Free chapter · Read without an account

Chapter 18

by @Mrs Alkali · Zaɓi na

ht


✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~

Page 1️⃣8️⃣ 




  A bangaren Aliyu ya isa , Nigerian Law School kano ( Bagauda Campus) lafiya kalau ya isa , school management din yaje duk wani sauran cike cike yayi su , yagama komai har an bashi daki, duk wani daki mutum biyu ne aciki, haka yadau jakansa ya nufi dakin da aka basa,
Key din da akabasa yasa zai bude kofar dakin ,yana sawa yaji alamar kofar abude take , da alamar abokin zamansa a dakin ya rigasa isowa, sallama yayi, daga chan cikin dakin aka amsa masa da yes come in shiga yayi cikin dakin, wani kyakkyawan matashi ne da baiwuce sa'ansab zaune abakin gadonshi , laptop ne akan cinyar shi, yana dannawa, jin anyi sallama ne yasa ya daina danna laptop din yamaida hankalinsa kan kofar dakin, ganin wani matashin balarabe yashigo dakin dauke da jaka akafadarsa yasa Khaleed zuba masa idanu, Aliyu ne ya karaso Mika masa hannu yayi musabaha sukayi, Aliyu ne yace sunana Aliyu Ibrahim daga management na school dinnan aka turoni wannan room din, dan murmushi Khaleed yayi yana shafa kansa yace nazaci baka jin Hausa ai, akaron farko da Aliyu yayi murmushin dayasa kyawawan hakwaransa fitowa, Wanda yasa dimples dinsa suka lotsa shi abun nabasa mamaki ,haka mutane dayawa suke fadamasa , Khaleed ne yace sunana Khaleed Adam waziri, naji dadin haduwa da kai, nima haka cewar Aliyu, ajiye jakansa yayi ya nufi toilet din dake cikin dakin alwala ya dauro fitowa yayi, Khaleed ne ya mikamasa sallaya ganin alwala yayi karba Aliyu yayi, sallolin dasuke kansa yashiga ramawa sanda ya idar sannan ya tashi ya nade sallayar ajiyewa yayi , jakansa ya nufa budewa yayi yaciro wasu riga da wondo masu taushi na Jessy bakine da ratsin green ajikin kayan toilet ya nufa wanka yayi ,daga cikin toilet din ya goge jikinsa ya chanza kayan ganin bashi kadaibane a dakin, fitowa yayi, azaune yasamu Khaleed sai dai yanzu waya yakeyi, Ammi ya jikin jawaheer din ta farkane, ehh tafarka yanzuma tashiga dakinta don ta kwanta, ajiyar zuciya ya Khaleed ya sauqe yace to Allah ya sauwaqe da ameen Ammi ta amsa sallama sukayi katse wayan yayi, 
Kallon Aliyu yayi yace yakamata mufita munemi abinci dan wlh yunwa nakeji, murmushi Aliyu yayi baice masa uffan ba saima kofan da yaga yanufa alamar fita zaiyi daga dakin, Khaleed ne yatashi binbayan aliyu yayi, aranshi yace ikon Allah da badon dazu yaji muryan Aliyu ba sai ya rantse yace kurmane, cikin school din suka nufa, duk inda suka wuce sai ankallesu musamman yan matan dake cikin school din, sabida haduwar da sukayi don shima Khaleed ba baya ba a wajen kyau.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol