Free chapter · Read without an account

8

by Hijjart Abdoul · ZUNAIRAH


*********Nanna ne ya fara fitowa da asuba ya ga wasu kyakkyawan yara su uku suna aikin decoration a dai-dai ƙofar parlourn su, mamaki ne ya kusan kashe shi. Ikon Allah me suke kuma anan? 

"Ina kwana Nanna". 

Mamaki kuma, taya suka san shi? 

"Lafiya qalau, waye ya sa su ku da wannan sanyin asubar? Kuna gani ruwa aka gama? Daga ina kuke? Ku su waye? 

"Zunairah ce ta turo min domin mu taya Samha birthday nata. Mu yi surprise". 

"To ku su waye". 

Amrah ta ce, "Ƙannan Murad ne". 

"Murad abokinta na camp? 

A tare suka jinjina kai. Murmushi shima ya yi ya ce. 

"Ya yi kyau. Kuma decoration ɗin ya yi kyau. Allah ya maku albarka". 

"Mun gode Nanna". 

Ayyan ya faɗa, shi kuma ya wuce yana juyowa ya kalle su. Sai da ya fita mai gate suke ce masa ai Zunairah ta san da zuwan su tun kafin wannan ranar tace duk sanda suka zo koda yaushe ne a bar su su shiga. Jinjina kai kawai ya yi Finally ƴar sa zata ba su mamaki wannan karan. Ba su yi surprising ɗin ta b, amma ita duk dabata nan gashi ta sa anyi surprising Samha. 

Mahmud ne ya fara fitowa kafin Ahmad ya biyo shi a baya sai kuma Nasir, suna fitowa suka fi karo da Happy birthday Other half.

"Kut****

Mahmud ya faɗa yana zaro wayar Ahmad daga gaban aljihunsa yaga date. 

"Kai ne ka shirya mata ko? 

"Wallahi bani ba ne ba, kawai tace min kar na tuna mata da birthday ɗin ta idan ya zo, zata yi surprising Samha". 

"Chaiii". 

Da gudu ya wuce ya tafi yana tashin Samha da ko tashi bata yi ba tana cikin bargo. Daga ita har bargon ya ɗago kawai, tana fitowa aka kunna wasu irin haske sosai tare da sakin surprise pieces suna ta zubowa aka kunna happy birthday to you, Amal ta turo cake ɗin, Amrah riƙe da Teddy Bear Ayyan riƙe da wani frame anyi wrapping nasa. 

Wani irin hawayene yake fara fitowa daga idan ta. Kafin ta kalla Mahmud ta kalla Ahmad, Nasir kam tsaki ya ja ya wuce masallaci baya san wannan haukar shikam duk zai ya gyara musu wurin zama yadda za su zauna da kyau. Ga kuma mai video nan sai video yake yi musu abin gwanin ban burgewa. Rike bargon ta yi sosai dan ba kayan arzki ne ba a jikin na ta. Hakan yasa ta taƙ rabuwa da shi, kafin Nasir ya fara yi mata mita. Duk da ba saban abu ne a wurin su ba wayo da kayan bacci a cikin gidan na su.

Share hawayenta ta yi sosai kafin ta kalla Mahmud dake riƙe da ita, tana takowa da ita sannan ta kalla Ahmad dake gyaɗa mata kai shima. Kawai rungume Ahmad ɗin ta yi a a madadin Zunairah. Hannunsa ɗaya yasa yana shafa kan ta cike da lallashi. 

"Ya isa hakan nan". 

Ya faɗa mata a hankali. 

"This your birthday last at home. Sauran kuma a sai gidan Miji idan anga dama a gayyace mu. Mu de ba zamu fasa cewa Happy birthday ba".

Mahmud ya faɗa. Ba wanda ya kula shi dan masu kula shi ɗin basa nan,.Ammar da Zunairah daman.

Cake ɗin suka yanka ta sawa Mahmud da Ahmad a baki. Kafin ta kalla Amal dake ta kallansu tana sakin murmushi sosai. Ta yanka wani ta kai bakin ta da shi sai kawai ta tsaya tana kallan ta. 
yi

"Open your mouth jare". 

Mahmud ya faɗa so friendly yana dafa ta, a hankali ta buɗe bakin na ta, ya sa mata, hakan ta bawa Amrah ma, da Ayyan. Duk ta sa musu a bakin. Batare da wariyar cewa ai ba ƴan gidan su ne ba. Slow waƙar da aka sa ne yasa Samha fara takawa a hankali. Sai de tana juyowa suka haɗa ido da Daddaa. 

"Albarkar asubar suke so ku kwashe mana a cikin gida? Ehhh? Daga ku har ubanku ni na rasa me yake damun ku. Wallahi kawai kashe ni zaku yi lokacina be yi ba...

Mahmud ya ce, "Tun muna yara ki ke cewa zamu kashe ki lokacin ki be yi ba, har yanzu kuma baki mutu ba". 

Carbin hannunta ta wulla masa ya matsa gefe yana dariya. 

"Mamuda ka fita a ido na na faɗa maka". 

"Ni fa bansan ya aka yi nake shiga idan ki ba". 

Da gudu ya fice jin za'a shiga sallah haka ma Ahmad ya mara masa baya. Kafin ta kalla Samha.

"Kin gadin shegen cake ɗin zaki yi ne? 

"A'a ina shigowa kaɗan". 

Taɓe baki ta yi ta koma ciki. 

"Munafuka mutum sai baƙin hali da tsirfar tsiya". 

Ta faɗa mata tana ƙarasa shigewa. Juyowar ta yi tana kallan su Ayyan dake tattare kayan su..

"Please ku barshi idan ba damuwa dan Allah, i can double the payment ko zuwa yamma ne sai ku zo ku kwashe". 

"Ok ba damuwa". 

Jinjina musu kai ta yi tace. 

"Na gode". 

"Ina ta sanku? 

"Mu ƙannan Murad ne, wanda suka haɗu a camp, to shine...

Be ƙarasa bata labarin ba ta katse shi ta hanyar sakin kyakkyawan Murmushi tana jinjina kan ta tare da shafa kan Amal.....

*********Sallama suka yi mata suka wuce abinsu, suna zuwa gida suka wuce ɗakin su suka yi sallah kafin suka fito suka shiga kitchen. Ayyan ya leka ɗakin Mommyn su yaga tana bacci har yanzu, maganin bacci suka zuba a mata tun jiya da daddare dan ko karen hauka ne ya cije su ba zasu iya fita da wannan uwar daren ba su ce za su yi aiki, yanzu ne zata ce sun dena aikin kwata-kwata. To me ya yi zafi?

"Mommy". 

Ya faɗa a hankali yana ɗan taɓa ta. 

"Mommyyyy". 

Ya sake faɗa yana bubbuga ta. 

"Uhmmm". 

Ta faɗa daƙyar tana buɗe idan ta dake cike da bacci. 

"Mommy lafiya? Naga baki fito ba, ko baki da lafiya? 

"Uwar ka ce ta sameni? 

Ta faɗa daƙyar tana so ta buɗe idan ta. 

"To ai naga anyi sallah fa har gari ya fara wayewa". 

"Mtsww". 

Ta sake faɗa a hankali tana sake gwada bude idan ta, daƙyar daƙyar de ta tashi ta yi sallah tana dafa bango. Tana idar da Sallah daƙyar ta samu ta yi azhkhar bata ma kammala ba ta hau kan gado ta koma bacci. Ba ita ta fito ba sai goman na safe ta ji ta garau sannan ta fito taga sun shirya abinci kamar yadda aka saba. Suna zaune suna karatun Alqur'ani sun tusa TV a gaba amma babu volume dake da ka suke karantawa ba Qur'ani hakan yasa idan su ƙyar akan tv suna kallan Home Alone.

"Ehh kwarai, ya yi maku kyau. Na ce ya yi maku kyau. Uban me ya hana ku zuwa makarantar? Kuka zo kuka tasa tv a gaba kuna kallo dan uwarku? 

Ayyan ya ce, "Mommy ina kwana". 

"Mommy ina kwana".

"Mommy ina kwana". 

Amrah da Amal suka haɗa wurin gaida ta. 

"Ni ga abinda na tambaye ku, shine kuke bani wata gaisuwar da sai kun ga dama kuke iya buɗar baki ku ce min ina kwana". 

Kallan juna suka yi suna maida kan su ga tv. Wai sai sunga dama. Zuwa ta yi ta fara buɗe warmers tana gani, babu yarda za'a yi ace ka kunshe abincin amma sai ca tace. 

"Ni ba zanci wannan abincin ba. A tashi a zo a girka min ɗanwake". 

Amrah tace, "Da muka ga kina son kunun gyaɗa da ɗumame ga yan balls da masa...

"Uban me yasa baku tambaye ni ba? Kuma wannan Masar ta yi tauri bata yi laushi ba ta tashi, sannan baku haɗa ta ba yarda ya kamata". 

Ta faɗa tana kai lomar masar bakin ta bayan ta dangwali roman naman kai da tsokar nama ta haɗa ta cusa a baki. 

Ayyan tsabar takaici shiru ya yi kawai.  Ai sunga fiye da haka ma. 

"Ni gaskiya a gidan nan na fara tantamar anya haifar mu aka yi kuwa? 

"Dan kut****ki tsinto ki na yi a bola dan uwarki baki da iyaye shege Yar iska, duk abinda nake maku a gidan nan? Me kuke a gidan? Ba abinda kuke yi daga na dafa sai ci sai kwanciya". 

Ayyan juyowa ya yi ya kalleta yadda take zaune a dining tana zabga loma amma tana famar yi musu gori..

"Hatta pant ɗin da kike sawa waye yake siyo maki? Ubanki be taɓa kawo ba. Na siya maki pad, na siya breziya, ga su kayan kwalliya na maki dinkin duk ubanki ya bani kuɗin ne? Meye na bana maku. Uban me neman kudin na ku yake yi maku, banda ci a ciki a yi ankom ƙawaye. Yau ke ce wurin ka za, gobe kune wurin kaza". 

"Shi kuma baya da aiki sai zuwa wurin ƙwallo, ana bada kuɗi suna kama stadium ayi ƙwallo ko? Asararren banza asararren wofi, haka zaku ƙare kuna bautawa abokai". 

Amrah tace, "Wanne irin anko na taɓa yi? Daga yin ankon Salaha shine za'a ce na cika anko? 

"Dan kut**** na yi ƙarya, na maki ƙazafi". 

"To Mommy nima ban taɓa ganin inda ta yi ankon ba....

"Shefe talikin banza talikin wofi, kai bana ganin laifin ka, tunda kai halitta ce ba'a gama maka ba shi yasa ka ke addabata, dan uwarka sai da ka yi wata hudu a cikin kwalba, shege talikin banza kawai". 

Tsuke baki kawai ya yi. Suka yi shiru. 

"Kuma wannan wainar an cika sugar, shima roman kun cika maggie da yaji". 

Ayyan ya ce, "Yanzu haka fa kin cinye kuma wallahi bamu ci ba, daman saura ne fa". 

Dariya tasa tace, "Aww haba? Aini na yi tunanin nawa ne". 

Ya ce, "Mu taɓa ki ce mun ci amanarki". 

"Yooo da naga kallo kuke shiyasa ai, ga ɗan saura nan, Amal zo ki ci". 

Ta faɗa tana ajjewa Amal shi kuma ta hana shi kwanon roman. 

Kawai sototo ya yi yana kallan Amal da ta zo ta amsa. 

"Munafuka". 

Ya faɗa yana mata warning da ido, ɗan yanzu ne sai Amal ta tona musu asiri be san wanne tsautsayin Baba yace su tafi da ita ba. 

Kiran da Murad ya yi mata ne yasa ta ɗagawa yana sa wayar a speaker. 

"Sai yanzu ka ga kiran nawa, kira tun jiya da Magriba? 

"Ki yi haƙuri". 

Ba zai iya cewa ya kira ba bata ɗaga ba. Amma yasan zata gani idan sun gama wayar. Gaisawa suka yi kawai kafin ya tambaye ta su Amrah. 

"Nikam baka da numbern su ne? Sai na turo maka idan baka da numbern su ai". 

"Ki yi haƙuri". 

"Mtsw". 

Amrah ta kalla Ayyan da ga zo ya zauna a kusa da ita suna kallan videon da suka turawa Zunairah. 

"Banga dalilin da yasa zata je camp ba, suna da kuɗi haka ta je ta sha wahala haka nan, suna daga zaune wallahi  za'a kawo musu certificate har gida". 

Ayyan yace, "Wannan abun da kika gani yana da wani abu, duk kuɗin ka indai kana son abun nan sai ka je ka yi". 

Taɓe baki ta yi tace, "Nikam bana jin zan je wannan wahalar". 

Ayyan ya ce, "Dan Allah ba su burgeki ba? 

"Wallahi sun burgeni sosai, musamman ma Babansu, kana gani zaka san akwai wani kyakkyawan connection a tsakaninsu yana san yaran sa kuma, itama da'alama bata ɓoye musu waye Ya Murad ba". 

"Ina kuwa? Ba irin mu, da ka yi kawa ka ke ɗari ɗari da ita kar a kunyata ka, shi yasa fa ba ruwana da yin wata ƙawa me ya aiki ne? 

"Ga Ya Murad nan shide ya yi abinsa". 

"Uban me kuke cewa? Na ji kuna cewa Ya Murad? 

"Mommaaaa bafa komai muke cewa ba, zancene muke yi". 

"Shi ɗan waken sai sanda aka yi ra'ayi za'a yi min?....

"Nikam rai na ya jima da faɗa min tsinto mu aka yi a cikin gidan nan". 

"Ehh fa, Amal ita ce mutum".

Suka faɗa suna tashi..

"Munafukai". 

Itama Momma ɗin ta faɗa tana binsu da ido.....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.