Free chapter · Read without an account

4

by Hijjart Abdoul · ZUNAIRAH

*********Washegari da safe a mugun gajiye ta tashi daƙyar ta tashi ta yi wanka ta wuce masallaci dan taga late ta tashi. Suna zuwa meditation kuwa kafin gari ya yi haske ɓoyewa ta yi a wani wurin clinic na su ta kwanta sai bacci. Har sai da gari ya yi haske sosai har an sallame su sun fara parade. Wani Soja ya ganta ya tashe ta tace masa ai kan ta ke ciwo. Daman ga idan ta ya yi luhu-luhu na bacci ga layi da take yi. Dole ka yarda bata da lafiya. Hakan yasa shi cewa ta wuce Clinic ta kwanta a kuma bata magani, daɗi kasheta, tana zuwa clinic aka ce ai ba'a attending mutane sai lokacin break fast ko an tashi daga parade ground idan ba emergency ne ba. Ji ta yi kamar ta shaƙe Chief ɗin Clinic da ya hana a duba ta, tana gunguni ta fito ta dawo parade ground ɗin duk ta yi laushi da ita, kana gani zaka san bata saba da wahala ba. 

Rayyan kuwa be wani tsaya tambayar ta daga ina take ba, yace ta hau layi, ita ce a gaban dake ita group ɗin team na su da ya kasa su zuwa kashi uku. Haka ta fito gaba suka cigaba da inda suka tsaya. Tana yi kamar ta faɗi haka take ji.

"Sir! 

Ta faɗa a hankali tana tsayawa daga yin match ɗin da yasa su sannan ta juyo. Ganin ta tsaya ya sa dukkan ƴan team ɗin tsayawa suma.

"Sir, please I want to pee". 

"Pee in my mouth". 

Ya bata amsa yana yi mata wani ɗan iskan banzan kallo. Sake turo baki ta yi sosai kafin ta cigaba. 

"Sir! Ni gaskiya ba zan iya wannan ɗaga muryar ba ina yin magana". 

Ta faɗa da iyakar gaskiyarta. Wani ɗan iska kallo da ya yi mata ne yasa ta ƙunshe sauran maganar ta tana cigaba da abinda suke yi. 

"Zo". 

Ya faɗa mata a hankali yana sake tamke fuskarsa sosai. A hankali ta je tana jin faɗuwar gaba sosai. Kamar ta je haka take ji. 

"Come". 

Ya sake faɗa mata ganin yadda take wani sanɗa-sanɗa. 

"Yi min up and down? 

Buɗe baki ta yi zata yi magana kawai sai hawaye sharrrr suka zubo mata. 

'Buddy duk kai ne ka janyo min wannan abun. Wallahi duka kai ne. Ba dan kai ba da duk haka bata faru ba'. 

Ta faɗa a ranta tana motsi da baki tana kuma yin up and down ɗin. Ga hawaye da take faman zubarwa. Tun jiya da ta zo ake azabtar da ita a wannan shegen camp ɗin. Kuma ba kowa ba ne sai wannan mugun. Ayi mutum sai mugunta, ya ɗauka tsayi da daren mutuwa, ga kuka ga gunguni ga punishment. 

Har aka tashi aka tashi suna abu ɗaya, ita tana Up and down su kuma suna parade ɗin ƙaddara, dan duk wanda be iya ba joining ɗin ta yake yi. Tuni suka sake shiga hankalin su sosai fiye da na farko. Iya ka gajiya kowa ya gaji, gashi babu damar yin wani motsi ko nuna gajiyawa. Idan ka yi mistake ka ci ubanka a hannun Oga Rayyan. Abin sam be yi musu daɗi ba. Haka kowa ya ja jikin sa suka wuce hostel na su. Yayinda ita kuma ta je can wurin wani building ta zauna sosai yake da nesa da hostel ɗin su. Kawai barandar wurin ce ta yi mata ga iskar wajen. Ta ciro wayar ta ta ga missed calls na ƴan gidan su.

"Nanna". 

Ta faɗa bayan ta danna masa video call. Yana zaune a office shima, kyakkyawan Murmushi ya sakar mata sosai yana kallonta cike da wani irin so mai tsanani. 

"Babyn Nanna me ya faru? 

Ya faɗa cike da kulawa ganin hawayen da ke kwance a cikin idan ta sosai. Ai be gama rude baki ba ta saki wani shegen kuka sosai. 

"Nanna ni nagaji, kullum sai wancan Oga Rayyan ɗin ya sani tsallen kwaɗo ya yi ta min mugun ta, yau kawai daga yin ƴar magana ya sani up and down. Ƙafana Nanna kamar ba'a jikina ba. Baka ji yadda cinyana ke min ciwo ba. Bayan abinda ya sani jiya. Shine yau ma ya sake sani wani. Nanna ni kawai nagaji zan dawo". 

Ta faɗa sosai tana zubar uban hawaye. Wallahi sosai ya ji tausayin ƴar ta sa, amma sai de kuma ko a fuskarsa be nuna ba. Calmly ya kalle yana ɗa ajje biron dake hannunsa. 

"Me na ce ki yi? 

Ya faɗa mata yana cigaba da kallanta. Shiru ta yi tana turo baki, sai de hawayen yana cigaban da zubowa a fuskarta. Ɗan murmushi ya yi ya ce. 

"Ka yi haƙuri, ni auren ne bana so nan kusa, na fi so na yi karatuna". 

"Karatun ki zaki cigaba a ɗakin mijin ki. Ko yau Daddaa sai da ta min maganar ku ke da Samha. Dan haka daga zaran kin dawo za'a yi auren ku. Daƙyar kina gani ya bari aka ɗaga wannan bikin". 

Wani kukan ta sake sa masa sosai harda sabuwar shashsheka, kuka sosai take yi bilhakki da gaskiya na nunawa a gajiyarta ga komai. Yayin da Nanna uffan be ce mata ba, ya cigaba da aikin sa kawai. Har sai da ta yi shiru dan kan ta, bayan ta kwashe lokaci tana faman kukan. Ta sa hannu tana share fuskar ta. 

"Baki son ki ke laifi ko? 

Ya faɗa a hankali yana kallan ta. Be jira amsar ta ba. 

"Baki da hakuri, ba kowa ne zai iya zama dake ba baku yi faɗa ba. Dan haka, babu ke babu yin wasu friends, babu ke babu shiga harkar kowa. Duk wanda ya maki, ki yi haƙuri ki rabu da shi ko da baki shiga harkar ba...

"Shikenan ina gani sai ake ci min mutunci? Ka san jiya me ma suka min? 

Ta faɗa cike da tuno abinda ya faru, sai kuma tace. 

"Ashe na faɗa maka ma, arnan ba su da kirki wasun su". 

"Ain't you do it for my sake? 

Shiru ta yi tana turo baki. 

"Please". 

Ya mata pleading, a hankali ta gyaɗa masa kai kawai..

"Ba yarda za'a yi mutum, baka yi masa komai ba ya sa ka wani abu. Idan ki ka kiyayeni trust my words ba abinda zai yi maki, he can't do anything to you unless kin yi masa laifi. Idan ki ka duba zaki ga ay first place ƙilan ke ce mai laifin". 

Turo baki ta yi idan ta na sake cikowa da ruwan hawayen cike da tsantsan Shagwaɓa. Gently ya sakar mata murmushi a hankali yana mata waving. 

"That's My Baby".

"I love you Nanna". 

"I love you too Babyn Nanna". 

Murmushi ta yi masa haka shima kafin ta kashe wayar tana kiran Mammy, itama abinda ta faɗawa Nanna game da abinda ya faru itama ta kwashe ta faɗa mata. Faɗa ta shiga yi mata sosai kafin ta ce. 

"Ba haka kika Babyn Mammy tana yi ba, ba ruwanta da kowa yanzu da ita ce bazaki taɓa jin tace wani abu ba. Amma ke bansan wacce iri ce ba haka". 

"Ni Mammy ki yi ta min faɗa". 

"To ko zaki dake ni ne? 

"Ni sai anjima". 

Ta faɗa tana kashe wayarta. Ganin kiran Murad yasa ta ɗagawa tana faɗa masa inda take.

"Kina nan ashe". 

"Eh". 

Kallanta ya yi, wallahi ta bashi tausayi dan kana ganinta kasan ta ji jiki sosai. 

"Mu je ka karani clinic, jikina duka ciwo, idan ina tafiya kamar zan faɗi". 

Jinjina mata kai ya yi kafin suka tashi suka fara tafiyar. Kawai ta ji ta yi karo da mutum ba wanda ya lura da shi sai karon da ta ji sun yi. Ɗagowa ta yi ta kalle shi kafin a hankali ta bi gefen sa tana ɗan durƙusawa tare da furta Sorry Sir ta wuce ta bashi waje. 

"Hi". 

Ta ji wani guy ya faɗa mata yana mata waving a hankali. 

"Is he your boyfriend? 

Murad yana murmushi ya girgiza kan sa a hankali ya ce, "She's my friend". 

Zunaira ta haɗe rai sosai suna ci gaba da tafiya sun sata a tsakiya shida Murad. 

"I'm Ezekiel Elliott". 

"Zunairah". 

Ta bashi amsa a taƙaice. Dariya ya yi a hankali ya ce. 

"I can't pronounce your name, but can I say Zee? 

"Since your name starts from Z". 

Ya sake faɗa yana kallan ta. 

"Sure". 

Ta ce da shi kawai tana harɗe hannu a ƙirji suka cigaba da tafiya. 

"You are so beautiful and attractive, your body is so hot....

Ja ta yi ta tsaya kawai tana kallansa ta kuma harɗe hannu sosai, hakan yasa shi tsayawa shima yana juyowa tare da yi mata kallan what? 

"Can you please get our of my side? 

"But why? 

"I said please". 

Ta faɗa masa tana ƙure shi da mumman kallon da ya sa shi jinjina mata kai alamar sure Baby. Ta ja shegen tsaki. Murad ya saki murmushi kawai yana cewa. 

"Ke kuwa kin yi new catch shine zaki kore shi? 

Ya faɗa in a playful tone. 

"New ɗan iska de". 

Ta faɗa tana murmushi itama. Suna zuwa clinic aka buɗe mata file ta je taga Doctor Murad na jiran ta. Kafin suka wuce suka tafi tare. Suna fitowa Wayarta na Ringing shi kuma Murad ya ga wani ɗan ajin su a clinic suna ta tattauanawa be fito ba ita kuma ta fito tana amsa waya, sam bata lura ba da ɓawon ayabar da wani ya ci ya ajje akan barandar tiles ɗin wurin, ta kuwa taka luuu ta tafi zata faɗi aikuwa ta saki wani shegen ihu tana jefar da jakar nata da wayar na ta da kuma bread ɗin ta da drugs ɗin da aka bata. Saura ƙiris ta kai kasa ta ji ta narai-narai a jikin mutum. Ajiyar zuciya ta sauke sosai kafin mutanen wurin su tattaso suna yi mata sannu suna tsinewa kuma wanda ya jefar da ɓawon abayar. Bude idan ta tayi a hankali ta ware shi tas akan Ezekiel. Gashi ya ƙi sakinta ya wani rungumeta a jikinsa yana shafa mata baya in a romantic way ɗin da zai catching feelings na ta harda su taɓa mata mazaunai. Wai shi ɗan iska. Ai kuwa ta ƙwace jikinta daga gare shi ta zabga masa mari.

"Fuck You". 

Ta faɗa masa tana huci tare da yi amsa alamar fuck you da hannu. Ta juya ta ta tafi, nan fa wurin ya kaure da cewar bata da kirki butulu ce waye da waye. Wasu kuma su ce ai shine ya so aci masa mutunci. Murad uffan be ce ba da yaga komai fitowar sa kenan, sai kayanta da ya tattara mata kawai ya bi bayanta. Ganin irin saurin da take yi kamar ta kifa. Ta zo tsallaka wani waje bata gani saura ƙiris ta faɗa Murad ya yi mata kyakkyawan riƙo sosai yana kallanta ganin yarda take yi duk ran ta a ɓace. Ga ya san ƙafarta dole ciwo take yi mata zuwa cinyarta, tsallen kwaɗo ba wasa ba ne ba fa, sannan ga yau sake yin tsami bayan na jiya da ta yi yanzu ma ga wani ta sake yi abun fa ba sauƙi sam. Shiyasa duk ta yi wani iri da ita, daga zuwa yau kawai ta fice a hayyacinsa, ga gajiya tafiyar, gajiyar bata tafi ba ansake loda wata akan ta wata ga rashin bacci. 

"Watch your self". 

Ya faɗa mata sosai yana kallanta. Ajiyar zuciya ta sauke tana sake tsuke baki. Gani take marin da ta yi masa sam be dace dashi ba. 

"How can he....

Kawai ta kasa ƙarasawa tana nuna kan ta, sai wasu siraran hawayen takaicin suke zubo mata. 

"Ki yi haƙuri". 

Ya faɗa mata calmly yana ɗan murmushi. Kafin ya miƙa mata kayan ta. Karɓa kawai ta yi tana kumbura fuska tana sa hannu ta share hawayenta. 

"Mu je ki ci abinci ki sha magani okay? 

Gyaɗa masa kai ta yi a hankali shi kuma yake mata kallo mai cike da tausayawa sosai. Haka de suka jera suka nufi Mami market. Suna zuwa hostel bacci ta ɗan kwanta ta yi, sai de har aka gama busa musu su fito tana bacci bata sani ba.

"Hey! 

Ta ji Muryan Rayyan sosai a kan ta yana zungurinta da sandar dake hannunsa, tsabar baccin dake cin idan ta, da ta buɗe idan sai ta mayar da shi luuu ta rufe. Yayin da shi kuma ya sake taɓata da sandar sai a yanzu be yi mata tsawa ba. Cike da wani irin turo baki ta sake bude idan ta mai cike da bacci sosai ta ware su akan sa. Sai de har yanzun bata jin zata iya bude idan na ta sosai saboda baccin dake cikin idan ta. Hannu yasa ya taba ta ya ji jikinta akwai zafi sosai. Hakan yasa shi sake taɓa ta yana ɗan marin fuskar na ta. Sai a lokacin ta ware su sosai akan sa ta ga ashe Rayyan ne, dan itakam ta yi tunanin baccin da take yi yasa shi zuwa mata a cikin baccin ta. 

"Tashi ki wuce clinic". 

Ya faɗa mata ba yabo ba fallasa. 

"Ain't you hear me? 

Ya sake faɗa mata, da sauri ta diro daga kan gadon tana jin cinyoyinta gaba ɗaya sun yi tsami. Saura ƙiris ta buge shi ya yi saurin riƙeta yana kallanta, tsabar yarda ta kasa tsugunnawa ta sa takalmin ta.

"Sir can you please help with my shoe....

Ai wani ɗan iskan matsiyacin kallo da ya yi mata ne yasa ta zubewa kawai a wurin tana sakin kuka, dan wallahi ta kasa, sosai cinyarta ke yi mata wani irin ciwo na tashin hankali. A ƙasa warwas ta zube tana sakin ihu. Wani ɗan iskan tsaki ya ja yana yin gaba. Sai kuma ya zo ya tsugunna ya kama kafar ya zura mata takalmin, Oga Kamal ne ya zo ya taimaka mata ya kaita clinic ɗin. Amma ƙasan ran ta kam tunanin ɗan kirkin da ya yi mata ya yi bata zata ba ma. 


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol