domin ya nuna mata kar tayi shirme. Lokaci ɗaya tsoro ya ƙara kamata. Ta sa hannu ta dangwalo abun, ta kalli gurin da kowacce jami'ya take da sunanta da hoton ta. Sarai ta gane ta Alhaji Madu da ta Sadau, har ma da sauran jam'iyoyi ƙananan da suke jikin takardar. Ta na zuwa sai kuwa ta dangwalawa Sadau a na gwamnoni, ta naɗe takardar ta saka ta cikin akwatin da babu takarda ko ɗaya a ciki sai tata. Duk da yadda gabanta ke faduwa bai hana ta juyowa ba, suka haɗa ido da shi. Ai da sauri ta kawar da kanta ta bar gurin da sauri ba tare da tayi magana ba. Haka shima Abbati lokacin da aka zo kansa Sadau ya zaɓa, sai ya zama su biyu ne kawai suka zaɓe shi sai kuma Hafsa da yanzu suka ɗinki da Abida har ma ta ce mata kar ta zaɓi Alh Madu. Gefe guda kuma Sani da Yakubu ne tsaye bayan sun gama kaɗa tasu ƙuri'ar suna ɗan hira kowa na jiran iyalansa. Suna tsaye a gurin kuwa sai ga Saddiƙa da Yusra ɗin sun fito cikin shigar sabbin dogayen riguna iri ɗaya. Hatta jakar hannunsu ma duk iri ɗaya harda wayoyinsu, sunyi kyau sosai fuskokinsu sanye da takunkumi suna kallon kowa ɗai-ɗai. Abun da yake rage musu Capacity shine rashin Mota, itama suna gaf da mallaka kaman yadda a kai musu alkawari.
Suna isa gurin yayi sallama da Sani ya saka su a gaba ya na mamakin shawarin da sani ya bashi, tafiya suke amma ƙare musu kallo yake ya na haɗiyar yawu, ya rasa ma wacece tafi burge shi yanzu a cikin su, domin tun farko Yusra yake so, duk da a lokacin ba shi ɗaya bane ya nuna yana sonta amma taƙi yarda da kowa, shi har ma walaƙanci take masa a duk lokacin da ya zo gareta da maganar so, daga baya kuma sai tazo da kanta ta sanar da shi muddin yana sonta to sai dai ya haɗa su biyu ya aura. Ya ce ba zai iya ba domin ba shi da kuɗin auran mata biyu ko ita ɗin ma dai da taimakon Allah, nan suka sanar masa da cewar su zasu bashi gida harma kayan aure, amma za'a bari akan shi yayi komai, gidan ma zai ce shi ya kama haya ne, jin wannan garaɓasar yasa ya yarda da gudu kuwa, haka aka ɗaura ba tare da kowa yasan gaskiyar maganar ba, sai dai lokacin da ya baiyanawa su Baba Manu cewar mata biyu zai aura abun ya bawa Kowa mamaki, barin ma sauran samarin da suke sonta wanda suka fishi fasali, sai dai daga ranar wasu suke masa kallon mai kuɗi amma baya son nunawa duk da dai gashi ga yadda yake. Tafiya suke amma ji yake kamar yaje ya rungume su ta baya ganin yadda suke tafiya suna rungume juna suna wasa da dariya. Suna zuwa kusa da unguwar su ya ce su karasa gidan yana zuwa. Haka suka wuce shi kuma ya nufi gurin samun mafitarsa.
Anty Hinde ta kalli Abbati da Abida da har sun ɗan rame tsabar wahala da rashin abinci. Ta zaro wayar ta da ta saya ta mikawa Abbati, sannan ta ce "Ina so ka riƙe wannan wayar gobe kaje ka sayar da ita, kuɗin na da yawa, sai ka sayi ƙarama kasa wannan layin a ciki, sauran kuɗin sai ka fara yin wani abu, dan Allah Abbati ka tsaya ka natsu kasan abun da kake yi, kuma ka dinga kirana, akwai numbar ta a ciki zaka ga an rubuta Anty Hinde, na san ita Abida ba za'a bari ta riƙe waya ba, amma kai za'a barka, dan Allah Abbati ka natsu, yanzu kun kai lokacin da ya dace kusan ciwon kan ku, ku tsaya ku gina rayuwar ku dan Allah, kaga kai da Abida yanzu kowa ya saka muku ido, amma yanzu idan kuka fara yin wani abu naku babu wanda zai zargi komai kunji". Abbati ya kalli wayar da take cikin kwalinta ya ce
"Waye ya baki naga sabuwa ce?"
"Zan faɗa maku amma ba yanzu ba".
"To ita wannan waye ya baki?" Ya nuna ta hannunta.
Ta ce "Uncle Gali ne ya saya min ita ranar".
Suka kalli juna cike da mamaki, Abbati ya kasa haƙura ya ce "Kuma da kuɗin sa ya saya?"
Ta hararesa tana kawar da maganar daidai lokacin da ta ciro atm ɗin ta a jaka. Tun ranar take ta nazari da zuciyarta akan ta bawa su Abbati atm ɗin ta ne ko ta bari a gurinta. Wata zuciyar na cewa ta bar musu idan yaso in zata buƙaci wani abu sai ta kira Abbati, domin kar ta bari a gurinta kuma Uncle Gali ya gani. Wata zuciyar kuma ta na cewa kar ta basu kuma suje suyi wasa da kuɗin, domin tana tsoron halin mutum, domin tabbas bata zargin su akan zasu ci amanar ta, amma dai yaran basa jin magana. Haka ta hakura akan zata basu kawai, shi yasa tun a hanya yau ta sake cire dubu ɗari biyar tasa a jaka. Kuɗin da ya rage a ciki miliyan takwas da ɗari biyar. Ta ce "Wannan katin cirar kuɗi ne nawa ne, Abbati da Abida ina so ku natsu da kyau ku saurare ni, duk gidan nan babu wanda na yarda da su kamar ku, kuma kuma nasan kun yarda dani, ban fadawa kowa yadda na samu kuɗin nan ba, haka ba wanda yasan nawa ne, na zaɓi na baku atm ɗin ne ku rika shi a gurinku domin bana so Uncle Gali ya gani, kuɗin ciki suna da yawa, dan Allah ku rike min alƙawari, ku cire duba dari biyar ku ƙara akan sauran kuɗin wayan ka kama sana'a Abbati wacce zaku riƙe kanku, ku ɓoye wannan atm ɗin kar wani ya gani, idan ina bukatar wani abu zamuyi waya da ku". Ta ƙarasa maganar kamar da ɗan fargaba a muryarta. Abida ta kalli Abbati cike da son yin tambaya. Ta ce "Anty nawa ne a ciki kuma waye ya baki?" Abbati ya gyaɗa kai alamar shima tambayar da yake son yi kenan. Ta ce "Yanzu fa na faɗa muku cewar bana son tambaya, zan faɗa muku komai amma ba yanzu ba, kuma kuɗin ciki suna da yawa miliyan takwas ne". Ta ƙarasa tana kuma nuna musu lombobin cire kuɗin. Abbati ya sake juya katin yana jin wani abu na faɗuwar gaba na zuwar masa. Ita kanta Abida saida gabanta ya fad'i jin yawan kuɗin. A haka Anty Hinde ta tafi ta barsu bayan ta ƙara jaddada musu cewar su kama yin wata sana'ar, kuma kar suyi wasa da kuɗin su riƙe mata alƙawari. Magana sukayi da ido kafin suka bar gurin bayan Abbati ya ɓoye wayar da katin.
Cikin gari kuwa haka ake ta fama da zaɓe ta ko ta ina. Ɓangare Saif kuwa kaman yadda yayi alƙawarin cewar ranar zaɓe zai yi video kuwa tabbas yayi a lokacin da yake zaɓar Alhaji Madu. Hakan yasa al'umma suka dinga zaɓar Madu, duk da cewar shima Sadau ɗin mutane nata sabar sa. Sadau dai yana cikin tashin hankali da mawuyacin yanayi, domin dai har yanzu basu ƙara magana da Hajiya ba, gashi ta bashi zaɓi biyu, kuma baiyi ko ɗaya ba, domin dai gashi yau ake yin zaɓe. Haka itama Hajiya Zinaru ta kwashi iyalanta suka kada ƙuri'a ita da mijin nata da ƴar ta ɗaya, wanda saida gidan jaridu suka ɗauka ana nunawa mutane lokacin da yayi nasa zaɓen. Nan suka koma gida suna kallo a tv yadda ake ta hada-hada, Hajiya Zinaru dai ta sake kiran malaminta ya tabbatar mata da cewar sune da nasara, hakan yasa ta ɗora ɗaya a kan ɗaya tana tare da bakin manyan mata da suka zo gidan domin taya ta zama, tasa anyi girki kala-kala da abubuwan sha. Shi kuwa Sadau ɗakin sa ya shiga ya daura a alaula yana ta addu'a, domin dai tabbas yana son mulkin nan, ko dan ya share laifin da yayi a baya, domin da zuciya daya yake son yin shugabancin garin Yalwa.
Haka shima ɓangaren Alh Madu, sosai ya saki kuɗi ta ko ta ina kuɗi kamar shara haka yake rabawa ga dukkanin mazaɓa, wasu gurin za'a tsaya ace duk wanda ya zaɓe shi za'a bashi dubu uku, wasu ace za'a basu shinkafa kwano biyu wasu taliya guda biyar. Da haka aka dinga yin zaɓen. Shima sai da ya je ya fara zaɓa da shi da ɗan sa da kuma Alu. Shima sai da akayi video, sannan shima Gwamnan da yake kai ɗin a kai masa video. A cikin wannan ranar Bilal ya fadawa Alu cewa a samo masa yara guda biyu ƙanana domin ya huta da su. Ai kuwa suna dawowa Alu ya ɗauki Mota. Har ya bar gidan Bilal ɗin ya kira shi ya dawo, ya fito cikin shigar kayan ƴan Ball riga da gajeren wando, sai wani farin taƙalmi ya shiga motar suka fita. Haka suka dinga yawo a cikin garin bai ga wacce tai masa ba. Har sun wuce wata mata ita da ƴarta suna tafiya a bakin titi, Bilal ya ce su dawo da baya. Haka suka tsaya a gaban su. Bilal ya ce "Wannan yarinyar tayi". Ya faɗa yana lashe bakin ba. Alu ya ce "Kaman fa tare suke da mahaifiyarta" Bilal ya daka masa tsawa ya na faɗin "So what dan tana tare da uwarta, Meye amfaninsu a duniyar, idan ma wani abu ya shiga tsakaninmu ba su zasu ci riba ba, to ko uwar nake so mai ta isa tayi?". Alu ya haɗiye yawo ya buɗe motar ya fito. Su kuwa suna tsaye domin an tare musu hanya gashi yamma ce suna sauri zasu isa gida domin daga gurin zaɓe suke, bayan tayi nata ne ta biya ta gidan kitso ta ɗauko yarinyar tata da a kaiwa kitso ƙanana masu yawa. Ya ƙara so gurin yana yin sallama kuma yana ɗora idonsa akan ƴar yarinyar da Bilal yake magana akai. Wannan ai ko sha biyu ba zata yi ba, amma dai fara ce gashi kanta ba ɗankwali kitson kanta kawai ya kai a sake kallonsa bare fuskarta. Mata tayi shiru bayan amsa salma. Cikin muryarsa ta mata ya ce "Amm Hajiya dama gurin wannan yarinyar taki nazo idan ba damuwa, ina son zanyi magana da ita domin ta burge mai gida na". Ya faɗa yana nuna cikin motar. Ta kalli Alu ta kalli ƴar tata kuma ta kalli motar da ake batun mai gidan na ciki. Ta ce "Burge wa wacce iri bawan Allah?" Ta tambaya da mamaki. Ya ce "Karki damu ba komai bane, zaku samu kuɗi muddin ta amince da shi". Matar ta ce "Bawan Allah amincewa wacce iri, Ni ban gane ba, domin ni dai bani da wata yarinya da har zata ma iya tsayawa da saurayi idan ma haka kake nufi". Alu da dama shima kunya ba isar sa tayi ba, ganin tana ɓata masa lokaci kuma yasan halin uban gidan nasa yanzu zai hasala, sai kawai ya baiyana mata abun da suke nufi. Ya ce "Hajiya duk fa mune anan daga ni har ke, kin san komai na san komai, wannan yarinyar taki ce ta burge mai gidana yake so ya ɗan hutu da ita, zai baku ko nawa kuke so". Ya ƙara sa daidai lokacin da Bilal ya danna homm ɗin motar ganin yana ɓata masa lokaci. A daidai wannan lokacin kuwa wannan matar ta ɗauke fuskar Alu da wani irin mari, wanda sai da Bilal dake cikin motar ya tsorata domin idonsa na kan su. Ganin haka ya fito da sauri ya nufi gurin. Ya na zuwa ya ɗauke matar da mari, sannan ya kama hannun yarinyar da nufin ya jata.
*****
ANTY HINDE
Sai misalin ƙarfe biyar ta bar gidan marayu domin kamar kullum idan har taje gidan sai ta shiga ko ina, bare yau da take da kuɗaɗe a jikinta, haka ta dinga rabawa yadda ba za'a gane ba, daga mai dubu ɗaya sai biyu. Su Baba Manu da Tani kuwa haka ta basu dubu biyar-biyar suna ta godiya. A lokacin ne ma Baba Manu ya fara mata magana akan gashi auran da yayi mata ya zama mata alkairi, yanzu da wanda ta kawo ɗin ne da yanzu yana ci mata mutunci domin ba zai girmama ta ba. Ita dai kawai murmushi tayi bata ce komai ba. Tun tana hanya take tsoron gamuwarta da Uncle Gali domin bata manta irin kallon da yayi mata ba. Tun da taga mashin ɗin sa a fake ta gane ya dade a gidan. Haka ta tura ƙofat ta shiga da sallama. Ta same shi yana cin abinci. Tai masa sannu zata wuce ya mike tsaye yana tsayar da ita. Ya ce "Meye dalilinki na zaɓar Sadau, sannan me kuke ƙullawa da su Abbati, domin kuwa daga ke sai shine kawai kuka zaɓi Sadau, shin me kuke ƙullawa, kuma a ina kuka san shi waye ya baku aikin ko Meye dalili, wallahi kika faɗa min ƙarya sai na kusa yin ajalinki a cikin gidan nan na rantse da girman Allahu". Ya ƙara sa yana ƙara zare mata ido. Sosai jikinta ke rawa fiye da ƙima domin yau ya ƙara rikeɗe mata. Ta ce "Wallahi babu komai kawai dai na zaɓa ne". Ta na rufe baki ya ɗauke fuskarta da mari ya ƙara mata. Ya cigaba da cewa "Idan baki faɗa min wanda ya saka ku ba Allah yau sai dai ki amsa wani sunan dan uwarki, tsabar kin raina ni ina kallonki kina kallona amma ki zaɓi wani wawa soko da baki taɓa sani ba, ga wanda ya inganta rayuwar da kikeyi". Anty Hinde ta fashe da kuka mai ƙarfi. Ya sake ɗauke ta da mari, ya sake kai mata sai ta goce ya samu jakar hannunta, sai kuwa ga jaka a ƙasa ga kuma kuɗaɗe ɗauri-dauri ga kuma wasu a baje a cikin palon. Cikin second ɗaya kukan Anty Hinde ya tsaya chak, shima sai da ya ɗauke wuta na minti ɗaya. Kallon kudaden yake yi kusan dubu ɗari biyar yake kallo domin ɗauri huɗu a daure suke sai ɗaya daga gani an taɓa ne. Kallonta yayi ganin yadda itama take kallon kuɗin kamar dai ta shiga matsanancin hali.
*****
GIDAN YAKUBU
Tun yana hanya yake ta tunanin yadda zai aiwatar da wannan shawarar da sani ya ba shi. Yau kwanan Yusra ne kuma da ita za'a fara. Maganin ƙarin sha'awa Sani ya ce yaje gidan sa ya karɓa, yace masa muddin wata tasha to fa dole ta bada kai bori ya hau, ai kuwa babu wani tunani ya amso bayan sun yi alkawarin zai biya idan aiki yayi. Sai dai gashi a kwano ɗaya suke cin abinci, kuma da mutum ɗaya yake so ya fara. Hakan yasa bai iso gidan ba sai bayan Isha. Yana shiga yaga ba kowa a palon. Sai dai kafin ya gama shiga sai ga Saddiƙa ta fito tana tambayar waye domin taji ana buga ƙofar. Ganin shine yasa tai masa sannu da dawowa tana ƙarasowa palon ta kunna kallo. Ta na zama Yusra ma ta fito. Zama tayi ba tare da tai masa magana ba. Yakubu ya ce "Wai ko ba'ayi abinci bane?" Yusra ta ce "Yau ai kasan bama gida dama kai muke jira ka dawo ka samo mana abun da zamu ci. Yusra ta ce "Ni kam bana jin yunwa ma, ku dai ku samo kuci". Saddiƙa ta ce "No sai ki kwanta haka a'a fa, bari ko nama ne sai muje tare kawai mu sayo". Shi dai bai ce musu komai ba har suka yanke cewar shi zai sayo. Haka suka bashi kuɗi ya sayo musu tsire ya kawo musu. Shi kuma ya shiga kitchen ɗin ya haɗa indomi. Ya na kitchen ɗin yana ta addu'a. Ai kuwa sai ga kiran Saddiƙa wai ya kawo musu abun sha. Dama suna da Banbancin ra'ayi na abun sha, shi yasa ya buɗe wanda Yusra tafi so ya zuba abun sannan ya kai musu. Yana shiga palon kuwa ya samu tare suke cin naman kaman yadda yayi hasashe, shi yasa ma bai zuba a ciki ba. Ya koma ya juye nasa abincin ya fito ya zauna yana ci yana kallon yadda take shan kayanta har ta shanye, a bunka da Yakubu, shima sai ya zuba a cikin ruwan shan sa ya sha. Sai da ya tabbatar an samu minti goma kafin ya kallesu ya ce zaije ya kwanta. Sukai masa sai da safe ya shiga ɗaki. Shiru-shiru bai fara jin komai ba har kusan minti ashirin, daga nan kuma ya fara jin kamar barci ga kuma zufa da yake karyo masa, daga haka kuma jikinsa ya fara sakewa, sai kuwa ya tashi zaune yana jin wani irin sauyin da bai taɓa jin irinsa na jikinsa ba, take yaji gashin jikinsa na miƙewa kaman ana sa hannu ana tsayar da su. Itama haka Yusra bacci ta fara ji mai ƙarfi da kuma wani irin mutuwar jiki, hakan yasa tacewa Saddiƙa zata je ta kwanta ne. Itama ta kashe kayan kallon ta tafi. Ta na shiga dakin ta samu Yakubu a zauna a kan gadon ya takure waje guda domin ya gama jiƙuwa. A lokacin da ta haɗa ido da shi take babban lamarin ya ziyarceta. Ji take kamar ana janta izuwa gare shi, idanunta har wani irin lumshewa suke yi tsabar abun ya shige ta. Ta na zuwa kuwa ta miƙa masa hannu ya kama. Ya jata kan gadon ya shiga rabata da kayanta har tana taya shi, shima ta taya shi ya cire nasa. Nan take suka fara aiwatar da abu cikin fitar hsitaci domin kowa ji yake idan bai samu biyan bukata ba zai iya mutuwa, ihunsu ya cika dakin wanda hakan ya sa Saddiƙa yin shiru tana son gano ihun Meye haka. Jin yana karuwa yasa ta fito daga nata ɗakin ta nufi palo, sai dai kafin ma ta ƙarasa ta ji ihun Yakubu yafi tashi domin dai buɗe baki yayi ya sakin ihu abun sa, ɗakin Yusra ɗin ta nufo gabanta na faɗuwa, ai kuwa ta hango ƙofar a buɗe domin basu ma rufe ba. Tana sa kai tayi mummunan gani, ga love ɗin ta da mijinsu a wani irin yanayin da bata taɓa kawo wa ba. Farko mutuwar tsaye tayi, domin ta kai minti guda ta rasa mai ya dace tayi, ga shi har lokacin basu ma san ta shigo ba, sannan yanayin yadda suke yin abun dama kamar sun saba domin gashi haɗin kai take bata. Zuciyarta ce ta shiga bugawa wani irin kishi da bata san tana yiwa Yusra bane ya tsaya mata a wuya, da gudu ta nufi kitchen ta ɗauƙo wuƙa domin shine kaɗai abun da take jin zata iya yi mai sauƙi a irin wannan lokacin, kawai ta kashe Yusra domin ta ci amanar ta.
*****
GIDAN MARAYU
Acikin wannan daren da akayi zaben ne Abida da Abbati suka dinga yin shawara akan yadda zasu yi. Sun Dade suna abu ɗaya kafin kawai suka yanke cewar suje suyi amfani da kuɗin Anty Hinde su sayi gida a cikin garin Yalwa subar wannan garin, in yaso daga baya sai su dinga biyan ta har su gama. Farko sunƙi yarda amma dai kawai suka tsaya akan haka domin kuwa an ƙara sako su a gaba saboda zaɓen da Abbati yayi. Ga shi har yanzu kowa na da tabon maganar da aka faɗa musu, na cewar Abbati ɗan gidan mahaukiciya ce, ita kuma a kwali aka kawo ta, sosai wannan maganar idan suka tuna da ita sai suga to ai babu amfanin zaman su s cikin gidan. Abida ta je ta dauko musu wancen kuɗin nasu, sai da dare yayi nisa sosai kowa yayi barci gidan tsit suka saci hanya da nufin fita. Sai dai suna zuwa kusa da katangar gidan suka ga an haske su da hasken fitila, kasancewar cikin dare ne. Hakan yasa suka tsaya suna bin hasken da ido har aka karaso. Hafsa ce ta ƙara so gurin har tana haki ta ce"Abida zan biku dan Allah?" Ta faɗa a hankali". Basu tsaya yin wani magana ba suka nufi waje. Sai kuwa gasu a wajen gidan marayu domin ta katanga suka haura. Suka cigaba da tafiya saida suka fita daga cikin garin gaba ɗaya sannan suka samu guri suka zauna domin ƙara sa kwana...📝
Tom taku ta same ku ƴan amanar S-reza. Wani abun ba'a cewa komai. Daga yau dai free page ya ƙare, kuma dai kun sani kuɗin littafina 500 ne kawai duk daɗin sa kuma duk yawan sa. Bana cika baki akan labari, ku kanku nasan kuna hango irin tashin hankalin da zai faru a cikin labarin na. Ga kaɗan daga ciki. Shin Bilal da Alu zasu samu nasarar ƙwatar wannan yarinyar a gurin uwarta? Hamm menene zai iya ƙwatar Anty Hinde a gurin Uncle Gali domin dai abun da yake zargi ne ya gani, a ina zata faɗa masa cewar ta samo wanna kuɗin har ya yarda?" Hahahah bari na fara dariya kafin na yi tunanin abun da zai biyo baya a gidan Yakubu. Shin wai yaya ma za'ayi Saddiƙa ta yarda da Yusra, kuma yaya zaman ma zai kaya bayan taci amanar ta, shi dai kam malam Yakubu dai yau take Ranar sallah a gurin sa😄. To ga kuma Abida da Abbati sun baro gidan marayu, shin ina zasu dosa? Kuma kuna ganin sun kyutawa Anty Hinde kuwa, kuma yaya zata kaya dasu a cikin garin Yalwa idan sunje? Tom gashi dai anyi zabe saura jiran sakamako, waye zai ci su Hajiya Zinaru ne ko su madu?. Ga kuma tsakanin Saif da iyayensa ta yaya za'a shirya, shin idan suka ci zaɓen yaya zai yi, kuma idan suka dad'i mai nene ribarsa? Wannan littafin ɗaya ne tamkar da biyar, akwai cin zarafi da ha'incin da yaudara, da kuma darasi mai yawa a kowanne ɓangare na cikin littafin.
Duk wacce take son karantawa zata biya 500 ne a saka ta a cikin group, babu jira gobe zamu cigaba da posting, domin tun ranar farko ma wasu suka fara biya. Kar ku bani kunya kaman yadda kuka san bana baku. Ga account number ***, Adam Salisu Opay. Sai a turo da shedar biya ta nan ***. Ko ayi min magana ta Whasop. Kar ku bari ayi babu ku. Muna da telegram group da whasop duk wanda kuke so. Ga kaɗan daga cikin littafan S Reza...
Amera da Adam
Ina muka dosa
Tsinuwar uwa
Uwata ce sila
A bar wa rai
Addininmu
Soo nee
Mutun da aljan
Gidan arna
Chakwakiyar soyayya.
Da dai sauransu.
Mu haɗu a VIP group Domin ci gaba da Tazara ***