Free chapter · Read without an account

Page 33 _ 34

by Harira salihu Isah · 💔NAUYIN BAKI👄💔 Na Uwar Batoorl

💔NAUYIN BAKI....👄💔

 

     Na

Uwar Batoorl.

𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠

    اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

🅿️ 33 _ 34

⭐️

Abba numfasawa yayi tare da gyara zama ya ce, "To Maman Abubakar, ban ƙi ta bakinki ba, amma dai duk a zantukan naku ke da Umar, ban fahimci dalili guda ɗaya da zai sa Abubakar ya ta da wannar magana a yanzu ba, hankalinshi ne ya ba da ajiya? Ko kuwa iliminshi ya bayar aro? Ko dai tunaninshi ya haɗa da magani ya kurɓe?"

Mama murmushi ta yi, don ta san dole sai ta sha fama da Abba dama, cikin kamalalliyar muryarta ta ce, "Abban yara a dai yi mana afuwa, amma ko guda ɗaya mai babban suna bai yi ba, a cikin ukun da ka lissafa, ƙauna ce da soyayya ta autarka suka ƙure shi, kuma a wannan fasali inma akwai mai laifi to ni ce, ina gaba a laifin, domin matsayina na uwa ga babana da autarka, ya kamata a ce na hango wannar soyayya, amma kuma ban mai da hankali ba har dai aka kawo yanzu, dan Allah a dubi ƙoƙon baranmu."

"Wannan lamari yana ɗaure mini kai yana bani mamaki wallahi, Abubakar na son auta, yaushe ma ya fara son nata? Tun kamun a tsayar da maganarta da Aliyu ne ko bayan an tsayar? Idan kamun a tsayar ne meyasa bai yi magana ba sai yanzu? Har kuma ya shige wa shi Aliyu gaba a maganar, sannan idan bayan an tsayar da maganarta da Aliyu ne, meyasa zai fara son ta bayan ya san akwai sadakin wani a kanta?", Abba ya ƙarishe maganar a kausashe, saboda ran shi ya fara ɓaci.

"A yi haƙuri Abban yara, amma tun Sadiya bata san kanta ba mai babban suna yake son ta, kawai ya jinkirta ne da niyar ta kammala karatu kamun ya mata magana, sai kuma aka samu akasi maganar Aliyu ta shigo, shi ne har aka samu akasi haka, amma amana afuwa mu daidaita komai mu gyara."

"Jin cewa Abubakar ya so auta ne tun ba yanzu ba, ya fi komai ɓata mini rai, domin ya fi muni a kan a ce ya so ta ne daga baya, duk da son ta bayan ya san akwai sadakin wani a kanta hakan ma laifi ne, amma gwanda haka, dan zan iya mishi uzuri tunda soyayya bata shawara take shigewa mutum zuciya, amma kuma wai yana dakon soyayyarta tun ba yau ba, dan sakarci da sokanci har ya shige wa wani gaba a kan batun aurenta, to ya fi komai ɓacin rai da muni, kuma wannan ba uzuri ne da zan karɓe shi ba balle na duba, ai Aliyu da ya shigo rayuwartata ya burgeni matuƙa, domin dama masu iya magana sun ce, idan ba ka yi ka bani waje, tunda shi bai da hankali da lissafi to wanda ya fi shi lissafi ya yi gaba, idan ba rashin lissafin ba to me amfaninmu na manya? Idan bai sanar mata ba saboda baya son karatunta ya katse, ai sai ya sanar mana mu iyayensu dan mu san da maganar, domin da ya sanar mana da lokacin da wasu suka zo da maganarta to za mu ce an mata miji, amma sai daga baya bayan banza, da shi aka yi komai, yana ji yana gani har shawara da shi an yi kamun aka yanke komai, aka tsayar da ranar biki, kuma sannan yanzu yau biki saura kwana biyar kuma a ce ga wannar magana, mahaukata ya ɗaukemu ko yara ƙanana? Me ya hana shi ci gaba da riƙe soyayyar a cikinshi yadda yayi niya? Ba duk dan yana so ya sa mutuncinmu ya zube a idon mutane ba? To ba mai ba wa Abubakar auren auta, ya ci gaba da riƙe soyayyar a cikinshi, ya mai da maganar ya haɗiye abarshi, mu ma za mu yi kamar bamu ji ba, a je a haka, Allah ya ba su zaman lafiya ita da Aliyu, ai shi ya zaɓi haka tun da ya shige gaba aka yi komai, wallahi wannan abin ya fi komai ƙona mini rai, Abubakar kam me ya ɗauke ni ne? Ƙaramin mutum yake son mai da ni?", a matuƙar hasale Abba ya ƙarishe maganar, dan zuwa sannan ran shi ya ɓaci sosai, domin ji yake wannan raini ne Sadeeq ya mishi, ya raina shi, idan ba raini ba me zai sa sai yanzu zai ta da maganar?

Mama a tausashe da muryar magiya ta ce, "Shiyasa tun farko muka nemi tuba kamun muka yi magana, domin tabbas mai babban suna bai kyauta ba, amma yana da dalili, kuma dalilinshi mai matuƙar muhimmanci ne, daliline wanda zai sa a amince mishi da auren Sadiya, domin ya cancanta, dalilinshi zai nuna gwargwadon yadda zai riƙe ta da amana idan ya aureta."

"Dalilin Abubakar na banza da wofi, raini ne kawai yake damun Abubakar ba komai ba, amma ba komai za mu haɗu ne, sai na saɓawa Abubakar fiye da tunani, domin bai isa ya mayar da ni ƙaramin mutum mai magana biyu ba."

"Abban yara dalilin mai babban suna yana kan daidai, duk ya yi wannan kuskuren ne saboda kiyaye farincikin auta, saboda yana son farincikinta fiye da nashi, saboda yana ƙaunarta sosai, ya zaɓi ta kasance a farinciki ko da kuwa zai rasa rayuwarsa ce..."

Abba katse zancen Mama ya yi ta hanyar cewa, "Indai da gaske haka yake nufi to ya rasa rayuwarsa mana ya barta da Aliyun, ta nuna Aliyu take so har kuma shi ya shige mata gaba, yanzu kuma me zai sa ya ta da wannar magana muddin yana son farincikin nata da gaske?"

"Ba mai babban suna bane ya ta da maganar, Umar ne ya bincika har ya gano haka, domin kasancewar babana a wannan hali yana damunshi matuƙa, shiyasa har ya bincika kuma Allah ya amince ya gano sanadin damuwar, muma kuma sai mu bai wa zuciyarmu haƙuri, kar mu duba komai kawai mu bai wa yaranmu abinda suke so, saboda Allah, domin sosai babana ya cancanci auren Sadiya fiye da Haidar, don cancantar Umar ya gano har ya sanar da mu maganar."

"A ba su abinda suke so? Kuna tunanin auta tana son Abubakar ne? Ko za ta haƙura da Aliyu ta ɗau Abubakar ne? Ina da yaƙini a kan cewa auta Aliyu take so."

"Ko shi mai babban suna sai da suka kai ruwa rana da Umar, sannan ya amince da batun auren har ya faɗawa Umar ɗin gaskiyar komai, dan haka Sadiya za ta iya cewa bata so da farko, amma ina da tabbacin aka mata bayani shikkenan za ta amince, domin duk wanda a rayuwa zai tauye kan shi domin kai ka wadata, to wannan babban masoyinka ne, da in ka rasa shi, kai da kanka za ka yi kuka da kanka, ba na yiwa Sadiya fatan yin da-na-sani a ɓangaren zaɓar miji, tunda aure rayuwa ce ta har mutuwa ake fata, ba zan ce Haidar baya son ta ba domin shi ma yana iya ƙoƙarinshi, amma kuma na fi hango mata alkairi a zama da mai babban suna, duk ma bayan haka Sadiyar ma tana son mai babban suna kawai duk sun kasa furta wa juna ne."

"Shikkenan, duk da ba ina nufin na yarda zan bai wa Abubakar auren auta bane, amma dai bari mu ji ta bakinta tunda kuna tunanin tana son shi ita ma, idan har ta yarda da aurenshi da kanta, to zan yi tunani akan mai ya kamata na yi, domin duk da haka ba yana nufin zan amince bane na aurawa Abubakar ita, amma kuma idan ta ce bata yarda da aurenshi ba, wallahi ko me zai samu Abubakar ba zan aura mishi auta ba."

Da sauri Umma da kanta ke gefe tana sauraransu, ta juyo jin Abba ya rantse, kallon Mama ta yi suka haɗa ido, sannan ta mai da kallonta ga Abba, shi ma haɗa idon suka yi, kuma ta ga alamar tabbaci a ƙwayar idanuwanshi, wanda ya ɗaura mata da tabbacin furci, ya ce, "Hakan nake nufi, kuma ba zan yi kaffara ba in sha Allah, don haka idan Maman Abubakar kin koma gida sai ki turo mini auta, kuma ban lamunta ba ki tilsta mata, dan na fahimci lamarin naku da son kai ya zo, domin ni ban ga wata cancanta da aka fi Aliyu ba, in sha Allah aka yi auren to shi ma da amana zai riƙe ta, kuma za ta fi samun farinciki ma a wajanshi saboda yana sonta tana son shi."

Murmushi Mama ta yiwa Umma da Abba, sannan ta ce, "Ka gama magana Abban yara, tunda ka ce na turo auta ai dama ce ka bamu, kuma mun gode, in sha Allahu kuma auta za ta amince da babana, domin ni sai yanzu ma nake hasaso irin soyyyar da suke gwadawa juna ba tare da saninsu ba."

"Koma dai menene, muddin ta nuna bata yarda ba, to kar wanda ya kuma mini wannar magana, indai bata amince ba to binne maganar nan za a yi kamar ba a yi ta ba, don baƙi za muyi, bai kamata su zo biki kuma ƙananun maganganu na tashi ba, in batu ya kai ga gidan surakunanta kuma wani damuwar aka saya mata tun kamun ta je", Abba ya faɗa yana miƙewa tare da nufar upstairs, yana mai jaddadawa Mama ta turo mishi Sadiya.

Abba na wucewa Umma ta sauƙe gauron numfashi, tare da cewa, "Allah ya kyauta."

"Amin Umman yara, kum Allah ya tabbatar da alkairi, domin muddin autarku ta auri babana to ba ku da wani kokonto, da amana zai riƙe muku ita da soyayya."

"Hmn! Magana ta gaskiya Sadeeq bai kyauta ba Maman Sadeeq, duk da ina son batun aurensu da auta, amma nima ina jin haushin abinda ya yi kamaar dai yadda abin ke ƙona ran Abbansu, duk me amfaninmu da idan bai sanar mata ba mu ba zai sanar mana ba? Sannan yanzu ma sai Umar ke bincikowa, da Umar bai binciko ba kenan idan abu ya zo da ƙarar kwana sai ya mutu haka? Kuma ko da Umar ya binciko har yana da ƙwarin idon da zai musa har sai an kai ruwa rana da shi kamun ya amince? Wannan wane irin hali ne? Me ke damun Sadeeq?"

Numfasawa Mama tayi tare da cewa, "Tabbas mai babban suna bai kyauta ba, kuma musamman wa ni, sam-sam bai kyauta mini ba ban zaci haka daga gare shi ba, domin wallahi ni mai ba shi auren Sadiya tun tana tsumman goyo ne, amma kuma ba komi na mishi uzuri, son da yake mata da son farincikinta da tunanin makomar karatunta shi ya ja komai, Allah ya shige mana gaba kawai ya tabbatar da alkairi nan dan wasu watanni mu fara ganin jikoki."

Murmusawa Umma ta yi tare da cewa, "To Amin Ya Rabbi, Allah ya musu albarka, ƴan baya ma Allah ya kawo musu abokanan zama na gari."

"Amin Ya Hayyu Ya Qayyum Umman yara, bari na wuce na samu na aiko autar taki, a samu a yi komai da zafi-zafi a wuce wajan", faɗin Mama da ta miƙe tsaye.

"To Maman Sadeeq, a isa lafiya, sannu da ƙoƙari, ki ja mini kunnen jikokinki fitinannun nan."

"Ƙawayena nitsatstsu dai ko", Mama ta faɗa tana dariya.

"Tunda dai kin ce musu nitsatstsu shikkenan, amma ba wai dan a nitsen suke ba, yanzu dai ƙyale ta maganar yara masu kama da masu jajayen kunnuwan nan, ki ƙaraso mu karya, sai ki wucen."

"A a Umman yara, ai ban ci ta saka komai a cikina ba, sai na je na turo Sadiya, ta zo an yi magana an wuce wajan, sai na tabbatar ta dawo ta shaida mini sun gama magana da Abbansu sannan zan karya yau."

Ƴar murmushi Umma tayi tare da cewa, "Abin na yi ne kenan."

"Saka wando ta ka ba", Mama ta faɗa tana dariya.

"To Allah shige mana gaba ya tabbatar da alkairi."

Da, "Amin Ya Allahu", Mama ta amsa tana murmushi.

A haka Umma da Mama suka yi sallama suna raha, Mama ta fice ta wuce gida.

  Umma komawata yi kan kujera ta zauna bayan fitar Mama, a sanyaye ta ce, "Ya Rabbi ka tabbatar mana da alkairin da ke cikin wannan lamari, idan Sadeeq alkairi ne ga auta ka amince wa aurensu, idan kuma ba alkairi tsakaninsu ka bai wa zuƙata haƙuri Ya Rabbi, ka tausashi zuciyar Sadeeq ka ba shi lafiya mai ɗaurewa, ka ara mishi juriya da jarumta, Ya Rabbi kada haka ya zame sanadin da zan rasa ɗa na, Allah ka sa muna da rabon ganin jinin Sadeeq, kar ya koma gare ka bamu ga jininshi ba, Ya Allahu", Umma ta ƙarishe addu'an, cikin matuƙar rauni da kuma tausayi irin na uwa, idanuwanta fal ƙwalla wanda suka gangaro tana shafa addu'ar, ta sani mutuwa dole ce kuma ko wani bawa lokacinshi yake jira, amm ba ta fatan ganin gawar ko da mutum ɗaya ne a cikin yaranta, tana addu'a dukkansu su sanyata a makwancinta na gaskiya, domin jin Sadeeq na ƙoƙarin rasa ran shi a kan auta ya fi komai ɗaga mata hankali, ba dan wannan ba da tana goyon bayan Abba na a hana Sadeeq auta, amma kuma batun rasa rai ya sa tana tausayin Sadeeq tare da yi mishi fatan samun Sadiya.

  Jiki a mace Umma ta miƙe da niyar haurawa sama, sai Khalid da da Sa'ad suka fito, sannu da aiki suka yiwa Umma, domin sun gaisa tun da sassafe bayan dawowarsu masallaci.

  Amsa sannun Umma ta yi, sannan ta ce, "Khalid ga abin karyawan mutanen asibiti Mamanku ta kawo ka haɗa ka wuce musu da shi duka, kai kuma Sa'ad zo ka karya kamun ka fita wajan aikin."

Khalid ya san nufin Umma shi ya je su karya a can asibitin, shiyasa bai wani ja magana ba ya ɗauka duka ya fice tare da yiwa Sa'ad ya dawo lafiya.

Umma da Sa'ad suka wuce dinning, Sa'ad yana zama ba tare da ya taɓa komai ba a wajan, idanuwanshi a kan fiskar Umma ya ce, "Umma me ya faru? Me ya same ki naga idanuwanki wani iri? Ko ciwo suke miki? Ko abu ne ya faɗa?"

Umma ƙaƙalo murmushi ta yi dan kawar da yanayin fiskarta, ta ce, "Ba komai Sa'ad, ka yi maza ka tafi ka ga takwas ta yi."

Sa'ad bai ja maganar ba, tunda dama ba musu suke da iyayensu ba, kuma wataƙila tunda ta ce ba komai duk da ya ga alamar akwai, to ba zai shige ita da Abba bane, wanda ba ruwansu da haka, na su kawai addu'a da fatan alkairi ga iyayen nasu ne.

Umma tana zaune har Sa'ad ya zuba abin karyawarshi ya soma ci, har ta miƙe tsaye sai kuma ta koma ta zauna, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon Sa'ad, cikin yanayi da ke nuna tausayin uwa da kuma soyayyarta ta ce, "Sa'ad, damuwar Sadeeq ke damuna."

Ɗagowa Sa'ad yayi, cikin kulawa ga mahaifiyarshi ya ce, "Me ke damun Yaya Sadeeq kuma Umma? Ina ce jikinshi da sauƙi? Jiya da muka wuni wajanshi fa har fita harabar asibitin ya yi, menene kuma ya faru?"

"Maƙasudin ciwon nashi nake magana a kai Sa'ad, abinda ya sa shi ciwon nake nufi ba wai matakin samun sauƙinshi ba."

"Menene Umma? Kun gano abinda ke damun Yaya Sadeeq ɗin kenan? Ni ai na jima da fahimtar abu na damunshi wallahi, duk miskilancinshi ya ƙaru a kwanakin, kai murmushi ma ta yaƙe yake yi, menene ke damunshi dan Allah Umma?", Sa'ad ya faɗa cikin zaƙuwa.

"Sadeeq son auta yake yi, tun ba yau ba tun tana yarinya, ɓoyewa kawai ya yi, kuma yanzu batun aurenta ne nake tunanin ya haddasa mishi wannar ciwo."

"What?, Umma da gaske ko da wasa? Yaya Sadeeq na son auta, autarku Sadiya? Tun ba yau ba, amma to meyasa ya ɓoye?", murya a ɗan sama kuma cike da mamaki Sa'ad yayi duk wannar magana.

Umma ta ce, "Son da yake mata ne kawai ya sa ya ɓoye, yanzu ma Umar ne ya gano in ba haka ba da ba wanda zai sani."

"No wonder, haba mana, shiyasa ashe duk ya zama so silent tun da aka tsayar da ranar bikin, domin ina kule da Yaya Sadeeq tun daga lokacin ne ya fara sauyawa, ashe soyayyar auta ce, kuma har yake ƙoƙarin mutuwa saboda haka, Allah mun gode maka da ka taƙaita mana wannar jarabawa, Allah ya yiwa Yaya Umar albarka da ya gano wannar matsala."

"Amin Sa'ad", Umma ta amsa cike da alfahari da Umar.

"Amma yanzu Umma ya ake ciki? Fatan dai an mayar da auren kan Yaya Sadeeq."

"To yanzu dai ba zan ce ga shi ba, domin Abbanku ya ce bai amince ba, sai dai da Mamanku ta mishi magana to ya ce sai ya ji ta bakin auta, muna fatan jin alkairi."

"Ahh! In dai ta auta ce kar mu wani damu, auta ai ba za ta ƙi auren Yaya Sadeeq ba, yadda take son sa shi ma yake sonta, ai dama auren junansu shi ne daidai, Allah dai ya tabbatar da alkairi, Allah kuma ya bai wa Haidar haƙuri da danga."

"Amin Sa'ad, wallahi ina tausayin Sadeeq sosai, amma shi ma Haidar ɗin tausayinshi nake, yanzu ba dan mutuwa ba ai da duk wannan mai sauƙi ne, sai a bai wa Sadeeq auta, shi kuma Haidar a ba shi Husna."

"Allah sarki rayuwa, Allah dai ya jaddada rahama ga mamatanmu, Allah kuma ya tabbatar da alkairi."

"Amin Ya Rabbi, ka yi ka gama ka wuce ko, bari na shiga ciki", Umma ta faɗa tana miƙewa, dan ta ɗan ji sanyi a ranta da magana da Sa'ad, saboda ko ba komai a maganganunshi akwai ƙarfafa guiwa da tabbacin in sha Allah Sadeeq zai samu auta, kuma hakan na nufin ba za ta rasa Sadeeq nata ba.

"To Umma, a fito lafiya."

Amsawa Umma ta yi ta wuce, har ta fara taka stairs ta tsaya tare da cewa, "Kar na ji wannar magana a bakin kowa daga ni sai kai sai kuma Allah, idan kuma ka labartawa wani Abbanku ya ji kai da shi ba ruwana", tana gama faɗa ta wuce abinta.

Sa'ad murmushi yayi tare da tabbatar wa Umma ba wanda zai ji, amma a zuciyarshi mamaki ne da kuma farin ciki, domin Sadeeq da Sadiya sun dace matuƙa, "Perfect match couples kenan", ya faɗi yana murmushi, yana mai tuno wani anko da Yaya Sadeeq ya yi shi da Sadiya ranar bikin kammala makarantarta, kyau suka yi wane amarya da ango.

⭐️

     SADIYA POV

        ***

Bayan ficewar Mama, Sadiya ta kammala sauran abubuwan, sannan ta wuce ta yiwa su Najla wanka ita ma ta yi wanka, Khausar ma wankar ta yi duk suka shirya, sannan suka fito suka zauna karyawa, Sadiya kasa haƙuri ta yi, domin da maganar a rai ta kwana kuma da shi ta tashi, tana sauƙe kofin kunu da ta kurɓa ta ce, "Aunty jiya muna magana bamu ƙarasa ba kuka fita, kamun ki dawo kuma na yi bacci."

Khausar murmushi tayi tare da cewa, "Eh small Mum haka aka yi."

"Aunty ina jin ki, wani irin soyayya kike nufi? Wani irin soyayya Yaya Sadeeq yake mini? Bayan irin son da muke yiwa juna."

"Table manners small Mum, let's finish eating first", faɗin Khausar tana kai spoon bakinta.

Sadiya bata kuma cewa komai ba ta yi shiru, har suka kammala karyawa, ta tattare kwanuka, ta gogewa su Najla jikinsu, ta wuce kitchen ta wanke abubuwan da suka ɓata sannan ta fito, su Najla suna wasa suna kallo a madaidaicin plasma da ke palourn, Khausar kuma na danna wayarta, a gefen Khausar ta zauna, sannan ta ce, "Aunty ina ji."

Murmushi Khausar ta yi tare da cewa, "kin matsu ki ji ne small Mum?"

Tura baki Sadiya tayi tare da jinjina kai cikin shagwaɓa.

Ƴar dariya Khausar ta yi tare da cewa, "Rigimammiyar Yaya Sadeeq, zai je ya cigaba da fama ai, dama shi ya ɓata ki, shi ya fara sai ya ƙarisa."

Murmushi Sadiya tayi kawai bata ce komai ba, tana dai sauraran Khausar ɗin.

Khausar idanuwanta na a kan wayarta ta ce, "Small Mum, ba soyayyar da kike nufi ta Yaya da ƙanwa bane, soyayyar da Yaya Sadeeq yake miki, halattaciyar ƙauna yake miki, wadda Allah ya halitta kuma ya halarta tsakaninku, Yaya Sadeeq na matuƙar ƙaunarki tun baki san kanki ba, Yaya Sadeeq na ƙaunarki da gasken gaske, Yaya Sadeeq ya haƙura ne har ya shige miki gaba a kan batun Haidar, saboda ke kika so hakan kuma kin nuna mishi hakan ne farincikinki, wanda nake da tabbacin indai Allah ya nufa, to ko muradinki na ya zame waliyyinki ne, zai zame ya ba da aurenki muddin hakan ne zai faranta miki, saboda shi Yaya Sadeeq he took your happiness as his priority, he don't match everything related to you da komai, duk abinda ya shafe ki so daban ne a wajanshi, but believe me small Mum, Yaya Sadeeq love's you soo much, he loved you since the first day he saw you, i meant the day you were born, and he keeps on loving you till date, soyayya ce Yaya Sadeeq ke miki wacce ke da wuyar samu, whoever sacrifice his life for your happiness, he means world to you, na sani kina cewa Yaya Sadeeq shi ne duniyarki, but you have to take it this way, ki faɗi kalmar da shauƙin soyayyar da take nufin ta mallakar juna ne ta hanyar aure."

"Pardon, Aunty ban fahimceki da kyau ba, am very sure kunnena abu daban suke jiye mini da wanda kike faɗa, and I don't know why", Sadiya ta faɗa cikin rashin fahimta.

Murmushi Khausar ta yi tare da aje wayarta a gefe, cikin tabbatarwa da cire kokonta ta ce, "Son soyayya ta saurayi da budurwa, that turns the lovers to husband and wife, wannar soyayyar Yaya Sadeeq yake miki, aurenki yake son yi."

Da wani irin expression Sadiya ke kallon Khausar, she's just staring at her without blinking her eyes, and without saying a word, kallon Khausar take deeply like she sees someone new not Khausar da ta sani.

Wannan kallon da Sadiya ke yiwa Khausar, ya yi matuƙar kaɗa Khausar, domin tana iya hango shock ɗin da Sadiya ta shiga, tana hango wani abu daban bayan shock ɗin, but she don't believe it and she wish ba gaskiya bane abinda take hangowar.

"Small Mum say something, kin yi shiru kina kallona", Khausar ta fara in a calm voice.

Sadiya saurin lumshe idanuwanta ta yi, zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri, idan ta ce za ta buɗe baki ta yi magana, she can faint saboda yadda take ji, she can't believe what Khausar just said, neither she can't understand too, she know this most be joking, but why she looks so serious while talking? Kuma meyasa sai yanzu za ta mata wannar wasa? Wasa irin wadda bata taɓa mata ba, kai babu ma wanda ya taɓa mata irin wannan wasa sai friend's nata da Khalid, and she stopped them as soon as possible, meyasa yau kuma Khausar? Kuma a irin wannan lokaci da take daf da kasancewa mallakin nitsuwar ruhinta Aliyu Haidar Al-Sad.

Khausar magana ta dinga yi tana ƙiran sunan Sadiya, amma ta yi nisa a duniyar tunani idanuwanta a kulle, hakan ya sa Khausar ta kai hannu ta girgiza ta tare da cewa, "Hey small Mum what's wrong? Are you okay? Ko maganar da nayi ne?"

Sadiya har ra buɗe baki za ta yi magana,  sai kuma ta fasa ta girgiza wa Khausar kai kawai, ta miƙe ta wuce ɗakinta without turning back, hakan ya sanya Khausar ta bi ta da kallo tana jan numfashi tare da cewa,  "Ya Allah ka sa ba abinda zuciyata ke zargi bane tun farko, Ya Rabbi khairan."

Khausar na zaune tana nata zancen zucin sai ga sallaman Mama ta shigo, amsawa tayi tana faɗin, "Sannunku da dawowa Mama."

"Yauwa Khausar, fatan kun karya? Dan na ce da Sadiya kada ku tsaya jirana."

"Eh Mama mun karya, ya su Umma da Abba?"

"Yauwa, suna lafiya, ina ita Sadiyar?"

"Yanzu ta shige ɗaki."

"Lafiya dai ko? Waya ta je yi ko kuwa ƙullen ne ya tashi?"

Murmushi Khausar tayi tare da cewa, "ko ɗaya, magana dai muka yi da ita sai ta tafi, ko amsa ma bata bani ba."

"Maganar mai babban suna? Daman baku gama maganar jiya ba?"

"Eh Mama, na dawo asibiti na samu ta yi bacci, sai yanzu muka yi maganar, amma dai bata ce mini komai ba ta tashi ta shige ɗaki."

"Ai kuwa shiga ɗaki bai same ta ba, dan bata ci ta ƙulle ba, ta bari sai ta zama amaryar sannan ta kama ƙullen ɗaki."

Murmushi Khausar tayi tare da cewa, "Da dai an barta ta huta, ina tunanin ta ji shock ne a kan maganar, ta shiga mamaki kamar yadda duk muka shiga."

"Ba hutu Khausar, yanzu daga wajan Abbanku nake, ya dage a kan batunshi na ba zai bai wa mai babban suna aurenta ba, to dai daga ƙarshe da na saka naci na samu ya ce zai duba lamarin muddin Sadiya ta yarda da auren, kuma kinsan idan ya ce zai duba kamar dai ya amince ne, kuma bana jin ba za ta amince ba, amma fa ya rantse idan bata amince ba, ba zai ba wa mai babban suna aurenta ba."

"Kamar dai yadda Yaya Sadeeq ma ya rantse ba zai aureta ba sai ta yarda, idan babu yardarta ba zai aureta ba."

"Shi ai mai babban suna dan sonta da yake ne ya faɗa haka, kuma dan farincikinta, amma Abbanku so kawai yake ya hana mu ita, amma in sha Allah yanzu zan shiga na mata magana na tura ta, sai ta sanar da shi da bakinta ta yarda, shikkenan an wuce wajan sai batun mu sake zage dantse wajan shirye-shirye."

"Haka ne Mama, Allah shige gaba ya tabbatar da alkairi."

"Amin Ya Allahu", Mama ta amsa tare da miƙewa ta nufi ɗakin Sadiya, da sallama ta shiga ɗakin, can ƙuryar gado ta hango Sadiya a kwance cikin bargo ta yi rub da ciki, amma daga yadda ta tallafe kanta da hannayenta da kuma yadda take motsa ƙafafuwanta za ka tabbatar idanuwanta biyu, hakan ya sanya Mama ta ƙarasa bakin gadon tana faɗin, "Kin daina amsa sallama ne inna uwasu?"

Sam-sam Sadiya bata ma ji motsin shigowar Mama ba, balle ta ji sallamarta, domin ta yi nisa a duniyar tunani, har yanzu zantukan Khausar ke amsakuwwa tare da maimaita kansu a kunnuwanta, ƙwaƙwalwarta da zuciyarta, tana kuma ƙoƙarin tariyo wani abu da Yaya Sadeeq ya mata mai kama da zancen Khausar, amma ta kasa gano wa.

Mama zama ta yi a gefen Sadiya, tare da kai hannu ta taɓa ta tana faɗin, "Me kike tunawa haka har baki ji motsina ba balle sallama na?"

Firgigit! Sadiya ta dawo hayyacinta tare da saurin janye hannayenta ta kife kanta tana sauƙe numfashi, dan ta ɗan razana.

Mama gyaran murya tayi tare da cewa, "Menene ya faru?"

Cikin rawar murya, Sadiya ta haɗe kalmomin bakinta tare da cewa, "Nothing, ba komai", murya a ciki-ciki Sadiya ta furta haka.

Mama jinjina kai tayi tare da cewa, tashi ki zauna to za muyi magana.

Ba musu Sadiya ta tashi ta zauna tare da sunkuyar da kanta ƙasa.

Mama sai da ta ƙare wa Sadiya kallo sannan ta numfasa ta ce, "Sadiya na tabbata kun yi magana da Khausar, kin kuma ji abinda ta faɗa sannan na san kin fahimta kuma..."

Da sauri Sadiya ta katse Mama ta hanyar girgiza kai tana faɗin, "Ban fahimta ba Mama, domin kunnuwana sun kasa jiye mini asalin abinda take faɗa, abu daban ta faɗan su kuma abu daban suka jiya mini."

"Me kunnuwan naki suka jiye miki?"

"Mama wai ni aunty Khausar ke cewa Yaya Sadeeq yake so, soyayya irin ta yin aure, irin dai soyayyar da Haidar yake mini", Sadiya ta ƙarishe maganar tare da ɗago kanta ta zuba wa Mama ido, cike da fatan ta ji saɓanin wannan daga bakin Mama.

Murmushi Mama tayi tare da jinjina kai ta ce, "Kin yi mamaki ko? Tabbas muma mun yi mamaki fiye da wanda kika yi, amma kuma gaskiya Khausar ta faɗa miki, daidai kunnuwanki suka jiye miki, kuma yanzu nima zan jaddada miki hakan dan ki fahimta, Sadiya daga mu har ke mun kasa harbo jirgin mai babban suna, yana sonki ne tun ranar da ya ɗaura idanuwanshi a kanki, ya ɓoye ne saboda ki kammala karatu tukunna, sai kuma ga maganar Haidar, sai ya cigaba da ɓoyewa saboda farincikinki ya fi mishi komai, ciki har da rayuwarshi, wadda hakan har yayi sanadin ya kwanta wannan ciwo, da ikon Allah kuma ya farka sanadinki, hakan ya sa Yayanki Umar ya binciko har ya gano soyayyar da mai babban suna ke miki, da irin sadaukarwar da yake shirin miki, na haƙura ya rasa rayuwarsa saboda farincikinki, kuma...."

Yanzunma Sadiya a kiɗima ta katse Mama da sauri, domin bata gane dogon bayanin Mama, tun tabbaci da ta samu na farko a kan abinda Khausar ta faɗa, shikkenan ta daina gane komai da Mama ke faɗa, murya a karye ta ce, "Amma Mama.....

***

Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.

●BAKANDAMIYA HIKAYA.

●WATTPAD

@Uwarbatoorl96

●AREWABOOKS.

@Uwarbatoorl96

●WHATSAPP

***

a kan Naira #500.

Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.

# Hareeyh

# ***

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩

# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &

# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol