Free chapter 路 Read without an account

FARGABA

by Ayshnur Pyar 路 MAKAUNIYAR HANYA

Wattpad@ashnurpyaar.

Page (3)

FARGABA!

Tun bayan da Irfan yaga gidansu khaleesat, yake zarya a kofar gidan kullum domin duba lafiyarta, sannu sannu yake jin sonta na dad'a shigarsa har mamaki yake na yanda sonta ya d'arsu a zuciyarsa daga kallo d'aya!
'Ko me hakan ke nufi?' yakan tambayi kansa.

Ganin ta samu sauki kwana biyu ne ya bijiro mata da muradinsa yana mai cike da alhinin gaggawan hakan daga garesa.

Sai dai sam Khaleesat tak'i bashi had'in kai, hakan kuma bai sanya shi ya karaya ba.

Ranar farko daya fara zuwa ta fito tayi masa godiya akan taimakon da yayi mata.

Washegari ma da yaje, ta fito.
Don haka kawai ta tsinci kanta da Jin nauyinsa, tana ganin girma da mutuncinsa sosai a idanunta, shiyasa take bashi lokacinta, ba don haka ba, tsarin da ta daukarwa kanta ba ta tunanin ko tsayawa tare da wani namiji za ta sake yi, bare har ta kawo tunanin wata alak'a mai kama da soyayya a tsakaninsu.

Jin hadafin dake tafe dashi lokaci guda khaleesat ta sauya mai tamkar ba ita ba, ta nuna k'in amince wa ga tayinsa a fili!.

Duk yadda ya so, domin ya shawo kanta, amma abu yaci tura.

Abu daya da ya tsaya masa a rai yanda cikin kuka take fada masa

"Baka san ko wacece ni ba, shi yasa har kake mafarkin Aurena, ni kuma ban shirya zama silar ajalinka ba!"

Wannan kalamai nata sun matuk'ar d'aure masa kai.

Tattare yake da tarin tambayoyi, gashi tak'i bashi aron lokacinta, bare ya samu amsoshin tambayoyin da suke kai kawo cikin birnin zuciyarsa.

Haka ya rink'a zarya a gidansu, amma kullum babu wani sauyi daga gareta.

Daga k'arshe sai ya zamana, ko yazo gidan, ta daina fitowa baki d'aya, haka zai je ya sha zamansa ya gaji, sannan ya tafi.

Shima ba a son ransa bane gabatar mata da soyayyarsa cikin gaggawa irin haka, matsin da Abbansa yayi masa ne.

****

Ana gobe k'arshen wa'adin da Mahaifinsa ya d'ibar mai zai cika, wani zazzab'i mai tsananin zafi ya rufe Irfan a d'akinsa.

K'anwar shi Saudat ce ta gano halin da yake ciki lokacin da taje kai masa Abinci.

Likitan dake duba su a gida aka kira.

Bayan ya gama duba shi da 'yan bincikensa, ya rubuta wasu magunguna da zai sha, sannan kuma ya ba Irfan shawarwari dangane da cire yawan damuwa da zullumin daya sanya a ranshi, don shine ya haifar mai da zazzabi, gami da yanayi da halin da yake ciki.

Jin kalaman likitan kawai Irfan ke yi.

'Amma taya har zai iya cire zullumi da kokonton ranar gobe a cikin ransa!?

Me zai fad'awa Mahaifin nashi, alhali yarinyar da yake tunanin ita ce tsanin da zai taka matakalar tsira daga kaucewa Auren wacce bai so, ta gaza fahimtarsa.

Ji yake a jikinsa tamkar ya fada cikin ramin da fitarsa abu ne mai matuk'ar wahalar gaske a gareshi.

***** *****

Wani kamilallen dattijo ne fari, mai k'warjini da kamala, zaune bisa d'aya daga cikin lumtsattsun kujerun da suka kewaye babban falon.

Da ganinsa, ka san yad'an manyan ta.
Alhaji Ahmad kenan wato Mahaifin Irfan.

A zahirance, idan ka kalle sa, ba zaka d'auka Irfan ne d'anshi na fari ba, bisa nazari da duba ga tarin shekarunsa. Da yake Allah bai bashi haihuwa da wuri ba, Irfan ne ya kasance d'ansa na farko, bayan shekaru kusan goma sha biyar da sukayi da Matarshi, kafin a ka samu cikin Irfan.

Bayan ta haifi Irfan, sai Aisha, da suka sake samu, wacce a ka sanyawa sunan Mahaifiyar Alhaji Ahmad. Daga baya kuma Allah ya amshi abarshi tun tana 'yar karamarta bata kai ga girma ba.

Sun dad'e ba tare da sun k'ara samun wani haihuwa ba. Kafin daga bisani Allah ya sake basu Saudat yar Auta! Domin tun daga ita basu k'ara samun wani haihuwar ba, shekaru kusan goma ne tsakanin Saudat da Irfan.

Irfan na zaune k'asan kafet gaban Mahaifinsa, don nuna girmamawa a garesa.

Gefe guda kuma Hajiya Aishat ce, Mahaifiyarsa.

Falon yayi shiru babu wanda yace wani abu, Irfan kanshi na sunkuye k'asa, jiran mai Mahaifin nashi zai ce yake yi.

Alhaji Ahmad ya matsu sosai! Da son ganin d'ansa yayi Aure ne tun yana da sauran numfashi a doran k'asa, a cewarsa.

Inda akayi rashin sa'a shi kuma Irfan sam! Babu harkar mata a gabanshi, bayi da ko budurwa, don ba kula mata yake ba, balle har ta kai ga ya gano wacce zuciyarsa tayi amanna da ita.

Mahaifinsa ya sha bashi lokuta mabanbanta domin ya gabatar mai da zab'insa, amma hakan bai samu ba daga b'angaren Irfan, har sai data kaiga Mahaifinsa ya yi ik'rarin yi mai had'i da yarinyar da yafi tsana a rayuwarsa gaba d'aya! wato Hafsat. (Wata 'yar aminin Mahaifinsa ce).

Ko da Mata sun k'are a duniya, bai tab'a mafarkin zai kasance a inuwa d'aya da Hafsat, matsayin abokiyar rayuwa ta har abada ba.

Saboda wad'ansu halayyarta mara sa kyau da sam! Basu yi daidai da tsarinshi ba.

Dalilin da yasa Irfan neman alfarma gun Mahaifinsa kenan, kan cewa zai fiddo da zab'insa akaro na farko kan dai ace a had'a shi da Hafsat.

Sai dai tunda ya nemi wannan alfarman kullum jiya iyau ake, ya kasa kawo wacce yake so duk da jiran da Mahaifinsa ke yi.

A wannan karon shine dama ta k'arshe da Abansa ya bashi, kan cewa, in har bai gabartar mai da yarinyar da ya zab'a ba, to shi zai had'asa da wacce yayi niyya.

Irfan ya shiga tashin hankali matuk'a, don bai samo mafita ba har ya rage saura kwana goma sha hud'u, wato sati biyu kenan daga cikin kwanakin da Abbansa ya d'ibar masa. Bai tab'a tunanin zai fad'a soyayyar wata 'ya mace lokaci guda a rayuwarshi ba, ya d'auki alkawarin kawo zab'insa ne, kawai don ya gujewa Auren Hafsat.

Sai gashi cikin sa'a guda na rayuwarsa daya fara tozali da khaleesat, ya tsinci kansa dumu-dumu cikin so had'e da begenta.

Tun daga lokacin daya fara d'ora idanunsa cikin nata, zuciyarshi take barazanar narkewa akan ta.
Yayin da gefe guda kuma wasu k'ididdigun kalmomin da yarinyar ke fad'a masa a duk sa'ar da suka kasance tare, kalaman sukan jefa zuciyarshi cikin rud'ani, had'e da barazana, ga cigaban numfashinsa a doran k'asa.

Baka san ko wacece ni ba, shi yasa har kake mafarkin Aure na, ni kuma ban shirya zama silar ajalinka ba

Wad'an kalaman suna d'imautar da zuciyar Irfan, amma duk da haka dai-dai da dak'ik'a d'aya tak! Bai tab'a jin zai sauya daga ra'ayinsa a kanta ba.

Alhaji Ahmad ne ya katse shirun nasu da soma tambayar Irfan.

"To gashi dai Allah ya kawomu cikar lokacin dana d'ibar ma, yau wata uku kenan cif-cif! Irfan.
Shin wace yarinya ce ka fitar a matsayin zab'inka? Ina sauraren ka".

Irfan ya sunkuyar da kai k'asa, ba tare da ya iya cewa komai ba.

"Ya naga ka sunkuyar da kai, kamar ba ka da abin cewa, don kar dai ka sake ka cemin a wannan karon ma babu wacce ka zab'a, domin ko wannan lokacin matuk'ar ka yi sake da damar da dana baka, har tsawon wata uku! To tabbas zaka karb'i wacce take zab'ina, ba zan k'ara yi maka wata alfarma ba, saboda haka kada ka b'ata min lokaci ina jin ka".

"Khaleesat sunanta....". Ya tsinci kanshi da furta wad'an nan kalmomin.

"Yar gidan wanene, waye Mahaifin ta?"

Tambayar da yake tsoro kenan dama daga bakin Abbansa, domin shi kansa bai san waye Mahaifin khaleesat ba, bata bashi damar sanin komai game da hakan ba, Ummanta kad'ai ya sani.

K'ok'arin seta kanshi ya yi, kafin ya amsa da fad'in sunan anguwar dasu Khaleesat suke, sai dai bai san menene cikakken sunan Mahaifinta ba.

"Wai menene dalilin da yasa ka fiye shiririta ne Irfan? Ance ma Aure abin wasa ne, kana son yarinya, zaka Aure ta, amma baka san wanene Mahaifinta ba! Ta ina zan fara aikawa gidansu?"

"Abba nayi kuskure amma in Allah ya yarda zan.....".

"Dakata!". Alhaji Ahmad ya tsaida shi, yana me d'aga masa hannunsa.

"Babu wata dama da zan sake baka, dan na fahimci cewa har yanzu baka gama shiryawa ba, hakan ke nunamin cewa lallai ka ba ni zab'in na had'aka da duk wacce nayi niyya, Insha Allah gobe zan tura Mutane gidan aminina, domin a nema maka auren Hafsat!".

Ji yayi kamar an dab'a mai wuk'a a kirjinsa, ambatar sunan Hafsa da Abbansa ya yi.

Pyar馃挆

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol