Free chapter · Read without an account
PAGE 60
by Aminatu Ibrahim · GANIN IDO
GANIN IDO 🥀🥀
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671
FREE-BOOK
PAGE 60
"BIBI...BIVILOVE...BIBINA..."
A hankali na motsa daga position É—inda nake akan gadon, sannan na shiga buÉ—e idanuwana slowly ina mai jin yanda Kai na yake wani irin sara min da amsar kuwwar Kalmomin da mutum É—aya ne kawai yake da dama da ikon sarrafasu a kaina a duk lokacin da yaso. Kalma ce wacce nake fata da burin sake jinta ko da sau É—aya ne a cikin rayuwa ta.
Sai dai kuma, Ammie na gani tsaye a gefena ita da Aunty Labiba suna mini wani kallon mai ɗauke da tsananin tausayi. Kallon da ya sarar mini da gwiwata ya kuma ƙara tabbatar mini da cewa na makara, domin dai ta tabbata cewa har yanzu dai ma mafarki nake ba, Dayaa na ya tafi ya barni har abada.
Duk da haka, Kalmomin da na ji su a kaina ne na shiga maimaitawa tare da yunƙurawa na hau dube-dube ina faɗin.
"Daaya na amsa maka...kana ina?"
Sai kuma na kalli Ammie na ce.
"Wallhy ina ji yanda yake kirana ko ku ba kuji ba ne?"
Kuka ne ya ƙwacewa Aunty Labiba wanda har yasa ta juya ta fice daga ɗakin ba shiri, domin ji take zuciyarta ba za ta iya ɗauka ba. Mutuwa mai yankan ƙauna. Kalli yanda kowa ya rasa nutsuwarsa dan Allah,ƙannensa, 'ƴa'ƴansa, iyayensa kowa ya ɗimauce.
Ammie kuwa, itama share hawayen ta ta yi tare da samun wuri a gefen gadon ta zauna ta kamo hannuna a hankali ta ce.
"Kin san me Beenafah? Rayuwa gaskiya ce, soyayya gaskiya ce, samun 'ƴa' ƴa samun farin ciki gaskiya ne,riskar yanayin baƙin ciki ma a cikin rayuwa gaskiya ne, dangi da abokai gaskiya ne, komai na duniya da kika yarda da gaske yana existing kamar yanda Ubangiji ya tsara mana....to itama MUTUWA gaskiya ce. Allah fa ya yi alƙwari da kansa kuma ya tabbatar da cewa, Wallahy dukkan wata rayuwa lallai mai ɗanɗanar mutuwa ce. Kafin mijin ki ya mutu...sai da Mahaifinki ya mutu, sai da Yayan mahaifinki ya mutu, sai da ƙaninki ya mutu, sai da kakarki da kanki suka mutu, sannan Mijin ki ya mutu, muma a haka watarana duk zamu mutu ɗin, sai dai mutuwa ba ta bada notice, duk lokacin da Allah yace ka bar duniyar...wallahy za ka barta ko ka shirya ko baka shirya ba. Za ki mutu, zan mutu, kowa ma zai mutu Beenafah, domin wannan duniyar ba ma tabbata ba ce, lahira ita ce gida na gaskiya wanda kowa a can zai tafi kamar yanda mijin ki ya tafi. Ki buɗe zuciyarki ki amshi gaskiya Beenafah,Ki yarda wanda ya mutu baya dawowa, abin da ya kamata ki yi haƙuri, ki ɗabbaka haƙuri mai kyau, in sha Allahu za ki zama mai nasara a rayuwa.... "
Wani irin kuka nake yi wanda matuƙar Kanada zuciya a ƙirjinka...to tabbas sai ka zubar da naka hawayen.
Kuka nake ina girgiza kai na na ce.
" Ammie ashe da ciwo haka? Da ciwo sosai Ammie...Na kasa yarda cewa wai da gaske ya mutu! Ammie ina zan saka raina? Ya tabbatar min da cewa lafiyansa ƙalau, tafiya muka shirya a ranar zuwa ƙasar Lebanon..Ammie ya saka burin aurar da su Aryaan..."
"Dukkan wani ɗan Adam da buri a rayuwarsa yake mutuwa Beenafah. A da ya kasance a duniyarsa shi kaɗai wanda ya cire rai da tsammanin cewa zai yi aure a rayuwar nan, a lokacin kuma yana da buri da addu'ar ko auren ne dai ya samu ya yi ko shi kaɗai ya yi Allah ya cika masa burinsa. kwatsam sai Allah ya haɗa ku kuka yi aure, sai kuma ya fara buri da fatan samun haihuwa wacce yake ji ai da ya samu haihuwar burinsa ya gama cika a duniya. Ya samu yaran, ya yi farin ciki, ya yi dariya ya yi kuka a tare da su, ya taka matsayi da rawar da duk wani nagartaccen uba yake taka wa. Bayan nan kuma, sai ya sake ɗora sabon burin Aurar da 'ƴa'ƴan nasa, amma sai rai ya yi halin sa...to ina tabbatar miki, wallahy tallahy da za'a sake dawowa da shi duniyar domin ya aurar da yaran, ko da ya cika wannan burin sai ya sake ɗora wani na son ganin 'ya'ƴan 'ƴa' ƴansa ma'ana jikokinsa da kuma sake burin aurar da Zarah da take ƙarama a cikinsu. Zai iya burin sake maimaita wasu shekaru hamsin ko fiye da haka tare da ke da kuma iyalinku. Kowa a haka yake tafiya Beenafah! To kinga ko a haka sai a godewa Allah. Wani ana haihuwarsa yake mutuwa, wani ana ɗaura masa aure amaryar ba ta kai ga tarewa ba zai faɗi ya mutu, wani kuma har ya mutu 'ƴa'ƴa ne ba zai samu ba. Saboda haka ki yi haƙuri, ki ci gaba da yi masa addu'a domin ita ce abun da yafi buƙata a halin yanxu. Hammodi ya rasu ba wai mafarki bane ko gizau abun yake miki, mutuwa gaskiya ce kuma hakan ce ta faru da shi. Ki yi haƙuri ki ƙwarara kanki ko don yaran ku. Idan kin zamto haka su da suke cikin giya da mayen mutuwar su ma ɗin ya kike so su yi?"
Kwantawa na yi a jikinta ina ta rusa kuka tare da jin yanda kalaman ta ke tasiri a cikin ruhi da gangar jikina.
" Ki yi hak'uri! Kowa haka ya ji, mutuwa ba ta daɗi, ita ce mafi girman ƙaddara a cikin rayuwar ɗan adam wanda take ɗauke shi a duk lokacin da Allah yaso, ko da ciwo ko babu ciwo. Mijin ki mutumin kirki ne Beenafah, ya samu yabo sosai. Ki godewa Allah ki ƙara godewa Allah. Ki yi haƙuri. Ki ƙarfafa kanki ko don ni mahaifiyarka da yaran ki. Shi kansa zai fi samun nutsuwar kwanciya idan kika daina koke-koken nan kika duƙufa yi masa addu'a dake da yaran ku.. "
Kalmomin sa ne suka shiga dawo min daki-daki a lokacin da mukayi 15 anniversary wanda muka yi a É—akin Ka'aba mai tsarki. Shi ne wanda ya kawo tsarin kuma muka tafi baki É—ayanmu muka yi ibada tare da yin addu'o'i...wallahy ji nake tamkar yanzu ne yake furta waÉ—annan zantukan a gare ni cewa.
" Bibi...ko a haka na mutu Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Na samu mata ta gari, na samu 'Æ´a'Æ´a na gari, na samu dangi masu so na waÉ—anda suka tsaya dani a kowane irin yanayi. Rayuwa ta yi mini komai..."
Jinjina kaina na yi ina share hawayena tare da kawar da tunanin ina mai jin wani irin É—aci na ce.
" Allah ya gafarta maka yasa ka a Aljanna maɗaukakiya, Allah ya bamu haƙuri da juriyar rashin ka, Allah ya shiryar maka da zuriyarka ya sa su zamto masu jinƙai da addu'a a gareka. Na yi alƙawari ba zan ƙara kuka ba, amma ka sani zuciyata za ta mutu da kewarka da kuma ci gaba da begenka har zuwa numfashina na ƙarshe..."
Hannunta ta kai a hankali tana bubbuga bayana tare da ƙara bani kalaman lallami da kwantar da hankali.
Da haka ta samu ta lallaɓani na ɗan ci abinci na yi sallah sannan muka fito inda na tarar Zarah tana kwance jikin Sis Nourah wai jikinta ya yi zafi tana jin zazzaɓi.
Wuri na samu na zauna ina mai saukar da kaina a ƙasa tare da share hawayena ganin yanda Hairiyyah ta yi wani iri duk ta zabge ta fi ce hayyacinta.
Mutane ne ta kowane ɓangare suke zuwa mana gaisuwa wadanda mafi yawa da cikinsu ni ban ma san su ba.
Shi ma Aliyu yana nan maƙale dani a duk inda nake, Su Aryaan ne ke can waje inda iyayen na su maza suke har aka kambala zaman makokin a hankali kowa ya shiga watsewa.
********
Bayan watanni shi da sun shuÉ—e, haka na ci gaba da ganin mutuwar mijina wasa. Ji nake kamar zai dawo, ji nake kamar komai wasa ne, amma kuma idan har ina son gaskiya...to fa ya tafi har abada ba zai dawo ba. Na yarda duniya ba ta tabbas, babu abin da yake É—orewa da ci gaba da wanzuwa sai Allah maÉ—aukakin sarki, shi ne wanda bai haifa ba kuma ba'a haife sa ba. Da yardarsa da amincewarsa komai na duniya yake tafiya.
Shekaru ashirin sai suka zamo mini tamkar kwana ashirin bayan na tabbatar na rasa shi har abada. Na amince da shi ba tare da na taɓa ganin fuskar sa ba. Na so shi so mai tsanani a lokacin da zuciya da ruhi suka amince da shi a matsayin masoyi wanda ya cancanta kamar yanda shi ma ya ɗauke ni. Mun gina rayuwa mai inganci da tarin albarkoki da alkairai waɗanda ba zan taɓa mantawa da su ba.
KuÉ—i ko mulki ko sarauta ko talauci babu wanda zai hana maka mutuwa idan lokacin ka ya yi. Da ciwo da babu ciwo idan lokacin ka ya yi sai ka tafi. Da ace lafiya ko kuÉ—i ne ko wani jindadi zai hana mutuwa, tabbas da Dayaa na bai mutu ba. Domin yana yawan zuwa check up kuma baya yawan rashin lafiya domin sai ya shekara bai yi ciwon kai ba. Amma da yake mutuwa duk bata duba wannan. Sai gashi ta É—auke shi ta barni da kewa.
Tun last week Ammie ta zo akan cewa tana so ta ji mi na yanke dangane da rayuwa. Ni dai ban ce mata komai ba, domin akwai abubuwan da nake hangowa da haskowa a cikin rayuwar 'Æ´a' Æ´ana.
Yau ma tunda na wayi gari ina kwance a É—akin sa na kasa tashi ma ko wanka na yi. Ko breakfast ban yi ba.
Hakan yasa Abdallah ya ƙara shigowa ɗakin ya same ni bayan ya nemi izinina ya zauna yana faɗin.
"Grandma ta shigo tana parlourn ki Maami. Yau har yanzu ko breakfast ba ki yi ba. Dan Allah ki daure ki tashi..."
Kallonsa na yi sai kuma na duba agogo ina faÉ—in.
"Miyasa ka ke gida har yanzu baka fita school ba?"
"Na gayawa driver na cewa ba zan fita school ba tun jiya. Saboda yanayin ki yayi kamar bakya jin daɗi. You are just hiding it Maami....Su Ya Aryaan ma suna duba abinci suka tambayi Miss Mairah ta tabbatar musu cewa baki fito ba kawai suka fice ba tare da sun ci abincin ba...ki na ji ko Maami...yanayin ki is killing us,we are not happy a yanda kike. Ke ce ƙwarin gwiwarmu kuma dogaronmu. Mun rasa Daddy...idan muka rasa ƙarfin gwiwarki zamu susuce rayuwarmu ta samu tangarɗa."
" Zarah fa? Mairah É—in ta gama shirya mata?"
Na tambaye shi, domin na yi ƙoƙarin kawar da zancen duk da cewa na san gaskiya yake faɗamin.
" Eh, tare suka fita da su Ya Arhaam É—in, sun ce sune za su ajiye su school É—in."
Miƙewa na yi na zauna a hankali ina mai share hawayena na jinjina masa kaina ina murmushi na ce.
" Abdallah! Ku yi haƙuri, ni ɗin tabbas na kasance mai tsananin son kai na, damuwata kawai nake dubawa, amma daga yau na yi alƙawari...zan yi iya yina."
Hannuna ya riƙa har bakin toilet yace.
"Ki yi wanka ki shirya kin ji Maami, ni zan je na haÉ—a miki wani abin karin da kaina. Grand Ma tana jiran ki."
Murmushi na yi tare da jinjina masa kaina ba tare da na yi magana.
Bayan na yi wankan na kambala na fito na shirya sannan na fito inda Ammie ɗin na gaishe ta sannan muka gaisa da Bahrain wanda ya iso ƙasar jiya da dare.
Kallona Ammie ta yi ta kira sunana a hankali ta ce.
"Beenafah!"
ÆŠagowa na yi na kalle ta tare da amsa mata sannan ta ce.
"ina ta magana tunda na zo ba ki ce komai ba."
Jinjina kai Bahrain ya yi idonsa a kaina cike da kulawa ya ce.
"Aunty Beena...Life won't continue like this. Dole ki farka ko don goben yaran nan..."
Jinjina kaina na yi ina share hawaye na ce.
"Daman na yanke wata shawara ne. A lokacin da ƙaddara ta haɗamu da Ya Mohaa, a Nigeria rayuwarmu ta fara, sai muka koma Dubai, wanda bamu taɓa kawo ƙaddarar zama a Oumdurman ba. Sai gashi ta kasance gidansa na ƙarshe. Ta dalilin sa ne muka zo nan ɗin, to abunda na yi tunani, idan na ci gaba da zama a nan, zan ci gaba da karyewa ne har abada. Zamu koma UAE tare da su su ci gaba da karatunsu ni kuma na ci gaba da kulawa da su. Akwai abubuwa da dama da yasa na zaɓi na koma can da zama, sannan a tsohon gidanmu zamu zauna inda muka fara rayuwa..."
Murmushi Ammie ta yi tana mai jinjina kanta ta ce.
" Ba komai Beenafah, tunani ne mai kyau, Allah ubangiji ya ci gaba da jiɓantar lamarin rayuwarku damu baki ɗaya. Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya ya baki ikon kulawa da Amanar waɗan nan yaran."
"Amin Ammie, na gode sosai."
Ɗan ƙara tattaunawa muka yi sannan daga ƙarshe ta kirasu Uncle Mu'aƙƙib ta sanar musu wanda ta ce ita ce ta kawo wannan shawarar da take tunanin kamar za ta kawo sauyi a cikin rayuwata. Cikin ikon Allah dai gashi kowa ya goyi baya hakan yasa muka shirya cikin wata ɗaya muka koma UAE inda tarihin rayuwarmu ya soma.
Alhamdulillah! Komawarmu sai in ce ta ƙara haske sosai a cikin rayuwata. Domin na ɗan saki raina duk da a gidan komai yana mini watarana kamar zan ga Dayaa na a ciki. Abubuwa da dama idan na tuna sai dai in shige ɗaki na kulle kai na na yi kukana ba tare da sun sani ba. Yarana sun kasance abun alfaharina, domin sun tsaya sosai wurin bani haɗin kai wurin gudanar da rayuwar tamu bisa tsari. Musamman su Aryaan da suka tsaya akan ƙannensu da basu kulawa yanda ya kamata. Sannan Emraan da Suhaib ma sun tsaya sosai a kansu musamman Emraan wanda ya tsaya kai da fata tamkar 'ƴa'ƴansa na cikinsa. Hakan sai ya ƙara kwantar mini da hankalina sosai Alhamdulillah.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar damu a kwana a tashi har su Aryaan ɗin suka kambala Degree ɗin su yayin da Abdallah ya wuce Jami'ar Madina domin karantar fannin larabci kamar yanda ya yi buri da shi da mahaifinsa. Daman shi ɗin rayuwarsa tun tashin sa ya taso ne da son gefen addini wanda a nan rayuwarsa tafi karkata. Tun a shekaru goma ya sauke alƙur'ani sannan yana da sha biyar muka yi masa walimar haddacewa wanda har abada ba zan manta wannan ranar ba, domin Daddynsu yayi matuƙar farin ciki har da kukansa akan yanda abun ya faranta masa rai. Shiyasa bamu hana sa akan abinda yake so ba. Kuma In sha Allahu, a hankali wannan kudurin nasa zai cika.
A shekarar da suka kambala karatunsu, a shekarar na samu Ammie muka tattauna tare da su Emraan akan zancen auren su Aryaan kamar yanda muka tsara. Bayan mun kai ƙarshe ne aka saka rana da lokaci inda Aryaan aka tabbatar da maganar sa da Siyama er Hairiyyah kamar yanda ya zaɓa sannan Arhaam da kuma 'ƴar gidan Raihab da Aunty Husaina wato Amal.
*******
Shiri muka shi ga yi na musamman wanda ta kowane ɓangaren sun ɗauki bukin da muhimmanci, kuma a nan muka yanke za'a yi domin a Oumdurman ma Jadda ta shekara biyu da rasuwa, hakan yasa muka yanke kawai a yi sa a nan ɗin.
Ana saura wata ɗaya Aunty Labiba suka iso da Aunty Nadeeyah domin kawai su kasance a tare dani wanda ba ƙaramin farin ciki ya bani ba.
Ina Zaune ina Gyarawa Zarah kanta wacce a yanzu itama ta fara zamowa Budurwa Aunty Labiba ta shigo.
Kallonta na yi ina murmushi na ce.
"Aunty Labiba kun ji ni shiru ko? Zarah ce ta sakani a gaba..."
"Ba komai ai, daman wata magana ce ke tafe dani."
Kallon Zarahr na yi na ce mata ta bamu wuri sannan na mayarda hankalina ina kallonta sosai na ce.
"Mummy Na'Imatu kuwa za ta zo?"
"Eh, Sun ce sai zuwa nan da sati biyu za su zo."
"Okay! Allah ya kaimu."
"Amin. Daman Beenafah, zance ne dangane da rayuwarki...babu wanda zai tilasta miki, amma zama a haka kamar ya yi wani iri Beenafah. Dole kowa yasan cewa kin yi rashi, amma rayuwa ba za ta ci gaba da a haka ba....ina neman afuwarki idan har maganata ta ɓata miki. Amma Emraan yace yana neman alfarma idan har zai yi yu, yana so zai aure ki...muma haka ɗin idan har ya kasance, to tabbas zamu fi kowa farin ciki, domin mun riga mun zamto ɗaya, idan har kina da buƙatar wani a rayuwarki, to tabbas Emraan ne yafi cancanta. Ya kamata ki ɗaura aure Beenafah ko don yaran nan.."
Wasu irin hawaye ne suka wanke mini fuska masu matuƙar ƙuna da zafi. Tabbas ba ita ce ta farko wacce ta fara mini wannan maganar ba. Ammie ta yi ta bina da zancen wanda har ta ga ji ta zuba mini ido.
Kallonta na yi ina mai jinjina kaina na ce.
" Na gode sosai da kulawa Aunty Labiba. Amma ki yi hak'uri ko Ince ki ce masa ya yi haƙuri. Na riga na gama aure a duniya. Babu wani namijin da yake burgeni, babu wani namijin da zai iya bani farin ciki kamar yanda mijina yake yi. Sai yanxu na fahimci ciwo da tsananin ƙuncinda ya kasance a cikin rayuwar Noura a wancan lokaci. Rasa miji babban ƙalubale ne a rayuwa..."
Cike da tausasawa ta ce.
"But at the end ta ɗauki shawara tayi haƙuri tayi auren, kuma ta yi farin ciki Beenafah..."
Girgiza kaina na yi tare da lumshe idanuna wasu irin zafafan hawaye suka sake sulalo mini na ce.
"I'm sorry Aunty Labiba...amma na riga na gama aure a duniyar nan. Har abada ba zan iya auren Emraan ba."
Ita da ta kawo shawarar...ƙarshe ita ce ta ɓige wurin lallashi da bani haƙuri har sai da na ji ƙuncin da ke zuciyata ya ɗan ragu.
Na san cewa Emraan tsayayye ne ga komai namu, duk wani abun da uwa da Uba za su yi wa 'ƴa'ƴansu, to tare da shi muke gabatar da shi, ko Walimar saukar Zarah wacce ita kaɗai ce Mahaifinsu Allah bai nufe shi da ganin wannan ranar ba, tare da shi muka halarta. Ko Abdallah da zai je Madinah, tare muka tafi gabaɗayanmu har Emraan ɗin wanda idan ba ka tambaya ba ba za ka ce ba shi ne mahaifinsu ba da gaske. Duk da cewa matsayin Uba daban ne a rayuwa, ba su taɓa neman wani abu da sunan mahaifi sun rasa ba, saboda ya tsaya a kansu bisa gaskiya da adalci wanda ba ya iya bambanta su da su Abeer.
******
Wannan hidimar ta tara mini mutanen da ban za ta ba ban kuma yi tsammani ba. Ko gefen Dr. Basheer kaɗai Su Mama Asma'u da su Mummy Sameera sun nuna mini karamcin da ba zan taɓa mantawa da shi ba.
Su Yaya Hafiz suma sun zo gabaÉ—ayansu har Yaya Ahlan mijin Aunty Aysha.
Su ma Maman Fakiha da Baba sun zo har da Barrister Jafar wanda ni tun da suka iso har yanzu ban sanya shi a ido na ba.
Hidima muka shiga yi sosai, inda a nan muke shagalin Su Aryaan É—in, da kuma gidan Suhaib sai kuma Qatar gidan Raihab wanda a can su Annie suka tsaya har sai da aka kammala É—aura aure sannan suka iso da Amarya.
Koda aka shigo da su aka ajiye su a gabana tare da su Aryaan ɗin. Kuka nake sosai ina mamaki da al'ajabi wai ni ce yau nake da yara maza da suka yi aure? Ni Beenafah! Allah mai iko da rahama. Ga shi yau wannan ranar ta zo, amma babu Daddyn Abdallah. Ina ma ace yana duniyar? Ina ma ace yana nan zaune a gefena wannan burun na shi ya cika? Haƙiƙa mun rayu, kuma mun yi farin ciki ga albarkar 'ƴa' ƴa Alhamdulillah! Amma duk haka...har yau na kasa sabawa. Dariyar da yanda ya nuna tsantsar farin cikin da nake ji da gani a kunnuwana da idunawana a lokacin da Arhaam ya ce shi zai yi aure a 25yrs ɗin shi. Kamar zai ga wannan ranar da gaske, har ya fara tunani ya fara tsare-tsare, ko a jirgi lokacin da za mu yi tafiyar ƙarshe zuwa Nigeria babu zancen da yake idan ba na auren na su ba. Ya ce zai zan yi gayyata Bibi...zan gayyaci mutane da yawa, wanda duk kuma bai zo auren Mazaje na ni da shi mun datse alaƙa har abada...dariya muka yi dukkanmu. Har Aryaan ya ce, Daddy wannan kalmar Bibin tun muna jin kunyar ta har mun saba da ita. Tun ba mu san mi take nufi ba, har muka fara wayon sani, ga shi mun girma amma kaƙi ka daina ta. Yana jin Aryaan ya dire ya kamo hannuna ya haɗe a cikin nasa yana kallon su yana murmushi ya ce, Cancancacciyar kalma ce da ta cancanci nagartaciyyar Mace kamar Mahaifiyar su. Ita ɗin ta kasance ta musamman kamar yanda na saba faɗa muku, ban san wata kalma da zan kira ta da ita wacce ke bani farin ciki ba Fiye da wannan Kalmar..idan kuma ka ji an daina ambatonta...to ka ƙaddara bana duniyar.
A hankali Aryaan ya ɗaura kansa akan ƙafata, muryar nan cike da nuna zallar karaya ya ce.
"Maami! Daddy kike tunawa ba? Muma É—in shi ne muke tunawa da irin É—okin da ya nuna da zuwan wannan ranar...."
Hawayena na share ina mai yin wani irin murmushi na dafa kansu sannan na ce.
"Haka Allah ya nufa, cewa Daddynku ba zai ga wannan ranar ba. Alhamdulillah! Ina farin ciki, domin na cika masa wannan burin nasa, an É—aura muku auren a ranar da kuka cika shekaru ashirin da biyar a duniyar. Ina muku fatan alheri da fatan zaman lafiya da farin ciki na har abada. Siyama...Amal..dukkan ku 'Æ´a'Æ´a na ne kuma jinina. Allah ya zaunar da ku lafiya ya baku zuriya É—ayyaba. "
Nan É—akin ya É—auka da Amin sannan aka fita da su zuwa gidanje su wanda muke fata su rayu rayuwa ta har abada.
Ina tsaye jikin windown bedroom ɗinsa ina kallon waje, zuciyata cike da marari da kewa na ji an turo ƙofar an shigo. Waigowa na yi sai naga Aryaan ne da Arhaam. Saurin share hawayena na yi ina mai ƙirƙirar wani murmushin na kalle su da alamun nuna mamaki na ce.
"Lafiya kuka dawo?"
A hankali suka tako a tare kowa ya É—aura kansa a gefen kafaÉ—ata suna faÉ—in.
"We love you Mammi....thank you for being a good mother to us. Kin tarbiyyantar damu da ke da Daddy, kun bamu farin cikin rayuwa, kun tsaya mana akan cika duk wasu mafarkai na mu, wanda a yau sun juye sun zama gaskiya. Muna alfahari dake, Allah ubangiji ya ji ƙan Daddy ya gafarta masa, ya ƙara jaddada rahamarsa a gare sa ya ƙara yalwata makwancinsa, Allah yasa ki gama da duniya lafiya yasa ki yi kyakkyawan ƙarshe."
Jinjina kaina na yi na ce.
" Amin ya Allah."
Daga nan na É—ago su tare da kama hannun su na koma jikin Window ina kallon waje na ce.
" Kun san ta ya muka fara da mahaifinku? We were met as a strangers, a hankali sai muka fara sabawa da juna, yakan mayar da damuwa ta ta zamto ta shi a kowane irin yanayi, yakan ɗauki farin cikina a matsayin na shi da dukkan al'amura na. Bai taɓa sa na ji cewa na yi taɓa nadamar auren sa ba, kamar yanda shi ma bai taɓa riskar nan wannan lokacin ba a rayuwarsa. Haƙiƙa mun so juna so na domin Allah ba don wani kyawu ko ƙyalƙyalin duniya ba. Mun so juna, mun kuma girmama juna, ya girmama Iyayena da en uwana kamar ya basu muhimmanci sosai kamar yanda ni ma na girmama na sa. Saboda haka, ina muku nasiha da ku ji tsoron Allah, ku daraja auren ku, ku yi rayuwar aure bisa gaskiya da adalci. Ku kula da wannan amanar, kun yi aure a cikin ƙurciya sosai, ina fata da addu'a da kuma roƙon ku akan cewa kada ku zamto masu hange-hange, rayuwar aure duk wanda ya gina ta fata yake ta ɗore har mutuwa. Kada ƙurciya ta ɗebeku ku riƙa tunanin aure-aure. Don Allah ku riƙe amanar en uwanku ku zauna da su tsakaninku da Allah. "
" In Sha Allahu Maami,mun ji duk abin da kika faÉ—a mana kuma zamu yi aiki da shi gwargwadon iko...."
Jinjina kaina na yi na ce.
"Allah yasa...Kuje, sai da safe. Allah ya bamu alheri."
*******
Wata ɗaya da auren na su aka shirya bukin ƙaddamar da su a matsayin sababbin shugaban nin Golden Pathways kamar yanda Emraan ya tsara, domin sun kawo girman da ya ga cancantar hakan, sannan daman mafarkin Daddynsu kenan da abun da ya tsara matuƙar abubuwa sun tafi daidai.
Bayan sun zamto jagorori muka shirya bayan watanni shi da muka tafi Sokoto wurin auren Kausar wacce zata auri wani matashin likita wanda ke zaune a nan cikin sokoto.
Koda muka isa an gama shirya komai har an shiga hidimar bukin. Muna É—aki muna tattauna zancen kuÉ—aÉ—en da za'a sa yi kayan gara dasu na kalli Ammie na ce.
"Wai dai Ammie shi ke nan kika hanawa Armaan Kausar da gaske?"
Dariya tayi ta ce.
"Bana so ne ta yi nisa dani Beenafah. Sannan Abbun ku ma haka, shi ma ya nuna rashin amincewarsa ya ce ya fi so tana a kusa da shi."
"To Allah yasa albarka yasa ace gwamma da akayi."
"To amin."
Daga haka ta samu wuri ta zauna sannan ta nuna mini gefenta ta ce na zauna. Ina jin ta kira a tausashe na san cewa maganar dai ce kamar kullum.
"Beenafah, kamar yanda na saba faɗa miki, zaman ki a haka sam baya mini daɗi. Beenafah idan kina zaune ke ɗaya, damuwa da tunanina ba za su taɓa barin ki ki zauna lafiya ba. Beenafah aure shi ne cikon kamalar Mace. Ki yi haƙuri ki yi auren nan ko don yaran ki musamman Zarah. Beenafah kada ki manta, na auri Dr. Basheer ne don kawai saboda ke a lokacin. Ke ce dalili domin kawai na ga cewa na cika miki burin ki na son auren mutumin da kika zaɓa. To miyasa ke ma ba za ki jaraba hakan ki gani ba? Na san cewa zuciyarki mijinki kawai take tunani,to amma ki hasko goben yaran ki, har kin aurar da su Aryaan, amma su kan su sun same ni akan cewa suna so ki yi aure, domin zaman ki ke ɗaya yana ƙara miki damuwa..."
Hawayena na share ina kallonta na ce.
" Ammie ba zan iya auren Emraan ba...dalilai da yawa sun sa ba zan iya auren Emraan ba Ammie...and su ma sauran mutanen da suke nuna suna so na ba zan iya ba Ammie ba.."
Hannunta ta É—ora akan kafadata ta ce.
" Beenafah kina ji na? Jafaru yana nan, Jafaru ya kasa aure saboda rasa ki da ya yi, ba komai bane yasa ya aikata duk abin da ya aikata kawai tsabar son da yake miki ne. Ki tausaye shi Beenafah ki ba shi dama dan Allah ko zai samu farin ciki kafin mutuwar sa ta riske shi. Wani lokacin halin da zuciya ke shiga ne yake sa tana aikata ayyukan da ba su kamata ba, amma shi ɗin kin fi kowa sanin cewa mutumin kirki ne. Dan Allah Beenafah ki daure ki ba zuciyar ki magana. Beenafah yanda Jafaru ya ƙare babu wata uwa ko uba mai burin ganin ɗansa a wannan halin, ki daure ko don darajar iyayensa da zumuncin da ke tsakaninmu ki amince ki aure sa."
Jinjina kai na nayi ina mai jin wani irin nauyi a ƙirjina na ce.
" Shi kenan Ammie...idan har hakan shi zai sa ki yi farin ciki zan yi.."
Murmushine ya suɓuce mata jin amsar da ba ta yi tsammaninta ba daga bakina. Hakan yasa ta miƙe cike da farin ciki ta ce.
"Na gode Beenafah. Allah ya yi miki albarka ya ƙara miki kwanciyar hankali da farin ciki mai ɗorewa. In Sha Allahu ana gama ɗaura auren Kausar gobe sai mu tattauna ke ma sai ku tattauna da shi domin ku tsayar da abun da ya dace."
Daga haka ta fice ta barni nan ina mai kwanciya akan gadon na fashe da kuka.
*******
Barrister Jafar kuwa, tun auren su Aryaan bai ƙara yin ido biyu da Ashiru ba sai yau da ta kasance ranar ɗaura auren Kausar wanda suka jima suna tattaunawa.
Jiki sanyaye ya kalli Ashirun ya ce.
"Ko a lokacin auren 'Æ´a' Æ´anta...na kasa haÉ—a ido da ita. Ina jin kunyar ta na abin da na aikata mata a lokacin. Amma har yanzu ina son ta..."
Wani murmushin Alhaji Ashirun ya yi sannan ya kalle shi ya ce.
"You made a big mistake Barrister. Tabbas ka aikata kuskure. Wato kasan wani abu? Idan mace ta nuna so akan wani wanda ba kai ba, matuƙar dai kana sonta da gaske kuma kana son farin cikin ta, to lallai ka nuna kana son wanda take so ɗin nan fiye da yanda ma take son shi, sai Kaga an zauna lafiya. A lokacin da na ga hotunansu na a lokacin da aka haifi su Aryaan,...sai a lokacin na gane, na kuma tabbatar da cewa shi ne wanda ya kaɗe mahaifiyarta ya kuma yi tafiyarsa. Sun riga sun yi aure har sun haihu,babu amfanin kawo abin da ba shi da amfani a wannan lokacin. Ta yi kuka, ta yi baƙin ciki ta kuma ci alwashi akan duk wanda ya kaɗe mata Ammienta. Sai daga baya na gan shi ya zo asibitin yana tambaya wanda ita a daren tana can wurin likitan da yake duba Ammienta. Ban san taƙamammen abin da yake tambaya ba domin ɓoyewa ma na yi don kada ya ganni, duk da cewa a rikice yake, na san cewa akwai wani abun da ke damunsa na daban a wannan lokacin, ina nan ina kallon sa ba jimawa ya juya ya wuce. Na gane motar kuma na gane shi, amma tun da har ta aure shi babu buƙatar sanar mata domin haɗa husuma tsakanin miji da mata abu ne wanda Allah da manzonsa ba sa so kuma suka yi hani da shi. To ni na faɗa maka wannan ne domin in baka misali in kuma nuna maka cewa ka aikata kuskure na bibiyarta da kuma furta kalmomin cin zarafi akan Mijinta..."
Jinjina kansa ya yi sannan ya ce.
" Ai komai ya wuce Alhaji Ashiru, domin ko ni yanzu idan na tuna wallahy kunyar kai na nake ji. Allah yasa dai ta amince min."
"To amin."
Daga nan suka wuce wurin ɗaurin auren wanda aka ɗaura ƙarfe biyu na rana.
Ana nan ana ta hidima, Ina tsaye a ɗaki ina magana da Abdallah da ke shaidamin cewa gobe zai koma school na ji wayata ta yi ƙara, ina dubawa naga cewa Ammie ce ke kirana.
Ina ɗagawa ta ce na zo Parlourn Abbu na sama ina da baƙo Jafaru yana jirana a can.
Wani irin yawu ne ya wuce mini da ƙyar sannan na kalli Abdallahn na ce.
"Sai ka shirya ba damuwa, shi ma Aliyu zai bi su Arhaam su koma gida domin exams É—insa wannan satin ne, duk da na san cewa ya sanar maka.."
"Eh Maami, ya faÉ—amin É—azu da safe."
"To kana da buƙatar kuɗi?"
Girgiza kansa ya yi yana mai mayarda kallon sa akan wayarsa ya ce.
"Nop! Ina da kuÉ—ina, ko last week Daddy Emraan ya tura mini da 500k. And Ya Arhaam ma ya ce idan na sauka zai tura mini wasu."
"Ok to, ka je ka ci abinci dan Allah kafin na zo. Zan je naga wani baƙo a Parlourn Abbu, ka nemo Zarah ka ce ta jirani ina zuwa yanzu, tun ɗazu nake kiranta a waya ba ta ɗagawa."
Yana fita na ɗauko mayafina na lulluɓa na shiga ratsa mutane har na yi nasarar shige wa cikin Parlourn.
Zaune na cim masa ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sanye cikin shiga ta manyan Kaya na alfarma.
Yanzu tsawon shekaru Ashirin da biyar kenan rabo na da nayi ido biyu da shi. Sosai ya canja a idona amma sam ban ji komai da ganinsa ba. Gyara zamansa ya yi yana mai yi mini murmushi ya ce.
"Hajiya Beenafah! Barka da wannan lokacin?"
Wani kallon na yi masa ina mai jin wani iri a raina na ce.
"Tsawon shekaru ashirin da biyar kenan..amma ko kaɗan ban ji tsana da ƙiyayyar da nake maka sun ragu a zuciyata ba. Komai da nake tunawa ina ganin ka yanzu sai yake min kamar yanzu ne yake faruwa. Kalaman ɓatancin da ka yi akan mijina sun kasa barin zuciyata. Tsananin fushi da ƙiyayyarka ne na gani kwance akan fuskarsa a ranar da ya kama ka a ƙofar gidansa. Jafaru har abada ba zan iya auren ka ba, saboda dalilai da dama..."
"Beenafah na kwashe tsayin shekarun rayuwa ta ba tare da na kula wata macen ba duk don saboda son ki da nake yi..."
"Kai ne ka ɗorawa kan ka, domin Allah bai ɗora maka ba. Wato kasan wani abu....rashin tawakallinka duk shi ne ya kai ka ga wannan Jafaru. Da ace ka yi haƙuri ka karɓi zaɓin Allah da ya rubuta cewa ni ɗin ba rabonka ba ce, da yanzu kana nan kana farin ciki kamar kowa. Amma dagewa da ka yi kace kai lallai sai ka yi fito na fito da ƙaddarar da Allah ya zaɓa maka, shi ne yasa ka ƙare a haka. Mijina ya nuna rashin jin daɗinsa akan bibiyata da ka dinga yi kana faɗin munanan kalamai akan sa, idan har a GANIN IDOn sa na juya maka baya da gaske, to mi zai sa bayan ƙasa ta rufe masa ido na dawo yin alaƙa da kai? Hakan ya nuna cewa na ci amanar sa kenan. Abun da ban yi a GANIN IDON sa ba, har abada ba zan aikata shi bayan shi ba. Ina son mijina sosai, nayi masa so da ƙaunar da ban yi wa wani ɗa namiji ba, kuma har abada ba zan yi ba. Mu ɗin a yanzu ba yara ba ne Jafaru...mun san abin da ya dace da wanda bai da ce ba..."
Wani irin abu ne ya ji mai matuƙar ciwo da raɗaɗin sai da yasa ya miƙe tsaye a zafafe, cikin tsananin kishi ya ce.
" Wai har yanzu ma da ya ji ma da mutuwa ba za ki daina wannan ba Beenafah? Ni fa ban aikata miki wani kuskure ba, kawai ni masoyin ki ne na Haƙiƙa. Ni ban taɓa cutar da ke ko mahaifiyar ki ba, amma shi wanda kike yiwa iƙirarin so idan ba ki sani ba, to shi ne nan wanda ya kaɗe miki mahaifiyarki da Mota har kika kusa rasa ta. Shi ne ya buge ta ya tafi ya barta..."
Wani irin tsalle zuciyata ta yi tsabar baƙin ciki wanda har ban san lokacin da na wanke masa fuska da mari ba ina mai jin yanda wata irin sabuwar tsanarsa ta shiga bijiro min ta kowane sassa na zuciyata.
Baki na na rawa na ce.
" Wai kai dan Allah wane irin mutum ne? To sai me? Sai me na ce don shi ne ya kaɗeta? Wannan mummunar maganar da ka faɗa mini a yanzu kana tunanin shi zai sa na ji tsanar sa ko me? To koma haka ɗin ne na yafe masa duniya da lahira, kuma Ammie ma ai ɗanta ne, kuma na san tabbas za ta yafe masa ita ma, na gode maka sosai da ka sanar da ni wannan, ko banza Kaga wannan nauyin idan har da gaske kake, to ya sauka daga kansa daga yau...Mamaki nake! Har da cewa ya mutu amma ba ka daina jin haushin sa ba. Kada ka bari 'ƴa' ƴansa su ji ka, domin ba za ku ƙarƙare da daɗi ba. Wallahy na tsane ka, tsana ta har abadan abada. Ko maza sun ƙare a duniya...ni ɗin ba zan taɓa auren mutum irin ka ba. Duk da cewa kayi shekaru...amma har yanzu har abada ƙwaƙwalwarka ba ta aiki yanda ya kamata. Ka tafi , kada ka sake dawowa inda nake na roƙe ka..."
Fitowa na yi na barosa a É—akin, domin wallahy idan na ci gaba da ganinsa tabbas zuciyata bugawa za ta yi na mutu. Na tsane sa ta yanda ban san ma ya zan misalta shi ba.
Sosai na yi ƙoƙarin ɓoye damuwata, domin bana so na wargaza farin cikin mutanen da suka taru domin mu.
Hakan yasa na yi tamkar wani abu bai faru ba. Na koma muka ci gaba da hidimarmu.
Da dare bayan an fito da Kausar an sanya ta a motar Alhaji Hashi ne Na ji Bahrain ya riƙo hannuna yana faɗin.
"Aunty Beena please zo ki ji minti biyu dan Allah.."
Kallonsa na yi sai kuma na ce.
"Bahrain koma miye ka bari na kai Kausar na dawo..."
"Noo...Aunty Beena please, it's urgent. Just two minute as I said."
Tun da muka tako bamu tsaya ko'ina ba sai bakin ƙofar Parlourn waje yana mai kallona cike da magiya ya ce.
"Kin ƙi ki saurari kowa Aunty Beena ta...dan Allah ki daure ki saurari wannan ɗin...nobody will force you, but Idan hakan ta faru, zamu yi farin ciki."
Wani irin dokawa ƙirjina ya yi wanda ban san lokacin da na waro ido ina Kallonsa ba na ce.
"Bahrain miye yake faruwa?"
Cikin sigar magiya ya ce.
"Idan kika shiga za ki ga ko miye, Aunty Beena dan Allah ki shiga."
Tura ƙofar na yi a hankali ina mai jera addu'ar neman tsari daga Allah domin ban san waye Bahrain ke ta yi wa wannan magiyar haka ba.
Tsaye yake yana facing window ta waje wanda ko da bai juyo ba nasan kowane ne. Jikina ne ya ɗauki ɓari yayin da na ji zuciyata ta yi wani irin nauyi. Shekaru Ashirin da Shida kenan, rana ta ƙarshe a tsakaninmu ita ce ranar da kunnuwana suka yanke daga jin muryarsa bayan Emraan ya yi nasarar fasa min wayata. A wannan satin ne na yi masa ganin ƙarshe, ganin da ban ƙara sanya shi a ido na ba sai yau. Ko lokacin da Daddyn Abdallah ya rasu cewa ya yi Ammie ta isar mini da gaisuwarsa, auren Su Arhaam da ya zo ni har aka kambala ban gansa a idona ba. Taron gamayyar kamfanoninmu da muke ma, duk da cewa yana cikin manyan ma'aikatanmu bai taɓa halarta ba, matuƙar dai da ni a ciki. Sai dai ya kawo wasu Uzuroran ya shimfiɗa.
Waigowa ya yi a hankali yana mai kallon fuskata zuciyarsa cike da taraddadi wanda ya rasa ma a wanne yanayi yake ciki.
Sautin muryarsa na ji a hankali ta fara sauka a cikin kunnuwana da cewa.
"Beenafah... Dan Allah ki zauna ki saurareni, ba zan taɓa takura miki ba, ba zan ɗaga murya ba, dan Allah ki zauna, ki zauna ki bani mintuna kin ji."
Wuri na samu na zauna ina mai jin yanda hawaye suka cicciko idona wanda ban san dalilin hakan ba.
"Ahm! Da fatan kina lafiya...ya kike ya iyali ya kuma ƙarin haƙuri? Allah ya gafarta masa ya ƙara jaddada rahamarsa a gare shi."
"Amin yah Allah, na gode sosai."
"Wato wata er magana ce ke tafe dani, ina fata ban takura ki ba Beenafah?"
Jinjina kaina na yi camly na ce.
"Ba komai, you can go ahead.."
"Beenafah kin tuna lokacin da muka rabu na ƙarshe a rayuwa? Tabbas a wannan lokacin ban san miye abinda ya yanke maganar da muke yi a waya ba a wannan ranar. But bayan abubuwa sun kasance haka, sai na ɗauka cewa yana daga cikin ƙaddarata. Na so ki tun a wancan lokacin, so mai tsanani wanda yasa na gigice na ɗimauce Beenafah. Kalmomin da na tsara domin faɗa miki a wannan ranar ban yi nasara ba Beenafah. Domin na riga na makaro, sai dai kuma suna kwance a cikin ƙirjina tsawon shekarun nan, ni na yarda da cewa so ɗaya ne,kuma daga lokacin da kika so wani bayan ni sai na hak'ura na kuma ɓoye shi can ƙasan zuciyata domin babu wata macen da ta cancanci kalmomina Beenafah tun a ranar da aka shaidamin zancen auren ki. Na rayu da matata domin bin umarnin Iyayena, amma so ɗaya na ke yi...domin ki na ke yinsa kuma daga lokacin da kika yi aure, a lokacin soyayya ta mutu daga zuciyata. Bana so in yi kuskuren bayar da kalamaina ga macen da ba ita zuciyata take so ba."
Miƙewa ya yi ya dawo kusa dani kaɗan yana mai ƙara kwantar da muryarsa ƙasa sosai yace.
" Beenafah! Ban zo wurin ki don neman soyayya ba a yanxu, na zo ne saboda na san ina son ki, kuma zan furta kalmomin a gare ki wanda shi ne karo na farko bayan na rasa ki a baya, INA SON KI BEENAFAH. Wannam ita ce kalmar da na so furta miki a wannan ranar. Ba lallai sai kin amsani ba, domin nasan cewa tabbas na makara. wanda ya yi nasarar auren ki, shi ne ya cancance su saboda ya kasance jajirtaccen miji na gari kuma uba na gari. Ina so don Allah ki amince ki aureni ko da ba ki jin komai a ranki na So gare ni. Ni ban damu da hakan ba, idan ka rasa masoyi... Abin yana da matuƙar wahala da zafi a zuciya. Mai yiyu wa ka ƙara jin wani son mai yi yu wa kuma ba za ka ƙara ji ba har abada. Ni ba zan taɓa yunƙurin goge tarihin mijin ki a zuciyar ki ba, domin hakan nasan ba abu ne mai yiyu wa ba. Ban zo domin maye gurbin sa ba, na zo ne don in taimaka miki wajen ɗaukar nauyin da ki ka shafe shekaru da dama kina ɗauke da shi ke kaɗai...Beenafah ki ba ni dama, ki ba ni damar da zan tsaya a gefenki domin na zamto inuwa a lokacin rana, mafaka a lokacin ruwan sama sannan kuma san yi a lokacin zafi,sannan na kasance kujera kuma mahutar ki a lokacin gajiya...na rasa damar faɗa miki waɗan nan kalaman na tsawon shekaru ashirin da shida da suka wuce...amma a yau..Allah ya ba ni wannan damar, ki amince dani kin ji. Ba lallai sai a yau ba, ba lallai sai gobe ba. Zan jira na tsawon gobe, jibi, gata har zuwa lokacin da kika ji cewa za ki iya."
Kuka na ke ina mai jin yanda kalamansa ke ratsani. Daman da gaske abun da ya yi niyyar sanar dani kenan a ranar Emraan ya karɓe wayata ya fashe ta a ƙasa? Shiyasa ya yanke wa kansa hukuncin ƙin raɓar duk inda nake?
Lumshe idanuna na yi a hankali sannan na buÉ—e ina mai jin wasu sabbin hawayen a zuciyata ina faÉ—in.
Haƙiƙa ba ka yi Ƙarya ba Yaya Ashiru da kace ka Makara. Tabbas ka makara ɗin na tsawon shekaru ashirin da shida, ka riga ka mara domin Dayaa ne kaɗai wanda yake zuciyata. Ya bani farin ciki da duk wani gatan da mace take buƙata a wurin mijinta. to amma nauyin da ka ajiye a ƙirjinka tare da haƙuri da ka nuna. A yanda ka girmama ni ka girmama Mijina, ka kuma jure tsawon shekarun nan ko bana jin son ka ba zan ƙi amincewa auren ka ba. Ko don na saka Ammie na farin ciki zan amince da kai. Ko don 'ƴa' ƴana da suka ga cancantar ya kamata ace na yi aure zan amince maka. Ko don Bahrain da ya cire nauyin da yake ji nawa ya yi mini maganar ka ba zan ƙi amincewa ba. Kalmomin Ammie ne a raina, wanda ta taɓa faɗamin cewa, ta aure Dr. Basheer ne ba don soyayya ba, sai don cike wani gurbi da ta rasa.
"Beenafah! Idan har na faɗa miki wata kalma wacce ba ta yi miki daɗi ba, dan Allah ki yi hak'uri. Ban ji daɗi ba Sam yanda ki ke ta wannan kukan haka. Da ace na san za ki zubar da hawaye haka, da tabbas ban aikata ba....Hawayenki na ƙona ni, dan Allah ki yi hak'uri."
Girgixa kaina na yi ina mai share hawayena na ce.
" Ba ka yi kuskure ba Yaya Ashiru...da in auri wani wanda bai cancance ni ba, gwanda na aure ka É—in domin kai ne wanda yasan zafina bayan mijina. Ba kuÉ—i ko wani matsayi nake nema ba. Ina so na auri wanda zai kula dani da taimakamin wurin kulawa da yarana ba tare da jin na takura masa ba nima kuma ba tare da na takura ba. Wanda zamu girmama juna mu mututunta juna ba don wani abu da É—aya yake da shi ba...."
"I promise you Beenafah… ba zan taɓa cutar da ke ba. Ba zan taɓa ɗora miki nauyin da ya wuce ƙarfin ki ba. Kuma ba zan taɓa neman ki goge tarihin wanda kika aura kafin ni ba. In sha Allahu zan kasance a yanda kike so na, zan kula da yaranmu da dai gwargwadon iya wa ta. Ba zan taɓa barin ki ki yi kuka ba, ba zan taɓa bari ki cutu ba."
Miƙewa na yi ina Kallonsa a hankali na ce.
" I will go now...domin ana jirana. In Sha Allahu zamu tattauna da Ammie da su Bahrain. "
Cikin farin ciki ya jinjina kansa yana murmushi ya ce.
" Take your time. Allah ya sanya alheri da albarka ya basu zaman lafiya."
"Amin. Thank you."
Ina fitowa na zuba ido ina kallon yanda kowa yayi cirko-cirko ana jirana,domin Kausar ta ce ba za'a ɗaga da ita ko'ina ba sai idan na zo. Hakan yasa na yi ƙoƙarin daidaita kaina na shige motar muka tafi muka rakata ɗakin ta wanda ya sha kaya na alfarma,sai dai mu yi addu'ar Allah ya bada zaman lafiya da zuriya ɗayyaba.
Bayan mun dawo, a daren Ammie ta same ni a É—akina ta ce.
"Beenafah! Miye kike yanke akan Jafaru?"
Kallonta na yi, sai kuma na Girgixa kaina na ce.
"Ammie ba zan iya auren Barrister Jafaru ba. Amma na yanke zan auri Alhaji Ashiru Ammie..."
Cikin wani irin farin ciki ta zo ta zauna a kusa dani tana murmushi ta ce.
"Kai Alhamdulillah! Gaskiya na ji daÉ—in wannan shawarar da kika yanke. Tabbas babu wanda ya fi dacewa dake idan ba Ashiru ba..."
"To amma miyasa a farko kika ce Jafaru ne yafi dacewa Ammie?"
"Saboda ya dawo ya nuna mini da shi da iyayensa yana so ya aure ki, and Ashiru shi bai ce yana son ya aure ki ba a yanxu...kin ce kuma bakya son Emraan da duk wani wanda ya zo domin ki. Hakan yasa na ga cancancarta sa, amma idan har Ashiru ya zo da zancen auren ki, to tabbas hankalina zai fi kwanciya da shi. Sai dai shi Jafaru ina masa addu'a Allah ya bashi wata wacce zai aura ko don farin cikin iyayensa. "
" Ba zan iya auren Jafaru ba Ammie..ina fata da addu'ar iyayensa da shi kansa su yafe mini. "
" In Sha Allahu zan yi magana da su kada ki damu. Yaushe kike ganin auren ya kamata?"
" Daga zaran na tattauna da su Aryaan..In Sha Allahu sai ku yanke lokacin da kuka ga cewa ya yi muku, sai a yi. "
Cikin farin ciki ta ce.
" Masha Allah. Allah na gode maka, Allah ya amintar dake yasa albarka a cikin wannan auren da za ki yi Beenafah."
"Amin Ammie."
Washegari da muka zauna muna tattauna maganar da su Aryaan na yi mamaki da suka ce wai an sun san da zancen domin Bahrain ya sanar da su labarin yanda Ashiru ya je neman aurena da kuma yanda na auri babansu. Hakan yasa suka ga dacewarmu tunda na ƙi ƙanin Mahaifin su cewa da Emraan.
Bayan Ammie ta gama jin ra'ayoyin kowa ta tattauna da Abbu da kuma su Annie da Raihab aka saka auren wata biyu mai zuwa.
Ashiru ya yi matuƙar mamaki da farin ciki domin bai kawo komai a nan kusa ba. Sam bai ɗauka cewar abin zai faru da sauri haka ba. Ya ɓoye so da ƙaunar da yake mata tsawon shekaru, ya Karɓi Sabila domin itace xaɓin iyayensa bayan ya rasa Beenafah, ya ɗauki soyayyarta ya binne a zuciyarsa ya rufe domin ya cire rai da sake samunta har abada. So ɗaya ne kuma ya gama so akan ta. Ko a yanzu...ya yi buri da saka ran cewa zai iya samunta bayan Mijinta ya rasu. To amma a yanda yake jin cewa ta ce ba za ta ƙara aure ba a wurin Bahrain. Sai ya cire rai sai kuma gashi Bahrain ya same sa akan cewa shi ka ɗai ne wanda yafi dacewa da yayarsa, saboda haka ina ba shi shawara akan ya je gareta. Hakan yasa lokaci ɗaya So da ƙaunar da yake ji suka motso masa zuciya, take duk wani sirrin da ya binne ya shiga fitowa a hankali yana sarƙafe masa zuciya. Sai ga shi cikin ikon Allah ya yi nasara. Da ya shaidawa Su Umma Ayya har da kuka tayi na al'ajabin wannan so da yake yi wa Beenafah. Nan suka yi masa addu'a da fatan alheri na cewa ko yanxu ɗin Allah yasa ita ɗin rabon sa ce.
Bayan na koma gida tare da yara na shirya kamar yanda muka tsara muka tattaro ni da Zarah da Aliyu muka dawo, wanda su Aryaan suka yanke cewa idan lokaci yayi ana saura kwana biyu za su zo.
Ana gobe É—aura auren ya zo yasa aka kira ni.
Yanda yake ta farin ciki ni abin har mamaki yake bani, domin ni Sam bana jin wani É—oki ko marmarin abun a raina. Amma shi sai murna yake yana bayyanar da farin cikin sa a fili.
Kallonsa na yi sai kuma na É—an murmusa na ce.
"Na zo sai kallona kake ka ƙi ka ce komai Yaya Ashiru..."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Maman Zarah har yanxu sai nike jin komai yana mini tamkar a mafarki."
"Allah ke nan! Shi ne mai yin yanda ya so a lokacin da ya so."
Ɗan ƙara gyara zaman sa ya yi yana mai ci gaba da kallona ya ce.
"Haka ne. To, daman dalilin kiran na ki shi ne, ina so mu tattauna wata magana ce mai muhimmanci ne Maman Zarah."
Kallonsa nake a hankali ina mai bashi dukkan nutsuwata na ce.
"Allah yasa lafiya.."
"Lafiya lau In sha Allah Uwar Abdullahi...daman alfarma nake ne ma. Na san cewa kinfi ƙarfin komai da nake da shi. Kuɗi, gida, jin daɗi da more rayuwa...duk kin yi mini rata nesa ba kusa ba. Da wannan nake neman alfarmarki, dan Allah ki daure ki zauna a gidan da na sama miki a Abuja, na san dai rayuwar nan ɗin da can ba ɗaya bane... "
Girgixa kaina na yi ina mai jin tausayinsa a raina na ce masa.
" Ai rayuwa ba za ta taɓa tabbata ba har abada, a duk lokacin da muka samu canjin ƙaddara, to dole abubuwan rayuwarmu su sauya Yaya Ashiru. Kai ne wanda zai aure ni a yanzu, kai ne kake da haƙƙin nema mini wurin zama, abinci da kuma sutura, nauyin ka ne kuma ba zan hana ka wannan ba. Zamu bika a duk inda kake da ni da 'ƴa'ƴana kuma zamu zauna da kai lafiya tare da iyalanka In Sha Allahu..."
Cikin wani jin wani irin sabon farin cikin ya ce.
" Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Na gode Beenafah, Allah ya saka miki da alheri. Allah ya bani ikon sauke nauyin da Allah ya É—ora mini...magana ta gaba kuma, a gaskiya ba gida É—aya na tsara za ku zauna da Sabila, gidanta daban naki daban In Sha Allahu."
Jinjina kaina na yi ina mai jin wani sanyi a raina na ce.
" Na gode sosai Allah ya saka da alheri. Ni zan shiga ciki,sai goben idan Allah ya nuna mana."
"Allah ya bamu alheri Hajiya Beenafah, na gode sosai, ki gaishe da yaran."
Washegari kamar wasan 'Æ´an yara aka shigo ana shaidamin cewa an É—aura aurena a karo na biyu da Yaya Ashiru.
Su Aunty Labiba, duk da cewa ban zaɓi ɗan uwansu ba. Sun yi matuƙar farin ciki da yi mini fatan alheri. Wanda har Emraan ɗin sai da ya kirani a waya domin bai zo ba. Amma dai su Hairi duk sun zo tare da Aunty Ziza.
Haka kowa ya shiga fatan alheri a gareni wai har da su da Arhaam a faÉ—in Congratulations Maami. Allah yasa albarka ya bada zaman lafiya. Su kaÉ—ai ne suke farin ciki amma Aliyu sam baya murna, da bakin sa ya faÉ—a min cewa shi baya son na auri wani, kawai na zauna abina a haka, Zarah kuwa sai murna take tana faÉ—in ai ko Daddy ba zai so zaman Maami a haka ba.
Sai da aka cika kwana biyu da ɗaura auren sannan muka hau jirgi zuwa Abuja. Kuka nake har muka shiga cikin gidan wanda ni kaɗai na san irin abun da yake damuna. Wai ni Beenafah ni ce yau na aka rako gidan wani wanda ba Dayaa ɗina ba. Rayuwa matuƙar kana numfashi to har abada baka rabuwa da jarrabawa, domin a hakan ni sai in godewa Allah. Saboda wata sai tayi aure uku huɗu a rayuwarta wata ma fiye da haka.
Ashiru kam duk ya ruɗe sai rawar ƙafa yake kamar shi ne auren sa na farko, bayan yana da matarsa har da yara huɗu wanda har ya aurar da ɗaya daga cikin su ta farkon mai 23yrs.
Gida ne babban gida wanda ni sam ban tsammata ba, akan ganin girman shi da tsaruwarshi ne sai dai shi flat Mansion ne amma yana da yawan É—akuna masu tsari mai kyau. Kayan da ma aka saka sun yi daidai da gidan wanda Bahrain ne da Ammie suka siya komai da komai daga waje.
******
Finale....
A hankali na fara sabawa yayin da rayuwa ta sauya mini a gidan Alhaji Ashiru,wanda ya ƙauna ce ni ya kuma nuna mini irin son da yake mini wanda ya yi ta dakonsa a zuciyar sa na tsawon shekaru.
Hakan yasa na samu nutsuwa daga ni har yara na wanda suke zaune a Dubai É—in gidan Daddysu Emraan, idan kuma sun samu hutu sai su dawo gida inda nake. Suma su Aryaan suna yawan zuwa dubani tare da matansu waÉ—anda ke da yara É—aÉ—É—aya a yanxu.
Abdallahna bawan Allah shi ma yana Madina wanda sai idan ya samu hutu ko wani sarari yake zuwa ya ganni har ya samu kambala Alhamdulillah wanda muka shirya muka je har Madinar aka yi taron ƙarewarsa, sannan su Arhaam suka shirya masa buki na musamman a Dubai ɗin muka je! Yanzu ya dawo inda nake kuma a nan Abujar yake neman auren wata yarinya wacce suka yi karatu a tare.
Sannan Aunty Aysha tana tare dani ga Baba Ustaz wanda ya tsufa sosai domin a yanzu yana gida ma ko'ina baya fita.
Idan na zauna wani lokacin ina tunani, sai in yi ta lissafin yanda muka faro da irin yanda rayuwa ta shiga sauyawa da irin jarabawowin da muka yi ta tsallakewa. Wani abun na kan yi murmushi, wani ya saka ni dariya, wani kuma ya sakani Kuka.
Yau ma koda muka wayi gari da labarin mutuwar Umma muka farka wadda tayi matuƙar girgixa Baban Muhammad.
Tunda ya fita masallacin asuba ma bai dawo ba. Gani ni har na kambala shiryawa Little Muhammad ma haka.
Shigowar Abdallah na ji yana faÉ—in.
"Maami kin gama shiryawar?."
Kallon sa na yi da alamar tambaya na ce.
"Na gama. To amma in Abban na ku yake?"
"Bai dawo daga masallaci ba?"
"A'a, bai dawo ba...ina ka baro shi kai?"
Sallamarsa muka ji yana faÉ—in.
"Ina ciki Maman Zarah, koda na shigo kina cikin toilet..."
Jinjina kaina na yi na ce.
"Ga abincin karyawa an gama haÉ—awa..."
Girgixa kansa ya yi ya ce.
"A'a, na gode. Amma ba zan iya cin abincin ba, idan kun gama shiryawa ku fito mu tafi."
Sosai nake tausaya masa, domin na riga na É—anÉ—ana zafin mutuwa na san ciwon ta. Mahaifiyarka ta rasu ai kam dole akwai raÉ—aÉ—i.
Da haka muka kambala muka fito muka kama hanya sai Gusau. Bayan an gama makoki na shirya tare da Abdallah muka je muka duba Mummy da Yaya Hafiz sannan muka je gidan su Maman Fakiha.
Yanda take bani labarin Jafaru akwai matuƙar tausayi a ciki, amma ni sam ban ɗauke shi komai ba. Domin shi ne wanda ya ɗaurawa kan sa. Da yace ya zaɓi ya mutu bai yi aure ba, wannan kuma damuwar sa matuƙar dai zai kiyaye kansa da dokokin Allah. Sai da muka biya gidan Fakiha sannan muka zarce gidan Aunty Labiba wacce ta cike da farin cikin ganinmu.
Bayan mun kambala zumuncinmu muka shirya muka dawo gida. Inda muka tarar Zarah da Aliyu sun zo wai a matsayin surprise wanda naji daÉ—in zuwan na su sosai.
Daman haka suke mini, sai ina zaune kwatsam sai na gansu sun zo dubani wai sun yi kewata.
Komai na rayuwa sai in ce Alhamdulillah! Domin ko a yanda en uwana da yara na suke ƙaunata da damuwa da dukkan al'amura na sai dai in ce Alhamdulillah!
Gina Masallatai, rijiyoyi, ɗaukar nauyin marayu da tallafawa bayin Allah shi ne aikina a yanzu wanda kullum bana gajiya da yi wa mahaifina da kuma Dayaa na hidima domin Allah ya kai ladar ƙabarinsu ya kuma gafarta musu. Addu'a ta har abada ba za ta taɓa yankewa ba zuwa gare su In Sha Allahu sai idan mutuwa ce ta riskeni. Haka ma 'ƴan' ƴansa kullum ina musu nasiha da su dinga yi masa addu'a a koda yaushe suna tunawa da shi.
Tammat Bi Hamdulillah!!! A nan na kawo ƙarshen wannan Novel ɗin nawa wanda ya kasance ƙirƙirarre. Ina addu'ar Allah yasa albarka ga darasin da ke ciki. Kuskuren da na rubuta ba daidai ba kuma ALLAH ka yafe mini amin. Na gode sosai masoyana da jimirin bibiyar wannan littafin. Allah yasa mu amfana da darasin da yake ciki.
Ganin Ido comment group.
Taskar gurinjo novels.
Wattpadians
Arewapen
Da sauran mabiya wannan littafin ina godiya sosai, Allah ya saka da alheri ya bar zumunci. Sai mun haÉ—u a littafi na gaba In Sha Allah. Ku kasance dani a koda yaushe.
#Aminaibrahim
#OumAmeer
#***
#9,December2025