Free chapter · Read without an account
Page-10
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By
*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page1️⃣0️⃣
Nan Bala ya yiwa motar key ya ja mu, idona na gefen glass ɗin mota ina kallon hanya tare da shiga tunani. haka muka kama hanya zuwa gidan marayu.
Juyowa Hajiya Rahama ta yi tana kallona tsawon mintuna kamar tana nazarin wani abu a kaina, ka na ta samu buɗe baki ta ce, "Nur?" Da sauri naɗauke idona daga gefe tare da dawo da su na amsa da cewa, "na'am Umma" saboda ta kirani da sunan da Ummana kaɗai ke kirana, sai na ji kamar Umman ce ta kirani. Hannunta ta ɗaura zuwa kaina domin jin na kirata da sunan Umma, "kin san ina mu ke zuwa yanzu?" Cewar Hajiya, girgiza mata kai na yi alamar a ah, sai ta kuma cewa, "gidan marayu zan kaiki, saboda ina ganin hakan shine daidai, ina fatan ranki bai ɓaci ba? kin ga dai babu inda na san danginki su ke bare na kaiki".
Murmushi na yi mata ina cewa, "nagode sosai Hajiya, kin riga da kin taimake ni kuma kin ba ni kulawa, ke mutuniyar kirki ce, ba abun da zan ce da ke sai na ƙara gode miki, kuma na san inda za ki kaini masu irin halinki ne ko?" Sai da ta sauke hannunta a kaina sannan ta yi min murmushin da bai kai zuciyarta ba, ta kuma maida kanta ga hanya. Ni kuwa ganin ba ta amsa min ba ne yasa ni yin shiru na kuma mayar da kaina inda ya ke ɗazu.
Mun ɗan yi tafiya mai nisa kaɗan, yayin da Hajiya Rahama ba abun da ta ke cigaba da yi sai tunani, "anya wannan hanyar da na bi daidai ne kuwa? Yarinyar nan tana da hankali, shin me zai hana ni in riƙeta? Kamar hakan zai fi, to amma! Na san Dadyn Abba yana wuyar sha'ani wani zubin, idan kuma na kaita ya ƙi amincewa fa?" Ta faɗi cikin ranta sai kuma ta girgiza kai.
Kamar wacche aka tsungula ta yi saurin raba jikinta daga kujerar mota tana cewa, "Bala samu wuri ka tsaya!" Kamar yadda ta ce ya samu wuri ya tsaya. "Hajiya fatan dai lafiya? Na ji kamar yadda..." kafin ya ƙarasa Hajiya Rahama ta ce, "ba komai".
Ni kuwa da ban fahimci dalilinta na cewa Bala ya tsaida motar ba na juya ina kallonta, "yata Nuriyyah, in ba damuwa ina son in koma gidana da ke, na fasa kaiki gidan marayu" "gidanki?" Na yi tambayar don neman ƙarin bayani, "Eh gidana, na fasa kai ki gidan marayu, na ji sha'awar ki zauna tare da mu, sannan kuma ina da yarinyar da ba ta wuci shekararki ba Asma'u, kin ga sai kuyi wasa tare da ita".
Murmushin jin daɗi na yi mata, yadda ta kula da ni a asibiti ba ƙaramin daɗi yai min ba, idan kuwa na bi ta kamar yadda ta ce, to ina sa ran samun sauƙi daga zafin ƙaddarata, ba tare da na daina murmushin ba na ce, "na amince Hajiya" shafa fiskata ta yi ta mayar min da murmushi, sannan ta juya gurin Bala da ke sauraronmu ta ce, "Bala juya motar nan, ina nufin mu kama hanyar Jos" da to ya amsa sannan ya fara motsa motar don cika umarninta.
Nan muka kama hanyar garin Jos (Plateau) inda gidanta ya ke. Mun kwashe 'yan wasu awanni kasancewar yadda wasu guraren hanya su ke da targatso, sannan kuma mun sha tsayawa a hanya, hakan yasa sai dare muka isa.
A daidai ƙofar wani gida driver ya dakatar da motar, ya fara latsa hon wanda hakan ya farkar da ni daga ɗan barcin da na nitsa, goge idona na yi ina bin ƙofar gidan da kallo ta cikin mota. Mai gadi ne ya fara wangale gate ɗin gidan hakan ya ba driver damar fara shigar da hancin motar ciki har ya yi parking.
Hajiya ta buɗe ƙofar ta fito, sannan ta miƙa min hannu ta taimaka min gurin fitowa, sanyi na ji ya dake ni bayan na sauka, gaskiya akwai sanyi sosai a garin, don ma hijabin da Hajiya ta siyan min babba ne shi ya ɗan taimaka min, domin da yagaggen hijabin da na fito da shi daga gida ne da sai dai ya ƙara min. Sai bin kyakykyawan gidan da kallo na ke yi idanuwana zuruzuru, domin ni dai ban taɓa shiga gida mai kyan haka ba a rayuwata.
Mai gadi ne ya iso yana gaida Hajiya Rahama tana amsawa nima na gaishe da shi, lokacin Dady wato mijin Hajiya Rahama ya fito harabar gidan da fara'a sosai a kan fiskarsa yana faɗin, "kun iso kennan? Me yasa ba ku sanar da ni ba? Ai da na tarbeku tun daga bodan shigowa Jos" murmushi Hajiya Rahama ta yi sannan ta ce, "shiyasa na ce gwarana na barka ka huta, domin kuwa zaka wahala" "hh to sannunku da gajiya na san kunsha jigila" ya kuma faɗi,
Hajiya ta ce, "gajiya kam akwaita wallahi". A hankali na durƙusa ina gaishe da shi, wanda sai à sannan ya ma lura da ni, da mamaki ya amsa gaisuwata kamar wanda aka yiwa dole, sai ya maida kansa ga Hajiya Rahama yana yi mata kallon tambaya, zuciyarta ce ya ɗan amsa kaɗan, "I'm sorry please, zan yi maka bayanin komai Dadyn Abba, ka ba ni dama kafin nan". Ba tare da ya amsa mata ba ya juya yana komawa ciki, itama ta bi bayansa ni kuma ina tsaye.
Ganin kamar ban biyota ba ne yasa ta juya baya tana kallona yadda na ke ta rungumar hannuna saboda sanyi, ta ce, "yata Nuriyyah taho mana". Simi simi na fara bin bayanta zuciyata na shiga cikin wata fargabar kuma, domin yadda Alhaji ya amsa min gaisuwan ya kashe min jiki sosai.
Duk da kasancewar dare ne bai hana ni kallon kyakkyawan falon ta hanyar haɗaɗɗun fitulun da ke ciki ba. Samun wuri na yi na raɓe à ƙasan lallausan kafet mai laushi kamar bredin da bai ƙone ba, sai ƙyaf-ƙyafta wa'yannan fararen idonunawan na wa na ke, madaidaicin bakina na motsi kamar yana neman magana, ba komai ba ne yasa ni hakan face sanyin da na ke ji yana ratsa jikina, domin kuwa ina ga da alama sinadarin sanyi na aiki a cikin falon.
Hajiya Rahama ce ta fito daga wani ɓangaren da ban san yaushe ta yi can ba, hannunta riƙe da madaidaicin plate da ke ɗauke abinci da jus sai kuma ruwan gora à ciki. A gabana ta dire komai cikin kulawa ta ce, "Nuriyyah gyara zama mai kyau, sannan ina so ki zage ki ci kada ki ce min wani kunya, a hanya baki wani ci abin..." ganin yanayina ne yasa ta dakata tare da ɗaga hannunta tana ɗaurawa kan goshina da na ke ta faman duƙun-ƙune shi cikin hijabi, "me ke damunki Nuriyyah?" Ta yi min tambayar, ni kuma cikin dan shaƙaƙƙiyar murya na amsa, "sssanyi na ke ji Hajiya".
Da sauri ta miƙe da cewa, "ohh sorry, yi haƙuri AC à kunne ƙila ba kya son sanyi sosai" ta faɗi haɗi da juyawa da sauri don zuwa kashe AC. Bayan ta kashe ta dawo wuri na da faɗin, "na kashe yanzu za ki ɗan samu sauƙi, ki ci abincin bari na kawo miki magun-gunanki sai kisha ki je ki kwanta kin ji?" Ɗaga mata kai na yi ba tare da na amsa ba.
Ahankali na fara jin sanyin na raguwa, sai kuma na fara cin abincin da ta kawo min cikin nutsuwa, bayan na gama godewa Ubangiji na.
Bayan Hajiya Rahama ta koma ɗaki tana zaune gefen gado, tana cin abincinta da ke kan ƙaramin center table, sai dai cin abincin ta ke kamar ba ta so, mijinta da ke gefenta ne ya kuma tambayarta karo na uku, "akan me zaki taho da yarinya nan? kawai don accident cikin rashin sani ya faru! A ina aka taɓa yin haka?" Ya faɗi cikin ɓacin rai.
Last page
___________________________________________________
Lallai! Ga dai Nuriyyah nan à gidan Hajiya Rahama, to kuna ganin mijin Hajiyar zai amince da zamanta à gidan kuwa? Ga dai maganar da ya fara, ya zata kaya?.
Mu kasance a next page don jin me zai faru gaba?
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_