Free chapter 路 Read without an account

KADDARARMU ce....6

by Nusaiba Ibrahim Rimi 路 茦ADDARARMU CE TA ZO A HAKA

馃 茦ADDARAR MU CE....馃憣
(Ta zo a haka)

鉁嶏笍Nusy bee
鉂わ笍*Young talented writers association YOTA*鉂わ笍 



My TikTok account 馃憞


***



My Instagram account 馃憞

***


My arewa pen link 馃憞


https://arewapen.com/u/nusybee143


*TALLA!TALLA!!TALLA!!*

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU茒I 茦ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA 茦WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA茒EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU苼A TA KAI TSAYE KU TUNTU苼E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL*馃憞
***, 
***

Page 6



Faisal ya yi murmushi mai sauti ya ce "all is well sweetheart,I hope kema lafiya kike"Aneesa ta yi 蓷an murmushi ta ce"lafiya nake,yanzu dai ka ce na zuba idanu zuwa next week?"

"Exactly my dear!a ranar za ki ga Faisal 蓷inki,Nima zan ga my Aneesa "ta yi murmushin jin da蓷i,suka cigaba da hira cike da farin ciki 

Sun kwashi wasu mintuna, hankalin Aneesa ya kwanta sosai, a茩alla ta samu nutsuwa tunda ta ji masoyin nata ya na lafiya,sun yi hira cike da farin ciki da soyayyar juna kafin su yi sallama

Ta kai mintuna biyar a zaune a 蓷akinta tana tufka da warwara kafin ta mi茩e ta koma 蓷akin Ammi,da sallama ta shiga, Ammi da take zaune gefen gado ta amsa da sallama tana 茩are mata kallo,gefen gadon itama ta zauna tana fa蓷in "Ammi wai me yake faruwa ne?meyasa yanzu Abba bai cika son ya kira mu a waya ba?"

Ajiyar zuciya Ammi ta yi ta ce "Nima abin nan ya na matu茩ar damu na wallahi,yanzu gaba 蓷aya abbanku bai cika damuwa damu ba,tunda ya koma,wajen watanni biyu kenan"

Kallonta Aneesa kawai take yi har ta gama magana,kafin a hankali ta ce"to yanzu menene mafita Ammi?meyasa Abba yake haka?"

A 茩ule ammi ta ce"shekarun mu ashirin kenan da aure tsakani na da abbanku,amma bai ta蓳a yi min haka ba sai yanzu don ya auri wannan matar,to gaskiya dole na 蓷auki mataki,don an ce haka suke da ba茩in asiri,ba sa barin mutum da matarshi ma,mune muka yi sa'a "Aneesa ta 蓷auke kanta daga kallon Ammi da ke ta kumfar baki sannan ta ce

"A ina kika san ta kika san halinta?"

Kai tsaye Ammi ta ce"拼ar unuguwarsu ce ta sanar da ni halinta,ta san su ta san family 蓷inta sosai"Aneesa ta 蓷an girgiza kai ta ce

"To yanzu wanne mataki za ki 蓷auka?"

Ba tare da tunanin komai ba Ammi ta ce"malamai magada annabawa xan ha蓷a ta da su su yi min ro茩o,da izinin Allah sai dai na ga bayanta na dai ta ga nawa ba,don yadda na auri abbanku tun bamu san kanmu ba in sha Allahu sai dai 蓷aya ya binne 蓷aya"

"To yanzu ke Ammi baza ki iya ro茩on Allan da kanki ba sai kin saka wani?"da sauri Ammi ta kalle ta kafin ta ce

"Manyan malamai ne ba wani ba,suna da 茩arfin yawu,da wuya su yi addu'a ki ga abu bai daidaita ba"Aneesa ta 蓷an girgiza kai cike da takaici,ta 蓷auki wayarta ta fice daga 蓷akin 




ASOKORO,ABUJA, NIGERIA 

Zaune take a gaban madubi tana gyara dogon brown 蓷in gashinta,daga ita sai bathrobe,a lokacin da wani zai ganta ba zai yi tsammanin ta iya wani harafi 蓷aya na Hausa ba,ta kai a 茩alla mintuna talatin tana gyara gashin nata, kafin ta kammala,ta sanya wasu fararen riga da wando hoodie,ta saki gashinta baya,babu batun 蓷ankwali,sannan ta janyo wayarta da take ta ringing tun 蓷azu tana kallon sunan wanda yake kiran nata a wula茩ance 

Tsaki ta ja ta mayar da wayar ma'ajiyarta,sannan ta zura slippers 蓷inta ta fice daga 蓷akin nata ta nufi downstairs 

A main parlour 蓷in gidan ta ci birki tana kallon wa蓷anda suke zaune kamar bata saba ganinsu ba, Ummi ce,wato mahaifiyarsu,sai Najwa,hira suke yi sosai,suna ganinta Ummul Ummi ta saki murmushi sosai tana fa蓷in "Welcome daughter!har na ce lafiya?na saka Najwa ta kira min ke a waya kuma tana ta kira ba ki 蓷aga ba, I hope all is well!"

A kaikaice ta 蓷an kalli sashen Najwa da take ta aika mata kallon banza,don sam Najwa bata tolerating wula茩anci da rainin Maleeka, ita ma Maleekan 蓷auke kai ta yi, maimakon ta bawa Ummi amsa sai cewa ta yi

"Ummi ina Lateefa da Mimi?"

Cikin sakin fuska Ummi ta amsa"Lateefa ta tafi wani birthday 蓷in 茩awarta, Mimi kuma ta na study room,kin san ta da maitar karatu"Maleeka ta 蓷an ta蓳e baki ka蓷an, lokaci guda kuma ta nemi waje ta zauna tana mayar da hankalinta ga kallon TV 蓷in da ke parlourn,su kuma suka cigaba da hirarsu 

Mintuna ka蓷an sai ga sallamar Lateefa,suka amsa mata,ta yi matu茩ar kyau cikin red riga da jan wando,sai wata 拼ar riga da ta 蓷ora itama fara,farar fuskar nan an yi mata light make up,ta sha kitso da jan attachment da ya sauka har gadon bayanta,sai 蓷an siririn mayafi da aka 蓷an 蓷ora akan attachment 蓷in aka yi crossing 

Kai tsaye wajen da Maleeka ke hakimce ta nufa bayan ta gaida Ummi,tana zuwa ta zauna tana kallonta ta na murmushi,kafin ta ce

"茦awata Ameera ta ce a gaishe ki"

"Ina amsawa"Maleeka ta fa蓷a ba tare da ta kalli Lateefa ba

Sam Lateefa bata damu ba,don ta saba da halin Maleeka,cikin fara'a ta sake fa蓷in"ta so ki zo fa,amma babu damuwa, wataran na san za ki je ko?"

Maleeka ba ta bata amsa ba,sai 蓷aure fuska da ta yi, alamun ta gaji da magana, murmushi sosai Lateefa ta yi,bata gajiya da yiwa Maleeka hira,ranta sam baya 蓳aci muddin tana tare da Maleeka ko me za ta yi mata,ta na jin da蓷in ta yi abu don ta burge ta ta ga ta burge ta 蓷in,don Maleeka tana tuna mata da wanda ta mallakawa soyayyarta kuma ruhinta,duk da abinda ke tsakaninsu

Muryar Ummi ce ta katse mata hanzari,ta yi saurin waigawa tana kallon Ummi da ke fa蓷in 

"Don kamar yadda abbynku ya gaya min ba zai wuce cikin satin nan ba in sha Allah"

"Yeeeeee!don Allah Ummi? yayana zai dawo? wallahi dama I'm missing him soooo much! wayyo da蓷i!!!"dukkansu suka kalli Mimi da ke fitowa daga study room tana wannan shirmen,har da tsalle da rawa

Lateefa da Najwa suka kama yi mata dariya,Ummi tana murmushi ta ce"sannu auta,ke kam auta akwai shirme,ai sai ki yi masa adduar dawowa lafiya ko?sai nake ga kamar ta fi wannan shirmen da kike yi"tuni Mimi ta nutsu tana ta murmushi,farin ciki fal ranta babban yayanta masoyinta zai dawo 

Da idanu ilahirin mazauna parlourn suka bi Maleeka da kallo,wadda ta kusa isa matattakalar 茩arshe na sashenta,fuskarta babu alamun wani abu na damuwa ko farin ciki,a maimakon haka ma zaman gashin kanta da ya sauko zuwa kafa蓷arta take gyarawa tana takunta cike da isa da izza 

Babu wanda ya yi gigin yi mata magana ko tambayarta ba'asi,don tsarin Maleeka ba'a tambayarta ba'asi ko a tsara mata yadda zata yi,yadda take ji da kanta ba zai bata damar sauraren wani da sunan son jin ba'asi ko neman chanjin rayuwa ba, kazalika babu mai ce mata don me ballantana bari 

Da daddare suna zaune dukkansu a dinning area suna cin abincin dare,sai surutu Mimi take yi cikin farin ciki tana sanar da Abby zuwan babban yaya

Murmushi Abby ya yi cikin takaici ya ce"ya ga dama kenan,to Allah ya kawo shi lafiya,amma wannan karon zan 蓷auki tsatstsauran mataki akan shi, because for sure na gaji da halinshi,this time zan nuna masa ni na haife shi ba shi ya haife ni ba, wannan karon sai ya gaya min wanene mahaifinshi tsakanin ni da wannan 蓷an iskan yaron"

Tuni fara'ar fuskar Ummi ta 蓳ace,ta ce"kai!wai menene matsalar yayansu ne?har yanzu yana tare da wannan yaron?muna gini yana rushewa?amma Abby ya kamata ka rin茩a bincike before ka yanke hukunci,kar ka je ka yi masa rashin adalci,na san baya jin magana,amma kuma I'm wondering idan laifin wancan yaron ne"

"Believe me, laifin shi ne cigaba da mu'amala da wancan yaron,amma na san ba laifinshi bane abubuwan da yake yi, I will talk to him in sha Allah,don Allah ka rage kyararshi don bashi da wani uba da ya wuce kai "Abby bai sake magana ba ballantana ya kalli Mimi da ke ta 蓳ata rai jin ana aibataata sweet yayanta 

Babu wanda ya kula da tashin Maleeka ta nufi sama tana danna waya,sai Najwa da ta bi ta da kallo,kafin cikin sanyin jiki ta girgiza kai,ta kalli Abby ta ce

"Abby I can't get what Maleeka is doing anytime ana batun big bruh,sai kawai mu ga ta tashi ta nufi sama,is she okay?"

"Don't mind her!"ita ce amsar da Abby ya bata ba tare da ya damu ba,sai ma abincinshi da ya cigaba da ci suna 蓷an ta蓳a hira da Ummi 




DODAN BARRACK, IKOYI, LAGOS STATE, NIGERIA 

A wula茩ance take kallon magungunan da Fareeda ta kawo mata,kafin ta ta蓳e baki tana 蓷aga su 蓷aya bayan 蓷aya tana 茩are musu kallo,tana kuma sauraren bayanin da Fareeda da 茩awarta Ruky suke yi mata akan maganin 

"Wannan wanda muka kar蓳o a wajen bokanmu na kwara ne,wancan wajen wani muka je a Bayelsa,wancan dun茩ulen kuma na wajen bokanmu na Enugu ne, magungunan akwai kaifi,amma akwai shara蓷i"

Sai da Maimuna ta gama wula茩anci kafin ta ce"menene shara蓷in?"

Wannan karon Ruky ce ta amsa"ya ce wai idan ana amfani da maganin nan,na Bayelsa,wai ba'a wankan tsarki,dole za ki daina Sallah, sannan kuma za ki yanka zakaru guda biyar ta baya ki binne,babbar matsalar ma ita ce sai dai ki yi da kanki"

Ga mamakinsu sai suka ji ta ce"babu matsala,yanzu a samo min zakarun,zan yi duk yadda ake so"

Fareeda ta jinjina abin a ranta kafin ta ce"yawwa!sai batun sakaryar kishiyarki,kin san ta yarda da duk abinda na fa蓷a mata?jiya ma ta tura min da 20k wai na kai malami ya yi mata addu'a"ta 茩arashe tana dariya 

Maimuna ta yi wani miskilin murmushi ta ce"ku bi ta a haka,sai ta san ni ba sa'ar yin ta bace ba,sai ta gane kurenta"Fareeda tana murmushi ta ce"na san za ki iya ai, Allah ya ja da ran uwar 蓷akina"Maimuna bata yi magana ba sai wayarta da ta janyo,a 拼an mintuna wayar Fareeda ta yi 茩ara,ta yi saurin dubawa tana fara'a,amma fara'ar ta 蓷an ragu bayan ta ga abinda Maimuna ta tura mata,cikin murmushin ya茩e ta ce

"Na ga sa茩o uwar 蓷akina,godiya dubu"Maimuna ta gyara zaman 蓷ankwalin kanta tana fa蓷in "yawwa!"

Fareeda ta kalli Ruky da ta 蓷auke kai tana danna wayarta,ta dake ta sake kallon Maimuna ta ce"uwar 蓷akina za ki yi min ciko ko?"

Wani kallon banza Maimuna ta yi mata tana fa蓷in "cikon me?kin ta蓳a ganin an bi ni bashi?"

Fareeda ta yi ya茩e tana girgiza kai,ta ce"a'a,kawai dai na ga 50k kika yi min al茩awari ne, shiyasa na tuna miki,na san baya sa蓳a al茩awari "ta 茩arashe tana 拼ar dariya 

Maimuna ta kalle ta ta watsar,ta ce"to ki cika da dubu ashirin da kika kar蓳a"Fareeda kamar ta kurma ihu don takaici,don tuni ta yi budget da ku蓷in,wani malolo ya tsaya mata a ma茩oshi,da 茩yar ta dake tana ya茩e ta ce

"To uwar 蓷akina godiya nake,yanzu dai bari mu tafi, saboda gobe asubanci zan yi zuwa Kaduna "Maimuna ta ta蓳e baki tana kallonta she茩e茩e ta ce"hala wajen wani kwarton za'a je ko?"

Fareeda ta yi dariyar dole ta ce"uwar 蓷akina zama waje 蓷aya tsautsayi inji kifi,dole mu motsa"ta mike tsaye tana fa蓷in"yanzu dai zamu 蓷auki hanya,sai mun yi waya"Ruky ma ta mi茩e tsaye, Maimuna ta kalle su ta 蓷auke kai tana fa蓷in"to a sauka lafiya"babu wadda ta sake magana suka fito daga cikin gidan

A bakin gate Ruky ta kalli Fareeda ta ranta yake a matu茩ar 蓳ace,ta ce"Madam a nan fa zamu rabu,amma Banga alamun za ki bani ha茩茩ina ba,me kike nufi ne?"

Rai a 蓳ace Fareeda ta kalle ta tana fa蓷in "cewa na yi ba zan ba ki bane?don Allah bana son hayyata"ta ja tsaki kafin ta cigaba da mita

"Kina ganin wula茩ancin da wannan tsinanniyar matar ta yi min amma kina batun ku蓷i saboda ba ki da tausayi"

Ruky ta gyara tsayuwa tana fa蓷in "ke dai saka min ha茩茩ina,sai mu yi magana daga baya"babu musu Fareeda ta ciro wayarta,cikin 蓳acin rai tayi wa Ruky transfer na 10k,bayan Ruky ta ga alert ta 蓷ago kai a wula茩ance tana 茩arewa Fareeda da ta 蓷auke kanta kallo,tana yatsina fuska ta ce

"Hajiya ban wani gane 10k ba,ta mece ce?"

Fareeda ta 蓷an daidaita fuskarta tana yin 茩asa da murya,cikin kwantar da murya ta ce"ki yi ha茩uri da wannan,yanzu dai Kaduna zan tafi gobe in Allah ya kai mu,kin ga bani da wasu isassun ku蓷i,wannan matsiyaciyar ta yaudare ni kan batun ku蓷in nan,ba don haka ba da komai normal,kin san na tambaye ta ku蓷in da zan damfari kishiyarta na wanene ta ce nawa ne,ashe wai abinda za tayi kenan, shegiya fasi茩a "

茦iris ya rage Ruky ta fashe da dariya amma ta danne,ta ce"gaskiya dai bata kyauta ba,amma yanzu ta sha ki a banza kenan?babu wani mataki da za ki 蓷auka?"

Wani kallo Fareeda ta yiwa Ruky ta ce"ashe kin manta wacece Fareeda, wallahi bata isa ta ci banza ba,jira nake sai ta gama yi min komai,ta share min hanya a gidan major,ta fitar min da kishiyar tata,ni kuma zan shiga gidan itama na fitar da ita,na nuna mata na fi ta iya bariki "Ruky ta yi 拼ar dariya tana yiwa Fareeda alamar jinjina da hannu, Fareeda tana murmushi ta tari taxi ta shiga tana 蓷agawa Ruky hannu, ita ma Ruky 蓷aga mata nata hannun ta yi har ta 茩ule

Tana 茩ulewa Ruky ta yi murmushi tana fa蓷in"duk ku gama haukanku,amma za ki sha mamaki tabbas, lokacin da kika fitar da Maimuna kina shirin shiga ki mi茩e Kafa na yi gefe da ke"daga nan ta tari taxi don zuwa hotel 蓷in da customer 蓷inta ke jiranta 




MIAMI BEACH, FLORIDA,USA

Kyakkyawan matashi ne sosai,wankan tarwa蓷a, mai mur蓷a蓷蓷en jiki,daga shi sai shotneaker da ba茩in glasses,waya ce a kare a kunnenshi,yana magana 茩asa 茩asa,da alamu bashi da son hayaniya 

"Why sweetheart?is there any problem bayan wannan?na gaya miki ba zan samu damar dawowa ba sai nan da ten days because akwai ayyukan da nake son na gama ne, but trust me sweetheart Ina gamawa zan dawo"ya 蓷an yi shiru alamun saurare

茒an murmushi ya 蓷an yi,cikin nutsuwar tashi ya ce"yeah I'm aware,kema kin san ina sane,and I know what I'm doing,so just relax, everything is moving smoothly "



#Nusy_bee
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol