Free chapter · Read without an account

Chapter 19

by @Mrs Alkali · Zaɓi na


✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~

Page 1️⃣ 9️⃣ 









Khaleed ne yace barin tambayi security n can inane capteria na school din, Aliyu ne ya tsaya Amma baice masa uffan ba tambayan security yayi nan yamasa kwatance, dawowa yayi wajen Aliyu yace muje, tafiya sukaciga dayi Khaleed ne yake bin kwatancen da security n can yamasa ahaka harsuka karaso capteria, table suka nufa zama sukayi, waiter ne ya zo da menu Khaleed ne ya karba ya gama dubawa Aliyu ya mikawa, kinkarba Aliyu yayi yace akawomin tuwon shinkafa miyar kubewa danye in akoi waiter ne yace yes sir Khaleed ne yace joloff rice and chicken,
Juyawa waitern yayi can saigashi yadawo da abincin komawa yayi yakawo musu ruwa, Khaleed ne yadau spoon yafara cin abincinsa, yayin da Aliyu ya wanke hannunsa acikin ruwan da waiter yakawo domin wanke hannu BISSIMILLAH yayi yafara cin tuwon sa da hannu, Khaleed ne ya zuba ma Aliyu ido jin ana kallon sa ya sa shi dago kansa ,idanu suka hada da Khaleed, dan murmushi Khaleed yayi, yadan shafa kansa, kallon Aliyu yayi yace,
Dafarko danaganka nazaci kai ba dan kasarnan bane, Amma yanda naga kanacin tuwon nan da hannu saiyabani mamaki, Aliyu ne ya dan murmusa, cire hannunsa yayi acikin plate din, kallon Khaleed yayi yace ni Dan gombe ne, Khaleed ne ya zaro idanunsa waje yace da gaske kakeyi, dariya Aliyu yayi akaron farko tun haduwar su yanayin yanda Khaleed yayi masa tambayarne yabashi dariya,
Khaleed ne yace ai Ammi na ma yar gombe ce da danake karami ina yawan binta yanzune dai zuwan sai a hankali yafada yana dan shafa kansa, Aliyu ne yawanke hannunsa tissue yadauka ya goge bakinsa,shidai Khaleed yana kallon ikon Allah, yanda Aliyu yake komai cikin nitsuwa da izza kai kace basarake ne, shidai harcikin zuciyarsa yakejin Aliyu ya kwantamasa arai,
Aliyu ne ya tashi kallon Khaleed yayi yace guy let's go tashi sukayi wajen biyan kudin suka nufa Khaleed ne yaciro ATM dinsa ya mika musu duka yace sucire harda na Aliyu haka kuwa akayi, Aliyu ne ya kalleshi kamar Wanda baison magana yace masa tnx Khaleed ne yayi murmushi yace haba ai munzama daya we are friends ai, class suka nufa don suna da lecture by this time.

 Jawaheer ce konce akan gadonta bacci take son yi Amma tagagara, in tarufe idanunta a maimakon bacci ya dauketa , sai fiskar balarabenan na cikin mota take gani, wani irin tsaleh zuciyarta ke yi, bude idanunta tayi a hankali tasa hannunta ta dafe saitin zuciyarta, a hankali ta furta, ina son shi, shine ZABI NA sake lumshe manyan idanunnata tayi,wani irin hawaye ne masu zafi suka gangaromata tagefen idanunta,ganin zuciyar ta bata mata adalciba , daga haduwar farko, mutumin da ko sunansa bata saniba, batasan daga wacce kasa yakeba ,ganin farko taji zuciyar ta takamu da mugun son shi tabbas shi ne ZABIN ta, wannan shi ake kira love at the first site, ada tana da burin duk randa zuciyar ta ta hadu da ZABIN ta tabbas zata sanar da Abba toh Amma a yanzu me zatacewa Abba, inyatambayeta mutumin da batasan inda ma zata sake ganinsa ba wannan wacce irin kaddara ce haka tacigaba da tunanin wannan kurman balaraben dan ita haka tasamasa suna acikin zuciyar ta.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.