Free chapter · Read without an account

Chapter 27

by @Mrs Alkali · Zaɓi na



✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~

 Page 2️⃣7️⃣ 

Khaleed ne yayi parking a bakin wani katafaren gate , Horn yayi, da gudu wani security yazo bude karamar kofar yayi yaleka ganin motar Khaleed ne yasa yakoma da sauri ya wangalemasa gate din, cillah hancin motar sa yayi acikin harabar gidan, wajen da aka tanada don yin parking din motoci ya nufa, parking yayi yakashe motar kallon Aliyu dake ta latse latse awaya yayi , Khaleed ne ya ce guy mun iso pha.


Ko kula shi Aliyu baiyiba, ya danjima yana danna wayannasa kafinnan ya kashe wayar ahankali ya maida ita aljihun sa, bude kofar yayi ahankali ya zura kafarsa waje fitowa yayi cikin nitsuwa Khaleed ne tsaye ajikin Motar yana jiransa, shi dai yana ganin ikon Allah awajen Aliyu, mutum sai izzah duk yadda akayi wannan jinin sarauta ne, mutum sai takama da izza.

Aliyu ne yayi jaran murya ganin yanda Khaleed ya tsuramasa idanu, Khaleed ne yace yayi dai saraki kaganka kuwa Aliyu, duddah bakataba bani labarin ka ba Amma dai daganinka anga jinin sarauta, murmushi Aliyu yayi baice masa komai ba, sanin bazai ce din bane yasa Khaleed fara tafiya Aliyu ne biye dashi abaya tafiya yakeyi cikin nitsuwa da izza, dawani kasaita, Khaleed ne yayi noking kofar parlourn, Abba ne ya Kalli jawaheer dake konce ajikin sa haryanzu, yace Mama na je ki duba ana noking din kofar , tashi tayi tanufi kofar budewa tayi, a hankali,Yaya Khaleed ne a tsaye abakin kofan wani irin ihun murna tayi tare da dale jikinshi riqeta yayi yashiga juyi da ita dan ba karamin missing din qanwar sa yayi ba, abokiyar fadan sa, jin wani daddadan murya na ihu ne yasa Aliyu kallon bakin kofar wata farar yarinya yagani ta dale jikin Khaleed sai dariya sukeyi, wani irin faduwa gabansa yayi, yarasa dalilin jin faduwar gaban hulanta ne yadan zame baya hakan yayi sanadin baiyanan dan gashinta da yake konce agaban goshinta ,dauke ido Aliyu yayi daga kansu, Ammi ce tace Allah dai ya nunamin randa zakiyi hankali daga zuwan mutane kintare musu hanya kaima babban banza sai ka biyemata, kunbi kun tsayar da bako a waje Khaleed ne ya sauke jawaheer yana dan sosa kai alamar ya dan ji kunyan abun da Ammi tace ,cike da nitsuwa yace Ammi nayi missing din kune wlh, dariya Ammi tayi tace toh ai sai kushigo kun tsayar da mutum a bakin kofa, sai alokacin jawaheer ta duba bayan yaya Khaleed,jin abunda Ammi take fada.


Ido hudu sukayi da Aliyu dake tsaye abayan Khaleed wani irin dafe saitin zuciyarta tayi da hannunta,wani irin zuramasa manyan idanunta masukama da mejin bacci tayi, Aliyu ne ya kauda kansa gefe ganin irin kallon da yarinyar take masa dan shi baicika son kallo ba, shiyasa shi bai fiye sabga da yaran masu kudi ba dan most of them basu da kunya.

 Khaleed ne yaja hannun jawaheer dan shi bai lura da halin da ta shigaba cikin parlourn suka shiga , direct.

Aliyu ne yashigo parlourn bakinsa dauke da sallama kasakasa, Ammi da Abba ne suka amsamasa, wani irin Zillow zuciyar jawaheer tashiga yi jin wani hadedden muryan dabata taba jiba, zuciyar ta ne tashiga tunani , tabbas wanna mutumin ne da suka hadu a mota,dama ashe ba kurma bane yana magana,kenan , Amma wanchan karon yayi kamar bayama jinta saigashi taji yayi sallama, toh ya akayi yasan Yaya Khaleed, tunanin tane yakatse jin Aliyu yana gaisawa dasu Abba da Ammi,.

Ammi ce tace to saikunta so aje aci abinci tunda kacemin kuna hanya nashiga kitchen da kaina na hadamu ku   lunch, da kaina  Abba ne yayi dariya yace dama nasani badon ni akayi wannan girke girken ba ashe dan gaban goshi ne zai zo shi akayiwa, dariya Ammi tayi tace toh alhaji bagashi yanzu za'aci dakuba, Abba ne ka kalli jawaheer ya ce mama na tashi muje tunda badan mu akayi ba Amma bazamuki ciba,
Ammi ce tayi dariya jin abunda Abba yafada.


Dukan su suna zaune akan dinning table din Ammi ce tashiga saving din su, kowa cin abincin sa yakeyi Amma banda Aliyu, yagagara cin abincin sai juya spoon din yakeyi a cikin plate din, don harga Allah shi dai bai saba da irin wannan abunba , amma dake su normal ne awajen su kowa sai sabgar gaban sa yakeyi ba ajima ba ya ajiye spoon din tashi yayi, Abba ne ya kalleshi yace badai har ka koshi ba, dan murmushi yayi, Ammi ce tace aikuwa ba abunda kaci, kadauka nanma gidane, ahankali ya ce nakoshi ne Ammi alhmdullahi, Khaleed ne shima yatashi yana goge bakinsa da tissue parlourn suka koma shida Aliyu hira Khaleed yakemasa Amma yana shiru kamarma bada shi yakeba.

Abba ne ya kalli yadda jawaheer taketa juya spoon din ta acikin abincin , Mama na lafiyar ki kuwa ko dai abincin ne bemiki ba, kallon Abba tayi da idanunta dasuka cika da hawaye kamar me shirin yin kuka tace Abba na koshi bana jin yunwa,tashi tayi tanufi parlourn zama tayi a kujeran dake facing din Aliyu ido ta zuba masa, saikace wata maiyyah.

Yana danna wayarsa yaji alamar ana kallon sa, dago kansa yayi charaf suka hada idanu da ita zuciyar sune tabuga atare a hankali ya janye idanunsa, ya maida akan wayansa cigaba da dannawayar yayi, Amma haryanzu yanajin alamar idanunta na masa yawo  ajikinshi.
Ta kasan ido yadan saci kallon ta still shi din dai ta kurawa idanu, Azuciyarshi yace wannan yarinyar in maiyace takama mutum wlh bazaiyi lasting ba,,yaya Khaleed ne ya lura da yadda Hankalin jawaheer ya koma kan Aliyu, kallon ta yayi yace ke Dalla me haka kinwani sa mutum agaba da kallo saikace wata tsohuwar maiya, jawaheer ce tabata rai tashi tayi tace don kasamu nazauna awajenka, to na barmaka wajen ma, tashi tayi tanufi hanyar dakinta, Abba ne yahau yiwa Khaleed fada yace tunda bakai take kallo ba to me naka aciki,salon katakurama Mama na shiyasa tunda katafi bama kewarka, a gidannan.

Ammi dai bata ce komai ba ,dan haushi yagama isanta kan lamarin jawaheer itama ta lura da yadda tasa abokin Yaya Khaleed agaba da shegen kallo sai kace bata taba ganin mutum ba, duddah Ammi ta fahimci yana da mugun kyau Amma ai ba yau jawaheer tafara ganin farar fataba, don tasha zuwa kasashen waje da Abba yawanci tana rakashi business in buqatar hakan tataso, Amma gashi daga fadar gaskiya ya hau Khaleed da masifa, ita tarasa wani irin so Abba yakeyiwa jawaheer da yasa baya taba ganin laifinta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol