Free chapter · Read without an account
Kamar da wasa pg 10
by Fatima Isah · KAMAR DA WASA
KAMAR DA WASA💘
Fatima Isa
(Mrs Umar)
Page 10
Kt garin ɗan marna
Cikin tsananin hayaniya da ihun yara. Cikin hanzari oga Umar ya iso wajen tamkar zai tashi sama
“La’ilaha illallah! Wannan wane irin abin kunya ne haka?!”
Oga Umar ne ya shigo da gudu cikin kayan soja, fuskarsa a murtuke, idanunsa cike da hushi, hannunsa rike da hularsa kamar wanda aka taso.
Ganin su Jannat da Joy suna buga juna a ƙasa, kayan jiki na ɓarkewa, yara na ihun
"Faɗa faɗa!"
Sai ya watsar da hularsa a ƙasa, ya nufe su da karfin da ba’a saba gani daga wurinshi ba.
“Ku Tsaya! Ku daina wannan iskancin haka!!”
Yara suka tsaya cak, wasu matan da suka fito raba faɗa suka ja baya.
Oga Umar ya finciko Jannat da hannu ɗaya, Joy da ɗaya. Ido cikin ido. Babu wani wasa a fuskar sa.
“Na ganku da idona! Ku duka, wannan wane irin abin kunya ne a ace block ɗin mu ya koma kamar gidan dambe. What nonsense is this?”
Jannat ta lumshe ido tana shakar numfashi. Duk da halinta, bata iya yi masa gardama ba. Joy kuwa ta riƙe ƙirjinta tana haki kamar za ta faɗi.
“Ku duba yadda kuka tarwatse layi gaban yara da mata! Wannan fa bariki ne, layi ne na mutane masu mutunci! Duk da sabanin ku, ba wannan ne mafita ba.”
Ya ɗan dakata, yana kallon kayan da suka yage a ƙasa.
“Kuna so a fara ɗaukan bidiyonku a saka ku a internet? To wallahi daga yau idan wani abu makamancin haka ya sake faruwa, sai kun bar wannan layi. Ku na ji na?”
Sai ya juya yana nunawa yaran da ke tsaye suna kallo.
“Ku koma gida! Wannan ba abin kallo bane!”
Sannan ya ce da Maman Jamila
“ku kuma a matayin ku na manya ko kunya bakuji ba kun kasa raba su kunzo kuna kallo"
"Wallahi oga kai ma kasan halin su su duka biyun wanene ba gwani ba munyi shiru ne kawai dan mu tsira da mutuncin mu"
Tsaki kawai yaja ba tare da ya yi magana ba ya juya yana tafiya.
Jannat ta kama Amina suka wuce. Joy ta janye jikinta tana shashshafa fuska. Layin ya fara watsewa.
Abinda ya bawa Jannat mamaki shine tana shiga taga Ummie zaune fuskarta ɗaure cike da takaici duk tunaninta bata block ɗin.
"Sannunki yar gidan masu dambe ni kam wai Jannat anya kanki ɗaya? I'm tired bakin cikinki bazai kashe ni ba Aisha dole babanku yazo gara mu mayar dake kauye kawai idan har kin samu miji a can kiyi aure ko haka zai saka kiyi hankali"
Cikin hanzari Amina ta ce.
"Wallahi Ummie babu ruwan aunty Jannat sun.."
"Rufe min baki duk ba shegiyar garin bace ke da ita ai duk kwaryar sama ce data ƙasa wallahi ni na haife ku amma na gaji da halinku"
Baki Jannat ta turo tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalinki Ummie form ma na siya na aikin soja nan da wata ɗaya na bar maki gidan"
Ummie ta dafe kirji kamar wadda zuciyarta zata faɗi.
“Jannat... aikin soja fa kika ce? A ina zaki fara da wannan halin?”
Jannat ta zauna akan sofa, ta zaro takarda daga jikanta, ta miƙa mata.
“Gashi nan sunayen yaran barrack ne da suka sayi form. Nayi wa Baba magana tun kafin ku dawo daga Zaria. Wallahi Ummie, rayuwar nan ta isheni. In babu mutunci, in babu ƙima, to me nake jira? A aikin soja zan samu daraja, ba a nan ba.”
Ummie ta karɓi takardar da hannunta da rawar jiki. Ta dube ta sama da ƙasa, sannan ta ce.
“Yanzu haka zaki bar gidan nan? Ko saboda ban goya miki baya ba? Jannat ki tsaya ki yi tunani. Wannan duniya ba ta tafiya da zuciya irin taki.”
Kai kawai Jannat ta murmusa.
“Ummie, zuciyata ce, amma burina yana nan na zama mutum mai tsayawa akan gaskiya. Idan aikin soja ne zai koya min nutsuwa, to Allah yasa in ci riba.”
Ummie ta ajiye takardar gefe tana girgiza kai, ba tare da wani ƙarin zance ba. Amina ta zauna kusa da Jannat, tana ɗora kanta kan kafadarta.
“Ina jin tsoro, Aunty idan kika tafi fa?”
Jannat ta shafa kanta. “Kada ki damu. Zan dawo da girman da kowa sai ya girgiza. Kuma idan har na tafi Depot...”
Ta yi shiru, ta ɗan kalli sama. Fuskar ta cike da hasken buri.
Numfashi ta sauke tare da jinjina kanta ta juyo ta kalli Ummie amma me zata gani sai taga tana hawaye da cikin tashin hankali Jannat ta isa wajanta duk rashin jina ina tsoro naga iyayena ɗin nan guda biyu cikin tashin hankali.
"Ummie meya faru kike kuka ba dai nice na saka ki ba"
Sai data ɗan lumshe ido ta girgiza kai kafin ta ce.
"Dole na kuka Jannat ni na haife ki nafi kowa sanin halinki a nan fama nake dake ina ga kin shiga aikin soja babu uwa babu uba babu mai kwaɓa babu mai kyara a lokacin kike da freedom ɗin kanki, sam ni dai ban amince da wannan aikin ba"
Ta ja numfashi, sannan ta ƙara da cewa.
“A lokacin kike da cikakken ‘yanci, ke kadai. Sam ni dai ban amince ba. Ba domin bana so domin ina jin tsoro, tsoron duniya da rashin tabbas.”
Shiru ya ratsa falon. Jannat ta kama hannunta, ta matse shi a hankali.
“Ummie! zan dawo ki ga abinda Jannat zata zama. Sai na zama abin alfaharin ki.”
Ummie ta kalli diyar tata cikin ido, hawaye na cigaba da gangarowa. A karon farko cikin dogon lokaci, ta ce:
“Allah ya tsare ki, Jannat. Kaico duniya, Allah ya nuna min rana da zanyi alfahari da ke.”
Jannat ta langwaɓar da kai. Amina ta share hawayenta da bayan hannunta, sannan ta ce cikin ƙananan murya
“Toh yanzu Aunty za ta zama soja kenan Jannat the brave soldier.”
Kowa ya yi shiru zuciyoyi cike da damuwa, amma cike da fata.
Bayan sati biyu
Abubuwa da yawa sun faru a wannan lokaci masu daɗi da marasa daɗi abin da dayafi min daɗi shine sabon mashin da papa ya siya min daya zo daga wajan duty sannan yace duk inda zani in tafi dashi ba tare da shamaki ba.
Sai dai kash abu ɗaya ke damuna a wannan kwanakin shine gulma da ta sake buɗewa a kan mu wadda har muka rasa dalilinta ko a islamiyya idan Ummie taje da zarar mata na magana da ta iso zasuyi shiru su dinga binta da kallo. Haka muma tun abin baya damun Ummie har ya kai ta fito fili ta fara mani magana a kan lamarin.
"Jannat ni kam wani lamari ke damuna da bana waya da babanku sai na ɗauka ko an kashe shi a wajan duty mata ke ɓoye min to amma muna waya dashi lamarin ya fara bani mamaki ko ke baki fahimci komi ba?"
Ajiyar zuciya na sauke tare da aje wayata da nake dannawa na ce.
"Ummie ni kaina naso maki wannan magana to ina tsoro kice kawai rashin hakuri ne irin nawa. Amma tabbas idan kikaga matan barrack na gungu gungu da sun ganka suyi shiru tabbas akwai dalili amma ko ma meye zamuji amma Ummie bakya tunanin."
Sai kuma ta yi shiru tana nazari
#Son zuciya
#Soyayya
#Yaudara
#Makirci