Free chapter · Read without an account

Chapter:5

by Rabi'atu Abubakar Umar · KO BA SO..

Fate has a strange way of bringing people together....

Ya na shigowa hotel din ya karbi makullan dakinsa, wanda kullum nan ya ke sauka ba canji, don ya ma sha bamban da kalar sauran ɗakunan VVIP ɗin komai an zuba mashi abin da ya ke bukata ne. Ya fi son zuwa hotel din nan fiye da gidansa, saboda a nan komai za a yi masa, ba tare da wahalar order abinci ko makamantan su ba. jikkarsa ya wurga a gado da wayoyinsa ya shige washroom din don ko wanka bai samu damar yi ba a gidansu. Ya na gamawa ya duba abincin da aka ajiye na safe, da alamu sun zaci tun safen zai iso. Sai kawai ya kira ya fadi abin da ya ke bukata. Sakwara abincin da suka fi so ne da shi da Momynsa, yanzu da ransa ya ke bace sai ya ke jin babu abin da zai iya ci sai favorite dinta. Hakuri suka ba shi akan Abincinsa zai zo nan da wani lokaci kasancewar babu shi a ƙasa.

Har ya fara bacci knocking ɗin da ya ji ya tada shi, lokaci daya ciwon kai mai zafi ya sauko mashi. Kara kwankwasawa a kayi, ransa ya ji zai kara hawa, ba za a iya shigowa ba ne wai sai an takura ma shi? A zafafe ya ce

"Come in"

Ya na tashi zaune ya dafe kansa da ke ciwo.

Dakin ta bi da kallo komai ash and black ne tun daga furnitures, cottons har rugs din. In da ya ke ta kalla duk da a zaune ya ke zata bada labarin dogo ne sosai. Jikinsa kuma babu kiba sosai, ba dai za a ce ramamme ba ne don akwai cikakkiyar kira, da damtse. Ta ga haka ne sakamakon farar rigarsa da ta ke armless.

Jin kamar ana kallonsa ya saka shi ɗagowa, suka haɗa ido. Da sauri ta janye idonta tare da karasa shiga, ta jera abincin. Tare da tsogwamin rashin amsa sallamarta da bai yi ba, cikin ranta.

'Ko da ya ke, kilan wani tsabar gayun ne ko kalar na su, wuya ya sha sarka ina kuwa zai amsa sallama'

Ta faɗi cikin rai. Ta na gamawa ta mike ta koma gefe ta yi tsaye kanta a kasa. Sai gani ta yi ya koma ya kwanta fuskarsa na kallon sama ya lumshe idanu.

An sha cewa ta na da kyau, fara ce ita amman yanzu da ta ga fuskarsa a fili sai ta raina na ta farin, don kuwa shi jikinsa akwai alamun laushi sosai, kuma da jan hankali.

'Layla' Ta ji wata murya a cikin kanta. 'Yaushe kika koyi kallon kurilla har haka?' sai ta yi saurin janye idonta, duk da haka sai da ta kula da plaster da ke manne gefen idonsa.

In dai kallo ne ya saba jin idanuwa bisa kan shi, sarai ya na jin yadda ta ke bin sa da kallo har zuwa lokacin da ta gaji don kanta.

Jin shiru ba ta tafi ba ya saka shi dagowa ya zuba mata ido, da nufin ko akwai wata matsala? Ita kuma ganin ya na kallon ta ta matsa kusa da abincin

"A zuba?"

Da yatsu yai mata alamar a'a ya koma ya kwanta. Ganin dai ta kuma tsayuwa ya ce

"Akwai wani abu?"

"A'a"

Ta bashi amsa.

"Za ki iya tafiya"

Ta dan yi tsaye, to ita ta tafi?

"Ba zan ci yanzu ba"

Ya sake fadi. Ta fita a hankali ta rufe masa kofar. A jiyar zuciya ta sauke tana jingina da kofar.

"Me kike yi a nan?"

Ta ji muryar Sarah.

"Ya ci abincin?"

Ta sake tambaya. Kai ta girgiza

"Ya ce ba yanzun zai ci ba"

Ta dan tabe baki, sai ki ringa dubawa duk bayan mintuna sha biyar. Daga haka ta wuce ta bar ta sake da baki cike da mamaki. To tsugunne bata kare ba kenan. Sai kuma ta fahimci lokacin tashin Sarah din yayi tuni amman bata tafi din ba kamar dai yadda Zee ta fada bata son tafiya in Fj na nan. Kamar daga sama sai ga Zee ta na washe baki ta iso

"To yaya? Bai yi complain ba?"

"Me yasa zai yi?"

Layla ta tambaya. Dan zaro ido Zee ta yi

"Ki na nufin bai ce komai ba har ya ci abincin ya gama?"

"Bai ci ba, ya ce sai anjima"

Wani kallon baki san me kike yi ba Zee ta bita da shi, kafin ta ce

"Sai kika fito? To wallahi kar kike bata minti biyar baki dubo ba. Kin san mai zai faru idan baki nan?"

Ta gyaɗa kai, sai ta ji tsoro na shigarta

"Idan wani abu bai masa ba, kai tsaye sama zai kira ya yi korafinsa. Sakamakon haka kuma kora ce."

Layla ta zaro ido waje.

"Kwarai kuwa. Shiyasa gara ki tsaya duk tsayuwar da za ki yi, har ya gama, idan ma korafin ne yayi maki ki je ki sauyo masa in na bada hakuri ne ki bada kar magana ta fito waje"

'Tashin hankali' ta fadi cikin rai. Ta na komawa ɗakin da sauri.

*

Duk wani tunaninsa ya ƙure shi akan waye ya siya building din nan amman ya kasa samun hanya. Mirgina kawai ya ke bisa gadon ya na faman cusa hannuwansa cikin sumar kansa, duk ya cukurkuda gashin.

"Khaleed?" Ya tambayi kansa, to amman ai kusan ko yaushe suna tare. Date din jikin takardun ma a ranar da suka tafi Kano ne. Sai yayi saurin girgiza kai.

Ba ma shi bane, duk kwakwar Khalid wajan son yin abu ba zai taba yi ba tare da amincewarsa ba. Amman ko ma waye wata rana zai sani ne, a je zuwa...

In da abincin ya dosa ya kalla, ya tashi ya dakko a kasa ya zauna ya na ci, tun da babu wajan cin abinci kasancewar a restaurant din hotel din kowa ke sauka ya ci. Na VVIP ne ke sama duk da haka abune mai wuya ya je. Kullum ya na daki idan ya zo, sai dai ko masallacin da ke waje like da hotel din, ko idan ya na san shan iska ya je bakin swimming pool ya zauna. Da ga ba haka ba babu abin da ke fito da shi haka kawai.

Lomar farko da ya kai ya ji an kwankwasa dakin.

"Shigo"

Ya fada bayan ya hade lomar. Bai kalli in da ta ke ba Amman zai shaida yarinyar dazun ce. Ya gane hakan ta knocking dinta. Ta samu gefe ta tsaya da yar tazara tsakaninsu kanta na kallon yatsun kafarta da ke zukar sanyin tiles duk da safar da ta sanya.

Tarin da ta ji yana yi ne ya saka ta kalle sa, sai kuma da sauri ta ga ya tashi ya shiga washroom, sai karar amai ta ji. Gabanta yai wata kalar faduwa ido waje ta na sauraron karar aman don ta kasa gasgata hakan'Kar dai abinci na ne?' ta faɗa a ranta fargaba na sake rufeta, tuni ta fara hado kan addu'o'i ta na yi.

  *****

Naseer...

Yadda ya ke kai lomar tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa da ta sha manshanu za ka rantse da yunwa ya wuni, duk da dai bambancinsa da mai yunwar kadan ne, don abincin Sophie sam babu dadi ba fasali a cikinsa.

Hajja ta zuba mashi idanu, ita tausayi ma ya ke bata, wanne kalar fada ne za ta yi wa Nasir ya ji ta? Wane kalar aurene ya ke yi, da sam bai ji da ganin duk wani nakasu a cikinsa?

Bakinsa cike da katuwar tsokar da ya kai baki ya dago ya dube ta. Ganin ta kure shi da kallo ya saka shi yin murmushi ya hadiye kafin ya ce

"Hajja halan kyau na yi maki yau?"

Ta buga masa harara.

."Wane kalar kyau kuwa za kayi min wuya duk kashin yunwa? Anya dai a tafi a haka Nasir?"

Ya tsame hannunsa daga cikin tuwon, da daman ya kai geji, ya na mikewa tsaye.

"Kai Hajja, wannan dai har da sharrinki. Wane ƙashin yunwa kuma kamar karamin yaro dai"

A Wash basin na dining area ya isa ya wanko hannunsa, ya dauki ƙaramin towel din da ke rataye a hanger a wajan ya tsane hannunsa, kafin ya dawo ya lankwashe ƙafarsa gaban Hajja din.

"Hajjarmu ki saki ranki mana uhm?"

"Nasir"

Ta kira sunansa. Ya amsa

"Tsanainka da Allah yaushe rabon da ka ci tuwo?"

Ya ɗan sosai kai.

"Tun wanda na ci zuwana na karshe kafin na yi tafiya."

Ya fadi gabansa na faduwa don dai ya san maganar gizo ai bata wuce ta koki, amman ya zai yi? Shi sam bai iya karya ba, ba ma zai iya yiwa Hajja karya ba da tuni ya kare Beelah dangane da hakan.

"Yanzu a ce magidanci kamar ka, ba zaka iya samun abin da kake so a gidanka ba?  Na fada maka ka samu yarinya a dangi ka aura ka botsare ka ki, shin yaya kake son na yi da kai? Ka na tunanin idan yau ace Hadiza na raye za ta barka haka a dai-daice hannun matarka?"

Ya girgiza kai. Don abin da ya sani ne, idan da Ummarsa na raye ko kusa ko alama bai isa ba, ba ma lallai ne auren su da Beelah ba yadda aka sha rikicin nan. Don ita kam akwai zafi kuma tana son yaranta fiye da kima.

Kiran wayarsa da aka yi, ya katse aka sake kira ya saka ta cewa

"Ka tashi ka je, idan ka samu lokaci sai ku shigo tare, tun da ita bata san zuwa gaishe da mutane ba"

Sanin shi na mutane ne, a fannin kasuwa ko yaushe ba a raba wayarsa da kara. Ita kuma matar tasa ba wai ta damu da zuwan bane. Sallama ya yi mata ya fice.

Nasir mahaifansa sun rasu a sanadin hatsarin mota da su kayi, shekara biyar kenan. Su biyu ne daga shi sai kanwarsa Amira, wacce ya bama shekaru  goma sha daya don haka ya ke kamar uba a wajanta.  Tun iyayensa na da rai Abbansa kamfanin robobi garai kala kala, da ya kawo karfi ya shiga kasuwar sai ya kara daga ta da kyau ta duk wani abu na dangin roba suna yi, har da kayan wasan yara kala kala, su na da rassa kuma a wasu garuruwan ma. A wajan Kakarsu ta wajan uba su ke, wadda daman can a gidan ta ke zaune, don haka ne ma gidan kusan ko yaushe ya ke cike da yaran 'yan uwa da kuma jikoki musamman da yake gida da za a zo aci abin duniya har a bar shi. Kusan yayyu da kannen iyayensa babu wanda bai so ace an ba Nasir diyarsa ya aura ba tun ma suna da rai, har yanzun kuma bata sauya zane ba, don kusan ma duk yan mata ne masu zuwa su tare a gidan. Gidansa ne dai ba su cika zuwa ba don Beelah ba wai ta na son baki bane acewarsu.

*****

Farha...

Kamar jira take Malamar da ke tsaye ta na ta zuba masu misalai a kan sentence structure, ta fita, ita ma ta yi zumbur ta mike. Wayarta ta fiddo da ga cikin jikka ta kira Meenah, jun har ta katse ba ta daga ba ta san bata fito daga lecture ba. Ta dan ja tsaki, ta gaji sosai da ciwon kai ta tashi, ba don C.A din da su ka yi yau ba ma da ba zata zo ba. Takawa ta yi har department din su Meenah din da ya ke ba coure dinsu daya ba, ita Science education ta ke yi, Meenah kuma Accounting. Ba ta dadewa da isowa ba ta ga sun fara fitowa, can ta hango ta, ta dinga daga mata hannu har ta hango ta.

"Yanzun can za mu wuce?"

Meenah ta fada yayin da suka dauki hanyar bus stop.

"Eh mana, gara na karba in san na gama duk wani shiri jibi ne fa"

Suka shiga bus suka zauna. Shiri suke akan fans eve din Fj da zai kama Asabar din nan. Riguna suka bada aka yi masu da p-cap mai dauke da sunansa, duk wata da take group dinsu ko ta ke following fage dinta kalar rigar za ta saka. A hanya suka sauka suka ida gangarawa shagon a kafa, yarbawa ne masu shagon sun kware wajan customizing komai, tun daga backpack,caps, mugs da ma duk wani abu da ya shafi printing da design.

Wani tsalle Farha ta buga yayin da ta yi arba da rigar. Don duk yadda ta ganta a waya, a fili ya fi kyau nesa ba kusa ba. Ta karbi gift din da ta sa aka hada mata, shi ma yayi matukar kyau don sai da aka bude ta ga komai yadda ta fada kafin a nannade kwalin. Ta karba suna ta godiya ita ma ta na yi suka fito shagon, wata ajiyar zuciya ta sauke. Ta dade ta na tara kudin nan, don ko abinci bata siya a makaranta ta kwammace ta boye kudin, daga karshe da ta ga lokaci na neman kurewa sai ta kwashi takalman Umma tana masu hoto mai kyau ta daura a status dinta, ga mamakin ta kuwa aka dinga siya musamman yan makarantarsu. Umma da Layla dai sun sha mamaki don Farha kwata-kwata bata da interest wajan saida abu, ita dai kawai a bata ta kashe. Babu dai wanda ya ce mata komai don a zaton su ma wani ankon ne ta je ta yayubo wa kanta, ta ke son siya don Umma ta ce kudinta sun gana ciwon kai wajan wani anko, Baba kuwa ba ma zata fara tambayar sa kudin anko ba, tun da zuwa bikin ma sai ta yi da gaske wasu lokuttan har da karya.

A hanya firar ranar suka dinga yi, har aka sauke Farha da ke gidansu ne farko kafin na su Meenah. Kay

an ta bata ta ce da dare ta lallaba ta kawo mata, don yanzun idan ta shiga da su zata iya cin karo da Umma kafin ta shige daki ta samu damar boye su.

🦋🦋🦋

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.