Free chapter · Read without an account

Part 7-8

by 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚 🖋️ · AMNA DA SAFNA


بسم الله الرحمن الرحيم 

اللَّهُمَّ صَلِّ وَ سَلِّمْ عَلَى نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ.


🖤AMNA DA SAFNA🖤

Part 0️⃣7️⃣▶️0️⃣8️⃣

📱Writing ✍🏼
Aisha G Umar 
🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️



Sai da ya kurɓi tea ɗin sannan yaƙara faɗin  "hakan kikeso Safna?"  Kanta yunƙura dan yin magana, ya shigo ko sallama babu, tun kan yayi magana idonsa ya faɗa kan Safna,  "what are you doing here?"  Ya furta haɗi da haɗe fiska,  "hee Yazeed, she's my daughter, zata iya shigowa lokacin da takeso kamar dai kai"  Dady yabasa amsa.   "Amma ba a ƙasa take yin magana dakai ba?, yau meya kawo ta?"  Ya ƙara tambaya.

"So take ta bar school, shine na keson naji masalar"  "barin school kuma?, to tayi me a gida? rabu da ita dad ba tinani mai kyau bane"  Yafaɗi yana hararar inda take, kanta na ƙasa yayin da zucuyar ta ke motsawa haɗi da tsoron abunda dady zai ce.

Ƙara faɗin  "baza kibar zuwa school ɗin ba, maza kije ki shirya ki wuce"  Yazeed ya faɗa, saurin tashi daga inda take tayi, ta fice, ranta fal farin ciki, koba komai taji daɗin zuwan sa, zata cigaba da zuwa school ɗin ta, Yazeed yafi raga mata akan sauran yaran, hakan yasa koda wasa bata son shiga harkar sa.

"Dad ai da baka saurare ta bama"  Dady  yace  "well dama so nake naji dalilin ta, amma ni kaina ai nafison taci gaba da karatun"  Yafaɗi yana miƙewa yayi musu sallama zuwa company.

Bayan yafita, cikin takaici da haushin ɗan nata, tace  "kai Yazeed!, wai menene matsalar ka da yin Makarantar Safna ko rashin sa ee?"  "No momy she's a little girl shiya sa zatayi tinanin hakan, taya za'abar ta tabar school ta zauna tayi me a Gida?, file ɗin dana baki ajjiya nazo amsa, jirana ma ake"
Cike da haushin maganar sa ta ɗauko mishi file ɗin, batare da sake yin magana ba ya fita.

Binsa tayi da kallon takaici, yadda ya rusa mata ƙaramar plan ɗin ta, ita tama rasa gane kan Yazeed, tsana ya ke nunawa ƙasƙas-tacciyar yarinyar nan kokuwa kula da ita yake?, 

Bayan isar ta ƙayataccen makarantar irin wanda ake kira sai ɗan wane da wane, nufan ajinsu tayi, tun kan ta ƙara sa ciki Aminiyar ta ɗaya tilo Raheena ta taho haɗi da yimata oyoyo, ta kama hannun ta har izuwa mazaunin su suka zauna, Raheena tace  "ya akayi kikayi latti besty? najira ki, har nayi tinanin tahowa kikayi"  ciro littafin ta tayi ba tare da tace mata komai ba.

AMNA 

Bayan me kunnuwan jaki ya gama lecture suka fito shan iska waje, zaune suke kusa da wata bishiyar Limis, a kan wasu daga cikin bencin makarantar, suna cin gurguru, su na hira, su huɗu, Amna, Zara, Nabila, da kuma Walid. Zuby ce tazo wucewa itama da ƙawayen ta, Jamila, zaliha.Tsayawa tayi tafara binsu da kallon tsana, wanda bakowa bane ya haddasa wannan tsanar face Amna.

Zuby yarinya ce mai matuƙar ƙoƙari, saidai tauraron ta ya dishe ne sanadiyyar zuwan Amna ajin su, saboda Amna ta take ta ƙoƙari matuƙa, bata taɓa zuwa na ƙarshe aduk abu na karatu, itace ta dawo ɗaliba mafi hazaƙa a jin su, duk da kuwa bata ɗaukar raini ko kaɗan, itafa Amna bataƙi su daku da kowaye ba, indai yashiga harkar ta, 

su karan kansu samarin makarantar basa gigin zuwa mata da maganar banza, bare ayi maganar SO, ai basu samu wannanr fiskar ba,  saboda daidai take da uban kowa, Hakan kuwa baƙaramin tsana ya haddasa mata, a cikin wasu daga cikin ɗaliban makarantar ba, musamman Zuby da ƙawayen ta, da kuma wasu maza biyar da ba a ajin nasu suke ba.

sunyi matuƙar sa mata ido akan glass ɗin da take sawa, har wasu na tunanin ko tana da matsalar ido ne, so suke kawai wata rana suga idon da take rufewa,Amna ba tada girman kai fannin karatu, wasu da dama sukanzo wurinta tayi musu bayani akan Subject ɗin da basu gane ba.

"Keh Amna duba yadda Zuby ke mana wani irin kallo"  Zarah ta faɗi tana taɓo kafaɗar Amna,  ahankali ta kai idon ta izuwa inda su Zubyn suke, sai da ta taɓe baki kana tace,  "rabu da ita babu abinda zata iya sai kallon ai"  kasan cewar babu tazara a tsakanin su yasa maganar ta shiga kunnen Zuby.

Takowa Zuby tayi izuwa gaban su ta dubi inda Amna take sannan tace  "ke Makauniya! ki kiya yeni niba kalarki bace, don haka kishiga taita yinki bafa tsoronki muke ba!"  "Lallai Zubi, ke har zaki cewa Wanke hannu ka taɓa Makauniya,  to kishiga taitayin ki, da alama baki san me ake kira da Danger ba ko?"  Wali ya faɗi hakan,

Murmushin gefen baki Amna tayi,  Jamila kuwa cewa tayi,  "don Allah rufa mana baki, dubeka ko kunya ba kaji namiji ɗaya cikin mata" kwashewa da dariya su Zubi suka yi, a hasale ya miƙe, dakatawa yayi yayinda Amna ta daga mai hannu, ta miƙe ta fara takawa izuwa gaban Jamila,  ta fara magana.

"Jamila kike ko Jumla?, inace ke kin taɓa ɗanɗana jan layin kinsan yadda yake, toh zaifi miki salama ki sawa bakinki kwaɗo"  riƙe kumatu Jamila tayi yayin da ta tuna marin da Amna ta taɓa yi mata,  komawa gun Zuby tayi, ta cigaba da faɗin  "ke kuma!, ni nafi ƙarfin in kiyaye ki sai dai in ƙyamace ki, saboda baki fara wanka ba bare har kifita inga abun kiyaya a tattare da ke"  tafaɗi tare da juyawa.

Zuby bata iya cewa komi saboda ba ƙaramin gamawa da ita Amna tayi ba,  sukuwa abokan Amna dariya suka farayi har da ƙyalƙyalewa,  da kyar suka tsaya da dariyar suka furta,  "da kyau!".  Nabila tace,   "wow Amna kinyi wallahi"  murmusawa kawai Amna tayi ta furta,  "let's go"  suka wuce su kabar Zubi da tawagarta.

Kiran Mubarak ne ya tsaidasu,  yana faɗin  "ashe ta nan kuke"  "Aboki na ya akayi yau kun daɗe a class"  "bari kawai wali yau dogon karatu mukayi"  murmushi dukan su sukayi,  Zarah tace   "Mubarak anyi abu baka nan"  "wani abu?"  "gani ya kori ji naso ace kagani"  Nabila ta faɗi hakan,  Mubarak yakuma faɗin  "hmm nasan bai wuce Amna ce ta buga game ba, saboda nasan ta"  dariya sukayi.

Wali yace  "Kasan sistern ka she doesn't take affence"  "it's ok" Amna ta furta ta sa hannu a jakan ta fito da gurgurun da yake daure a leda yaji madara, tana ƙara faɗin  "ga naka dan na kusa cinyewa ma"   "aiko da kinbiya"  Yafaɗi bayan ya ansa, shima ya fito mata da chocolate yace, 

"kinga chocolate ɗin da na siya miki, amma bazan baki ba"  kwacewa tayi  "basai ka bani ba na ƙwata"  gaba ɗayan su suka sa dariya.  Mubarak bai da Abokai, hakan yasa Abokan Amna ne nasa.

YAU ASABAR RANAR HUTU,  

Gari ya waye tangararan, zaune gaba ɗayan su suke akan tabarmar Ummee suna karin kumallo,  Amna tace  "Ummee me zaki dafa mana da rana"  "ko gama cin na Safe bakiyi ba amma kina tambayar na rana"  "eh ɗin ina ruwan ka"  mubarak yakuma cewa  "akoi ruwana ai Ummee na kika tambaya"  dakatar dasu Mamma tayi da Fadin

  "kai kai so kuke ku ƙware ne?, to bari kuji bamai kawo muku ruwa in ku ka ƙware kuna abu kamar ƙananun yara"   dariya Ummee da Baba sukayi,  Amna ce ta dubi Mubarak tace,  "laah Mubarak da kai fa Mamma take"   "a ah dake dai, dan Mamma ɗaukar ki take ƙarama"

Bugu ta kai masa a cinya, tare da hararar sa,  "wai Allahna wannan hannun ƙarfen naki kika samin?"  Darawa su Mamma suka yi, mamma tace  "Ƴan rigima"   "yakamata ace Amnata ta fara girki tunda batason akira ta da ƙarama ko?"  Baba Yafaɗi hakan yana kallon Amna,  Ummee tace 

"aikuwa dai gata ta tsani ko zuwa kitchen bere girki itafa kawai a dafa abata"  "cab Ummee to ai in mutum yaci Abincin Amna wllh sintirin bayan gida zaiyi ranar, kofa riƙe ludayi bata iya ba"  turo baki tayi tana faɗin  "Mamma kin ganshi ko!"  Dariyar suka ƙara yi,  Ummee tace,  "yaran nan in ka biye su, baza kaci abinci ba har yayi sanyi,  

KADUNA Safna

Ba ƙaramin ruwa akayi ba jiya da dare gari ya ɗau sanyi sosai, hakan yasa bacci yazama mai Daɗi a wurin masu gata, amma Safna kuwa, kasan cewar yau Asabar babu Makaranta, hakan ya zame mata dole da ta tashi tayi dukkanin aikin cikin gida, koda kuwa saukan ƙanƙara ake. Sanin hakan yasa tunda suka tashi asuba sukayi sallah su kayi karatun Alqur'ani, batayi gigin komawa bacci ba.

Lulluɓe Ammu tayi da lallausan bargo, ido suka haɗa da Ammu, ganin yadda ta keyi mata kallon tausayawa yasata tsayawa, ta shapa kan Ammu tana ƙirƙiro murmushi a fiskarta cikin sassanyar muryar ta tace,  "my Ammu na kinsan mene ne?, yau tashi nayi da karsashi a jikina sosai, koda ace duk gidan nan akace na gyara zan iya"  

Ganin yadda tayi maganar sai itama ta maida mata murmushi, acikin ranta kuwa,  tasan Ƴarta so take kawai ta cire ta a damuwa, domin tasan wahalar dake tattare da aikin gidan,  aikin da mutane shidda keyi, su ɗin ma suna daɗewa kafin sugama, amma ace mutum ɗaya zaiyi, saboda rashin imani duk ranar asabar da lahadi Safna ce meyin aiki a gidan in aka cire girki.

Fara aikin tayi, gurin ƙarfe bakwai ta saki aikin, taje ta kaiwa Ammu breakfast, sai dai ita bataci ba saboda so take ta gama aikin cikin lokaci, don ƙarfe goma ne time ɗin da hajiya tasa mata lokacin gama aikin, kuma ta san ta kamar yunwar cikin ta, gashi aikin kuwa da uban wuya, tana rokon Allah ya kiyaye mata ciwon baya, saboda yadda take aikatuwa a wannan ranakun.

Karfe tara da en mintuna ta gama aikin cike da gajiya ga yunwa, tana gamawa ta nufi kitchen dan ɗaukar abincin ta da ta ijje, sai dai tana buɗe inda ta ijje abinci yace ɗauke ni inda kika ijje ni.

Dube dube tafara yi acikin kitchen ɗin dan samun abinda zata kashe yunwan cikin ta dashi, tunanin ta ne yatsaya ganin kret ɗin Ƙwai, ɗaukar biyar tayi, ta soya atake, ɗaukar bred din da ta gani a gefe tayi, haɗi da godewa Allah. Zama tayi da bismillah ta fara antaya wa acikin ta.

"Kai ka kai bred ɗina?"  Saurin sakin bred ɗin tayi ta miƙe à rarrabe ta furta,  "Ru....Ru....ki...dama....na.. ki..ne?"  Ta ƙarasa à tsorace,  sai da Ruki ta ƙaraso gaban ta, cikin ɗagun murya tace,  "mayunwaciya yanzin abun da na ijje zaki ɗauka?, harda soya Ƙwai, wato kin samuri ko?"   Juyawa tayi ba tare da tsayawa jin abinda safna zata ce ba,  tayi hanyar falo, binta Safna tayi à baya tana bata haƙuri,

Tsayawa Safna tayi ganin an shiga falo, sannan ga Hajiya a falon.

🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol