Free chapter · Read without an account

Page-9

by 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚 🖋️ · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁




Free book📓



By


*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page9️⃣






Har sai da na fito nan ma ta kamoni ta mayar da ni kan gado, kallonta kawai ni na ke yi da tunanin wace wannan matar?.

"Zan yi sallah" na faɗi da sanyin murya, kallona ta yi sannan ta ce, "za ki iya yin sallah a haka? Ba kyajin komai a kanki?" Nan ma na ɗaga mata kai alamar eh. Murmushi ta yi min sannan ta shinfiɗa min ɗankwalinta a ƙasa, kasancewar da ma kayan majinyata ne a jikina yasa ta kuma ba ni mayafinta na fara gabatar da sallah, duk da da ƙyar na ke yinsa, amma haka na yi ramuwar sallolina duka har na idar.

Ita kuwa hajiya Rahama kallona ta ke yi tana murmushi, da tunanin yarinya ƙarama haka amma ta san darajar sallah sosai. Bayan na idar ta kuma mayar da ni kan gadon, daidai zuwan wata nurse, ta zo duba marasa lafiya shine ta biyo ɗakin, "yarinya ki na da buƙatar wani abu kamar abinci?" Cewar Hajiya Rahama, kafin na yi magana nurse ta ce, "karki damu madam, alluran da akai mata za su taimaka mata wurin jin yunwa, in the morning sai ki nema mata abincin" ta ɗora da cewa, "ya sunan yarinyar ta ki madam? She's beautiful".

Shiru Hajiya Rahama ta yi domin kuwa ba ta san sunana ba, ni kuwa mamaki na ke yi da jin nurse ɗin ta ce wai ina da kyau, duk da cewa lokacin da Ummana ta ke rayé, ta sha sanar da ni cewa ni kyakykyawa ce, har wani lokaci takan kirani da mybeautiful Nur, to amma tun bayan zaman da na yi da su Inna Jummai, sai na ke ganin kamar duk duniya ma babu wanda ya kaini muni, domin kuwa furucin da su ka sha yi min.

"Eh what is her name?" Nurse ta kuma tambaya tana murmushi, lura da na yi wannan matar tana shirin kame-kame yasa ni na amsawa nurse tambayarta, domin kuwa dama ai na san matar ba ta sanni ba kuma nima ban santa ba, "my name, Nuriyyah" "wow madam sunan 'yarki ya min daɗi" cewar nurse tana cigaba da gyaramin ledar ruwan don ya shiga jikina da kyau. Kwantawa na yi tare da rintse ido saboda yanayin da na ke jin jikina. Ita kuwa hajiya Rahama kallona ta ke yi kawai ba tare da ta ce uppan ba.

WASHE GARI.

Hajiya Rahama ta kula dani sosai, jikina kuwa alhamdulillahi na ɗan ji sauƙi ba laifi.

Hajiya ce waje tana waya da mai gidanta, inda ya ke tambayarta ya jikin yarinyar? Ta amsa masa da sauki alhamdulillahi, "ina fatan iyayenta sun fahimce ku ba su yi fushi ba?" Cewarsa, ta ce, "a ah ban ma tambayeta ba tukunna, gani na yi ya kamata na ɗan bari, jikin na ta ya daidaita sannan sai in tambayeta" ya ce, "kin yi abin da ya dace, domin idan ta samu natsuwa sosai za ta fi yin magana da ke cikin hankali, to Allah yasa mu da ce, ya kuma ba ta lafiya".

"Ameen, ina yarana su Sadiya?" ."ai kin san yaran na ki sai tambayana su ke Momy Momy ba ta dawo ba, zuwa office ma sun hanani ko fita ban yi ba, ina tare da su", murmushi mai sauti ta fitar ka na ta ce "yaran Momy kenan, da ba don kada dare ya yi min a haya ba, da na taso zuwa anjima idan na gana da parents ɗin yarinyar" haka su ka cigaba da hira har ta yi waya da 'ya'yan na ta, daga ƙarshe ta katse kiran.

hajiya Rahama ce zaune a gefena, ganin na samu sauƙi ne yasa ta yanke shawarar tambayana, cikin kulawa ta dube ni ta ce "yarinya ki ka ce Nuriyyah sunanki koh?" na ɗaga mata kai alamar eh, sai da ta yi murmushi tare da cewa, "ok ke 'yar garin ce?" "Ni? Wani gari?" Na yi mata tambayar cikin muryata a hankali, don ban fahimceta ba, "Bauchi" ta ba ni amsa, girgiza kai na sa ke yi na ce, "a a Adamawa na ke".

Hajiya Rahama da mamaki ta ce, "Adamawa kuma? Me ya kawo ki Bauchi to? Ko kun zo ziyara da iyayenki ne? Ina su ke? Faɗa min saboda na san yadda zan nemo su, domin na san yanzu haka suna cikin damuwar rashin ganinki". Shiru na yi kaina a ƙasa ba tare da bakina ya motsa ba.

Tambayar ta kuma yi min a karo na biyu, sai da na share ƙwallan da ya zo min sannan na yi dauriyar cewa, "Ummana ta rasu da Abbana har da Annur ƙanina, duk ba sa nan, duk sun rasu" ina kai ƙarshen maganar kuka ya kufce min, saboda ji na yi kamar ta motsa min wani tsokar da ke ɓoye da kewansu.

Dafa ni da hannu biyu ta yi tana rarrashi na har na yi shiru, cikin tausayawa ta ce "ayyah I'm sorry 'yata Allah ya ƙara ba ki haƙurin rashinsu, but tell me inda danginki su ke" "ni ma ban san ina 'yan uwansu Abba su ke ba, Inna jummai ce kawai na sani da Halima, su kuma sun koreni".

Jinjina maganar Hajiya ta yi ta ce. "Allah sarki, na tausaya miki sosai, amma dole insan inda danginki su ke, saboda insan ina zan kaiki idan aka samemu, yanzu kenan babu inda ki ka sani?" Ɗaga mata kai na yi ina share hawaye. Sai da ta ja numfashi mai ƙarfi sannan ta miƙe zuciyarta fal tunanin abun yi?.
 
BAYAN SATI ƊAYA. 

Kasancewar babu wanda zai tsaya a tare da ni, hakan yasa hajiya Rahama ta ƙi tafiya har sai da mu ka kuma yin kwanaki har sati ɗaya a asibiti, domin sai da aka cire min duk wasu bandage ɗin da aka sanya min.

Jikina alhamdulillahi na warke sosai, sai 'yan abun da ba za su gagara ba, bayan an sallamemu mu ka fito harabar asitibiti, babu abin da ya ke yawo a zuciyata fa ce fargaba, domin kuwa ji na ke kamar na cigaba da zama a cikin asibitin nan, domin Hajiya ta kula da ni sosai, to idan na fita gurin wa zan nufa? Ina zan je? Ya zan yi?.

Bala ya riga da ya isa cikin motar har ya ta da shi, abin da ya ke jira kawai hajiya Rahama. Juyawa Hajiya Rahama ta yi tana kallona, yayin da cikin ranta ta ke ta aikin saƙa da warwara, dole ta san yadda za ta yi da yarinyar nan, domin kuwa barin yarinyar a wannan yanayin bai dace ba, ita mace ce, kuma marainiya, ba uwa ba uba, haƙiƙa barinta kuskure ne, dan zai iya sanadin ɓacuwan rayuwarta, to kuwa tana ganin gwara ta kaita ko gidan marayu ne?.

Bayan ta gama saƙe-saƙen zuci, ta durƙusa ƙasa haɗi da kama hannuna, ƙasa na yi da ido ina kallonta yayin da idanuwana su ke cike da hawaye, kasa magana ta yi saboda tausayina da ta ji ya kuma shiganta, miƙewa ta yi tare da juyawa tana kiran Bala, bayan ya iso ta ce da shi, "Bala ka san garin nan sosai, akwai inda ka sani ake ijje yaran da su ka ɓata? Ko kuma dai gidan marayu?".

Saurin ɗaga kai na yi ina kallonta jin ta ambaci gidan marayu, kenan ni za ta kai? Bala ya ce, "eh Hajiya akwai wanda na sani, yana nan a Low-cost housing Estate, babu nisa da nan sosai" sai da hajiya Rahama ta ja numfashi sannan ta ce, "mu je can ɗin" da to ya amsa sannan ya juya ya shige mota, kama hannuna ta yi ta sanya ni cikin motar, ni kuwa ban san farin ciki zan yi ba ko baƙin ciki, tun da ban san ya can gidan marayun ya ke ba.

Nan Bala ya yiwa motar key ya ja mu, idona na gefen glass ɗin mota ina kallon hanya tare da shiga tunani. haka muka kama hanya zuwa gidan marayu.


Last page
___________________________________________________


Shin Hajiya Rahama za ta kai Nuriyyah gidan marayun? Idan ta kaita hakan zai zame mata sauƙi ko wuya?.

Mu kasance a next page don jin me zai faru gaba?




_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol