Free chapter · Read without an account

Page-6

by Aisha G Umar · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*

(*F.W.A)*©✍️

⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍

___________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.

❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁

Free book📓

By

*Aisha G Umar*

_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Page6️⃣

Daidai lokacin Inna ta fito daga cikin ɗaki idonta kaina, tana aika min wani irin kallo, sannan ta fara takowa gabana, zuciyata ne ya tsinke ko da ganin tana tahowa inda na ke, na kuma damƙe jakar Abba da ke hannuna.

"Keh me ki ke wani ƙura min ido kamar za ki cinye ni? Dalla ban wuri ina wuce! Kin yi wani kanannaɗe hanya mtsww" cewar Inna ta ƙarashe da tsaki, sannan ta matsar da ni gefe da ƙarfi ta wuce. Ban san lokacin da na sauke wata ajiyar zuciya ba, saboda ni da fari ɗauka na yi wani abun za ta min.

Nufar ɗakinmu da na yi niyya tun farko na yi, na je na buɗe 'yar bakkon kayana na sanya jakar a ciki.

BAYAN NA YI SALLAR ISHA'I.

Ina zaune akan darduma ko tashi daga kai ban yi ba. Halima ce ta shigo ɗakin ba tare da ta yi sallama ba, inda na ke ta fara kallo tana jin ƙiyayyata na sake shigewa cikin ranta, takowa ta yi zuwa inda na ke tare da, ɗaura ƙafarta akan ƙafata da ke tanƙwashe ta baya, dama ban canza daga zamar sallahn da na yi ba. Ina jin zafi saboda da ƙarfi ta ke takani, amma da ya ke na san akwai ƙudurin da ke zuciyarta na aikata mun haka, shiyasa na daure ban yi magana ba, sai dai na janye ƙafata haɗi da tankwashewa.

Ganin hakan ne ya sa ta saki murmushin da ta ke yi min idan har tana son yi min sharri, sai kuma ta mayar da ƙafar na ta gurin dukana ta baya, tana haɗawa da tokarina. Nan ma bance da ita komai ba sai haɗiye hawayena na ke yi, samu damar miƙewa na yi don in bar mata wurin, in fice daga ɗakin ma gaba ɗaya, inyaso sai ta yi barci sai indawo inkwanta.

Kafun na matsa daga inda take na ji ta turani da ƙarfi na faɗi ƙasa, kallonta na yi tare da share hawayena, na fara ƙoƙarin tashi ina gyara hijab ɗina. Ganin ban tanka mata ba yasa ta ce, "amma ke Nuriyya an yi mara zuciya wallahi! An dai ji kunya, mai baƙar zuciya irin na iyayenta kawai, iyayenki mutanen banza ne!".

A hasale na ƙarasa miƙewa ban san lokacin da na sauke mata mari a kumatu ba, sai da na maretan sannan na lura da abun da na yi, ta ke na zare ido ina kallonta. Ita kuwa Halima da hannayenta duka biyu ke kan kuncinta ta ɗago ido tana kallona, bakina na ke son buɗewa don na ba ta haƙuri, amma na kasa cewa komai. Halima da dama kamar jira take sai kawai ta sa ihu, ta yi ƙasa har da birgima tana kuka.

Kallonta na ke a tsorace domin na san cewa na yi babban ɓaran-ɓarama, na ja wa kaina ruwa ko kuma ince kogi ma gaba ɗaya, domin kuwa tabbas na san yau dai ni kam sai ta Allah, take jikina ya fara ɓarin tsoro, zuciyata ta hau bugu da sauri.

Inna Jummai kuwa kukan masoyiyar 'yarta da ta ji ne, yasa ba shiri ta salleme sallar da ta ke, wanda daman dungura goshi kawai ta ke yinsa, bayan ta fito daga ɗakin wani irin sauri ta sa, kan ta ƙaraso ɗakinmu ta zabga tuntuɓe ya fi a irga. Tana shiga ɗakinmu ta nufi Halima cikin tashin hankali.

"Me ya same ki? Me akai miki Halima ki ke wannan kukan? Faɗa min!" Inna ta faɗi tare da sanya hannu tana ɗagata sai kuma ta juyo tana min kallon tuhuma. Ni dai dama babu abin da na ke sai zazzare idanu jiki na ta karkarwa, Halima kuwa da ya ke dama tana daga cikin irin munafukan yaran na, haka ta zage cikin muryar kuka ta fara faɗin, "Inna ce miki ta yi mayya, don na ce me yasa za ta ce miki haka shine ta rufe ni da duka, ta haɗa da cewa ke azzaluma ce kuma muguwa, wai da za ta samu dama sai ta koremu daga gidan nan, ai ba namu ba ne".

Zuciyata ce ta cigaba da tsalle, saboda kalamai masu muni da Halima ta ce wai ni na faɗesu, da sauri baki na rawa na ce, "Inna wallahi ban..." Ai Inna Jummai ba ta bari na ƙarisa ba ta katseni cikin ɗagun murya, "ke Nuriyyah! har kin isa ki zageni haɗi da muggan kalamai haka, sannan kuma ki dukan min 'ya? Da me ki ka fi ta da har zaki dake ta? Wato kin samu wuri ko?" Ja baya na fara yi ina girgiza mata kai hawaye na zubar min, "Inna dan Allah kar ki dake ni, wallahi na rantse da Allah ƙarya Halima ta ke yi, ni ban ce miki abin da ta ce ba Inna" na yi maganar ina ta sharɓar hawaye, domin kuwa tuni na tausayawa kaina.

Nan na ji wata maganar da Inna ta ƙullo daga bakinta tana hurgo min, wanda na gwammace da dukan nawa ta hau yi har sai na suma, "ba duka ba zagi ai Nuriyyah! Ba ubanki ne madafanki ba? To don shi na ke raga miki dama yanzu kuma ba shi, don haka kafin ki fitar da mu daga gidan nan ni zan fitar da ke, yau ɗin nan za ki bar gidan nan Nuriyyah! bari na har abada!". Tana faɗi ta kama hannuna tana ja na zuwa waje. Tashin hankalin da na shiga sai da yasa na ji kamar jiri na neman ɗaukata.

A haka ina kuka ina roƙonta, amma ina kamar wacce ta haɗiyi maganin rashin imani, ba ta ko saurarena, ƙofar gida Inna ta nufa da ni, hakan ya tabbatar min koran na wa za ta yi kamar yadda ta ce. Buɗe ƙofar ta yi haɗi da hankaɗa ni da ƙarfi zuwa waje, sai da hannuna ya gurje a ƙasan yayin faɗuwa, "Inna dan allah dan Allah Inna, ki yi haƙuri ki yafe min, ki tausaya min wallahi ba zan sake ba, Inna ki yi min dukan tsiya, ki dake ni ko da me, da duk abun da ki ke so Inna, amma don allah kar ki koreni daga gida, kar ki ce inbar gidan nan, ni ƙarama ce Inna yanzu idan na bar gidan nan ina zan je? Dare ya yi Inna". Ina kaiwa ƙarshen maganar na kuma fasa kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Kallona take yi cikin halin ko oho, domin kuwa magiyan da na ne yi mata ko a jikinta, sai kallon mara galihu da take jefo min, a ƙufule ta fara cewa, "munafuka! Ga ki sai iya shararo zance, in kika fara zayyano magana kamar wacche aka jona a wuta, to koma gurin ubanwa ki ke so ki je, wannan ba damuwata ba ne, in kinso ki je gurin dangin munafukar uwarki, ko kuwa ki je na ubanki, ke koma iyayen na ki zakj bi ki mutu, wannan ke ta shafa ba ni ba Nuriyyah!".

Ina cigaba da giɗa mata kai akan kada ta aikata min haka, Halima ce ta zo riƙe da bakkon kayana a hannunta, tana cewa, "yauwa Innata, ga tsumma-karan kayantan nan". Inna ta amsa sannan ta hurgosu kaina, Halima dariya ciki-ciki ta hau yi tana kallona, Innata ƙara cewa, "kuma wallahi tallahi idan na ji hannunki a ƙofar nan kina bugawa, ko kuwa na dawo na same ki jikin ƙofar nan, to wallahi na lahira sai ya fi ki jin daɗi Nuriyyah, sai kin gwammace kiɗa da karatu!" Tana idawa suka shige tare da banko ƙofar.

Sai da na rintse ido domin ji na yi kamar har da zuciyata su ka rufe, ɗage kaina na yi sama tare da buɗe idon, ina kallon sararin samaniya da hadari ya haɗu sai faman walƙiya ya ke.

Last page

___________________________________________________

Toh fah, Inna ta koran mana marainiya Nuriyyah, shin ya zata yi? Ina zata nufa?.

Mu kasance a next page don jin me zai faru gaba?

_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.