Free chapter · Read without an account
Chapter 6
by Amanarcool · AKWAI SILA
💦 AKWAI SILA 💦
BY AMANARCOOL
YOTA ID/021
PAGE 11-12
Gudu yake yi da motar kamar zai tashi sama a haka ya ƙarasa gida yana jin zafin zuciyarsa na raguwa, duk da ba iya haka ya so yi masa ba, ko salla babu ya shiga falon gidansu, Mama na zaune taga Jiniyo ya shigo kamar wanda aka tunkoɗo, bai yi mata magana ba ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya zauna akan kujera, yana jin me ya sa ma ya gudu bai tsaya ya karya masa ƙafa ba? Tsaki ya yi yana jin tsanar mahaukacin mai tsanani a zuciyarsa.
Joriyya na zaune a kan gadonta, tana jin zuciyarta kamar an ɗora mata wani abu mai nauyi, a duk lokacin da ta rufe idanunta sai ta hango yadda mahaukacin ya faɗi, da lokacin da ya miƙa mata hannu, da ajiyar zuciyar da ya sauke. A hankali ta ce "Ya zan tafi? Ya zan bar shi haka? Ya zan tafi ba tare da na san ko zai ci abinci ba?". Kuka ne ya kuma ƙwace mata, kwanciya ta yi ta ci gaba da kukan.
Tunda Jiniyo ya bar gurin, yake zaune riƙe da hannunsa da ya fara kumbura, wasu ƙananun jijiyoyi sun fito, fatar hannun ta yi ja sosai. Ya kalli hannun kamar ba nasa ba, ya tsaya yana rawar sanyi da raɗaɗin da ya ke yanka masa tun daga yatsunsa har zuwa kafaɗarsa.
Ƙoƙarin tashi yake amma gwiwoyinsa sun kasa ɗaukar nauyinsa, sake buɗe idonsa ya yi kamar wanda ya ga wani abun tsoro. A hankali yake motsa hannun yana ƙoƙarin danne raɗaɗin da yake ji, wata ƙara ce ta suɓuce masa. Ya kalli ƙofar kangon, yana jiran ko zai ga wadda kullum ke zuwar masa da abinci ko murmushi. Sai dai ya ga wayam babu komai sai iskar da ke shigowa tana shigar masa hancinsa tare da tunatar da shi cewa yau shi kaɗai yake cikin Duniyar da bata da suna. Karensa na tsaye sai zagaye shi yake yi yana fitar da harshe.
Momy na falo ta ji shirun Joriyya ya yi yawa tunda ta shiga ɗaki ba ta fito ba, tashi ta yi ta shiga ɗakin, kwance ta tarar da ita numfashinta na fita sama-sama, da sauri ta ƙarasa inda take "Auta lafiya? Ina fatan dai ba jikin ba ne?". Cikin fizgar numfashi ta ce "Momy ƙirjina, zuciyata, zan mut..." Ba ta ƙarasa ba jikinta ya fara girgiza idanunta suka birkice nan take jini ya fara zuba ta kunnenta da hancinta, fashewa da kuka Momy ta yi, ta fara jijjigata "Auta Auta ciwon ne ya tashi? Don Allah kar ki mutu Auta, kin ga abin da muke yi miki gudu ko? Shi ya sa ba ma son kina shiga damuwa". Momy ta rikice sosai ganin wannan karon hadda jini ke fita a jikin ƴar ta ta. Wani irin yunƙuri Joriyya ta yi, ta ja numfashi mai haɗe da gurnani daga haka ta yi ɗif. Ihu Momy ta yi ta sauka daga kan gadon ta yi waje da sauri, ɗakinta ta je ta ɗauki wayarta cikin ruɗani ta fara kiran Dady, sai dai wayar ba ta shiga, nan ta ƙara shiga ruɗa ni ta koma ɗakin Joriyya da sauri, tana shiga ɗakin, turus ta yi ta ƙame a bakin ƙofa tana kallon abin mamaki da al'ajabi. Joriyya ta gani zaune kamar babu abin da ya faru da ita, ta yi shiru tana kallon gefe.
Cikin sarƙewar murya ta ce "Auta"
Ɗago da kai ta yi ta kalli Momy ba ta ce ƙala ba "Auta babu abin da ke damunki ne?" Momy ta yi maganar tana zama kusa da Joriyyar.
"Momy"
"Na'am Auta"
"Ka da ku kai ni gurin Anty Na'ima ba na so, idan kuka kai ni can mutuwa zanyi".
"To Auta ki kwantar da hankalinki in sha Allah ba za ki je ba, amma da sharaɗi ɗaya, sai in za ki daina shiga harkar wancan mahaukacin?". Shiru ta yi ba ta amsa ba, daga ƙarshe ta yi kwanciyarta, ganin haka ya sa Momy tashi ta bar ɗakin don ta san ba kulata za ta kuma yi ba.
Wasa-wasa mahaukacin nan ya kasa iya tashi. Hannunsa ya yi kumburi sosai har ya fara sauya launi. Ya matse yatsunsa, yana jin wani irin raɗaɗi mai zafi, ya cusa hannun a ƙirjinsa yana neman sauƙin ciwon da ba zai samu ba. Ya jingina da bango yana fitar da numfashi mai zafi kamar mai ciwon daji.
A hankali ya fara furta wasu kalaman da shikaɗai ya san me yake faɗa, ya lumshe idanuwa yana jin zuciyarsa na yi masa nauyi fiye da kowane lokaci, hanjin cikinsa sai ƙugi suke yi alamar babu komai a cikin nasa. Sake buɗe ido ya yi ya kalli ƙofar kangon ya sake rufe idonsa, yana son tashi ya je bolar da yake zama amma babu hali. A haka ya koma kada kai ya kwanta cikin mawuyacin hali.
Yau lamarin Joriyya ya ƙara tsorata Momy, ya ba ta mamaki matuƙa, ta fara gasgata cewar akwai abin da basu gane ba akan Autar ta ta, yarinyar da idan ciwon nan ya tasar mata da ƙyar yake lafawa, sai gashi yau ya kwanta cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ya zo da wani sabon salo. Ko da Dady ya dawo ta gaya masa abin da ya faru shima ya tsorata matuƙa. Cikin dare suka je ɗakin Joriyya a kwance suka same ta tana kuka, jikinta ya yi sanyi, idonta a kumbure. Momy ta zauna a gefen gadon ta dafa kanta ta ce "Autata ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, ai na ce miki ba za ki je ko ina ba kina nan tare da mu, dama munyi hakan ne don nema miki mafita amma tunda baki so Shikenan, sai dai idan baki daina wannan damuwar ba, da shiga harkar mutumen can, dole ne ki bar ƙasar nan".
Joriyya ta gyaɗa mata kai, hawaye na zuba a idonta kamar ruwa, ta ce "Momy shi fa? Wane hali zai kasance a ciki? Wa zai kula da shi? Shi baya da kowa? Babu mai sonsa ne?".
Momy ta runtse ido ta ce
"Allah zai kula da shi. Kin yi abin da duk wata zuciya mai tausayi za ta yi. Amma yanzu ki kwantar da hankalinki. In sha Allah komai zai tafi daidai, zamu sa a riƙa kula da shi a bashi abinci ba tare da kin je gurinsa ba". Shiru ta yi ba ta kuma magana ba, ta zubawa Dady ido tana kallonsa.
"Dady"
"Na'am Shalele"
"Mu je yanzu mu kai masa abinci yunwa yake ji". Dim! Ƙirjin Dady ya yi, ya runtse kafin ya ce "Shalele kwanta ki yi bacci da safe sai mu je". Daga haka ya buɗe ƙofa ya bar ɗakin.
Momy tasa hannu tana rufe bakinta jin kuka na ƙoƙarin ƙwace mata, ta miƙe a hankali ta koma bakin ƙofa, tsayawa ta yi cak, ta juya ta kalli Joriyya "Allah ya tsareki Autata" ta furta cikin rauni.
Ɗakin Dady ta wuce da sallama cikin murya mai raunu ta tsaya a bakin ƙofa
Amsawa ya yi ya ce "Shigo"
Shiga ta yi yana zaune a gefen gado hannunsa riƙe da kansa, tun da ya dawo daga ofis baya cikin nutsuwarsa, abubuwa da yawa na damunsa, ga matsalar Joriyya, ga wani abu mai girma da yake ɓoye a cikin ransa wanda baya fatan fitowarsa.
Momy ta sauke ajiyar zuciya.
"Alhaji Joriyya ba ta cikin hayyacinta fa, wannan lamarin ya dame ta sosai".
Dady ya lumshe ido, ya ɗauki lokaci kafin ya buɗe su. "Na sani Shafa, amma dole ne mu yi wannan tafiyar matuƙar naga abin yana neman fin ƙarfinmu, wane irin al'amari ne haka? Lokaci ɗaya yarinya ta rikice akan mutumin da kowa ke gudu".
"Alhaji kamar akwai abin da ke damunka bayan wannan?"
"Ina ma akwai, bari mu gama da wannan matsalar tukuna, shi ne abin da ya fi muhimmanci a yanzu".Ta yi shiru tana kallonsa, yanayin sa ya nuna cewar akwai wani abu mai girma da yake tsoro fiye da komai. A haka shiru ya shiga tsakanin su, haka suka kwanta ko wanne zuciyarsa a cunkushe.
Washegari kafin kowa ya fito Joriyya ta fita harabar gidan cikin sauri, idanunta a kumbura, ta kusanci get ɗin gidan security biyu suka taso da hanzari.
"Baby Joriyya ina zuwa haka?"
"Fita zanyi" ta bashi amsa
"Ba za ki fita ba, ki yi haƙuri umarni ne daga oga".
Ta tsaya gabansu tana rawar sanyi da kuka "Ku matsa ku matsa na wuce!" ta ɗaga musu muryarta cikin tsiwa da hargagi "Ba za ku takura mini ba, zan je duk inda nake so, ku matsa mini!" Mamaki ne ya cika su, ƙaramar yarinya da ita amma muryarta ta cika da hargowa da tsanani kamar wata babba.
"Haba Shalele don Allah ki koma ciki…"
"Ku ƙyale ni" ta katse su tana fashewa da kuka, ta fara ture su da ƙaramin jikinta, ta hau ihun da ya karaɗe ko'ina, "Kada ku hana ni, don Allah ku bar ni na gan shi, ba daɗewa zan yi ba yanzu zan dawo".
Hankalin security ya tashi sosai. Wani daga ciki ya nufi cikin gidan a bakin ƙofa ya ce karo da Dady ya fito da sauri jin ihun Joriyya, ƙarasawa ya yi yana faɗin
"Me ke faruwa ne?"
Ganin ya yi Joriyya ta yi tsaye idonta cike da ƙwalla tana neman ɗaukewar numfashi "Shalele" ya kira ta cikin murya mai rauni "Me yasa ki ka fito haka? Ina zaki je ne?".
Da sauri ta ƙarasa gareshi, ta kama rigarsa tana kuka kamar za ta suma.
"Dady don Allah zan je in duba shi, zai mutu da yunwa idan ban je ba!".
Dady ya furzar da iska mai zafi, ya lumshe ido "Shalele na ce ba za ki je gurin wancan mutumin ba, ki manta da shi!"
"In manta da shi? Dady ya zan manta da shi?" Ta rushe da kuka tana girgiza kai. "Dady shi baya da kowa, ni ce kawai nake zuwa gurinsa ina taimaka masa" Momy da ta fito a guje ta tsaya zuciyarta na yi mata zafi, tana jin kalmomin ƴarta na ƙona mata rai, hana mata fita Dady ya yi ya jata zuwa ciki ya zaunar da ita, ɗakinsa cikin damuwa da rashin sanin abin yi.
Yana zaune a kangon nan kamar jiya.
Ƙura ta lulluɓe shi, hannunsa ya ƙara kumbura har fatar ta fara tsagewa a gefe, karensa na zagaye da shi yana yi masa kuka da wata irin murya da ba a saba ji ba.Ya ɗaga hannun yana kallonsa kamar an canza masa shi. Hawaye ya gangaro gefen idonsa, ya jingina kansa a kan dutse yana jin zafin ciwon na ratsa shi. Da ƙyar ya iya miƙewa tsaye ya fito ya zauna a cikin bolar da ya saba zama, mutane na wucewa suna kallonsa, sun ga halin da yake ciki amma ba wanda ya tsaya, ba wanda ya yi tunanin me ya samu wannan mahaukacin a hannu? Ba wanda ya damu da ciwon sa. Wasu yara ma jefa masa tsakuwa suka fara yi suna ihu da dariya, wani ƙaton dutse da aka jefo masa ne a hannun ya sa shi sakin ƙara yana ɓoye hannun nasa a baya. Karensa ne ya zo da sauri bakinsa riƙe da leda baƙa, ya ajiye a gaban mahaukacin, da ƙyar ya sa hannunsa mai lafiya ya buɗa ledar wani abinci ne da ya fara lalacewa, cikin rawar jiki ya fara tura wa cikinsa abinci, yana gama ci ya leda a gefensa da kingin ruwa a ciki ya ɗauka ya shanye, nan take cikinsa ya ƙulle ya fara murƙusu a gurin.
Joriyya na zaune a falo ta yi shiru kamar wadda ta amince da duka umarnin da aka gindaya mata, sai dai shirun na rigima ne, sulalewa ta yi kamar iska ta fita daga falon ta ɓoye cikin fulawowi, sai da ta fake idon security, mai gadi ya shiga banɗaki tabi ta ƙaramar ƙofa ta bar gidan. Ta fara gudu saman titi kamar za ta tashi sama. Jikinta sai rawa yake yi, duk nisan tafiyar nan Joriya ba ta ganta ba cikin ƙanƙanin lokaci kamar walƙiya ta isa bakin bolar, jin motsi ya sa shi ɗagowa. Joriyya ya gani tsaye tana kuka tana magana "Na zo, na zo, gani na zo, me ya sa meka a hannu?" ta durƙusa gabansa ta kama hannunsa, ta ji da zafi kamar wuta, ta yi ajiyar zuciya mai tsami, cikin kuka ta ce "Yi haƙuri yi haƙuri, me ya sa meka a hannu? Garin yaya ka ji ciwo haka?" ta faɗa hawaye na bin fuskarta.
Ya saki wani irin kuka na manya, ba irin na hauka ba, kuka ne mai cike da ƙunci yaron da ya rasa komai, kafin ta yi magana ta ga motocin gidansu sun tsaya a bakin titin. Dady ne shi da security ɗinsa, Dady ya fito cikin hargowa, ya nufi gurin zuciyarsa cike da jin haushi da baƙin ciki.
"Shalele!"
Miƙewa ta yi ta fara kuka "Dady ka bar ni da shi don Allah ka bar ni ka duba hannunsa!"
Mahaukacin ya ja baya yana kuka yana ɗaga hannunsa da ya kumbura sosai. Dady ya kama Joriyya ya cireta da ƙarfi daga gurin "Shalele ki tsaya, ta ya ya ki ka fito daga cikin gidan nan?" Ta riƙe rigarsa tana kuka tana girgiza kai. "Dady kada ka tafi da ni don Allah kada ku raba ni da shi!"
Amanarcool ✍️
***