Free chapter · Read without an account

Chapter 14

by @Mrs Alkali · Zaɓi na



✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~

🆓 Page 1️⃣ 4️⃣







Girgiza kai Ammi tayi jin abunda jawaheer take cewa , Ammi ce tace to Allah ya shiryeki jawaheer nikam barin fita induba, inga me ake ciki ,fita Ammi tayi daga motar baba idi ne yataho da gudu agaban Ammi ya zube yace hajiya wani abune kuke buqata, 

Ammi ce tace baba idi angane matsalar motarnan kuwa kodai haryanzu ba a kaganeba, ehhh wlh hajiya dama yanzu nake shirin naje nafamiki sai dai pha ayiwa alhaji waya ,afadamasa halin da ake ciki inyaso aturo wata motar tadauke ku Ammi ce tace aa baba idi karka damu , kaduba mana waccar motar data tsaya agabanmu inda space sai mu karasa aciki naga kamar kano suma suka nufa, inyaso kaikuma saika kira makaniki inya duba motar sai ka taho da ita, toh hajiya, angama.

Tashi baba idi driver yayi motar dasu Aliyu suke ciki yanufa magana yayiwa drivern motar nan drivern yace akoi space yo ai ko ba space sai ya dauki wadannan mutanen dagani manyan mutanene motarsu tasamu matasala kamar kataba su jini yafi to, yo shi karen haukace ta cijeshi da zai ce ba space, baba idi ne yadau kudi masu yawa ya bawa drivern motar su Aliyu nan drivern yashiga godiya , sabi da yasan kudin yafi kudin motar ta su, baba idi ne yaje yacewa Ammi ansamu space , hamdala Ammi tayi leka Motar tasun tayi ta window kallon jawaheer tayi tace toh gimbiya saiki fito mutafiko, zumbura baki jawaheer tayi, Ammi ce tace to shikenan in bazaki wuce ba ni barintafi inyaso kya jira baba idin kwataho tare inya nemo makaniki aka duba motar,wani irin zabura jawaheer tayi jin an ambaci sai ta jira baba idi, fitowa tayi daga motan, tana wani daure fiskanta.

Masha Allahu, Allah yayi hallitta anan jawaheer bata da wani tsayi sosai, kuma ita ba guntuwa ba ce wato irin matannanne da ake kira tsaka tsaki sanye take da riga t-shirt da wondon jeans, wondon yakamata sosai musamman wajen tudun hips din ta dan bata da kiba sosai amma kuma baza ace mata siririyaba ,jikinta dan lumui lumui ne sai wani uban hips da Allah ya bata kai kace ciko ne tayi intana tafiya harwani juyawa sukeye zakace da gangan take motsasu alhalin ita batasan ma tanayiba, tana da madai daitan breast suna da girma amma ba irin sosai dinnanba ,bakar abaya ta daura akan Riga da wondon dayake jikinta, abayan tana dauke da flawi masu ratsin golding kafanta sanye yake cikin takalmi sneakers golding color na mata, wani dan karamin jaka ce a hannunta, black in colour, ita da wannan matashiyar matar da zata kai kimanin shekara 50 aduniya kallo daya zaka musu kasan suna da alaka da junansu sabida tsananin  kama da sukeyi.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.