Free chapter · Read without an account

Chapter 17

by @Mrs Alkali · Zaɓi na

✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~

Page 1️⃣ 7️⃣







Alhaji kasan habeeb yana mutuwar son jawaheer,tun da haryanzu batasamu ZABIN nataba me zai hana a aura mata habeeb din kodon ceto rayuwar ta, in mukacigaba da zuba mata idanu haka zatacigaba da fama da wannan ciwon har ya kai matakin da doctor yace in ba asamamata mafita ba akoi matsala,
Sanin kankine bazan taba yiwa jawaheer auren dole ba dan haka zanjira ZABIN ta, ko yau jawaheer takawomin ZABIN ta zan Aura matashi ko dangidan uban waye ne a fadin kasarnan, indai dukiya da alfarma suna aiki to zantabbatarmiki da hakan.
Shiru Ammi tayi ,tana tunanin wannan son da Abba ya keyiwa jawaheer, baya wasa da duk abunda ya shafeta, anya hakan zai haifar musu da da mai ido kuwa,

Bayan wani lokaci A hankali jawaheer take bude idanunta dasuka mata nauyi, hannunta ta daura akan maranta da yake dan mata ciwo, Abba ne yatashi da sauri ya nufeta zama yayi agefenta hannunsa yadaura akan fiskar ta shafa gefen fiskar yayi yace mamana kintashi ne, kai ta dagamasa alamar ehh, sannu ya jikin naki, ahankali ta bude baki tace da sauki Abba,
Yunkurawa  tayi zata  tashi Abba ne yakamata ta zauna , kallon Ammi dake tsaye tana kallon ikon Allah,yayi yace zo kikamata Ammin yara akaita dakinta tayi wanka, 
Ammi ce ta matso kama jawaheer tayi ahankali tatashi Ammi ce tanufi dakinta da ita,
Katon daki ne me dauke dawani shegen set na royal bed da Waldrop din sa da komai na dakin golding color ne da surkin milk, daganin dakin kasan  bakaramin kudi aka kashe masa ba,
Ammi ce tazaunar da ita abakin gadon, toilet ta nufa,ruwa me dumi ta hadamata acikin kwanon wankan dawowa tayi tace mata oya tube kizo ingasamiki jikinnaki, turo baki jawaheer tayi, Ammi ce ta harareta, a hankali tashiga rage kayan jikinta, tarage daga ita sai bra da pant toilet din ta nufa wuce Ammi tayi tashiga cikin toilet din Ammi ce tabiyo ta abaya wani dan karamin tawol Ammi tadauka aruwa me dumin tasaka shi , cireshi tayi ta matse shi, daurawa jawaheer tayi akan maranta Wani irin zabura jawaheer tayi, rike hannun Ammi tayi kallon ta Ammin tayi wani rau rau da ido tayi Ammi ce tace sakemin hannu ko in sabamiki, idanunta ne suka cika da hawaye tace Dan Allah Ammi kimin a hankali, wlh dazafi.

Cigaba da gasamata maran Ammi tayi bayan tagamane tace maza kitube kiyi wankan saura karki fito da wuri, fita Ammi tayi daga toilet din,
A hankali ta ke takowa cikin dakin bayan tagama wankan, wajen dressing merro ta nufa zama tayi akan kujerar wajen , batajin shafa komai ajikinta ,don haka turaren humra ta dauka ta shiga shafawa ajikinta, nan da nan dakin ya gauraye da kamshin turaren humran, dan jawaheer akoi son kamshi, tashi tayi Waldrop din kayanta tanufa, budewa tayi, acike yake da kaya kai kace banamutum daya bane , wani riga taciro marar nauyi pink colour jikin rigan roba ne , ko bra bata sakaba pant kawai tasaka  , rigan yazauna dass ajikinta , zakace dan ita kawai aka dinka rigar, gaban merron taje ta tsaya turare ta dauka ta fesawa jikinta , hand Drayer ta dauka tashiga busar da gashin kanta dayake kwance har gadon bayanta ,baki ne sosai gashin gashida tsayi sai dai bashida cika sosai shiyasa bata fiye son kitso ba, yawanci kullum a tsefe zakaga kanta , bayan tagamane ribom tadauka pink colour ta daure kannata dashi, wani sassanyan kyau tayi kai kace ba yar Nigeria ba ce tayi kama da irin yarannan na turawa, kofa ta nufa a hankali take tafiya, Abba ne zaune da Ammi suna cin abinci jin alamar ana sauqowa yasa Abba daga kansa hangota yayi tanufo inda suke, kujeran gefensa yajamata, karasowa tayi, 
Hannunsa yamika mata kama nasa hannun tayi a hankali tazauna a kan kujerar da yaja matan,
Da kansa yatashi saving dinta yafara , fried rice yasaka mata dan dedai a plate paper cikin yasa mata a gefen bai samata salak ba sabida yasan bata cika son shi ba, cup ya dau ka wani Dan flask maikyau ya bude ruwan tea me zaifi sosai wan da yasha kayan kamshi ne aciki tsiyaya mata yayi, Ammi dai batace komai ba inda sabo yaci ace tasaba , yadda Abba yakeyiwa jawaheer,shi kullum kallon yarinya yakemata,bata taba girma a idanun sa tun Ammi namasa fada har tagaji tazubawa sarautar Allah ido, da ace ba ita ta haifi jawaheer ba ,da zatayita samun matsala tsakaninta da Abba dudda ma yanzun ba tsira tayiba.
Mika mata cup din yayi karba tayi tace thank you Abba, ahankali ta kai cup din bakinta ,zukan tea din tashigayi a hankali , zafin tea din yana ratsa kasan maranta dama sabida haka ne yasa Ammi tamata tea din na musamman.
Sanda ta shanye duka sannan ta ajiye cup din a hankali ta tashi zata bar wajen , batare da tataba abincin da Abba ya zubamata ba, Abba ne yace ina zuwa Mamana baki ci abincin ba kuma, dan yamutse fiska tayi tace Abba banajin cin abincin yanzu, anjima zan ci, kallon ta yayi yace toh shikenan kije ki konta ki huta, anjima inason magana dake ,jinjina masa kai tayi, dakinta ta wuce .

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol