Free chapter 路 Read without an account

Kamar da wasa pg 4

by Fatima Isah 路 KAMAR DA WASA

KAMAR DA WASA馃挊

Fatima Isah

(Mrs Umar)

Page 4

Ta Dikko 蓷akin kara

(Katsina state

Kamar yadda Ummie ta bada sako ta dafa masu 蓷an wake haka kuwa aka yi tana cikin rabawa maman Emma ta iso wajan ta da tsohon cikinta.

"Jannat yau 蓷an wake ake mana to ai kam zanci"

Baki na ta蓳e tare da juya kai tamkar bazan tanka ta ba kafin na ce.

"Ai da ya ke soja na biyan kowa sai kije ki yi kema?"

"To yau kuma abin ya dawo kaina"

Baki na sake murgu蓷a mata tare da cewa.

"Wannan kuma ke kika sani"

Ta bu蓷e baki zata sake magana na 蓷auki kwanon 蓷an wakena na wuce 蓷aki. Dan ba karamin haushi matan layi ke bani ba saboda ina sane da irin gulmata da suke na bu蓷e babin zagina.

"Amma yanzu aunty Jannat ko ba komi matar nan yaci ace kin bata abinci nan ko 蓷an koyarwa irin ta addinin mu"

"To banyi niyya ba kuma babu wanda ya isa yasani abinda banyi niyya ba. Amma tunda kai kaji ka gani zaka iya bata naka"

Kai Ahmad ya girgiza tare da cewa Allah ya ganar dake aunty Jannat"

"Amin dan uban..."

Bata karasa ba ta yi shiru saboda shigowar Ummie tare da daka mata tsawa ta ce.

"To sababba ke da wa kuma, you ba. You will never change"

"To Ummie kinsan meya faru ne"

"Rufe min baki mutuniyar banza Amina meya faru ko da yake duk jirgi guda ya kwaso ku, Ahmad fa蓷a min"

Fuska Ahmad ya 蓳ata cike da takaicin 'yar uwar ta shi ya fa蓷awa Ummie duk abinda ya faru tun daga zuwa 蓷ibar ruwansu har dawowar su ya zuwa yanzu.

"Kai Jannat wannan mugun hali naki na bani tsoro wallahi yanzu ke bakiji kunyar yiwa oga Musa rashin kunya ba. Yanzu kina nunawa su maman Emma mu musulmi muna da wani hali ko?"

Baki ta turo cike da jin haushi ta ce.

"To ai ba ni na ce musu su yi ta gulma ba. Waye ya ce su zauna su yi ta lissafin rayuwar wasu? Ni dai gaskiya bana son shiririta, duk wanda ya tsare min hanyar rayuwa, sai na tsare masa."

Ummie ta girgiza kai cike da takaici, ta ce,

"Wallahi Jannat ke ba zaki ta蓳a chanzawa ba. Haka zakiyi ta biyewa zuciyarki har rana ta waye ki ki zo kina da na sani. Ko wa yan gaya maki ki zama mutuniyar kirki haka?"

Ahmad na gefe ya yi ajiyar zuciya, yana 茩o茩arin kai ruwa daya aje a bakinsa, Amina kuwa ta kurawa Jannat ido, cike da damuwa.

Ummie ta cigaba da cewa,

"Ina gaya maki Jannat, mace da ke da matsayi a al鈥檜mma ba a santa da zagi da magana marar da蓷i ba, a santa da ladabi da biyayya. Wannan halin naki sai yayi sanadiyyar..."

"Ummie dan Allah ki yi shiru kada ki yi min baki. Kuma sai na zauna ina tausayawa mutanen da suke ta tunzura ni da gulma da raini. Life isn鈥檛 for pleasing people. I鈥檓 not that girl."

Amina ta girgiza kai tana mamakin tsagwaron rashin kunyar da Jannat ke nunawa.

"Allah ya shirya ki aunty Jannat, wallahi kina gaban malamin sakandare sai su 蓷auka baki zauna aji ba"

Jannat ta 蓷aga kafada.

"Well, good for them. Ni ba wanda ya isa ya toshe min baki. In ba haka ba me zai sa har yanzu matan layin nan basa barci idan sun ji sunana? Ko gaisuwa sai sun girgiza kamar ana yanka musu hanta."

Ummie ta zaro ido tana kallon ta.

"Kai Jannat? Ai wallahi ba girma ba hankali, idan kika ci gaba da haka sai kin rasa komai. Kin fi 茩arfin nasiha ne? Kuma ki sani ba har abada zan zauna ina kallon ki kina wulakanta kowa ba."

Ahmad ya dube ta cikin tausayi.

"AuntyJannat ko da kinsan ana tsanarki, ai ba dole bane ki tsani kowa ma. Ki sauya hali ki ga yanda rayuwa zata sauya miki."

Jannat ta juyar da kai.

"Hmm... sauya hali? Sai dai ku sauya tunani. I'm not here to please anybody. Su zauna da gulmansu ni kuma zan ci gaba da zama Queen of Drama."

"Ai ke da shaidaninki sai ku ci gaba"

Shiru 蓷akin ya 蓷auka, Ummie ta juya tare da girgiza kai, cikin zuciyarta tana jin ba茩in ciki da takaici. Sai ta kalli Amina da Ahmad, ta ce

"Ku ci abincinku. Ni na gaji da maganar banza."

Jannat ta juya ta shige bedroom tana huci kamar wuta, kwanon 蓷an wakenta a hannu. A ranta tana cewa

'Ni ce Jannat. Idan suka so su 茩i ni, idan ba su so su 茩i ni sau dubu. Ba na ro茩on soyayya daga matan gulma.

******

Washegari

Da safe, kafin rana ta haska sosai, hayaniyar yara da ihun gaisuwar bariki ta kara蓷e block. Jannat tana zaune a bakin kofar kitchen, tana goge takalminta da brush kamar yadda ake wa 'sabin sojoji horo. Wani kallo take wa kowa kamar ta fi kowa.

Sai ga Maman Latifa da wasu daga cikin makwabta sun fito, kowacce na 蓷auke da tsintsiyar shara.

"Jannat, ba za a kawo mana ruwa ba ne kamar yadda aka saba kuwa?" Maman Habeeb ta tambaya tana zura mata idanu.

Jannat ta 蓷ago kai da dabara ta ce,

"Wanda ya saba kawo muku ruwa yana da kafa, ya kawo muku. Ko ni ce tap?"

Dariya mai zafi ta kwashe da ita tana mur蓷e idanu. Maman Habeeb ta ce,

"Wallahi yarinya kin wuce gona da iri. Kin raina mu!"

Jannat ta ce,

"Toh madam, ni ban raina ku ba. You people just like forming importance. Wallahi I鈥檓 not impressed."

Duk sai suka 蓷an tsaya suna kallon ta. Da suka ga ta 茩i dawowa da martani, Maman Jamila ta ce da murya mai kauri,

"Wai mahaifinki soja ne, amma kin kasa ladabi? Shekarunki nawa baki iya gaisuwa da girmamawa ba?"

Jannat ta mike tsaye, da girmamawa amma da harshen tsokana.

"Ina kwana manyanmu. Lafiya? An tashi lafiya? ku daina yin kamar za ku cinye ni"

Ummie ta fito tana daure fuska.

"Jannat! Ki dawo ciki yanzu nan!"

Jannat ta ce,

"Ummie ki bar ni da su. Wallahi sai sun gane ni ba yar dare bace. Ina da yanci Zage su ba zai canza gaskiyar da nake ciki ba."

"Allah ya shirye ki!" In ji Ummie.

"Ni dai nace amin, amma wallahi su ma sai sun farka daga abinda suke min. We can't all be pretending while dying inside."

**

A gefe guda, matan bariki suka fara gulmata ko wane block maganata ake yi

"Wannan yarinyar za ta jawo wa mahaifinta matsala. An ce sam ta zame masu 茩arfen 茩afa"

"Idan har suna da dangantaka da ofis, ya kamata su 蓷auki mataki. Yarinya na bariki amma kamar tana zaune a kauyen natsinta."

"Kam ai kema kisan waye oga Adamu zani ce ta tadda muje"

"To Allah kyauta"

Wannan hira duk a wani layi ne daban ake yinta.

**

A 茩arshe, Ummie ta kulle 茩ofa ta koma ciki. Amma zuciyarta cike take da dardar, dan tana jin kamar wata gagarumar matsala na shirin afkuwa ko dai daga ofis, ko daga cikin danginsu.

#SON ZUCIYA

#SOYAYYA

#MAKIRCI

#YAUDARA

Yanzu ne wasan zai fara kudai ku tsaya a kan a kwatunan wayoyinku ni kuma zanci gaba da nisha蓷antar daku馃グ馃グ馃拑馃徎

#Bemty's kitchen

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol