Free chapter · Read without an account

Chapter 29

by @Mrs Alkali · Zaɓi na



✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~


Page 2️⃣9️⃣

Zara'u ce take tsugune agaban murhu hannun ta ne rike dawani dan plate na roba ,sai fifita wutan takeyi ,amma yaki kamawa, saima wani uban hayaki dayakeyi, kasancewar ita cen danyu ne gashi garin da sanyi, tun da hantsi ta daura abincin amma haryanzu fama takeyi da itacen.

Idanunta ne suka kada sukayi jazur ga wani irin zogi da radadi dasuke mata, tana durkushe agaban murhun ne hajiya Mama ta shigo, direct bata tsaya ko ina ba sai cikin kitchen din, dan taji motsin zara'un achan da alamar tana chan din.

Hajiya Mama ce tace mezangani haka zara'u haryanzu abincin bai karasuba, abu tun karfe 10:am nasafe ace haryanzu karfe 2:00pm na rana baki gamaba wannan wani irin girki ne sai kace maidafa naman giwa haba, jama'a in ba dai kashemu kike so kiyi da yunwaba ai yakamata ace angama wannan girkin.

Hawayen da zara'u take riqewa ne suka zubomata kallon hajiya Mama tayi,tace mama itacen ne danyu basa ci tundazu nake fifita wutan Amma yaki yakama.

Hajiya Mama ce tace a'a zara'u karkiwani fake da itace kice dai kinyi niyan kashemu da yunwa ne kawai ki ce dai shegantakar taki ce ta motsa, inbanda shegantaka irin taku ta yaran zamani nawa dan wannan girkin yake , Allah natuba ,Amma batun kice ita ce basa ci ai bai ta soba, ma toh nima dakike gani tunkafin kizo gidannan da irin su nake amfani, kuma sumul garau nake girkina da su, dama yaran zamani haka kuke da dan banzan gandan tsiya ga shegen nawa awajen aiki, gashi ko girkin naku inkunyi ba ciyuwa yakeyiba sai kubi kuyi abu baigama nunaba, "amma kun iya saka miji a daki kuhana shi fita neman halal"

Mansoor ne yayi sallama shigowa yayi hannunsa dauke da bakar leda hajiya Mama ce tace har andawo yace Allah yayi Mama, "hajiya Mama ce tace to sannu da dawowa amsamata yayi idanunsa nakan zara'u dake tsugune riqe da plate din roban da take ta fifita wutan,amma haryanzu baikamaba sai hayaki da yakeyi ,Mansoor ne yace "kardai haryanzu ba agama abinci ba, zara'u ce tadago jajayen idanunta wanda duk hayaki yagama kumbura su, ga shegen zogi da sukemata,,

"Kallon Mansoor tayi tace eyyi ba a gamaba kasan itacen danyu ne basugama bushewa ba shiyasa tun da kafita fama nakeyi "

"Mansoor ne yace mata sannu da kokari"

"Yakamata in anbiyani salary na wannan watan sai inmiki refiling na gas,,

"Hajiya Mama ce tayi charaf tace kaiya wani kokari tayi, Yarinya sai shegen son jikin tsiya, Ace tun karfe 10am nasafe tadaura sanwa Amma haryanzu karfe 2 00pm Bata gamaba, shine kaikuma harda wani cemata sannu saikace wacce tayi abun arziki, dama kai kake daure mata gindi agidannan shiyasa bata ganin girmana,, kuma harda wani refiling na gas zakayi mata , "toh a hirr dinka wlh karka kuskura, girkin itace ma ya muka kare dashi intayi ba nuna yakeyi ba , bare kuma wani gas Allah natuba.

"Mansoor ne ya sunkuyar da kan sa kasa, "yace ayi hakuri hajiya Mama "insha Allahu za'ayi yanda kikace.

Hajiya Mama ce ta tabe baki tace uhhmm inbanyi hakuri ba ya zanyi salon akashe mutum da yunwa ne gawani barnan kudi da akabijiro dashi wai shi refiling to nidai nace badani za'ayi wannan almubazzarancin ba ahto"

"Zara'u ce ta taso daga tsugunon datayi agaban murhun inda Mansoor ya ke tsaye ta nufa,,

" Bakar ledan dayake hannunsa tasa hannu takarba,, hajiya Mama ce tayi charaf tace me muka samu ne, a cikin ledan.

  "Kawo ledan mugani, zara'u ce ta bude ledan.

"Hajiya Mama ce tace ohh ni Yar nan wato bankai kimikomin ledan ba Kenan dole sai kin leka ciki,,kin rigani ganin me a ciki kenan  ah lallaekam koda yake ba laifinki bane laifin wanda ya sakarmiki ledan ne.

" In banda dan yau ace ga uwar ka a tsaye Amma ka dau leda ka mikawa matar ka agaban idon uwa, kai gaka suda uwar soyayyah koh , toh wlh kabi a hankali.

"Manzon Allah (SAW) sanda yace kabi uwa, kabi uwa, kabi uwa, har sau uku " kafin ya ambaci abi uba.

Amma shine ka murje idanunka agaban idona ka zabi matar ka, wlh kayi hankali da duniya .

" Yoh Allah natuba lahiranka nake jaramaka, in bandama dan yau wani amfani zara'u takemaka wanda ni ban makashiba, nifa na haifeka acikanah, nasha kashin ka da fitsarin ka ga ka da shegen kukan dare, haka nayi ta fama da kai na jure, haba Mansoor, shine yanzu agaban idona ka zabi matar ka.


"Niko nace anya kuwa hajiya Mama takuwa san amfanin zara'u awajen Mansoor,😂 zamu fadamata ne ko mubari tafahimta da kanta..?

"Mansoor ne yasa hannu ya karba ledan daga hannun zara'u jin irin sababin da hajiya Mama takeyi harda jawomasa "hadisi"

Karban ledan hajiya Mama tayi , budewa tayi "pants ne da bra aciki ,
"Hajiya Mama ce tahau salati me zangani haka Mansoor, ace lalacewar taka takai zara'u ta aikeka sayan kayan ciki na mata.

"Kai kuma ba kunya ba tsoron Allah kaje kasayo, ohh yaran zamani kenan ina zakuje da wannan dabi'an, ta ku ta rasar kunya.

"Mansoor ne ya ce dama tacemin tana da bukatan su ne nata sunfara lalacewa, shiyasa danabi ta shagon abokina nasayamata, su.

"Hajiya Mama ce tace zancen banzan kenan duk dai hanyan lalacine wannan,,

Hajiya Mama ce tafito da pants da bra din, rabawa biyu tayi, mikawa zara'u rabin tayi,, 

"Zara'u ce tadaga ido ta kalli Mama alamar bangane me kike nufiba,,

"Hajiya Mama ce tace ungo mana ko bazaki karba bane in hada duka, nima ina da bukatarsu kinga saikiyi amfani da rabin nima nadau sauran rabin kinga kowa ya amfana,, ai.

"Zara'u ce tafashe da kukan da tajima tana tarewa, bubbuga kafanta tahauyi akasa ,, Mama ce tasake baki tana kallon ta, tace haba sai yanzu nagane ashe Mansoor"goyon kaka ka auro shiyasa take sake kamar sakainar kashi to wlh ka gayamata nan ba gidan iyayen ta bane, in zata shiga ruwan hankalin ta gara ta shiga, atoh gidan miji ba gidan iyaye bane.

Intasaba musu shegantaka achan to nan bahakabane dan aure ba wasabane,,

Zara'u ce ta ruga da gudu ta nufi daki tana kuka, hajiya Mama ce ta wurgawa Mansoor pants da bra din data raba tace gashi saika karasa ladanka tunda karikosu daga kasuwa bakaji kunyaba ai saika karasamata da su daki ba laifi bane kaga ladanka ya cika cif ciff,

"Jiki a salube Mansoor ya karba pants da bra din yanufi kofar parlourn su,,

"Hajiya Mama ce ta juya tana ta mita ta nufi bangarenta, tana rike da ledan pants da bra din da ta raba musu ita da zara'u.


TOH JAMA'A HAUSAWA SUNCE  LAIFIN DADI KAREWA....!!!

SHIN ME YASAMU JAWAHEER ME MUSABBABIN CUTAR TA......? 

SHIN ALIYU YA GANE JAWAHEER KUWA....?

SHIN JAWAHEER TANA AUREN ZABIN TA KUWA......?

SHIN JAWAHEER ZATA BAIYANA WA ALIYU SHINE ZABIN TA ,......?

SHIN ALIYU ZAI AMINCE DA SOYAYYAHR JAWAHEER KUWA.....??

WACCE IRIN ZAZZAFAR SOYAYYAH KUKE GANIN ZA A BUGA A TSAKANIN ALIYU DA JAWAHEER...?

YA ZAMAN ZARA'U ZAI KANSA CE, DA HAJIYA MAMA  SHIN ZA A SAMU SAUYI KUWA...?

SHIN ZARA'U ZATA SAMU MAFITA ACKIN RAYUWAR AUREN TA DA MANSOOR KUWA.....??

SHIN MANSOOR YANA RIKE AMANAR ZARA'U KUWA..?


SHIN ZARA'U TANA NADAMAR AUREN ZABIN TA KUWA....?

SHIN KUNTUNA DA ALWASHIN DA JAMILA TAYI NA  AUREN ALIYU KUWA...?

SHIN ME NE A SALIN MAHAIFIYAR ALIYU...?


SHIN ABBA ZAI IYA YIN KOMAI AKAN FARIN CIKIN JAWAHEER KAMARYADDA YACE KUWA,, IDAN NACE KOMAI TOH PHA INA NUFIN KOMAI CIKI HARDA NEMAWA JAWAHEER AUREN ALIYU KODA KUWA HAKAN YA NA NUFIN RASA KOMAI NASA CIKI HARDA AL ADUNMU NA HAUSA/FULANI.......!!! WASA FARIN GIRKI, INA MAI TABBATAR MUKU DA CEWA GABAN YAFI BAYAN DADI,,,,,I PROMISE YOU GUYS 🥰


KUBIYONI DOMIN SAMUN AMSOSHINKU DA DAMA ACIKIN WANNA GAGARUMIN LITTAFIN NAWA MAI DAUKE DA ILIMANTARWA ,NISHADANTARWA ,DARRUSAN RAYUWA KAI HARMA DA DANASANI , HADE DA ZAZZAFAR SOYAYYAH, DAMA SAURAN ABUBUWAN DA BAN LISSAFO SU BA, DUK ZAKU SAMESU ACIKIN WANNA GAGARUMIN LITTAFIN ✨ZABI NA ✨ 🥰 


KARKUBARI ABAKU LABARI...NAMUKU ALKAWARII BAZA KUYI DANASANIN BIYA BA......!!!
KARNACIKA KU DA SURUTU SAI NAJIKU.
MASOYANA  A NUNAMIN KAUNA WAJEN SAYAN LITTAFINA.🥰.   ,,,,ONE LUV,,,,

SEE YOU GUYS 🖐️🥰

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol